Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Tabarmar Kashi Book 2 Page 32

*_TABARMAR KASHI *

Book 02 Page 32


Da gaske ba zata kalleshi ba,duk iya yadda yake tunanin zai shawo kanta taqi kallonsa,a dole ya ajjiyeta ya miqe don zuwa toilet,ya wuce bandakin yana waiwayenta kafin ya dauke kai ya shige bakinsa dauke da addu’ar shiga bandakin.

Koda ya gama wankan ya jima yana kwararawa kansa ruwa,zuciya qwaqwalwa da qirjinsa sunyi wani fresh,dukka wani nauyi rudani da kuma dabaibayewar tunani kamar an sanya almakashi an daddatsesu.

Koda ya fito still idanunsa suna kanta,ta cure jikinta sosai cikin duvet din kamar bata bugatar shaqar iskar dakin,qarasawa yayi gareta a tausashe ya danja duvet din,da sauri ta kamashi ta cukuikuye da kyau jikinta har kyarma yakeyi

“Ba abinda zan sakeyi miki,gate up na taimaka miki kiyi wanka” tabbas da zata iya da harara zata dago ta galla masa,amma kuma tasan ba zata iya hakan ba,don babu abinda ya jawo mata shan wannan baqar izayar sai bakinta da idanun nata data kasa kiyayarsa kamar yadda yace

“Kiyi haquri ki taso na taimaka miki,ba zaki iya tashi ba”

“Bazan iya tashi ba sabida kasan ka baje kolin muguntarka a kaina ko?” Ta fada yau din muryar tsiwar ta koma muryar shagwaba qwarai da gaske. Siririn murmushi ya kufce masa yana tuna abinda ya tarar tattare da ita

“Kaina bisa wuyana,i apologize fa,zan kuma ci gaba da apologizing din koda yawun bakina zai qare” kafin tace komai sukaii sautin bugu sosai,knocking akeyi da qarfi qarfi,kafin daga bisani muryar hajiya qarama ta wanzu a gurin

“Toufeeq, toufeeq” karon farko da yaji wani abu a kanta,wato duk wata kima tata da girmamawa da yakeji a duk sanda ta kirashi a yanzun sai yakejin babu ko daya

“Toufeeq ka bude, ko jikin ne?” Ta sake fada tana qaguwa da tsaiwarta a gurin saboda hankalinta a mugun tashe yake,kukan da meenal keyi mata da alwashin da takeci tana jin tsoron faruwar wani abun

“Am feeling better,na sha magani”

“Ban yarda ba, ina falo inason magana da ku”

“Okay” ya amsa mata a gajarce.

Idanunsa ya maida ga sãahar

“Gate up please” ya fadi a tausashe yana bata hannunsa,sam bata buqatar wani taimakonsa,don haka ta ture duvet din da wani dan guntun qarfinta tana miqewa. Saidai tuni ta maida fuskarta ta kife tsakiyar pillow jikinta na rawa

“What’s happened?” Ya tambayeta a tsorace yana takowa kusa da gadon

“Stay away please,cover your body” sai a sannan ya tuna cewa qaramin pant ne a jikinsa wanda iya gaba da bayansa kawai ya rufe masa, murmushi ya saki wanda yayi masifar yiwa cute face dinsa kyau, murmushin da ya jima bai sauka akan fuskarsa ba akan wata diya mace,bai musa ba yaja qaramin towel ya daura a qugunsa

“Okay,zaki iya tashi yanzu” ya sake fada yana sake miqa mata hannun. Koda ta tashi din gocewa hannun nasa tayi,ta dauke kai kamar bataga taimakon da yakeson bata din ba,ta soma sauka a hankali daga saman lallausan gadon da ya kafawa rayuwarta tarihin da bata tunanin wanzuwarsa ba tsakaninta da MT JARMA din ba.

Sai data huta a bakin gadon sannan ta soma takawa zuwa bandakin. Bai fasa ba ya bita da kallo yadda take takawa cikin sanyi da nutsuwa har ta shige ta tura qofar.

