Breaking News

Uncle Datti 11-12


1️⃣1️⃣—1️⃣2️⃣

B’angaren Aina tunda ta bar d’akin Nana, d’akin Datti ta nufa tana kunkuni ciki-ciki tana cewa” wai ni nana zata raina wa hankali? Ko ina yarinyar ta kwaso makircin banza da bakin hali, wallahi Nana halin ta ya sha bam-bam da na zuri’ar mu”, har ta shigo cikin d’akin bata k’arasa fad’ace fad’acen ta ba”.
Datti na daga uwar d’aka yaji muryar ta ya fito da sauri, lafiya wife kike ta masifa ke kad’ai wa ya tab’a min ke”.
Kwafa taja mai k’arfi cike da tarin takaicin me yasa bata kama Nanar ta nad’a mata d’ankaren dukan da zata dawo cikin hayyacin ta ba”.
Tsintar kanta tayi da tsantsar jin kunyar k’azafin da Nana tayi mishi, anya zata iya fad’a mishi kuwa? Kai ko me zai faru gara ya faru, yaga ya san irin zaman da zaiyi da Nana idan da hali ma ya d’an ja baya da ita tunda ta kasa fahimtar halayen Datti.
Jin shirun yayi yawa  ya jawo ta jikin shi ya tausaya murya yace” kin yi shiru wife baki amsa min tambaya ta ba”. Sai yanzu ta samu damar amsa mishi wallahi ba wai shiru nayi maka ba kawai dai rasa abunda zan fad’a nayi, maganar ce da nauyi da kunya bayan haka idan kaji dole sai ranka ya b’aci  hakan hmmmm hmmmm, sai ta hau kame-kame”.
D’aurin d’ankwalin da ke kanta ya zame a hankali suman ta suka baje a samar kafad’an ta, hannu ya kai yana wasa da su yace” ina sauraranki, just tell me”.
“Ka san me?
A’a, tare da girgiza mata kai.
Diffffffff tayi shiru hakika ta so ta b’oye mishi amma zuciyar ta ya gaza hakura, wai ace duk irin son da kake nuna wa Nana ta rasa irin kasafin da zata yi maka sai na sharri? Cewa tayi wai jikin ta kake so!
What!!!!!! Yayi saurin ture ta daga jikin shi tare da nanata k’almar jikin ta nake so! Ta yaya zan nemi yarinyar da ta taso a gabana, wacce d’igan hawayen ta na bugan zuciya ta……….. Wallahi Nana bata yi min hallaci ba, so take ta shafa min bakar fentin da ba zan iya gogewa ba.”
Ganin yanda hankalin shi ya tashi sosai tace” kwantar da hankalin ka my one ai fenti kam sai dai ta shafa ma kanta amma ba kai ba, ni shaida ce kuma iyayen mu shaida ne baza ka tab’a aikata mummunar aiki ba, mun fi kowa sanin irin lalurar da take damunka shekara da shekaru wanda har abada babu maganin ta, muryar ta ne ya soma rawa da kyar ta iya saitawa tace” tunda nake da kai baka tab’a ko da romancing d’ina bane ballantana aje ga maganar sex.
Wani irin sassanyar ajiyar zuciya ya sake a heart d’in shi cewa yake” I’m sorry wife bani da wani zab’in da ya wuce na cin amanar ki, i tried harder naga na cire sha’awar Nana but every day and night tamk’ar dad’a hura min sha’awar ta ake”.
Daren ranar Aina sai jujjuya maganar Nana take yi a ranta da kyar ta samu ta runtsa, Datti kuwa ko a jikin shi domin ya san babu wani k’ofa da ya bari wanda zai tona asirin shi.
Washe gari da safe har d’aki Nana tabi Aina ta tarar da ita tana gyaran bed ta gaishe ta ciki-ciki ta amsa. A cikin dare d’aya duk idanuwan ta sun jeme sun kod’e.
Matsawa tayi gefe kad’an ta tallafe fuskanta da tafin hannun ta tana kollon yanda Aina ke gyaran tana so tayi mata magana amma sannin kanta ne ba sauraran ta zata yi ba sai ta wuce kawai ta fita za ta  d’aki ta tarar da Datti a parlour yana waya, har ta  wuce  yace” Ke Nana zo nan”. Kamar bata ji shi ba tayi banza da shi”. Ba k’iran ki nayi ba ko bakya jina ne”, ta taho tana gimtse fuska”.
