Breaking News

Uncle Datti 37-38


3️⃣7️⃣—3️⃣8️⃣

Juyowan da zaiyi tayi ido hud’u da shi…….ido waje ta zaro dan ganin wannan mutumin ne amma samm zuciyar ta ta kasa yarda da shi…………., sai ido take bin shi da shi ba tare da tace komai ba, kamar kullum murmushi ya sakar mata tare da k’awar da kanshi suka ci gaba da hira da Inna.
“Hawaye ne ya cicciko mata a idanuwan ta………menene kuddurin da yake da shi akan ta da zai tsare ta na, juyowa tayi da sauri zata bar wajen Inna tace” ina kuma zaki y’ata koma ki zauna “.
Bata son da da ita ba shiri ta samo guri ta zauna ta k’asan ido take fuskar shi, tana so ta gano wani abu game da shi.
Sai take ganin kamar da ban-banci tsakanin fuskar da take gani a duhu……….lallai Amintacce yana wahalar da zuciyan ta wajen gano ko shi d’in wanene and she can’t tress him.
Da wanan tunan har ya bar gidan ba tare da ta sani ba.
Inna na zaune taji barci ya fara d’aukan ta tace wa Nana ta taso suje su kwanta, sai a sannan ne ta dawo daga rakiyar tunanin da take, jiki a sanyaye ta shige d’aki ta kwanta itama Inna tayi nata d’akin.
B’angaren Inna tana shigowa d’akin taji wayan ta na ringing a samar drawer tayi sauri ta picking ta manna wayar a kunnen ta, suka gaisa da juna”.
” Yaya amanata Inna da fatan kina kular min da ita?
“Ehhhh gwargwadon iyawata ina yi sai dai fa yarinyar har yanzu bata hak’ura da batunta na komawa gida ba, baka ganin ya dace ace ta koma gida?
” Uhmmmmmm ya fad’a cikin muryar shi mai dad’in sauraro, har yanzu ba’a kai matakin da zata koma ba……..burin nawa bai gama cika ba amma saura k’iris”.
D’oguwar ajiyar zuciya taja ta sauk’e a hankali…………to amma ya kamata ace ka bayyana mata kanka……ina tunanin ta fara zargin wani abu………..,ka san bana ta tashi hankalin ta saboda kar abun ya shafi juna biyun ta………..
“Wani irin abu yaji ya daki zuciyan shi mai kama da mashi dan jin ta ambaci sunan ciki……….shikenan Inna zan duba na gani ki d’an bani lokaci kad’an kafin nan na gama cimma burina”.
” Uhmmm, shikenan tunda kace haka……Allah ya taimaka ya bada sa’a ina yi maka addu’ar cimma burin ka”.
“Ameen, Ameen inna na gode, daga nan suka yi sallama ya kashe wayan.

Tunani ya dumiya a ciki she ma kanshi bashi da piece of mind akan killace ta da yayi but bai da option than yayi hakan……….., waya ya d’auka ya dailing wata number ya manna a kunnen shi daga d’ayan b’angaren aka d’aga.”
“Har yanzu baka kai gida bane naji kamar kana tuk’i ne?
” Yeah of course amma saura kirissss.
“Owk….. Owk…..to yaya mission d’in?
“Dariya yayi a dai-dai lokacin da ya k’arya steering motar ya shawo kwana,” gaskiya mutumina kwakwalwar ka na jaaaaa ban yi zaton yarinyar nan zata yi saurin gano wani abu ba sai yanzu………., ya bashi labarin yanda ta tarar da shi a parlour “.
” Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauk’e tare da gyara kwanciyar shi a kujerar da ke babban parlourn gidan su yace” dama na san dole za’a rina shi yasa tun farko na shirya hakan”.
Basu wani dad’e da wayan ba suka yi sallama da juna………, daren ranar da tunanin yarinyar ya kwana ga uban zafi da ranshi ke yi mishi…….., abubuwa da yawa sun saka shi a gaba sun hana zuciyan shi sakat.
B’angaren Inna kuwa bayan ta gama waya da mutumin taji an bud’e k’ofa an shigo…….., Nana ce ta tsaya daga bakin k’ofa ta jingina bayan ta da jikin k’ofan hawaye na bin bayan fuskar ta d’aya bayan d’aya, da alama taji duk abunda suke fad’a cuz a hansfree wayar take.
Jikin ta ne yayi mugun sanyi ta taso da sauri tayi wurin ta zata lallashe ta Nana ta ja jikin ta da sauri cikin kuka tace” Irin zamar da zamuyi da ke kenan? Ashe dama kina sane da komai kike b’oye min………da na d’auka ke mai tausayina ne amma yanzu na gano cewa da had’in bakin ki ake so a cimma buri a kaina……..kuka ne ya ci k’arfin ta tayi shiru tana sheshshekar kuka…….laifin ta ne da ta yarda da da ita tun farkon zuwan ta gidan har take bata girma ta d’auke ta a matsayin dangin ta duk da dai ta san cewa bata tab’a ganin ta ba sai a gidan amma haka ta ammince da ita.
