Breaking News

Uncle Datti 31-32


3️⃣1️⃣—3️⃣2️⃣

Tsorone ya gama kamata ta saki wani firgiccen k’ara yayin da nunfashin ta ke k’orarin d’aukewa luuuuuuu ta tafi zata fad’i Usman yayi saurin janye allurar yana cewa” innalillahi wa’inna ilaihiraji’un duk ya fita a hayyacin shi cuz tsoro yake karta mutu a hannun shi ta b’ata mishi carrier d’in sannan kuma karyayi kisan rai.
Gani yayi jini ya b’alle mata yana bin k’afar ta abunda kenan ya d’aga mishi yanka kan kace mai ya hada uban gumi, saboda tsabar tashin hankali ya rasa ta inda zai fara” kar dai ace ya committing suicide? Fita yayi cikin tsananin tashin hankali yana bude kofa Datti da ya had’e kai da jikin bango ya d’ago da sauri yana fad’in lafiya? Is it successful……. Maganar ta makale mishi a sanda ya had’a idanu da Usman…….. Not really Nana is dying da wani irin murya ya furta maganar tare da kawar da eyes d’in shi gefe tunda yake bai taba jin dana sani ba irin ta ranar have it been bai bada gurguwar shawara ba and kuma yayi hunkurin taimaka ma abokin shi da bai jefa kanshi cikin wannan halin ba”.
Ido ya bishi da shi a tsorace ya fiddo su waje zuciyar shi kuma sai kad’awa yake a take ya jikin shi ya d’auki rawa……, bud’e baki yayi zai yi magana amma ya kasa dunkule hannun shi yayi a haukace ya shako Usman” you killed her? Ka kashe min Nana? Gara na kashe ka kowa ma ya huta idan ya so nima a kashe ni, fada yake amma kana gani ka san hankalin shi baya jikin shi.
Kuka ne ya kwace ma Datti sosai yayi saurin sakin Usman ya hada kai da jikin bango ya saki malalacin kuka, ganin idan suka ci gaba a hakan anything can happen gashi ko kadan Usman baya son kowa ya fahimci halin da ake ciki and Datti kamar so yake ya tara mishi mutane yayi sauri jawo shi ciki.
Ba k’aramin tashin hankali yayi ba da ya ga Nanar shi a kwance a kasa a matsayin gawa, sai yaji duk ya tsane kanshi. Rungumo ta yayi jikin shi yana kuka yana girgizata, ranar Datti ya ga tashin hankali marar misaltuwa. Hawaye ne masu uban dumi suka soma gangarowa a saman fuskarshi suke diga akan fuskarta, a hankali ta ja numfashi ta bud’e ido a hankali tana kare ma d’akin kallo……idanuwan ta ne ya sauka akan jinin da ke zubo mata a take tunanin abubuwan da suka faru ne ya dawo mata……….. Shikenan sun Rana ta da baby d’inta Datti ya tsane ta tunda har ya nemi ya cutar da d’an shi da ke cikin ta, ba tare da ta d’auke idanuwan ta akan jinin ba cikin zuciyar ta tace” daddy d’inka baya sonka baya k’aunar ganin ka a duniya, ya toshe kofar da zaka shaki iskan duniya…….., ta zabura ta hankad’a Datti da bai ma San da farfad’o ba cikin rashin sa’a ya buge kanshi da gefen table na Office d’in, zafin ya shige shi sosai har ya dafe gurin tare da sakin yar k’ara ashh………ko kad’an bata ji tausayin shi ba ta hau ja da baya a firgice tana cewa i hate you! na tsane ka Datti…….bana kaunar ganin ka again…….
Kalaman ta sun kona mishi rai sosai har ranshi yake jin zafin su fiye da zafin da kanshi ke yi mishi, Yunkurin nufar Nanan yayi yana cewa” karya kike baby baki tsane ni…, kina sona baby ……bana son wannan wasan it really hurts.
Allah ka kuskura ka karaso nan sai na kashe ka, mugu azzalumi kawai ta saki wani irin malalacin kuka mai cin rai, a zuciyanta sai cewa take” they have succeeded in  about my baby”, why Uncle……… Wannan shine soyayyar da kake ikirarin kana nuna min duk irin zaman da muka yi a baya?
Har ranshi yake jin kukan nata ga wani uban ciwon kai da ya addabe shi lokaci guda, ba tare da ya fasa ba ya hau takowa a hankali……..Usman shima dai yana jin kanshi cikin wani irin hali taimakon shi d’aya da Nanar bata mutu ba, shine yayi karfin taro Datti” baka da hankali ne? Baka jin abunda da take fad’a ne? Do you want to loose your life”. Cikin tsawa yayi maganar cuz komai zai iya faruwa dan ya lura Nanar zata iya aikata fiye da abunda ta fad’a. Baka jin abunda take fad’a ne? Barni nake ta kashe ni zaifi min sauki fiye da zazzafar maganar da take fad’a”. Babu yanda baiyi da Usman ba ya ki sakin shi basu san sanda Nana ta fice da sauri ta bar wajen ba.
Tafiya take tana waigewaige kamar wata  mahaukaciya jini na d’iga daga jikin ta lokaci guda  jiri na neman d’aukan ta har ta fito kan titi kenan wani uban jiri ya d’ebe ta ta fad’i k’asa daga nan bata kuma sanin inda kanta yake ba.
B’angaren Datti kuwa hankalin su ya tashi sosai sun duba ko ina basu ganta ba, suna cikin tafiya eyes d’in Datti ya sauka akan jinin, hannun shi har rawa yake ya nuna wa Usman…..na tabbata jinin Nana ne wannan………,baby ina kika shiga kika barni……duk ya rikice.
Calm down let’s follow her footsteps, na tabbata baza ta b’ace mana ba. Cewar Usman kenan cikin tsananin tausayin halin da abokin nashi yake ciki. A tare suka hau bin duk inda suka ga jinin har suka fito bakin titi daga nan kuma suka tsaya cirko-cirko, hankalin su ya k’ara tashi fiye da na baya……sosai kansu ya mugun kullewa cuz basu ga wani alama da ya nuna cewa ga hanyar da ta bi ba, illa gani suka yi jinin ya tsaya a dai-dai gefen titi”.
Hawaye masu uban d’umi suka fara rolling akan fuskar Datti bai san sanda ya juyo da sauri ba Usman na kiran shi amma ina ko tsayawa bai yi ba ya nufin motar shi…….. Wani irin wawan reverse yayi saura k’iris ya rage ya buge Usman ya tsaya a gaban shi yana yunkurin tsayar da shi cuz a yanda ya ga Datti ke cin uban motar anything can happen cuz ba a cikin hayyacin shi yake sarrafawa ba. Datti inaaaaa ko tsayawa bai yi ba a d’ari ya fisgo ta ta ya bar wajen da mahaukacin gudu har yana bad’a k’ura…………….

