Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Tabarmar Kashi Book 2 Page 9

Book 02 Page 09


Muryar maji dake dauke da wani allausan sauti me cike da nutsuwa ce ta mamayi kunnenta. Wata nutsuwa ta saukar mata wadda ta sanyata amsa sallamar cikin tsari.

“Ina fatan binty bakiyi fushi da ni ba,inataso na kirayeki amma ban samu damar hakan ba‚nadeeya kamar rowar rak’am(number) dinki takeyi” murmushi säahar ta saki me cike da kunya,ai ita ya dace ace ta nema maji din,don rashin kyautawa tunda tabar gidan bata sake nemanta ba

“‘Masa’al khair” säahar ta gaidata

“Masa’an nur ibnaty kina lafiya ko?,ya iyayi ki?”

“Bikhair walhamdulillah”

“Ma sha Allah, ya kuma shire shiryen aure? muna hanya cikin satin nan in sha
Allah” nauyinta ta sake ji ya kamata,saita kasa magana

“Ina fatan za’a yi haquri da halin moha,ya taso me wani irin zafi da rashin son raininaso qwarai na saisaita wannan dabi ar tasa,saidai ban rayu dashi ba,ya sake zuwa kuma bayan ya girma Allah ya jarabceshi da wata irin jarabawa data sanya dabi’unsa suka sake zafafa,ina rogon alfarma ayi haquri da shi,a kuma yi qogari a saita min shi, kyawawan dabi’u da na san dasu na haifeshi su dawo gangar jikinsa suyi tsiro, zuciyarsa ta zama irin ta kowa”

“In sha Allah” kawai ta fada,don batasan fadin kowacce kalma da zata nuna ta dauki alaqawarin,saidai daga qasan zuciyarta tana mamaki,dama shi din bai rayu da maji ba”?

“Inason diyata tafi kowacce amarya kyau a duniya,don wannan shine karon farko da za’a aurar da moha a gaban idanuna,akwai me gyaran amare da zata iso nan da jibi daga nan gasar tare da ‘yar uwata,ina fatan diyata zata bada hadin kai?” Sosai abun ya yiwa sãahar girma,suma da gaske suka dauki bikin?,sun dauka auren gaske ne kenan?,ba yadda ta iya ta amsa a sanyaye da

“To,mafi mishkila,jazakillah bi khair”

“Nice da godiya da shigowa rayuwarmu da kika yarda zakiyi” maji ta amsa mata cikin qauna da kulawa,har cikin jininta takejin qauna da soyayyar sãaharita din ma’abociyar sallar dare ce,a duk sanda ta roqawa rayuwar toufeeq da nadeeya abokan rayuwa na gari sai taii sãahar ta sake kwantawa qwarai a ranta,tana ta qoqarin ganin yadda zata qulia al amarin tana daga can,sai gashi cikin hikimar
Allah komai yazo cikin sauki darajar istikhara din data dinga yi tana neman zabin Allah.

Ganin kamar saahar din tana kunyarta ya sanya tayi mata sallama,tare da gaya mata tayi serving number dinta a wayarta,koda tana da bugatar wani abu kada taji komai,kai tsaye ta kirata.

Gudun mantuwa da girman majin ya sanya tana ajjiye wayar afifa ta dauki wayar tata ta fara duba tarin miscall din data samu,wasu na cousins dinta ne wasu na yayunta,wasu numbers dinma batasan nasu waye ba.

Tana tsaka da saving kira ya shigo wayar tata,kamar ba zata daga ba,saboda batasan number din ba sai kuma ta dauka din ta kara a kunnenta. Baquwar murya ce a kunnenta,ta amsa sallamar da akayi mata

“Sunana elyas,ina daya daga cikin ma’aikatan
MT JARMA,na kira ne bisa umarninsa,yace na shaida miki,idan akwai wasu kudade da kike bugata na hidindimu ki fada sai a tura miki” wani irin baci ranta yayi qwarai ta mige ta zauna sosai,ma’aikacinsa ne,tasan kuma irin respect din dake tsakaninsu dashi, uwa uba ma shi din dan aike ne gaba daya bashi da laifi sai ta rasa abinda zatace masa,ta lumshe ido takaici yana cin zuciyarta

“Hello madam,kina jina?”

