Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Tabarmar Kashi Book 2 Page 26

Book 02 Page 26


.. Anyways, nazo wajen masoyina ne kuma mijina” daga haka ta juya ta nufi office din kai tsaye. Zallar mamaki ya hana saima cewa komai,sai kallon zallar mamakin da ta bita dashi. A cikinsu wace ainihin matar tasa?,ko mata biyu ya aure lokaci guda basu sani ba?.
A nutse take takawa cikin living room din dake tsare da sofas masu tsada da aka sake zubawa,sofas din da kake da ikon lanqwasa su duk shape din da kaso,daga kujera me qaramin table a hannunsa zuwa matsakaicin gado tare da pillows. Jakar hannunta ta ajiye saman sofa din a hankali. Kalaman ameesha ne suka fara dawo mata fes cikin qwaqwalwarta. Siririn tsaki taja gana jin zafi a zuciyarta da matar ta kasance mahaifiya ga fadeela, juma’ar da zatayi kyau tun daga laraba ake ganeta, kuma ita din ba qanqanuwar yarinya bace, dukkan alamu sun nuna zaiyi wahala a samu karamci kamun kai da sanin ya kamata daga gurin matar, kalaman bakinta kawai sun gama gayawa säahar wacace ita din. Sake jan tsaki tayi tana nufar gofar da
aka rubuta Toilet daga samanta da wani irin rubutu
ruwan azurfa. Tura bandakin tayi ta shiga tana binsa da
kallo komai kar kamar ka zuba abinci a ciki kaci. Fitsari
tayi ta daura alwala sannan ta fito ta tayar da salla. Ko’
bayan ta idar zamanta tayi saman lallausar abun sallar
dake ajjiye har guda uku a wajen. Tana azkar kadan
kadan tana tunanin abinda zata ci.

Fuskar haseena dake shigowa da kwanukan abinci
ne ta dawo mata,cikin shigarta dake nuna halittar
sirantakar da Allah yayi mata tako ina wanda wala’alla ita
bata ganin hakan. Gefe daya kuma fuskar saima ta
fado, duk yadda takeson kore tunanin komai daga ranta
amma sai ta gaza aiwatar da hakan?. Wai meye tattare da shi da sauran maza basu dashi suke wannan parade
din a kansa,kamar qarar wayarta shine amsar
tambayarta sai kira ya shigo mata,wanda shine ya zama
silar yankewar tunaninta ta dauki wayar tana dubawa.
Bestie afifa ce, saita saki murmushi sannan kuma ta tura
baki gaba,tabbas sai ta fanshe shakulaton bangaron da
afifan tayi da ita ta daga wayar ta koma saman abun sallar.

“bestie bana yi, bestie kinci amanata” sãahar ta fada
tana harara wayar tamkar dai afifa na wajen

“Don Allah bestie kiyi haquri, wallahi ban taba
experiencing irin wannan yanayin ba a rayuwata” afifa ta

fada da muryarta data gama komawa me sanyi. Ta fahimci maganar afifan, don haka ta sanya hannuita toshe bakinta saboda dariyar da take cinta

“Na miki uzuri bestie, Allah ya bada lafiya”

“Wai Allah bestie, naga rayuwa,sai yau na samu space da hayatee ya taho company” baki sãahar ta tabe, ita kwata kwata wadan nan sabgogin basa burgeta ko kusa ko alama,kafin tace wani abu afifa tace

“Amma bestie lafiyanki qalau kuwa? ,kina cikin hankalinki kike shirin sakarwa mata mijinki?,wannan na ciki wannan ta shigo?” Maganar tadan baiwa sãahar mamaki

“Kamar yaaya? dama na aureshi ne don na kula sa sabgoginsa ko kuma na kula da diyarsa?” Ta jefawa afifa tambayar. Goshinta ta dafe tana lumshe ido, sãahar dai bata canza ba?,a kwanakin d sukayi tare ta dauka komai ya fara canzawa dangane da junansu a zukatansu

“Saahaaarrrr……. please ya kamata ki koma cikin hankalinki,hayatee yazo office dinsa ya taras da hakan, saboda yana kishinsa yana kishinki kuma yana kishina yasa ya gayamin….i was so shocked…
…nasan

ba haka bestie na take ba, aure ai ba abun wasa bane

bestie, ko banza igiya ce me girma a tsakaninku…
…moha
ba normal irin gama garin maza bane,wannan abun da kike na shakulaton bangaro ba komai zai haifar miki ba sai d’a maras ido, ki tsaya kawai kiyi abinda ya kamata ki manta da komai” baki sãahar ta tabe

“Yaushe kika koma me bada shawari?, kinje kin kurbi giyar aure ko?,hmmm sannu farin shiga,to na gode da shawara,amma ni ba ruwana da abinda ya shafi rayuwarsa,wannan shi ya zabarwa kansa,ya auri mata dubu ma ya kula million a yau duka shi yaso, zan wuce gida yanzu lokacin tashi ya kusa,idan na isa zamuyi waya,inason mu tattauna akan wani abu daya fara tunani a kai”

“Allah yasa maji ta aura masa uku tsala tsala larabawan
Algeria”

“And so what!” Ta fada da lafazin da ya sanya fifa shegewa da dariya

“Allah sarki bestie,Allah ya baki lafiya,sannu” mamaki ya kamata,me afifa ke fada?,kawai sai ta sauke wayar ta kashe,taga alama so take kawai ta tuburata.