Gida ya nufa ya ko gama daidaita parking bai yi ba ya nufi parlor ya banko kofan da karfi Aina na zaune akan carpet tana yankan farce ta mik’e a da sauri a kuma razane ta tsorata sosai. Ganin Datti tayi a cikin yanayin da tunda take bata tab’a ganin shi a ciki ba……..sai surutai yake like he wasn’t in his senses” Nana ki fito na san gida kika taho  baza ki gudu ki barni ba……..dan Allah idan hiding kanki kike karna ganki dan kin tsane ni ki fito na ganki ko da sau d’aya ne nayi miki alkawarin ba zan sake tak’ura miki ba”………Zuba mishi ido Aina tayi da mugun mamaki” dear ba tare kuka fita ba ai bata dawo ba”.
What? Ya fad’a da wani irin murya yana zaro ido waje, ” kina nufin kice min bata taho nan ba…… Ohhhh Aina stop please joke apart, this is not the right time to joke……..  sai ya hau dube-dube ko zai  ga hanyar da Nana zata  fito”.
Ji tayi zuciyar ta ya mugun kad’awa ta had’iye miyau mai d’aci, duk da dai cewar bata fahimci abunda ke faruwa ba amma jikin ta na bata ba lafiya ba, to idan ma lafiya ne ina me yasa yake tambayar inda Nana take bayan a tare suka fito? Me yasa ya shigo gida cikin wannan halin? Cakkkk maganar ta ta mak’ale a sakamakon ganin stained na jini a gaban rigar shi ta hau bin shi da birkitaccen kallo shima bin inda take kallo yayi da sauri…….tsam bai lura da hakan ba……., Magana take yi kamar ta mai stammering tace” Ina…..ka samo wann….an? Idan kashe ta kayi kayi gaggauwan fad’a tun kafin na aikata mummunar abu akan ka”.
Kuka mai tsananin k’arfi ya kwace mata cikin sheshsheka yace” nima ban sani ba……..bansan inda take ba……….. Aina ki yarda da ni ban kashe ta ba”.
Idan ba kashe ta kayi ba ina ka kai min ita? Baka da wani hanya da zaka kare kanka Datti you better tell the truth.
Inalillahi wa’inna ilaihiraji’un Aina kanki d’aya kuwa? Da bakin ki kike cewa na kashe Nana? Me ta tsare min da har zan kashe ta bacin kin san irin son da nake mata?”
Toshe kunnuwan ta tayi cikin sauri ta fashe da wani irin malalacin kuka mai cin rai” me yasa ba zan yi zargin ka ba bayan na san cewa a tare kuka fita, and kuma ka dawo kai kad’ai ba tare da ita ba?
“Yana jinta tana sambatu ya fice ya bar gidan ya nufi gidan su Ummi, da Aina ta san irin halin da yake ciki yayi imani ba zata tab’a jifan shi mugayen kalamai ba, cuz duk yafi kowa jin zafin rashin Nana a gare shi, ta ko ina idan ya rasa ta kamar ills ne ga rayuwar shi”.
Da taimakon Allah ya samu ya iso gidan.
D’akin tsohuwa ya nufa ya tarar da parents din su gaba ki d’aya a d’akin suna tattaunawa…..yayin da Fu’ad ke kwance a kan carpet ya d’ora k’afa d’aya bisa d’aya yana latsa waya, fuskar shi kuma na kallon bakin kofan d’akin”.
Kallo daya Fu’ad yayi mishi ya d’auke kai kamar bai ganshi ba yaci gaba da abunda yake yi a waya”. Shi kan tsamm hankalin shi baya jikin shi bai ma san da Fu’ad d’in bama balle ya damu da hakan.