Duk da yana cikin wani razani da fargaba amma murmushi bai kasa boyuwa daga kan fuskarsa
ba, hannuwansa ya sanya duka biyun ya kama gashin kansa da kyau ya riqe yana murmushin, kafin daga bisani kuma ya saki kan nasa,ya koma bakin gado ya zauna yana daukar wayarsa tare da laluben number dr raheema,don a yadda yaga tana takawa yasan tabbas zata bugaci wani taimako.

Tana cikin ruwan zafin amma hawaye takeyi,tabbas jarma ya mamayeta,ko daya batasan wannan qaddarar zata tarar ba a dakin, da ba ciwo ba,ko suma yayi babu abinda zai shigo da ita. Cikin zuciyarta takejin wani qunci da takura,wannan rayuwar bata shiryawa yinta ba kwata kwata,amma tabbas daga wannan ya gama,ba zata iya ci gaba da zama da shi ba,tunda har yaci amanarta ya karya alqawari da yarjejeniyarsu.

Cikin wata irin nutsuwa ya shirya kansa a cikin wasu pajamas masu dogon wando da dogon hannu,gefe guda a ransa yana juya al’amarin hajiya qarama,zuciyarsa ta riga da tayi rawa cikin al’ amarinta,yana kuma bugatar nutsar da hankalinsa da zurafafa bincike cikin sirri da takatsantsan, muddin tana da hannu akan ciwon fadeela da gin yankewar al’amarinta baya tunanin zai iya yafe mata. Sai daya waiwaya ya sake kallan dakin kafin ya fita,har lokacin bata fito a bandakin ba,ya ja qofar ya rufe yana fatan tayi zamanta kada tace zata gudu a dakin.

Cikin wata sassanyar nutsuwa dake saukar masa yake takawa,har ya isa falon. A tsaye ya zamu hajiya qarama,meenal na zaune saman sofa da idanunta da suka canza launi. Kallo daya tayi masa taji wani mahaukacin kishinsa kamar zai hallakata,sai ta kasa dauke ido daga kansa,yayin da shi kuma ya tattara hankalinsa kan hajiya qarama idanunsa shima a kanta sanda yake zama saman kujera

“Me ya sameka haka? yanzu baka da lafiya sai ka zauna a daki baka shaidawa kowa ba?,banason wannan sakacin naka toufeeq” idonsa yadan lumshe yana samun daidaito cikin nutsuwarsa bayan ya kira sunan Allah

“Da sauqi alhamdulillah”

“Mun godewa Allah” ta sake fada cikin nuna kulawa

“Ina ita nanny din?” Ta tambayeshi tana dubansa. Kansa ya sake dagawa ya aje mata wani kallo,sai tadanyi relax kadan cikin mamakin yanayin kallon nasa

“Wa fa?”

“Nannyn fadeela,säahar”

“Bata jin dadi,but she’s my wife, not a nanny please” ya fada da wani irin sanyi, sanyin da ya kunna wuta a zukatansu ita da meenal, qarin mamaki kuma ya zauna sosai a zuciyar hajiyan. Lallai da hausawa ke fadin BABA MA DA BABANSA sai yau ta sake gasgata hakan,waye haka ya tsayawa yarinyar?, ko da yake bai kamata tayi mamaki ba,domin qila tarihi ne yakeson maimaita kansa,yadda mahaifiyarta ta hana mata samun mahaifinta wato dr mamman girema,haka takeso ta hanawa meenal samun toufeeq,sanann ta zame dukka wani martaba izza tata da fada aji da take da ita,wanda sam ba zata taba bari hakan ya faru ba koda zata rasa komai nata,toufeeq shine Target dinta,shine plan dinta na shekara da shekaru.

“Oh,yayi…..saboda ita kenan ka kori ‘yaruwarka data damu da lafiyarka? ta kasa sukuni da haqurin jiranka ka fito tayi tattaki ta sameka har inda kake?” Hannunsa yayi folding a qirjinsa,yayi wani relaxing, kai tsaye idanunsa cikin na hajiyan

“Hajiya,ya kamata ki nusasheta bambamci tsakanin jiya da yau,ya kamata ta fahimci ma’anar alfarma ta dan adam da yadda ake keta ta haramunne a shari’ ance,ya dace ta dinga banbance hagunta da damanta,sannan ya cancanci tasan yadda ake iya kama zuciyar namiji da wasu nagarta da kyan zuciya nutsuwa hankali da sanin ya kamata” ya furta yana dunqule hannunsa guri daya da kyau. Saroro hajiyan tayi cike da tsantsar mamaki,yau tana ganin wasu baqin halaye da dabi’u daga toufeeq din. Kamin kowa a cikinsu ya sake cewa wani abu takunta cikin taushi da qamshinta ya mamaye gurin.