Zuciyar Inna ya karaya sosai da jin kalaman yarinyar” Ba cutar da ke zamu yi ba ki yarda da dukkanin abubuwan da nake fad’a miki……….,
Cike da takaicin maganar Nana ta juyo ta dube ta” ta yaya zan k’ara yarda da ke bayan da had’in bakin ki aka b’oye min ainihin fuskar Ammintacce da kuma hujjar zamana a gidan nan tare da ku?
“Na sani ni mai laifi ne a gare ki amma ki daura ki dubi magana ta da fuskar fahimta………
Ba zan tab’a fahimtar ku ba har a bada………, barin d’akin tayi ta koma nata da sauri ta fad’a saman bed ta shiga rusar kuka kamar ranta zai fita…………, abu ta tuno da sauri ta mik’e da sauri ta d’ago rigar ta tana shafa cikin ta………..da gaske ne baby ne a ciki d’ina?
Is it true that baby d’in nan na Uncle d’ina bai zube be?
” me yasa Inna bata fad’a mata cewa cikin ta bai zube ba bayan ta sani………….
Kuka ne mai tsananin k’arfin gaske ya kwace mata na tunawa da rayuwar da suka yi da Datti” ya treating d’inta kamar k’are, ya maida ta kamar jujin shi, ya maida ta tamk’ar rigiya a duk sanda yake bukatar ruwa ya zira gugan shi ciki ya d’iba…………, at the end da ya d’irka mata ciki sai ya manta da irin rayuwar da suka yi a baya, at yayi yunkurin zubar mata da cikin…………, hawaye mai uban d’umi ta ya sake bin kyakkyawar fuskar ta tana shafa cikin tace” baby d’ina dady d’inka baya son mu? Ya maida mu useless, he tried to murder us.
Idan na haifo ka ka fito duniya kar ka d’auki irin halin mahaifin ka………,kar ka kasance cikin jintsin maza marasa sha’awan mata like daddy d’inka………..bana son halin mahaifin ka ya shafe ka…………..bana so ka taso da halin akuyanci irin na mahaifin ka…………cuz idan ka taso da hakan zaka zamo mutum mugu mai son kanshi……….zaka yi cuta irin na mahaifin ka……….., promise me cewa idan ka fito duniya ka zamo mutum kamar kowa baza ka aikata abunda mahaifin ka ya aikata ba………….,abun da ke cikin ne ya fara motsawa kamar yana jin ta………murmushin mai d’auke da hawaye ya subuce mata ta ta sauk’e rigar ta koma ta kwanta……….tana mai ci gaba da kukan ta…….ta ko ina bata da sauki ga matsalar da Datti ya jefa ta a ciki ga kuma Ammintacce da saboda bakar kudurin shi ya ki barin ta ta tafi gida.
Cikin kwanakin ta d’aga hankalin ta sosai kullum cikin d’aki take bata saukowa sai idan yunwa ya addabe ta kafin nan ta nemo abinci taci ta koma. Inna ta damu sosai da wannan sauyi na ta sammm bata jin dad’in hakan domin Nanar bata tab’a bari su had’u ko da kuwa sun had’u bata bata mata maganar har ta gama abunda ya kawo ta ta koma d’aki.
A lokacin tsananin kewan gida na kama ta idan ta tuna sai tayi ta shafar cikin ta tana kuka shine kad’ai abunda yake saka ta jin sauki a halin yanzu.
Shima kanshi Amintacce bai ji dad’in hukumcin da Nana ta d’auka ba………,hakan ya sa ya gane cewa duk rubutun da yake bata bata karantawa………, da ace tana karantawa da ba zata d’aga hankalin ta ba……..da zata fahimci asalin kuddurin shi na yi hakan……cuz yayi rubutun ne ta yanda zata gane ko waye shi da kuma kuddurin da da dalilin kin bayyana mata fuskar shi da yayi……..
Wata rana da ya shigo gidan da rana ya haye sama daga bakin k’ofa ya tsaya yana mata magana da tattausar muryar shi wanda kusan kullum kamar ana k’ara mishi zaki yace” ko da sau d’aya kin yi tunanin bud’e takardun nan da na baki kin karanta?
“Ko wace takarda da dalilin rubuto ta me yasa baki bud’e kin ji hojjojin da na rubuto ciki ba…….,
” Sheshekar kukan ta ya jiyo ba shiri ya runtse ido, da ta san me yake ji a ranshi da ta hak’ura da kukan nata”.
Mik’ewa tayi daga kwancen da take ta tako har bakin k’ofa ta tsaya……..baka da wani hujjar da zaka ajiye ni a nan, idan har zaka iya rubuto min takarda kamar yanda ka fad’a na tabbata babu abunda zai hana ka bayyana min kanka”.
Bana bukatar karanta komai ka rik’e hujjarka kuma ka ci gaba da b’oye kanka, sai ta durgusa a k’asa tare da jingina bayan ta a jikin murfin k’ofa ta saki wani irin malalacin kuka mai tsuma rai.