Gad’an gadan ya nufi gaban iyayen nasu da gwiwa biyu ya zube a gaban tsohuwa yana cewa” tsohuwa ina Nana take? Kinga ta boye ko ta tsane ni bata son ganina”.
Ba tsohuwa kad’ai ba hatta iyayen nasu sai da suka cika da mamaki”. Baba babba yace” kaci gidan ku, kai ba’a tambaya inda take ba dan ka raina mutane kake tambayar ta?
Ince Nanar a gidan ka take?
Shikenan na kad’ai wallahi baba babba guduwa tayi…….Nana ta gudu ta barni babu inda ban duba ba amma ban ganta ba”.
Salati suka doka su duka tsohuwa ta rik’e hab’a tana tafawa,” garin yaya hakan ta faru me kayi mata ta gudu? Cewar Umma kenan ta mik’e a fusace tayi maganar.
” Ummaa ku yafe min a halin yanzu ba zan iya fad’an mugun abubuwan da na aikata muku ba…….na cuce ku na cuce ka ina……….ba zan yafe ma ka ina a bisa abunda na aikata ba”.
Umma da zuciya ya gama d’iban ta ta kai hannu zata kwala mishi mari Alhaji yayi saurin dakatar da ita. Koma ki zauna Umman Datti ba za aiyi abu cikin fushi ba. Baza ta iya jayyaya da shi ba tana ganin girman shi ko ba komai mahaifine a gare ta tunda uban mijin ta ne, ba dan ta so ba ta koma ta zauna tana jan kwafa” ai raini ni ne ban da haka me yasa zai dubi saban  idon su yace ba zai iya fad’an musu abunda ke faruwa ba?
Baba babba ma ji yake kamar ya kai mishi bugu wata kila idan yaci uban shi da kyau zaiyi bayani”. Fu’ad kam bai san sanda ya mik’e ya shak’o kwalan rigar Datti ba duk irin tsawar da Alhaji yayi hakan bai hana ya sake shi ba, aka hau bam-bare Datti daga jikin shi” wallahi k’arya kake…. Kayi kad’an ka salwantar da rayuwar Nana ……dole you must pay for it”.
“Enough baba k’arami ya daka mishi tsawa yayi saurin sakin Dattin jikin shi na kad’awa……. Baba karami ba dan na san cewa kaine mahaifin Nana ba da cewa zanyi tsintota kuka yi? Kai da Ummi kun cuce Nana da kuka bada yardar ku ma Datti…….. I warn you several times without number amma ga irin ta nan yanzu wa gari ya shafa? Ku sani baku ji komai ba tukunna sai zuwa gaba zaku yi dana sani wanda zai zamo marar amfani”. Yana gama fad’a yayi hanyar d’akin shi ya had’a kai da jikin bango yana rusar kuka”.
Ba komai ne ya tsaka shi hakan ba illa tsananin tausayin Nana da ya gama mamaye ilahirin bargon jikin shi…….Allah yayi gaskiya da yace idan zaka so mutum kaso shi d’an dai-dai, idan zaka k’i mutum ka k’i shi dan dai-dai masoyi na iya zama makiyi haka zalika makiyi na iya zama masoyi, gashi duk irin soyayyar da Datti yake ikirarin yana nuna wa Nana he end of hurting  and ruined her life.
Magana yake a k’asan zuciyar shi” Duk inda kike ina tare da ke Nana idan bana tare da ke zuciya ta na tare da ke na kudurta a raina sai na kwace miki hakkin ki, ko ta wani hanya sai na ka amsa laifin ka Datti,, da ka ki da ka so sai na fallasa asirinka”………