Sahar ce sanye da wata baqar doguwar riga me sulbi wadda keda wani irin ado da wasu zararruka masu daukan hankali, fuskarta tayi fayau,ta sake wani irin kyau da fresh,sannan kuma ta ciko lokaci daya, sassanyan kyan nan nata kamar an sake qara mata shi,fatarta da idanunta sun qara wani haske da girma. A hankali take takawa kamar wadda ke tausayin gasa. Kai tsaye ya bita da kallo yana fahimtar tafiyarta ta canza sosai, kuma yasan hakan baya rasa nasaba da abinda ya faru a tsakaninsu.

Idanunsa ya lumshe tsigar jikinsa na zubawa lokacin daya tuna abinda ya farun mintunan da suka shude,yana ji a ransa inama lokacin ya sake dawowa,yayita kuma tabbata a haka ba tare sa ya wuce ba. Ido suka hada dashi,wani qasaitaccen murmushi da yayi matuqar qara masa kyau kwarjini da cikar kamala ya sakar mata yana lullumshe mata idanunsa. Sai take ga kamar dariyar mugunta yake mata,wannan yasa ta langabar da kanta gefe tana jifansa da harara, abinda ya zama kamar wani wasan soyayya ko cusa haushi a zuciyar hajiya da kuma haseena.

“Ina zuwa madam?” Ya fada cikin matuqar girmamawa,kanta tadan juya kadan,ta cije tana qoqarin tauna maganar da zata gaya masa,saboda cikin jikinta takejin akwai idanu a kanta

“Zanje duba fadeela”

“Uhmmmmm” taji muryar hajiya qarama na fadi, idanunta kuma a kanta.

Kai tsaye ya miqa mata hannunsa,ta gane me yake
da bugata,kuma a lokacin taji ba zata iya wofantar da
abinda yayin ba,duk da zuciyarta cike take da
haushinsa, amma wani abun kana yinsa ne ko ka barshi saboda wasu idanu masu guda da illa.

Cike da mamaki yaga ta garaso a hankali ta dora zara
zaran yatsunta cikin nasa,wani irin abu me dadi ya saukahar tsakiyar zuciyarsa,ya maida hannun ya rufe ruf ya kuma jawota a tausashe ya zaunar da ita a kusa dashi cinyoyinsu suna gogar na juna

“Ba yanzu ba,bakijin dadi,Dr raheema na hanya” ya fada yana sake game hannuwansu guri guda. Cikin nacin kallo da son tantancewa hajiy qarama ke garewa säahar kallo, gabanta na wani irin faduwa,tana hango canji muraran daga fuskarta,lokaci daya ta qara wani haske da sheqi

“Innalillahi,na shigesu” ta furta lokacin da zucivarta ta
ayasa mata

“Kodai ciki ne?”

“‘Ina fatan haka” taji muryar toufeeq yana sake matse
hannunsa cikin nata. Sai a lokacin ta fahimci a fili tayi maganar kuma a bayyane. Cikin sauri da son gyara takunta ta saki murmushi

“Ameen Allah,lallai da duk duniya na kasance mutum ta farko wadda zatafi kowa farinciki,fatana ko yaushe ahalina su qara yawa,don haka nake qoqarin ganin samun dai daito tsakaninka da ‘yar uwarka” yadda hannuwansu ke cikin na juna yaci gaba da taba zuciyar meenal din,bata da zarrar cewa toufeeq din komai,saboda ayau din kwarjinin dake kan fuskarsa kamar ya zarta na kullum,sai gani sukayi kawai ta miqe ta fice da sassarfa tana toshe bakinta saboda sabon kukan da yake shirin qwace mata.