Wani irin kuka yaji ya kwato mishi ya hau rerawa ya hau bugun k’ofan, muryar shi na breaking yace” kar kiyi saurin yanke hukunci akan akan abunda baki sani ba……….takardar nan shine sirrin duk wani abunda kike so ki sani game da ni………..
“Dakata malam ba zan bud’e ba nace…..ka barni na tafi gida na gaji da wahalar da ni da kake yi. Suna cikin hakan ne yaji an dago shi ta baya……….Inna ce ta fito daga d’aki zata lek’a ko Nana ta fito parlour sai taji muryar Amintacce na kuka………, shine ta hauro taji menene ya faru………
Jikin ta ya mutu sosai da ta ga shi a hakan abune mai matukar wahala ka ga namiji yana kuka wi-wi da hawayen shi sai gaji Amintacce yana yi.
“Muryar shi taji tana cewa” Inna kin gani kuka take yi kice mata ta daina bana so?
Takardar da na rubuto mata ma tace baza ta karanta ba yaya tace so na saka raina?
“Ni na fita jin zafin killace ta dani amma dole ce ta sa babu yanda na iya…………
” Shiru Inna tayi sunyi matuk’ar bata tausayi sosai daga shi har ita Nanar……….
“Ban ga laifin ta ba dan tak’i bud’ewa kamata ka janye maganar burin da kake son cikawa ka fito mata ido da ido ta san komai game da kaiiiii.
“Hawaye mai uban d’umi ya matsa” Shikenan  Inna yanzun nan zata san ko ni waye kuma a yau d’in nan zan zata koma ga iyayen ta ko da kuwa burina bai gama cika ba amma Alhamdulillah ko a haka ma ya wadatar……….bud’e ki ganni a yau zan bayyana miki kaina.
Tana jin su kuka yaci k’arfin ta she cried bitterly, da dishashshiyar muryar ta tace” bana son ganin fake fuskar ka da a kullum kake yaudara na dashi cewa fuskar Amintacce ne bayan ba hakan bane…………,
“I hate to see your face……..na gaji da yaudara da zulumin da kake barina da shi a duk lokacin da nayi arba da fuskar ka…………., kuka ta kuma sakewa har tana shid’ewa.
“Billahil Azeen nine Amintacce ba da fuskar da kika saba ganina zaki ganni ba……..i bet you yau na shirya bayyana miki furkar da ya dad’e yana b’oye miki…….bud’e ki gani nana nine………..,
“Enough please!!! tayi sarin katse shi cikin kuka,  na gaji da jin yaudarar ka please let me be………duk ka bi ka hana zuciya ta sakattttt ko da yaushe cikin fargaba take, i don’t want to see you…….i hate you most.
Maganar ta ta k’arshe yayi mishi zafi da yawa……..ba tare da ya furta komai ba ya sa kai ya fita daga gidan Inna har waje ta bishi tana kwala mishi k’ira amma ko tsayawa bai yi ba.
Mota ya shiga da uban gudu ya ke jan ta kamar zai tashi sama sai da yayi tafiya mai nisa kafin ya parking ba tare da ya fito ba ya fiddo dawa ya dailing wani number………daga d’aya b’angaren aka d’aga tare da sallama”, maimakon yaji an amsa mishi sai ma jin sautin sheshshek’ar kukan shi, da mugun mamaki yace” Subahanalillah! Me ya same ka kake kuka? Waittttt tell me please, duk a rikice yake maganar”.
“Ina son mission d’in nan ya k’are daga yau…….daga yau, yarinyar tana bani matsala sosai ban jin zamu d’ore a hakan”.
Doguwar ajiyar zuciya ya saki yana sauraran shi har sai da ya gama kafin nan yace” tun farko sai da na warning d’inka akan wannan plan d’in, ni ban ga dalilin da yasa baka so ka yi ido hud’u da ita ba………..yanzu yaya kake ganin za’a ending mission d’in?
“I really don’t know, har yanzu burina bai gama cika ba…….., ka san for how long na d’auka nake neman hanyar da zan cika burina?
Ya gyad’a kai kamar dama yana ganin shi.
” You won’t know ni kad’ai na san irin adadin lokacin da na d’auna ana zaman jira.
“Ka ending wannan plan d’inka please ni kaina wallahi k’arfin hali kawai nake yi a duk sanda na je mata a matsayin kaine, sometimes tausayin ta har kusan saka ni kuka yake yi, tana narkar min da zuciya musamman da cikin ta ya fara tsufa d’in nan”.
Da haka suka yi sallama ya koma gida ya kwanta da tunanin kala-kala a ranshi….that night he cried bitterly har sai da hawaye suka k’afe mishi a ido”.