Bangaren Nana kuwa satin ta biyu tayi ba tare da ta san inda kanta yake ba a lokacin babu irin cigiyar da su baba Babba nasu bayar ba a kafafen yad’a labarai, har hotunan ta an buga a jarida sannan kuma ana haskawa a akwatin talabijin amma ba wani takamammen amsa da zai bada tabbacin an gano inda take”.
Datti ya birkice ya koma wani iri magana d’aya biyu zai yi sai ya had’a da sunan ta suma mutanen gida hankalin su ya tashi sosai, Ummi wani sa’in ta fake idon su Umma ta lab’e a wajen da babu mai ganin ta tayi ta rusar kuka, addu’a iya addu’a suke yi kuma suka bada taimako almajirai na taya su yi, Aina ma ansha fama da ita sosai dan sai da ta tattara ta koma gidan har zuwa yanzu  cewa take Datti ne ya kashe Nana ta d’auki k’aran tsana ta d’ora mishi, ta wajen Aina baya samun sauki haka ta bangaren zuciyar shi ma dafi ne na rashin babyn shi, ga wani mugun sha’awar ta da yake mugun bijire mishi har yana jin cikin shi nayi mishi ciwo time-time. Ko kad’an bai bari iyayen shi sun fahimci halin da yake ciki ba cuz idan suka gano cewa sha’awa na damun shi zasu suspecting d’in shi k’arshe ma dole su yarda da abubuwan da Nana take fad’a a kanshi idan kuma hakan ya faru dole kowa ya tsane shi.
Dana sani iya dana sani yayi kan muguwar kaddarar shi ji yayi ma da ace sha’awar ne ma kwatata baya ji da yafi mishi sauki kan ace sai mace d’aya take iya biyan mishi bukatun shi”.