A nutse ta maida wayar jakarta,ta fidda wata siririyar roba doguwa da bata rabo da ita ta murza turare,ta warware lafayarta ta gyara zamanta sosana ilkinta,ta kuma gyara daurinta,sai gashi ta fito d’ass da ita,wani sirrintaccen kyan amarci da batasan dashi ba yana bayyana saman fuskarta. Jakarta ta dauka ta rataya a hannunta ta fito daga resting room din.

Wayam mazaunin saima yake, ba kowa sai takardu da na’ura a gurin. Kanta ta sanya kai tsaye office din nashi, ta murda qofar ta turata.

Idanunsa na zube fes akan qofar yana qarasa jin abinda ameesha ta fadiwa sãahar a waya ta a dazun data kira kafin ta ajjiye masa wayar ta fice. Can qasan maqoshi ya amsa sallamar,ta tako zuwa ciki ba tare data dubi fuskarsa ba kamar tasan ita din yake kallo,hakanan bata kalli ko sashen da meenal ke zaune ba,wadda ta ajjiye basket din saman table dinsa ta kuma zauna saman kujeru biyun dake gaban table din nasa,idanunta a kansa tana qoqarin shanye maganar daya gana gaya mata,tana jin zata iya jure koma meye, tunda ta sanshi,ta kuma yi imanin dama bawai zata sameshi ta sauqi haka ba. Dan binta yayi da kallo,sai itama meenal din ta rakashi da kallon, ta kuma janye idonta daga kan sãahar bayan ta tabbatar sãahar din idanunsa suke kalla. Haka kawai wani irin bacin rai ya cika masa maqoshi,yana datse kiran ameesha ita kuma haseena ta sanyo kai da tarkacen kayan abincinta. Can cikin ransa yana jin zafin me yasa zata daga wayar ameesha har ta bashi?,me kuma yasa ta barwa meenal damar shigo masa office da kayan abinci?.

Ido meenal ta qangance, tun daga zuciyarta har ruhinta tana jin matsanancin kishin kyan da säahar ke dashi,yau ne tayi mata kallon fes ta gefen idanu,duk yadda takeji da gayu da kyau sai takejin a yanzun ta muzanta idan aka kwatantata da säahar din. Duk da shigarta shigace ta gargajiya a wajen meenal,don ita bata taba kwatanta sanya suttura full irin hakan ba,to amma ayau sai taga shigar tayi mata mugun kwarjini, abinda bai taba faruwa da ita ba.

“Ina da abunyi so zan wuce gida, inason tsaiwa na dauki fadeela” ta gaya masa tana sake matse agogon hannunta ba tare da ta kalli fuskarsa ba. Zare idanunsa yayi daga kanta a hankali yana dai daita zamansa.

“Tana da abunyi ma take ce masa?,waye bashi da abiny kenan” Bata jira amsarsa ba ta tako a hankali ta qaraso gaban table din nasa amma ta left side dinsa, akwai file da take da bugatar dauka kuma suna ta wajen,abinda ya qara kusanci kenan a tsakaninsu sosai,sassanyan gamshinta na haurawa hancinsa yadda ya kamata,tsaiwar da tayin kuma a wajen ta baiwa haseena damar ganinta sosai fiye da dazun. Zara zaran yatsunta da suka sha lallae tabi da kallo a sace, kamar yadda shima nasa idanun suka sauka akai,launin kalar tana bala’in jan hankalinsa. Hannu yasa da sauri ya dafe wani file da take shirin cirowa,wanann ya baiwa hannuwansu damar haduwa guri guda,take haseena taju zuciyarta
tamkar zata fashe,ta dauke idanunta daga kai tana
migewa.

“Ki koma dasu gida,bana da enough time da zan iya cin
abinci har haka a office” ya bata amsa yana maida file
din tare sa cirowa sãahar din na gasansa daya tabbatar
shi take nema. Tana karba ta soma takawa zata bar
gurin,lokacin meenal ke maida kwanukanta cikin
kwandon tana jin wani bacin rai ranta kamar zai fashe.
Bata taba zaton zai watsa mata gasa a ido ba yace ta
koma da abincin ba,ta hada komai a gaggauce ta nufi
hanyar fita tana qoqarin danne fushinta da hawayen da
ya cika mata idanu,saboda batason matarsa taga
karayarta. Meenal na fita tabi sahunta,saidai kafin takai
ga fita ya amsa mata zancan dauko fadeela daga
school,har yanzu ransa na susa,tare da jin bacin rai da
mamakin yadda ameesha ta samu number wayar office
dinsa bayan yayi blocking nata a dukka wani layi da
yasan zata iya samunsa.