Bayan kwana biyu abubuwa sun dad’e cunkushewa wa Amintacce duk sanda ya so ya so ya shawo kan matsalar abu ya ci tura, a duk sanda ya shigo digan sai ya haura d’akin Nana ta bud’e amma ta k’i bud’ewa hakan zai koma cikin k’unan rai. Inna ma tayi nata iyakan k’ok’arin amma duk da haka still Nana tana nan akan bakan ta…….., yanzu kam ma idan zata sauk’o sai ta tabbatar babu kowa a parlourn kafin ta fito tana gama abunda zata yi ta koma ciki………, haka zata zauna ta saka cikin a gaba tana kuka she knows that babu k’ofan guduwa daga gidan cuz akwai tsaro na musamman da aka yi ma duka k’ofofin gidan.
Yau ma kamar kullum tana d’aki tana kwance taji haka kawai tana so ta watsa ruwa rabuwan ta da wanka har ta manta, mik’ewa tayi ta sauko ta nufi ban d’aki ta had’a ruwan wanka ta tayi tana gamawa ta fito ta d’au rigar ta zata saka taji yak’i shiga……..kusan kala goma ta duba duk sun ki shigan ta kawai sai ta sa kuka……….ta hau dube-dube ko zata yi sa’a ta samo wanda zai yi mata dai-dai bata samu ba haka ta hak’ura ta maida wanda ta cire sai hawaye take yi cuz kayan sosai yake tashi da tsami.
Tunanin yanda rayuwa ta sauya mata…..da dai yar gata ce ummin ta na ji da ita haka Uncle d’inta Datti daga baya komai ya cakude mata ta fad’a k’azamar rayuwa.
Datti ya cuce ta da ya jefa ta cikin tsaka mai wuya Amintacce kuma ya zalumce ta da ya killace ta a guri d’aya ya barta tana azaftuwa da rashin iyayen ta. Ta sani sune silar jefa ta cikin wannan halin amma duk da haka tana jin son su a ranta she knows that suma sunyi kewan ta da yawa kamar yanda ta ke jin nasu.
B’angaren Datti kuwa yana nan a sume a wajen bai kuma sanin inda kanshi yake ba sai wajen goma da rabi na dare shi d’in ma uban sanyin hunturu da ke busowa cikin d’akin ne ya dawo da shi cikin hayyacin shi.
A hankali ya bud’e ido yana gama bud’ewa ya ga jikin shi ko kaya babu sai a sannan ne ya mik’e ya lalumi kayan shi ya saka……..cikin ta d’an fad’a mishi ba laifi tunda har yana iya takawa.
Amma ba wai ya daina jin feelings d’in bane kwata-kwata.
Komawa yayi ya kwanta kwanta………sai yaji gaban shi kamar an sa mishi peper ya zaro shi da sauri yana matse ido yayin da zafi ke ratsa shi a take jikin shi yayi zafi rad’au.
Hankalin shi yayi matuk’ar tashi na ganin yanda wurin ya koma, shi dai ya gamu da jarrabawar rayuwa yana tunanin ya fita daga wannan sai ga wani kuma ya dawo, hawaye ne ya gangaro mishi mai uban d’umi duk muguwar jarabar shi ce ta jawo mishi hakan. Maida bananar shi yayi cikin wando yana maida kwallar azabar raddin zafi…….yayin da hawaye sabobbi suka hau bin fuskar shi…………., cikin daren ya k’ira mumber d’in Usman ya hau jero mishi abun da ke faruwa cikin kuka mai tsanani.
Shima kan shi Usman d’in ya tsorata matuk’a da lamarin Datti…….., bai k’ara tsorata ba har sai da ya shigo gidan cikin sa’a kuwa Fu’ad na maib parlour a kwance yana jin muryar Usman ne ya taso ya bud’e mishi…………, ko tsayawa baiyi ba ya haura site d’in Fu’ad da sauri,  shima Fu’ad na ganin haka yayi saurin komawa ya kwanta…….a yanayin Usman d’in ya shigo gida ya tabbatar mishi ba lafiya…….dole da akwai abunda yake faruwa da Datti………to ko yaje ya duba shi ne…..ko ma dai menene yayi d’an uwan shi ne……….ba da son rashin bane yake keeping malice da shi.
Mik’ewa yayi ranshi babu dad’i hayi hanyar d’akin da sauri………, da ya tuna cewa ba lallai ne su bari ya san abubuwan da suke b’oye mishi ba yana  kaiwa bakin k’ofan sai ya ja ya tsaya yana tunanin ya shiga ne ko karya shiga ……….
B’angaren Usman bayan ya shigo d’akin sai ya tarar da abun da ya mugun d’aga mishi hankali…….a yanda ya zata ba hakan ya tarar ba  domin da ya bud’e dan ya duba sai ya gaban Datti yanda ka san sab’ule haka ya koma.
“Salati ya doka a rikice yayi saurin rufewa yana maida kai gefe ya rutse ido da k’arfi he never expect cewa haka abun yayi tsananin………..ya dube shi” yace garin yaya hakan ta faru…….? Me kayi dick d’inka ya koma haka?………, Datti dai sai ido yake ta bin shi da shi hawaye na zubo mishi ya kasa controlling d’in su, hannu ya kai yana dungurar pillow d’in dashi Usman ya bi bayan shi da kallo to his greatest surprise sai ya ga k’atuwar rami fad’in shi ya kai k’aurin dick d’in Datti a jikin pillow, da mugun mamaki ya gwalala ido yana kallon Datti? Pillow ka ci?, gyad’a kai yayi alamar eehhhh.
