Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Tabarmar Kashi Book 2 Page 37

_TABARMAR KASHI_*®

Book 02 Page 37


Yana jin qarar rufe gofar saima ya tako zuwa gaban saahar din, saman qafafunsa ya tsugunna vana dubanta da wannan zafin da har yanzu baibar saman fuskarsa da kuma zuciyarsa ba. Kauda idanunta tayi daga kansa tana jin wata shakkarsa tana shigarta,scene din da ya gabatar yanzu a nan ya sake tabbatar mata har yanzu TOUFEEQ JARMA shine dai,a gareta ne kawai ya sauya.

Yatsunsa ya sanya ya dawo da fuskarta saitin tata fuskar, sai ta sake kau da kai,ya sake maido fuskar tata ta sake kawarwa,a karo na uku ya sake juyo da ita a zafafe sannan yace

“Idan kika sake juyamin qeya sai na miki hukuncin da na fahimci shi kikafi jin toro,idan baki wasa ba saidai a kawo wheel chair a daukeki, kada ki manta ina da sofas masu taushi a resting room” izzarta ce ta motsa,ya akayi ta bari ya karanci ta tsorata da abinda yayi mata?. So take ta gaggaya masa magana, amma ta sani daga qarshe yamutsatan da batason yayi shi zai aikata mata

“Na kusa kawo qarshen komai” ta fada qasan ranta a fili kuma tana hade rai

“Wayonki da tsiwarki dukka yau na rainasu, saboda baki kishina saiki bar duk wata karya da godiya su dinga tunkarar mijinki gaba gadi ko ‘yar shakkarki basa ji saboda sunsan lusara ce MATAR TOUFEEQ?” Da gayya ya kira mata lusarar saboda ta motsa wani abu dake danqare a zuciyarta,yaci nasara kuwa,don take bacin rai ya bayyana

“Ko ba komai ya kamata su dinga jin shakkar tunkarata
haka kai tsaye saboda KE”

“‘Ina ruwana da abinda ya shafi rayuwarka?,rayuwarka
daban tawa daban,ka taba ganin anyi kishin abinda ba’a so?, ba’a kuma damu da shi ba?” Ta fada itama gaba gadi. Murmushi ya saki karon farko shima zuciyarsa a yau ta dandana dacin kalmar RASHIN SO da kuma QIYAYYA. Kai ya girgiza

“Tashi mu tafi gida” ya furta yans miqewa tare da ja baya ba tare saya sake bi ta kanta ba. Ranta a quntace itama ta tashi tana jin haushin maganar da ya gaya mata, bataso yabar zancan iya haka ba,sai gashi yayi kamar komai bai faru ba.

Baice mata ci kanki ba a mota har suka dauko fadeela suka wuce gida yana jinsu sunata sabgarsu,bai ce musu komai ba kuma bai hanasu ba. Yau din sun koma da wuri, yana zaune a motar yana kallonsu har suka qule a sassansu fadeelan, kai ya jinjina

“Zanyi maganinki” ya fadi qasa qasa, kafin ya kashe motar,ya barwa jibril key din a jiki ya fito yana cewa

“Kada kayi nisa,zamu sake fita kaman nan da one hour”

“Okay sir” ya fada cikin girmamawa.

Falon wayam,har yanzu Jacob bai dawo ba, hakanan har yanzu bashi da tsayayyen gurin cin abinci. Bai tsaya dogon nazari ba ya wuce bedroom dinsa,don yana matuqar bugatar ganin Dr jarma a yau din,don a gobe yace masa zaiyi tafiya,morning flight zaibi, dukbda dai har yanzu bai gaya masa inda zashi ba, kusan kuma basu saba hakan dashi ba, shima bai matsa da tambaya ba, kasancewarsa mutum ba me bun qwaqwafi ba yasan idan ya dace yaji tabbas zai gaya masa. Ya fara zare kayansa, idanunsa suna bisa gadon Duk lokacin da ya kalli gadon babu abinda yake tuna masa sai wancan moment din, wani abu guda daya da ya tsaye masa a rai, ya kuma kasa mantawa, abinda duk sanda ya tuna sai yaji ilahirin tsigar jikinsa ta tashi, ko me vakevi kuwa.

Wani qaramin murmushi ya subuce masa lokacin da ya tuna da sauran abubuwan da suka faru,gaba daya bata da wayo sam ta irin wannan bangarorin, autar ce da gaske

“Akwai tsiwa,sai tsoro” ya furta gasa gasa, ya dan kada kai yana jin buqatuwar kasancewa da ita na mamayarsa.

Abinda ya farun ya zama kamar ta lasa masa zuma me azabar zaqi ne a bakinsa, kwana biyu rak amma ji yake kamar ya shekara rabonsa da ita, laluben rigimar da zai jawo kawai yakeyi wadda zata bashi dama ya sake kutsawa zuwa wannan alfarmar tata da yake fatan ya dawwama har abada a cikinta.