“Fadeela nada driver,so ba buqatar kije daukota,ki tsaya
kiyi aikinki” waiwayowa tayi ta kalleshi sosai,sai lokacin
taga yadda yanayin fuskarsa ya canza da kyau

“Ba dole bane ace driver kullum shike da alhakin
jigilarta,daga yau shima na soke wannan saidai idan da wani dalili me qwari” barin aikin da yakeyi yayi, ya dauke hannunsa yana soke yatsunsa guri guda, idanunsa a kanta. Cikin ransa yana jin kamar ba wannan aikin ya kamata ta bawa muhimmanci haka ba,yayin da wani sashe na zuciyarsa kuma yake son daga martaba da kimar abinda tayin tare da son gamsar dashi

“Zauna muyi magana” yayi furucin cikin rashin son wasa a fuskarsa. Kai tadan dauke, kamar ba zata zauna ba kuma ta dosana kadan a saman kujerar

“Kome zakiyi kiyi qoqarin kare martabar hajiya,saboda ita din kamar maji take a gurinmu” kai ta girgiza

“Ba maji bace,ba kuma zata taba zama maji ba,am sorry to say ban yarda da kowa ba akan fadeela,saboda nayi experiencing wani abu da yaso tarwatsa rayuwata shigen abinda fadeela ke shirin fuskanta daga gurin mutumin da yafi kowa kusanci dani” ta qarashe maganar muryarta tana rawa. Har cikin jikinsa yaji wani abu ya tsarga masa,ta miqe tana qoqarin boye qwallarta,batason zubda hawaye a gabansa

“¡ have to go” kamar bazai amsa mata ba sai taga ya mige,ya tura kujerarsa baya ya fito a hankali daga gurin ya zauna saman resting chair yana maida takalminsa,ya daura agogonsa sannan ya dauki wayoyinsa da system dinsa sannan yace

“Let’s go” sosai tayi mamaki, saboda bata taba kawowa zaice suje din ba. Danne mamakinta tayi tayi gaba yana biye da ita a baya.

A hankali take takawa da irin takunta nan qafafunta akan tsari,wanda sai kayi tsammanin tana sane take shirya takun nata daya bayan daya. A hankali a hankali sai taji kamar gafafunta suna neman hardewa wannan va sanya ta sake rage saurinta sannu a sannu har ya cimmata suka dai daita kafada. Kusan a tare suka daga idanu suka kalli juna,sai kuma kowa ya dauke kansa yaba basarwa, itakam harda qarin matsawa gefe.

Ihun murna kawai fadeela tadinga saki sanda taga sãahar harda abby dinta wai sun biyo daukarta,abinda bata taba samu ba kenan. Yana zaune vana kallonsu ta cikin glass din yana jin wani farinciki na ratsashi saboda walwalar da ya gani saman fuskar fadeelan,wai me ya hanashi yin hakan shi tsahon shekarun da suka shude? ya barwa driver komai da komai na hidimar daukota da kaita?. Ido ya lumshe yana jin wani farinciki.

Duk yadda yaso ga dannewa amma ya kasa sai da ya furta

“Thank you”sanda take maida murfin motar tana rufewa.
Cike da mamaki ta kalleshi sai kuma ta basar

“It’s my pleasure” ta amsa masa tana dire school bag din fadeela da tuni ta haye jilkin Abby dinta tana cewa yau itama ‘van class dinsu sunga abby dinta da mammanta sunzo daukarta kamar yadda ake daukar kowa.

Sanda suka isa gida ko sassanta bata shiga ba suka wuce sashensu, nadeeya daketa zuba idanun dawowarsu ta tarbesu suka dunguma,shi daya ya wuce ciki, sai daya shiga yaga dining wayam sannan ya tuna Jacob fa bava nan, garamin tsaki yaja ya wuce bedroom dinsa. Duk abubuwan daya aiwatar tun daga wankansa canza kaya da fresh milk da yasha ba hakan bai mantar dashi tunanin dake magale a kwanyarsa ba,meye yasa tace bata yarda da kowa ba? me yasa wani irin rashin jituwa yake gudana tsakaninta da hajiya qaraman cikin dan lokaci kadan?,da wannan tunanin ya gama hutunsa cikin sashen,har aka kirayi magariba yayi alwala suka fita sallah shi da jibril. Bayan ya dawo sallar sashen hajiya qarama ya shiga,don bayan ya fito jibril ya shaida masa sau uku tana aikowa kiransa, ba’a gaya masa bane sabida sunsan dai dai lokacin hutawa yakeyi.

Yaji dadi da bai samu meenal ba a sassan,ya samu guri ya zauna yana gaidata

“Ka kusa fin garfina ai toufeeq” hajiya ta fada tana tara hawaye cikin idonta. Mamaki abun ya bashi qwarai

“Me kuma ya sake faruwa,i thought kun gama magana
da Dr ko akan komai?”
[22/09, 10:23 am] +234 703 451 7171: *HUGUMA*

* TABARMAR KASHI *

Post a Comment for "Tabarmar Kashi Book 2 Page 26"