” Zauna anan”, yayi mata nuni da kujerar da ke gefen shi.
Ido yabi ta shi yana kallon ta for  some minutes yana karantar ta ya hango zallar kiyayyar shi ne a bayyane a fuskar ta”. Huci mai zafi ya fetsar. Me yasa kike da taurin kai ne Nana? Me yasa baza ki bani abinda nake nema ba kika wahalar da ni? Kina tunanin kina da wata mafita ne?
Zuciyanta ne ya soma bugawa da k’arfi dakewa tace” Allah shine kad’ai mafita kuma shine shaida na”. Shi zai kare ni daga sharrin ka”.
Eye glass d’in fuskar shi ya cire ya sake binta da kalo yana mamakin yanda take zaro zance, kar dai yarinyar nan ta daina ganin mutunci na? To ya na iya dole ne daure tunda ita ce jigon yaruwa na”.
Tunda kince haka mu zuba ni da ke, ba zan fasa bibiyar ki ba kuma baki da wani makwanci da ya wuce d’aki na, Tashi yayi ya fita Office ya barta tana ruwan hawaye.
Taci kuka sosai kamar ranta zai fita da kyar ta lallashi kanta ko sallama da Aina bata yi ba tayi Family house d’in su tana isowa ta tarar da su a parlour suna hira, cikin kuka ta shigo ta fad’a jikin tsohuwa tace” I’m dead”, na daina zama da Datti kenan umma, Ummi………, JIKINA YAKE SO!.
Da mugun mamaki suka d’ago suna kallon ta, cikin had’in baki su biyun suka ce” bamu fahimce ki ba”, yi mana maganar gwari-gwari ko zamu fahimta”.
Da kyar ta iya tsagaita kukan tana jan ajiyar zuciya irin ta wacce taci kuka sosai d’innan sannan ta kwashe komai ta fad’a musu, salati suka saka gabaki d’aya suna mamakin abunda ya fito daga bakin ta”.
Ummi ce dai ta fara magana tace” Kin ban kunya Nana, ban tab’a zata irin sakayyar da zaki nuna ma Datti kenen ba, ke kuwa ba zaki duba irin halaccin da yayi miki ba? To ki sani ko mutuwa tana shakkar idon mahaifiya”.
Tsohuwa da ta cika tayi fammmm tace” kyale ja’ira sakarya, ince ba shine ke sangarta ki da ranki ya b’ace yayi fushi da mu amma kya zo da wani zance marar dad’in ji?
Umma dai na jin su bata tanka musu ba har saida tsohuwa ta gama maganar ta kafin tace” abu d’aya ne ya b’ata maganar ki ya kuma hana mu gaskata zancen ki, yanda kika san dutse haka Datti ya d’auki jintsin mata shi yasa baza mu yarda da abunda kika fad’a ba”.
Guntun hawaye ne ya zubo mata”, me yasa rayuwa ke neman turning mata up side down ne? even her mother that suffered during her pregnancy bata yarda da ita ba? Me yasa ba za su gaskata ta ba? Sai yanzu take gaskata maganar Aina da tace babu wani k’ofa da zai tabbatar da cewa jikin ta yake so”.
Tunowa tayi da cizon da tayi mishi ta share hawayen tare da jan majina tace” shikenan zan ko tabbatar muku da gaskiyar maganata ina so a k’ira min Datti yanzun nan ku duba bayan hannun shi na dama idan har aka ga shattin yatsu ajiki, to dole ne ku yarda da ni……….., Dole ne ku yarda da cewa JIKINA YAKE SO!

Manage please bana jin dad’in jikina.

eedatou

*💫SHINNING STARS WRITER’S ASSOCIATION*

”’The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers.”’

https://m.facebook.com/110896360504039/photos/a.110896457170696/110898470503828/?type=3&source=45

🍇🍇🍇 *UNCLE DATTI*🍇🍇🍇.
”’JIKINA YAKE SO!”’
*WRITER OF*
*1.MAGANIN MATA(DAMUWA)*
*2.WAYE MACUCI?*
*3.RAYUWAR SUMAYYA*
*and now*
*4.UNCLE DATTI(JIKINA YAKE SO)!*

©
*eedatou✍🏻*
”’Follow and ✅ote me on Wattpad”’: *eedatou*

*FREE PAGE* *WHATSAPP DA FACECEBOOK*

*WATTPAD DUKA LITTAFIN FREE*

No comments