A gurguje ya shirya bayan ya fito, cikin wani yadi me azabar kyau da daukar idanu sky blue,yana da taushi da kuma qarancin kauri, jikinsa sai fitar da qamshi yakeyi me dadi, saidai kuma cikinsa wayam yake yunwa yakeji amma ya bari idan sun fita ya laluba gidan abingi me kyau yayi takeaway.

Half cover me kyau ya zubawa gafansa ya dauki wayarsa dake tsuwwa yana duba me kiran. Sajjad ne,ya kara wayar a kunnensa yana ficewa. Har yayi gaba ya tuna yanason magana da nadeeya, don haka ya koma da baya ya shigal sashen.

A parlor ya samu nadeeyan tana kallo,gefenta bowl ne da aka yayyanka kankana ayaba da madara,sai abun sugar dake ajjiye ba’a kai ga zubawa ba.

“Ina zuwa” yace da sajjad yana sauke wavar idanunsa akan bowl din sanda take gaidashi

“Wannan fa?”

“Aunty N ce ta hada zata sha, fadeela ta tasheta kitchen wai tayi mata veggies couscous” a nutse ya koma ya zauna,ya dauki bowl din ya fara juyawa

“Kun zuba sugar ne?” Kai ta girgiza

“Bata saka ba” bismillah yayi ya fara sha, gardin madara dana fruit din dake ciki suka gauraye harshensa,sannu sannu sai gashi ya gama da shi gaba daya ya ajjiye bowl din tare da nufar kitchen din, gamshin da yajeji a ciki yana jan hankalinsa.

Tsaye take gaban gas ta bawa gofa baya,sanye take da wata farar gown cotton me hannun vest, iyakar gown din qaurinta,saidai ta fidda shape dinta qwarai,ko a inda yake tsaye yana hangenta,yana iya gain faffadan qugunta da ya zamu ado da tsayayyun mazaunai. Ido ya lumshe vanayin jikinsa ya fara canzawa, qwaqwalwarsa na tuna masa maganar was abokan sajjad

“Mace me qugu da hips duniya ce, ai tayi alaji” ya yarda da hakan dari bisa dari, a yanzun ya zama shaida akan hakan. Amma muddin maza suna iya banbance irin wadan nan halittun daga wajen mata bayan ba matansu bane na aure, to ya zame masa dole yayi dukkan me yiwuwa ya bata dukkan tsaro da kariya fiye da yada zai bawa duk wani abu nasa kariya, domin shi yasan me yaji a jikinsa,me kuma ya gani yake kan ganin. Qamshinsa kawai ta shaqa ta tabbatar yana gurin, amma saboda tana kokwanto sai tayi kaman tana gyara jelar gashinta dake fake tsakiyar kanta ta kalli gefanta.

Yana tsaye yana kallonsu, fadeela take zubawa abinci,sai ta maze kamar bata ganshi ba,ta kammala zubawa fadeelan ta miga mata,sai ta kwasa da gudu tana ficewa. Maida spoon din tayi cikin tukunyar tana niyyar rufewa. Caraf ya kama hannunta ya riqe, sai ya zagaya ta bayanta ya manne jikinsa ta bayanta yana sake riqe daya hannun nata,ya zamana dukka hannuwanta suna rige a hannunsa

“‘Na yarda marowaciya ce ke” ya furta cikin hade rai ya miga hannunta dake rige cikin nasa ya dauki plate, ya sarrafa daya hannun nata da nashi hannun ya zuba couse couse din,sannan ya sake mata hannu yana tallafe plate din.

Jikinta na rawa ta rufe tukunyar, tayi taku biyu zata bar kitchen din yasha gabanta yana kai lomar abincin bakinsa. Da ido ya tsareta yana ci gaba da cin abincin wani irin taste dadi yana ratsashi, duk yadda jacob yakai ga iya abinci,ya kuma sallama masa akan hakan a yau yaji wadda ta dameshi ta shanye.

Yadda baice mata komai ba haka itama bata ce masa ba yadda bata nema ya bata hanya ba shima bai bata din ba,a haka yaci gaba cin abincin yana kallonta,har nadeeya da taji shurun yayi yawa sãahar din bata fito ba, kuma tanason gaya mata ta fiddo wasu fruit din yaa moha ya shanye wancan,da ta leqo ta gansu a haka,sai tasa sawunta a likkafa cikin sand’a ta koma,kuma har ta koma din ba wanda yaji motsinta a cikinsu.

Lomomi kadan ya rage ya ajjiye plate din saman freezer wadda tafi kusa dasu

“Baiyi dadi ba” ya fada yana yarfar da hannunsa,ya juya ya dauki ruwa ya balle murfin yana sha yana karantar fuskarta. Tayi algawarin daina biye masa, don haka sai ta rabashi kawai ta fita a kitchen din.
Murmushi ya saki, yadda yaga ta iya jurewa batayi magana ba,duk da ba haka yaso ba, don bakinta yazo ya sake sha, don hakan ba garamin dadi yakeyi masa ba.