“Shiru Usman yayi yana tunani” wani irin caccaka yayi ma pillown da har dick d’in shi zai sauya halittan dick d’in shi……….
Jikin dagon ya bi da kallo ya ga stain d’in jini ashe garin caccakar pillown dan jaraba  bai sani ba a lokacin har yana had’awa da jikin gado, shi dai a lokacin idanuwan shi a rufe suke bai da burin da ya wuce ya rabu da feelings d’in da ke damun shi.
“Sai hawaye ya k’aryo ma Usman na tsananin tausayin abokin na shi……..cuz he knows that he was suffering a lot.  Treating na wajen yayi yana ma mishi fad’a sosai ya dinga bin abun a hankali idan ba haka ba zai iya rasa ranshi……, Allah friend idan baka controlling kanka wata rana sai dai a tsinci gawan ka a d’aki………, k’arya murya yayi irin na wanda take cikin azaba yace” to yaya kake so nayi bacin baby ta tafi ta barni……..?  Maganar sai ya bama  Usman tausayi  yace” daurewa zaka yi ka cire sha’awar nan a ranka………, sannan ka dinga azumi akai-akai shine dai shawara ta gare ka”………….,
*Usman don Allah kaci gaba da rik’e min sirrina……….bana son kowa ya sani…….daga ni sai kai sai Allahn da ya halicce mu.
“Huci mai zafin gaske ya sake” gana ganin binne sirrin da muke yi shine solution na problems d’inga? Wallahi Datti na fara karaya da lamarin ka………….bana jin zan iya rik’e maka sirri”.
“Miyau mai d’aci ya had’iye zuciyan shi na mishi suya uba uba ga pain na dick d’in shi ya dame shi………Usman ko mutuwa nayi bana kaunar su baba Babba su san abunda na aikata………., jikina na bani rayuwana ba mai tsawo bane………ko da bayan raina idan baby ta dawo kace ta yafe min abunda nayi mata………,ba laifina bane da na kasance mai tsananin son na kusance ta…………., zan mutu ne da ciwon son baba……., k’asa jurewa yayi da sauri ya rufe bakin shi yace” baza ka mutu ba…….da yardar Allah Nana zata dawo cikin rayuwar ka……….,
Datti kam sai girgiza kai yake yi a zuciyan shi yana cewa” kayya!!!!!! bana jin zan kai har zuwa wannan lokacin da zanga baby ta dawo……….
Bayan Usman ya gama dressing na wajen ya duba wristwatch d’in shi ya ga karfe goma sha d’aya na dare yayi saurin sallama da shi ya bar d’akin tare da tabbatar mishi cewa gobe idan zai dawo”.
Bud’e k’ofan da zaiyi ya ga Fu’ad tsaye a gurin hawaye na rolling a fuskar shi hakan ya sa ya tabbatar da cewa ya ji abunda suka fad’a………”
From head to toe ya watsa mishi muguwar harara zuciyar na bashi kamar ya nemo wuk’a ya dab’a mishi………amma sai ya dake yace” Usman  kai ba mosoyin Datti bane…….kai kububuwan macijine………, da ace kai aminine na kwaraiiii maimakon da ka jefa shi cikin wani hali hanya ya kama ta ka nemo yanda zaka yi ka ceto shi daga ramin da ka bada gudumawan ya fad’a ciki……….., kana ganin kayi mishi aldalci, kayi ma iyayen mu adalcin b’oye musu gaskiyar lamari?
Kai butulu ne……..kaci amanar amminci da abota…….kuma Allah ba zai barka ba………., yana gama fad’a ya bangaji kafad’an shi ya wuce ya barshi tsaye baki bud’e galala yana bin bayan shi da kallo, da k’ar ya ja tsummokaran kafafuwan shi yayi gaba.
B’angaren Fu’ad har inda Datti yake kwance ya tsaya a kan shi har yanzu hakayen basu d’aina saukowa akan fuskar shi ba shi hawaye Datti hawaye, k’arfin hali yayi yace” kai d’an uwana duk abunda kayi ba zan so ka kasance a hakan ba amma sai dai ka kasance mai kunnen kashi…….me ribar boye musu gaskiyan da kake yi?
Datti ka rubuta ka ajiye zuma sai da wuta……….., yana gama fad’a ya koma parlour ya bar Datti da zancen zuci yana maimata k’almar “Zuma sai da wuta”. K’almar ta tsaya mishi a rai sosai.
Washe gari kamar yanda Usman yayi alkawari hakan ta kasance sai da ya biya ta gidan ya duba lafiyar shi kafin nan ya koma Office ya hau duba files d’in da ya tarar nurse ta kawo mishi baya ta aje saman table. Tun yana bud’ewa yana fahimtar me files d’in ke d’auke da shi tunanin maganganun da Fu’ad ya fad’a mishi daren jiya ya hau yawo a kan shi yana birkita mishi tunani………daga  k’arshe ma kasa fahimtar komai yayi ba shiri ya rufe gaba d’ayan su ya maida inda ya d’auko su kana ya dunkula hannun shi yana tunani”.