Sai da Nana ta shafe wajen sati biyu da kwana hud’u kafin nan ta farfad’o ta bud’e ido a hakali tana kallon wuri……yunkurin mik’ewa tayi taji kanta nayi mata wani irin zogi tayi saurin dafewa da sauri sai ga hawaye na bin kuncinta. Tunowa tayi da abunda ya faru da ita ta matso hawaye mai uban d’umi Shikenan Datti yayi nasarar zubar mata da cikin ta, she lost her baby,  wani irin rashin imani ne ace at this early edges of hers abubuwa na faruwa da ita beyond her expectations, she didn’t deserved this at all, rayuwar da zo mata b’aragurbi wanda ake k’ira bahaguwar rayuwa”. He puts her through much pains da kwakwalwar ta sunyi kad’an su d’auka.
Tana cikin tunanin ne taji muryar wata mata tsohuwa wacce tayi sa’an k’akarta tsohuwa tana cewa sannnu baiwar Allah, masha Allah kai mun gode ma Allah da ya saka kika farfad’o lafiya……………, hawaye ne ya mak’ale a fuskan ta na tare da ta furta komai ba ta d’ago mata.
Abinci matar tasa aka kawo mata mai ji da lafiya ta taimaka mata ta kaita band’aki tayi brush tare da sheka wanka ta fito sai taji kamar yan zare mata kaya wani iskan dad’i ne ya soma shigan jikin ta ta lumshe ido ta bud’e a hankali tare da nemo towel ta d’aura a k’ugun ta ta fito.
Ga mamakin ta ta ga har matar ta fito mata da sabbin English wears guda biyu duka dogayen riguna, hannu ta mik’a ta d’auki d’aya daga ciki ta saka, sosai tayi mamakin yanda aka yi matar ta kawo mata kaya dai-dai size d’inta Tana gama sakawa taji an bud’e kofan an shigo, matar ce ta ta shigo dan ta duba ko ta gama, muje kici abinci na san zuciyar ki cike da tambayoyi kafin na amsa miki nafi son kici ki k’oshi”, babu musu ta bi bayan matar suka fita tana gaba Nana na bin ta a baya har dinning area.
Makeken gida ne na gani na fad’a ko mai na gidan rassssss tsayawa fad’an kyau da tsaruwan gidan ma b’ata lokacin ne an kashe dukiya iya dukiya komai na gidan was well arranged.
Tun daga nesa take jin kamshin abincin duk ya cika mata hanci, sai taji wani irin mugun yunwa ya addabe ta kamar taci babu”.
Kujera matar ta jawo mata tace zauna a nan itama ta jawo ta zauna ta hau serving din ta ita dama a koshe take shiyasa wa Nanar kad’ai ta saka, ba shiri Nana ta hau kaftar abinci tana ci sai tausayin ta ya kama matar ai dole ta dinga dagargazar abincin cuz tunda aka kawo ta gidan banda drip babu abunda take sha”.
Sai da ta cinye tass kafin taji cikin ta ya k’oshi ta kora da ruwa tayi gyatsa matar tace” a k’aro miki ne?
Da tsiririyar muryar ta tace” na koshi”.
Parlour suka koma suka zauna Nana dai Allah-Allah take matar ta fad’a mata yanda akayi ta tsinci kanta a gidan amma ta kasa tambayar ta da matar ta fuskanci hakan tayi murmushi cikin zolaya tace” da kin kwantar da hankalin ki yammata ba gidan yanka mutane kike ba, na ga kin zaku ki san yanda aka yi ki zo gidan nan ko? To bari na baki labari, ta gyara zama Nana ta gyara zama itama kafin nan ta fad’a bayani kamar haka ” sunana Sumaiya amma ana k’irana da inna, nayi aure da mijina tunda muke bamu tab’a samun haihuwa ba har mijin nawa ya koma ga Allah”. Kafin mijina ya rasu hamshakin mai kud’i ne na gaske bayan rasuwar shi