Hadiye wani abu me tauri hajiya qaraman tayi cikin murmushin yaqe

“Allah ya raba lafiya” banbarakwai sahar taji, mamaki ya sake kamata lokacin da taji yana amsawa da ameen, sai ta faki idanun hajiyan ta zame hannunta daga nashi, saboda yadda yake yamutsa hannun nasa cikin nata tamkar yana amfani da damarsa ne.

Zaman bai dauki lokaci ba Dr raheema ta qaraso,cikin girmamawa ta gaida hajiya qarama,ta amsa mata cikin izzar nan tata amma faran faran

“Ki dubamin ita da kyau don Allah” tace da Dr raheema.

Murmushi ta saki kawai

“To hajiya,in sha Allah” ta fadi tana maida hankalinta a kansu

“Ku qarasa ciki,ko da clinic zakuyi amfani?” Kai Dr raheema ta girgiza

“Inajin basai munje ba, indai ba worsening matsalar tayi ba”.

Tana zaune daga gefan gadon ta rasa ta yadda zata yiwa Dr raheema bayani,wannan wanne irin abun kunya ne shikam,yana neman bata kunya da tona mata asiri.

Sai kace wata virgin zai dauko mata likita?.
Dai dai lokacin ya buda qofar dakin ya shigo yana sauke boyayyar ajiyar zuciya sanda idanunsa suka sauka a kanta,tsaida shi hajiya qarama tayi tana masa kukan tare da fadin yan wulagantata,ya canza totally mace na son rabasu,shi kam bai iya wannan jidalin ba, bugu da qari a yanzu ma shi bashi da wani guarantee a kanta,tana cikin suspect, bazai kuma taba nutsuwa ba har sai ya samu yaqini da tabbacin komai

“Sir batace komai ba” Dr raheema mai yawan fara’a haquri da sanin ya kamata ta fada. Hannuns a qirjinsa ya tako ciki

“First night ko first day dinta zance,shi tayi a dazun, so kamar yanayin tafiyarta nake gain ya canza,and jikinta akwai dumi sosai tun dazun, duk da taqi yarda da hakan” ya furta dukka bayanan idanunsa a kanta,yanajin kamar ya hadiyeta. Idanunta fal da qwalla ta dubeshi, tanason sake harararsa ne ko zata zamu relief din abinda yayi mata

“Nifa bazawara ce Drya za’a ce saboda na samu wani ciwo dalilin hakan?” Ta fada cikin dan zafin rai. Idonsa ya lumshe murmushin nan nasa dan kadan me taushi na subuce masa,can qasan ransa kuma yana jin babu dadi,don da alama kalmar BAZAWARA din ta tsaye mata a rai.

Cikin kulawa Dr raheema ta ajjiye kayan aikinta,ta dawo dab da ita ta zauna tana game hannunta cikin nata

“Ba abun mamaki bane yadda kowacce mace ta banbanta haka suma mazan suke da da banbanci kin gane?” Tayi mata bayanin a taqaice,jin tayi shuru sai ta dora

“Yadda muka banbanta a halittar jikinmu hama suma mazan suka banbanta,kowacce mace akwai yanayin halittar ta,jikin wata jikinta yafi na wata tsukewa,kamar yadda suma mazan halittarsu ta wani tafi ta wani,zai iya yiwuwa a auren mace na biyu ta fuskanci jin ciwuka da sauransu, saboda qila ta qara samun tightness,sannan shi kansa mijin nata data sake aura wala’alla yafi na farkon cikakken.

“Don Allah Dr” ta fada da sauri tana rufe idanunta.
Wannan karon sai da dariya ta qwacewa Dr raheema
“Kin fahimta kenan ba sai na garasa ba?” Kai ta gyada mata sau biyu da saurinta. Shima murmushi yayi mai sauti wannan karon, wanda ya tsaye ma säahar,taji kamar da biyu yayishi,sai ya juya yana nufar qofa don ya basu guri.

A nutse ta sake mata bayani yadda zata fahimta,hakan ya sanyata tunani me yawa

“What a difference?” Ta samu kanta kanta da fadin hakan,sai kuma taji haushin kanta ya kamata

“Difference din ganiya” ta sake fadi tara fada ita da zuciyarta har tana tsuke garamin bakinta.
“HUGUMA*

Post a Comment for "Tabarmar Kashi Book 2 Page 32"