“Gaskiyar Fu’ad ne bai rike abota da hannun biyu ba……..babu abokin da zai yarda ya jefa abokin shi cikin rami maimakon ya samo shi ya fidda shi cikin ramin sai ma ya hau hakar kasa yana watsawa domin ya ciki ramin da yake ciki………,
Duk irin uban sanyin A\Cn da ke ratsa shi bai hana zufa ya k’aryo mishi ba ya ciro hanky a aljihun wandon shi yana gogewa.
” Datti bai cancanci hakan daga gare shi ba……..bayyanar sirrin shine iya adalcin da zai mishi ko da kuwa baya so , kuma ko da kuwa zai zamo k’arshen abotan su da shi kenan.
Da wannan tunanin ya wuni a Office yana yi.

Haka Datti yaci gaba da zama cikin wannan halin a kullu yaumin baya samun barci fama yake da wannan ciwon sosai……., domin wani sa’in ma duk da irin zafin da gaban shi ke yi mishi sha’awar tana damun shi…….baida option haka zai danne pillow da iya kacin karfin shi yana neman biyan bukata……daga k’arshe ma ya fad’a a sume, baya sanin inda kanshi yaks har sai sanyin hunturu ya busu ya shige shi sosai kafin nan ya farfado ya ga yayi ma kanshi illa har, a hakan ma Allah ya taimake shi yana had’awa da azumi da shi ya sa yake samun saukin feelings ba ko yaushe yake ji ba.
Cikin lokaci ya zafge ya rame yayi baki kamar ba shi ba, Fu’ad hankalin shi ya mugun tashi domin shi kad’ai a gidan ya san irin abunda ke damun d’an uwan shi su Umma duk basu sani ba sai dai sunyi mamaki da suka ji kwana biyu wurin shi shiru, amma sai tunanin su ya basu wata k’ila gajiya yayi yayi zuciya ya koma gidan shi.
Aina ma bata wani damu ba tun da rashin ganin shi da bata yi ba………sai dai acikin kwanakin tana jin fad’uwar gaba mai tsanani…….time to time gaban ta sai ya fad’i.
Wata rana da daddare tana barci tayi wani mugun mafarkin da ya d’aga mata hankali wai Datti na ta amman jini yana nuno mata wata yarinya a can nesa da su bata iya ganin fuskar ta, kokarin rarrafawa yake ya kamo yarinyar a duk sanda ya kusa zuwa dafffff da ita sai ta b’ace, duk sanda ya so ya kamo ta baya iyawa gashi jini ta hanci jini ta baki duk ya b’ata mata jiki da shi………., bakin shi ta lura yana motsi kamar yana so yace mata wani abu………sai ta kai kunnen ta kusa da bakin shi tana kuka………kice rokar mini ita……, Na…….,sai ga gudan jini k’ato ya futo mishi ya fetsar idanuwan shi na rufewa a hankali……..ganin haka ta tashi ta runtuma a gude duk yanda ta so ta d’aga k’afa ta kamo ta amma sai ta k’asa, har ta gaji ta hau nishi da kyar tana d’aga k’afa sai ji tayi an Saki salati ta bayan ta da k’arfiiiiii a take awon muryar ya hau yawo a kwakwalar ta………a take tsoro da firgici suka kamata ta juyo da sauri dan ta gane muryar Datti ne………. firgigittttttttt fa farka a barcin ta hau salati tana dube-dube ita kad’ai…..wannan dare bata kuma komawa barcin ba gani take idan ta koma zata tarar ya mutu.
Washe gari wuni tayi jugumm duk an rasa gane kanta banda sunan Datti babu abunda take fad’a…………., ita gida zata koma ta nemo mijinta tana son shi bata so ya mutu ya barta, shine fa hankalin su duk ya tashi Alhaji da kanshi ya d’au key na mota ya nufi gidan  Datti ya tarar k’ofa a garkame mai gadi ya sanar mishi cewa rabon shi da ya ga maigidan da matar gidan har ya manta, ba dan zaman mutunci da suka mishi ba da ya dad’e da barin gidan ya gaji da bauta babu salary.
Da Alhaji ya dawo ya fad’a musu abunda ya faru sai hankalin su ya fi na farko tashi, sunyi sakaci da wauta da har suka yi tunanin yana gida bayan sunfi kowa sannin halin da yake ciki…….kar shima guduwan yayi.
Ummi kam rushewa tayi da kuka dama k’irisss take jira” duk laifin mu ne da muka yi watsi da halin da yaron yake ciki gashi nan shima ya gudu kamar  yanda y’ar uwar shi ta gudu”.
Mardiya kam banda kuka babu abunda take yi ita tafi ganin laifin Umman su fiye da na kowa…..tana sane da hurar da Umma ke yi mishi……..gashi nan ta jawo brother d’inta was no where to be found.