dangin shi suka kwashe komai da ya mallaka suka rik’e na takaita miki na sha fama sosai da wahalar rayuwa kafin nan Allah ya had’a ni wani yaron kirki shi yayi sanadiyan zama na a nan  a matsayin na dinga kula da ke, tunda aka kawo ki gidan nan yake hidimar jinyar ki doctor ne ya neman miki na musamman har gida yake zuwa duba ki, jinyar sati d’aya cikakkiya aka yi miki kafin nan aka shawo kan matsalar, likitan ya tabbatar mana cewa a kowa lokaci zaki iya farfadowa kuma insha  Allah baza ki farfad’o da wata matsala ba Alhamdulillah sai gashi kin farfado lafiya.
Shiru tayi ta mik’e a hankali ta d’au goran ruwan faro a fridie Nana na bin ta da ido ta b’alla ta sha kafin nan ta rufe murfin ta d’ora a kan table ta koma ta zauna. Haka yayi ta faman jinyar ki sau d’aya yake zuwa a rana yana duba lafiyar ki tun da nake bai tab’a fad’a min sunan shi ba kuma nima ban tambaya ba………., da dai naga baida niyan fad’a min da kai na na tunkara mishi yace min”ammintacce”, da sunan zan dinga k’iran shi kenan. Jira ni ina zuwa ta fad’a ta mik’e ta shige d’akin da yake a matsayin mallakin ta ta fito ta wasu takardu guda hudu d’auke da rubutu a jiki ta mik’a wa Nana”  Ga wanan shi ya bani yace a duk sanda kika farfad’o na baki. Hannu Nana ta mik’a ta karba takardar zuciyan ta cike da tunanin wannan bawan Allah da ya taimake ta,, haka suka yi ta zama inna na bata labari tun tana nokewa har ta d’an saki jiki da ita, ba laifi matar tana da kirki sosai.
Da daddare d’akin da ta farfad’o ta ganta a ciki shi ta nufa tayi lamo akan gado ta fara yunkurin bud’e takardar d’aya bayan d’aya, har ta warware duka sai ta fasa ta ninke ta ajiye cuz a halin yanzu bata da lokacin da zata karantawa ta koma ta kwanta da tunani kala-kala a kasan zuciyar ta zata so ta san. *WAYE WANNAN MUTUMIN DA YA BOYE SUNAN SHI YA KIRA KANSHI DA AMMINTACCE?* *ME NENE DALILIN DA YA SA YA TAIMAKEcomment
Kwanan ta hud’u a gidan ba tare da ta had’a ido da Ammintacce ba, da ta gaji da zuba ido ta tambaye Inna” wai wannan mutumin baya bayyana kanshi ne? Dariya inna tayi tace” kece dai kawai bakya ganin shi amma ko d’azu da kike d’aki ya shigo kuma ya tambaya lafiyar ki, nace mishi mishi kin farfad’o ma”.
Hmmmmm Inna wannan mutumin da ban ala’jabi yake ace har yau ban san wa ke taimakona ba?
“Ke dai bari kawai nima dai da farko lamarin shi tsoro yake bani daga baya kuma na fahimce shi mutum ne mai saukin kai marar son fitina”.
Don Allah Inna idan mutumin nan ya sake zuwa ko me nake yi ki had’a ni da shi”.
” To idan har ya ammince da hakan babu matsala.
Washe gari da safe bayan sunyi breakfast Nana na kwance a akan kujerar three seater tayi pillow da cinyar Inna, suna hirar su, a cikin kwanakin sun saba sosai har Nana ta kan manta wasu abubuwan da suke damunta duk da dai cewar har yanzu da gurbin mik’in da ke fame a heart d’inta.
Inno hawaye ne ya gangaro saman tsiririyar fuskarta, Inna taji d’umin hawaye ta mirgina kan Nana tace” Subahanalillah? Y’ar nan me ya faru kike kuka?
” Wa ya tab’an min ke? duk ta rikice.