Bai ganta a falo ba,cikin dakewarsa wanda ba zakace shine ya gama neman rigima yanzu ba a Kitchen ba yace da nadeeya

“Daga yanzu zuwa ko ysuhe, duk lokacin da hajiya ta fita unguwa ko wani guri ki sanarmin, immediately, but ina bugatar sirri,kin gane?” Kai ta gyada sannan tayi masa a dawo lafiya,cikin ranta tana mamakin dalilinsa na bata wannan aikin.

Kamar zata kifa lokacin da take sauke masa ruwa da drinks sanda yake zaune a gaban Dr jarma. Tun bayan da yayi aure wanna shine ganinta dashi na biyu,saboda gaba daya ta daina zuwa gidansu. Ko bayan data fita bayan hannunta ta sanya tana share hawaye, ta gaji da zaman jiran nan, ta qagu alqawarin da mommynta tayi mata na cewa nan da wani dan lokaci zai kawo kansa wannan algawarin ya cika,haqiqa akwai mutane da yawa da sai ta dauki fansa a kansu,hajiya qarama data zama mutum ta farko wadda ta yaudareta game da lamarin toufeeg tana cikinsu,koma tace itace mutum ta farko.
Tun zamansa gaban Dr jarma ya fahimci kamar cikin farinciki Dr jarma din yake, bai taba komai cikin abinda aka kawo masa ba kamar ko yaushe ya gyara zama,kansa a qasa bakinsa cike da addu’ ar Allah ya dorashi kan Dr din

“Abba alfarma nazo nema” ya fada yana dan shafa sumarsa dake sheqi.

Zamansa ya gyara yana dubansa

“Wacece alfarma kenan Muhammadu?”

“Abba,don Allah inaso SAHR tayi zamanta a gida,duk aikin da kake tunanin zata tayani, i can do it gaba daya ni kadai,idanma akwai buqatarta, zan ajjiye mata komai a study room dina ta ding aikin daga gida” dan shuru Dr jarma yayi na wasu sakanni, daga yanayin maganar toufeeq kadai ya shanshano wani abu, can gasan ransa dariya tana son kamashi amma ya danneta,sai yadan bata rai kadan

“Yanzunma kanason ka koreta ne da baqin halinka yadda

ka saba ko kuwa?” Da sauri ya girgiza kai

“No, Allah abba ba haka bane”

“To yaya ne?” Yayi masa tambayar yana tsirashi da ido
tare da son qureshi,don yanason samun tabbacin abinda yake zargi. Sumar sa kawai yayita shafawa,ya kasa cewa Dr jarma komai, baisan ya zai furta masa ba,ta yaya zaiyi masa bayani? abban baisan akwai kunya tsakaninsu ba?

“Muhammadu, ka gayan gaskiya”

“Abba…. I don’t know how to explain, kawai dai…..
Banason yadda maza suke kallonta,nayi duk iya bakin
gogarina akan hakan ta daina faruwa, har hijabai na dinka mata, amma wallahi abba a banza,abun is annoying me”

Dariyar da Dr jarma yaketa boyewa ta kufce masa, yayi qas da kansa yana kallon yadda toufeeq din da magana doguwa ke masa wahala amma yadda ya karkace yanata rattabo masa bayani wanda simple question ne da a amsa daya ya gama da ita. Ta wani gefen sai zuciyarsa ta karye yana tuna shekarun baya rayuwa tsakaninsa da SHIFA MAJI,yayi gogarin dai daita fuskarsa ya daga kal yana kallon toufeeq sanda yake fadin

“Don Allah abba a barta, kada kace a’ah” kafadarsa ya dafa yana murmushi

“Daina rogona muhammadu,mutum da matarsa?, ko a
baya ma ai ni bance dole ba, ta fuskar alfarma nazo, kuma naga kayi accepting, ko a lokacin inda kace ba zatayi yi ba ba komai, matarka ce qarqashin dukkan mulkinka da ikonka take,sai abinda kace zatayi,tunda bakaso na janye ta zauna ta kulamin da muhammaduna” sai a lokacin kuma kunya ta saukar masa,yayi qasa da kansa yana qoqarin tuna da meye da meye ne ya gayawa dr jarma din.

“Na gaya maka zanyi tafiya ko? gobe zan wuce Algeria”

ya fadi yana duban toufeeq

“Algeria abba?”

“Eh, zanje na gyaro wata barna, fatana Allah yasa kada gyaran ya daukeni lokaci mai tsaho, don banajin ko da zanyi shekara zan iya dawowa ba tare da na samu yadda nakeso ba” maganar ta dan Sanya toufeeg a duhu,amma duk da haka yayi masa addu’a da fatan alkhairi sosai, suka fada hirarsu irin ta d’a da uba.
[28/09, 9:21 am] +234 903 576 5837: “HUGUMA*

 

Post a Comment for "Tabarmar Kashi Book 2 Page 37"