Baba Babba cikin dakiyar zuciya yace” ba kuka ya kamata kiyi ba Ummin Nana………, idan da laifin mu a sakacin b’atan shi shima ai da nashi laifin…….., munfi kowa dacewa ya fad’a mana damuwan shi mu da muke a matsayin iyayen shi amma baiyi hakan ba…….me yasa ba za mu fusata ba”.
“Baba karami zaiyi magana Alhaji yayi saurin dakatar dashi” ya isa hakan yanzu mafita muke nema ta yanda zamu b’ollo wa lamarin, yanzu yaya kuke ganin za’a yi?
Gugum suka yi bai tare da samun mafita ba kowa na bin kowa da kallo.
Suna nan carko-carko a parlourn har wajen k’arfe bakwai na dare ko wannen su sai uban zufa yake had’awa, Usman ne ya shigo gidan a dai-dai wannan lokacin yana ganin su ya sha jinin jikin “shi…….bab….a sannun ku”, ya fad’a cikin inda-inda.
Around takwas da rabi sai ga Usman ya shigo gidan dan ya duba shi sai ganin su yayi ko wannen su hankali a tashe, ba shiri ya ja jinin jikin shi cike da fargaba.
Kallon kurilla suka yi mishi suna mamakin zuwan shi a wannan daren ko dai shima ya samu labarin cewa Datti ya gudu ne……..?
Tsohuwa dai k’irjin ta sai bugu yake fattttt fatttt tana so ta tambaye shi amma tsoron ta kar ace shima Usman d’in bai san inda Dattin  yake ba.
” Don Allah ya Usman kar kace kaima baka san inda yake ba………., bana son ka furta min cewa d’an uwana ya b’ace ba’a san inda yake ba…….., duk a cikin kuka tayi maganar.
“Shiru yayi kamar yana tunani……, ya so ya b’oye musu amma condition d’in da Datti yake ciki ya sa ba zai iya b’oye musu ba cuz he is in a critical condition, Datti bai gudu ba yana nan cikin gidan nan fama yake da rashin lafiya shi yasa baku ganshi ba, ku biyo ni na inda yake, yana fad’a ya haura saman D’akin Fu’ad da sauri suna bin shi a baya.
A kwance suka tarar da shi a kan bed  fuskar shi ya kod’e fatar jikin shi ya koma kamar na mai ciwon Aids, yana had’a ido da su sai ga hawaye babu bakin magana.
Aina ta rushe da gunjin kuka ta rungume shi cikin rashin sa’a garin fad’awa jikin shi ta bata sani ba ace hannun ta ya kai wajen peppered bananar shi ya kwalla k’ara da k’arfi tare da nuno wajen yana yarfe hannu, yaji azaba sosai kamar ranshi zai fita.
Saurin ture ta daga jikin shi Usman yayi……….kunya ce ta sa shi tayi k’asa da kai sai yanzu yaji rashin dacewan abunda yayi………,
Muryar Alhaji yaji yana cewa” me ya same shi a wajen ne yake ihuuuuu haka?
Da murya irin na marar gaskiya yace” Allah baba ku gafarce, na b’oye ban fad’a muku ba cewa Datti na fama da ciwon al’aura kuma ciwon ne ya kwantar da shi ya hana shi fitowa”.
“Whattttt ka san me kake fad’a kuwa?
” Ba tare da ya furta komai ba yayi yunkurin zame bed shit d’in tsohuwa da su Umma suka yi saurin kawar da Ido su baba Karami suna gani sai da suka kad’u, salati suka saki gabaki d’aya dai-dai lokacin Usman ya rufe su Mardiya suka juyo da kan su, sai gani suka yi iyayen maza suna had’a gudu sun rasa ta cewa.
Shigowan Fu’ad kenan ya tarar da abunda ke faruwa, da ya d’au ka ba wani abune mai girma ba sai da ya shigo ya gani da idanuwan shi hankin shi sai ya tashi………, sai yayi nadamar kin fad’a ma iyayen su da yayi, ko da yake ba laifin shi bane hasalima bai tab’a gani ba sai yau, da d’inma maganar su yaji shine ya san cewa Datti baida lafiya amma bai san cewa ciwon yayi tsanani har haka ba.
Fad’a baba Karami yake yi cikin fushi ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ta ciki” yanzu a naku wautan kuna sane da halin da yake ciki shine baku fad’a mana ba? musamman kai Fu’ad ku kwana tare ku tashi tare da mutum yana jin jiki kamar haka baka fad’a a d’auki mataki ba?
” Mugun kallo ya watsa ma Usman a ranshi cewa yake zaka yi baya ni ne, a fili kuwa yace” wallahi baba ban san rashin lafiyar nashi ya kai har hakan ba, ga babban maci amana nan da ya b’oye muku, kuma ya san komai yake binnewa, duk suka bi bayan Usman da kallo.
“Kallon Datti yayi da gefen ido ya ga yana girgiza mishi kai yana ruwan hawaye ma’ana yana warning d’in shi no matter what happen karya sake ya fad’a kawai sai yace” Kaiiiiii  Fu’ad  kaji tsoron Allah me na sani da har zan b’oye musu?