Maimakon da ta amsa mata sai ta hau sheshshek’ar kuka hankalin tsohuwa ya dad’a tashi” Ya salam! don Allah kiyi ma Allah ki fad’a min idan da wani abu da nake yi miki wanda bakya so sai na daina”.
Ganin yanda hankalin Inna ya tashi sosai ta share hawayen ta” babu komai Inna ina so naje gida ne, ina son ganin Ummana”.
Shiru Inno tayi ta sani da gaskiyar Nana duk inda take dole tayi kewan mahaifanta amma  a halin yanzu bata da ikon da zata bata izinin tafiya, da ita da Nanar duk a karkashin wani suke”.
Cikin hikima tace” kwantar da hankalin ki idan ammintacce ya zo zan fad’a mishi, insha Allah zai maida ki gida kamar yanda kika bukata.
Da wannan tunanin ta samu har Nana ta hakura ta tsaida kukan, zama suka yi shiru-shiru bai shigo ba gashi yanzu wajen k’arfe biyar na yamma.
B’angaren Ammintacce kuwa yau tun safe ya ke son ya ga ammanar shi amma ba hali abubuwa sun d’an shige mishi gaba hakan ya saka bai samu daman shigowa da wuri ba, sai wajen k’arfe tara da rabi ya samu daman isowa gidan a lokacin har Nana ta gaji da jiran tsammanin fatu tana gyangyad’i Inna ta raka ta d’aki ta kwanta”.
Shigowan shi ciki yayi dai-dai da lokacin da inna ta juyo kenan zata koma d’akin ganin shi da tayi ta hau washe baki tana gaishe shi, cikin girmamawa ya amsa mata.
“Ya amanata Inna? Da fatan bata yi miki rigima”?
” Murmushi tayi cikin jin dad’in yanda yake ganin girmanta tace” hmmmm ammanar ka na nan lafiya cikin amminci sai dai yau ta so ta bani matsala yau”.
Fitina ta sakar mini har da kuka wai tana son ganin Umman ta”.
Shiru yayi for some minutes yana tunani sai ya mik’e yace ina zuwa, ya sa kai ya shige d’akin.
A kwance ya tarar da ita barci ya fara d’aukan ta, ya zauna a gefen bed d’in in a cool voice din shi cikin barcin ta taji muryar shi yana cewa” *BA YANZU ZAKI KOMA GIDA BA IDAN LOKACI YAYI DA KAINA ZAN TAIMAKA MIKI WAJEN HAD’A KI DA MAHAIIFAN KI”*, ya bada baya zai fita kenan ta mik’e a zabure kafin ta kai ga tsaida shi tuni ya fice daga d’akin yayi sallama da tsohuwa ya fita, cikin rashin sa’a ta fito ta tarar babu shi, tsohuwa kad’ai ta gani a parlourn ta koma tana maida numfashi da kyerrrrrrr har sai da tsohuwa tace lafiya kike irin wannan numfashin?
Innaaaa sai ido muryar da taji ya rikita ta sosai idan ba mafarki take yi ba ta so ta gane mai irin muryar nan. “Ammintacce”, ta furta da wani irin dishashshiyar murya, wani buri yake da shi akan ta wanda yake son cimmawa?
Anya bata kuma fad’awa wani mugun tarkon d’a namiji ba? Me yasa bai  bayyana mata ko shi wanene  ba da dalilin da yasa ya boye ainihin sunan shi, yake amfani da ” Ammintacce a matsayin sunan shi”?
Pls share votes and comment

*eedatou*

*πŸ’«SHINNING STARS WRITERS ASSOCIATION*

”’The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers.”’

https://m.facebook.com/110896360504039/photos/a.110896457170696/110898470503828/?type=3&source=45

πŸ‡πŸ‡πŸ‡ *UNCLE DATTI*πŸ‡πŸ‡πŸ‡.
”’JIKINA YAKE SO!”’
*WRITER OF*
*1.MAGANIN MATA(DAMUWA)*
*2.WAYE MACUCI?*
*3.RAYUWAR SUMAYYA*
*4.UNCLE DATTI(JIKINA YAKE SO)!*

©
*eedatou✍🏻*
”’Follow and ✅ote me on Wattpad”’: *eedatou*

~Comments d’inku na jiya sun rikirkitana ni, wannan page kyauta ne na ware ma dukkan masoyanaπŸ’˜πŸ’˜~

No comments