“Ina jinka,elyas ko?” Kai ya gyada

“Yes madam”

“Bari na baka shawara,koda gaba kada ka sake yarda ka shiga irin wadannan abubuwan,saboda bai dace ba,kudi kuma kace masa har yanzun dai bashi da kudin da zai bawa sãahar….” Cikin kunnuwansa ta
qarasa fadin kalaman,yadda yaga elyas yayi shuru yana qifta idanu yasan akwai matsala,ya fahimci tana da tsiwa da rashin barin kota kwana,zata iya fadin wata maganar ma da zata iya zubda masa girmansa a idanun yaransa.

“Da wa kike?” Sautin murvarsa dake da wani irin zurfi da haiba suka sauka mata a kunne a lokacin da bata zata ba,dalilin da yasa batace komai ba kenan har ya sake maimaita tambayarsa. Cikin dakiyarta tare da son fanshe bacin ran da afifa da sauran family ke gasa mata saboda yadda suketa shirin biki tace

“Ni ba wulagantacciya bace, kuma bana neman komai a gurin kowa,ka rige arziqinka na rige mutuncina” wani irin zafi maganarta tayi mata,yaji babu dadi sosai a ransa,saidai takaicinsa ragagge ne tunda umarnin maji ya cika

“Hey!,watch your words.…karki dauka
kiranki yana da alaqa da damuwa da akayi dake..
bazanvi tolerating nonsense ba,don bazan biva sadakinki sannan na dauki wadan nan tsiwar da rashin kunyar ba” daga haka ya kashe wayar yana furzar da iska me zafi daga bakinsa. Lallai idan batayi wasa ba sai ya mata horo me tsanani, ya cire duk wannan jin isar tata da rashin kunya,abinda takeyi masa kaf tarihin rayuwarsa ba wanda ya taba gwada masa irin hakan sai ita. Wani mugun tsaki yaja ya jefar da wayar,maji ce sila,inda ta fahimci maganarsa tun farko da bata sanya yasa ay! kiranta ba. Ya miqe tsaye yana boye hannunsa a aljihun trouser dinsa,yana jin zuciyarsa na sake zafafa,dai dai lokacin da sajjad ya shigo dauke da wasu manya manyan kwalaye shi da jibril. Har suka gama ajjiye kwalayen jibril ya juya ya fita baice musu ta tafas ba. Zama sajjad din yayi ya fara bude kwalayen,wasu irin shegu suit ne da yadiddikan vicuna,qiviut fabric guanaco da baby cashmere wadanda duka aka viwa wani lafiyayyen kwantaccen dinki. Kallo daya zaka yiwa kwalayen zuwa sutturun ciki kasan maqudan kudade kamfanin da yayi kwangilar aikin ya lasa daga hannunsu

“Here’s our wedding attire,ya ka gansu?” KO duban inda yake toufeeq baiyi ba,don dama yana cike da sajjad din. Tafiya yayi ta sati daya,amma kafin ya dawo sajjad din ya sanya an canza komai na sassansa,an canza tsarin komai ma,ya zuba masa dukka wasu kaya da suke favorite dinsa a design da kuma color,sannan ya fidda sashen da aka zuba jeren säahar din. Yayi masifa kamar zai ari baki har sai da girjinsa ya dinga zafi kasancewar bame doguwar magana ba,yana ganin kaf girman gidan da sassan da yake dasu amma ya rasa inda zaiyi mata matsugunni sai cikin sashensa? haka ya haqura ya gaji,don sajjad ya gaya masa yayi din waye zai aureta da za’a ajjiyeta a wani muhalli na daban,sanann muddin yaci gaba to zai sanarwa da Dr girema auren meye zaiyi,da kuma abubuwan da yaketa yi din,wanda sam basu dace ba,don meye bazai sassauta zafin kansa ba?. Haka ya gama qure sajjad da zazzafan kallon nan nasa ya debe fararen idanunsa yabar masa wajen,yasan indai yaci gaba da tsayawa sajjad bazai gaji da gasa masa magana a fakaice ba,shi kuma bazai iya doguwar magana ba.

Yanzun ma key din motarsa ya dauka
ya fice daga gidan shi daya,ransa a bace,shi dinma bai duka duka wannan hidimar zaa yita yiba me hana mutun sakewa,hatta da fadeela yanzun ganinta sai lokaci lokaci,duk sun yamutsa gidan da shirye shiryensu,yau basu nan gobe basu can,cire wancan canza wannan siyo wannan ajjiye wancan,duk Dr girema ya daure musu qarqashin ko nawa sukeso zai dauka ya basu. Ko su jibril da sukayi yunqurin biyoshi hanasu yayi,bai tsaya ko ina ba sai bristol palace,ya kama royal suit da ya saba ya wuce ciki bayan ya kashe dukka wayoyinsa yana fatan samun relief ya kuma daidaita kansa,shi kansa yasan yanata misbehaving ne,yana kuma batawa sajjad wanda dama shi kadai yake iyawa dashi,yasan abinda ya faru dashi a baya yake hunting mind dinsa,yanaso yayi cooling temper dinsa kafin ya dawo cikin gidan.

*******Kayanta taketa hadawa guri
daya,amma fiye da rabin hankalinta ya dilmiya a zuzzurfan tunani. Idan lissafinta yayi dai dai,ranar da zata isa Nigeria ya kama saura kwana biyu rak a fara bikin,kamar yadda kwanan wata ya nuna mata jikin dallelen invitation din me rubutun ruwan gold a jiki, wanda har yanzu hasken katin da tsarinsa basu bacewa idanunta ba,don sam baiyi kama da katin biki ba. Jagwab ta koma ta zauna saman kujera,ba qwarin zuciya ba har gwarin gangar jikinta tana nema ta rasa, komai gani takeyi yana fara zuwar mata a cakude,ko a mafarki bata taba tunanin akwai wani abu da zaizo ya rusa tsarinta ba dai dai da qiftawar idanu, bata taba kawowa wata mace zata shiga rayuwar toufeeq ba baya ga hassenarta wadda aka fi sani da MEENAL YA’AQOUB AJI,saugin abun har yanxu ta tabbatar meenal din bata san da zancan ba,don ko jiya sunyi waya kuma lafiya lau suka gama sukayi sallama.

Sautin qarar wayarta ya tabbatar
mata da shigowar kira wayarta,ko da ta duba taga sunan baby na kamar yadda tayi saving number meenal haseena sai da gabanta ya fadi,ta zauna sosai tana daga wayar da hanzari,don jikinta ya bata ta faru ta qare.

Yadda ta zata din kuwa haka ne,kukan meenal haseena kawai ya tabbatar mata da zarginta,cikin hargagi da daga murya da muryarta da tayi sirantaka da yawa har take bada wani irin amo da ba kowa yakewa dadi ba

“Momy? kina ina akaci amanata?, kina raye kuwa momy?”

“Ina raye baby meenal,ki kwantar da hankalinki,ba wani abu bane babba”

“Ta yaya zakice ba babban abu bane,bayan next week zaiyi aure? zai auri wata bani ba,bayan kinyimin algawarin bazai sake auren kowacce diva mace ba bayan ni?,yanzu duk zaman da nayi shekara da shekaru ina jiransa ya tashi a banza?,duk wani buri na da naci a kansa ya zama mafarki?”

“Haseena!”

“Momy!!! ba abinda zakicemin,na dauka ina da uwar dana wuce nayi kuka na zubda hawaye na? ta isa ta sharemin kowanne kuka nawa ashe kuskure nayi!”

“Meenal ki saurareni mana,kin manta wacece fauziyya?,kin manta waye toufeeq a wajena?,ubansa ma ya yake a gurina barshi?” Maganar ce ta sanya meenal din yin shuru,saidai har yanxu bata fasa kukan da takeyi ba

“Wallahi momy idan har ban auri yaa toufeeq ba mutuwa zanyi”

“Indai kinga baki aureshin ba saidai idan bana raye,ke ko bana raye saikin aureshi,shine mijinki” hajiya qarama ta maimaita da confidence,tana ajjiye wannan alwashin har tsakiyar zuciyarta

“Wani ma yayi rawa bare dan makadi?,bani da qwai a duniyar nan fa sai ke,ke kadai na mallaka kuma duk duniya babu wanda nakeso kwatankwacin yadda nake sonki,idan ban sama miki farinciki da jin dadin rayuwa madawwami ba me nayi kenan?,koda tsiya koda arzigi saikin mallaki muradin ranki,ki rubuta wannan ki ajjiye,alqawari ne dauka”

“Ki tabbatar kin cikashi momy,saboda komai zai iya faruwa,inason na auri yaa toufeeq a watannin da muka riga muka tsara tun farko,bazan iya jurewa rashinsa na tsahon wani lokaci ba,bazan iya jurewa ganinsa da wata mace ba bayan ni”

“Ki kwantar da hankalinki ki kammala exams dinki,sati biyu fa kacal ya rage,a satin bikin ma zan miki booking ticket,ko Dr jarma banason ya sani,saidai kawai suga isowarki”

“Thank you momy”

“Naji,amma haka zamu rabu kina wannan kukan don kawai ki hanani sukuni?”

“Na daina”

“Kin tabbatar?”

“Kinsan idan na fadi abu bana canzawa ai”

“‘Yayi kyau,ki huta da kyau” . Wani qaimi taji yana shigarta tare da karsashin son ganin ta gudanar da komai,don haka ta sake migewa tana qarasa hada kayanta,tare da duba jirgin garfe nawa zata bi.

********Tun daga saukarta farkon layin zuwa shigowarta cikin gidan hankalinta ya soma tashi,ta sake tabbatarwa eh lallai aure MT JARMA zaiyi,irin auren kuma dake nuna cikin wadata da tarin arzigi za’a yishi,ba irin aurensa na baya ba. Abinda ta lura dashi cikin nutsuwa da zurfafa dubanta akan kowa,kamar kowa fuskarsa dauke take da annuri da farincikin auren,komai na gidan an canzashi an sake masa fasali da tsari, hatta da uniform na ma’aikatan gidan kuwa. A ranar kasa zaune tayi ta kuma kasa tsaye,hatta da fadeela da nadeeya bata samu ganinsu ba a ranar,don ba’a basu zama ba,yaa moha zai dawo musu da masoyiyarsu,a wannan karon da a sunan nanny ba,a sunan MATARSA ta sunnah.

Tanason ta fita don fara aiwatar da wasu abubuwa,amma baqin da aka fara yi a gidan da abokan kasuwancinta da suketa zuwa ganin kaya sun hanata motsawa,komai kawai yinsa takeyi ba cikin nutsuwarta ba,tana da bugatar zuwa ta sabunta tsonon aikinta,don dama an jima ana gargadinta akan hakan, bata fuskanci da gaske bane sai da taga kwabarta tana shirin yin ruwa. Komai a quntace take yinsa cikin yage da tsabar duniyanci wajen iya boye damuwa da tashin hankali ta kuma bi sahun ‘yan murna da Allah ya sanya alkhairi.

*_KALLON KALLO *
??????
[14/09, 7:42 pm] Mimah Yusuf: *HUGUMA*

 

Post a Comment for "Tabarmar Kashi Book 2 Page 9"