“Da safen nan ina wajen aiki ya bugo min waya ya sanar dani halin da yake ciki shine nayi mishi treatment lokacin sauri nake yi cuz ina da aiki shi yasa ban fad’a muku ba……., ko shigowa na da niyar fad’a muku nashigo da naji kuna tambayana shine na kawo ku inda yake”.
Mamakin irin k’arfin hali na Usman yayi sai ran Fu’ad ya b’aci zuciya ne ya kawo Fu’ad iya wuya yace” Wallahi k’arya kake munafuki, ya san komai boye muku yake son yi!!!!!!!!!!!!
“Baba sirrine rufaffiya wanda ku baku sani ba……….
” Usman Adalcin da zaka yi ma Datti kenan ka fad’a musu………na san shi ya gargad’e ka da hakan shi yasa baka son fad’a……..,idan har Datti ya mutu ka sani kana da laifi mai tsokaa kaima Allah ba zai barka ba………,
Sai jikin Usman yayi sanyi sosai ya juyo yana kallon Datti kayi hak’uri abokina dole na fad’a musu su san komai, daga nan ya kwashe komai ya fad’a musu, da irin shawarar da ya ba ma Datti na aikata barnar da yayi duk ya fad’a musu.
“Sunyi mamaki sosai har ransu basu gamsu da abunda Usman d’in ya fad’a ba, k’ila sun shirya hakan ne dan wani nufi na su amma bari suji daga bakin Datti.
” Datti da gaske ne abunda Usman ya fad’a a kanka?
” Hantar cikin shi ya kad’a, Usman baiyi mishi adalci ba da ya fad’a musu…….., amma ko da zai mutu ba zai tab’a amsa laifin da bakin shi ba, tunda basu da wani hujja da zasu bayar wanda zai tabbatar da hakan.
“Abba ban san komai ba sharri suke min…….,
To kunji yace bai aikata komai ba kuma muma mun yarda da hakan
Shiru Usman yayi dama ya san dole za’a rina ba kowa ne zai yarda da abunda ya fad’a ba haka kuma dole sai ansha daga da Datti wajen fad’ar gaskiya.
Suna cikin hakan ne wani irin wawan ciwon ciki ya turnik’e Datti…….numfashin shi ya hau d’aukewa sama-sama, sai nishin azaba yake yi………..,suka d’ago shi zasu da niyar su kaishi asubiti yace musu a’a ba zai tafi ba……..su barshi a gida kawai rayuwar shi ne ya zo k’arshe, ciwon ajali baya jin magani.
Mata suka rushe da kuka wi-wi da hawaye.
” Fu’ad dai hawaye kawai yake yi……..ko mutuwa ce zata d’auki d’an uwan shi yafi son ya bayyana musu komai zai fi mishi kwanciyan hankali ko da ya mutu ne……………, sai dai Dattin yana da taurin kai yak’i bada had’in kai, gefe ya matsa shi kad’a yana feeling pains kamar an tsoka mashi a kasan zuciyan shi, dole ne ya tursasa d’an uwan shi ya fad’a laifin da ya aikata,
Dole ya bi duk hanyar za zai bi ya cimma burin shi na tursasa mishi fad’an gaskiya ba zai barshi ya mutu a matsayin mai laifi ba……..ta wace hanya zai bi yayi hakan……………

B’angaren Nana yau tun safe bata fito ba tana d’aki sai wajen k’arfe tara na dara taji uban yunwa ya kamata ta fito tana neman abinci.
Har ta d’eba zata koma taji k’afarta ya zungure wani abu………bata sani ba ashe da mutum a parlourn dama yau through babu wuta shi yasa bata gan shi ba.
Tsoro taji zata koma da baya yayi saurin riko hannun ta tun d’azu ya zo yana jiran zuwan ta, Amintacce ne ya bugo mishi waya yace duk halin yaya ya san yanda zaiyi ya kawo mishi amanar shi, gashi damar da yake da shi kenan idan har ya bari ta tafi ba lallai ne ya samu wannan daman ba.
Ihuuuu zata kwala yace” shttttttt nine fa, sai tayi shiru cuz ta gane ashe mutumin nan ne dai.
A masifan ce ta cuno baki kamar yana ganin ta” malam sake ni na koma ko?
“Naji zan barki amma da kin bani lokaci kad’an……..
” Baza ka tab’a samun lokacina ba….har abada ka daina yaudara ta da fake fuskar ka”, ta fizge hannun ta zata shiga.
“Naji na yarda daga yau amma yau d’aya ki bani lokacin ki idan yaso har abada karki sake bani, rashin bani had’in kai a wannan lokacin zai iya haifar da matsala babba.
Ganin yanda ya marairaice mata ya sa tace shikenan na yarda.
” Alfarma nake nema ki bini mu tafi wani waje ni kuma nayi miki alkawarin a cikin daren nan zan sada ki da mahaifan ki……….., karki yi zargin cutar da ke nake son nayi nayi miki alkawarin cewa babu abunda zai same ki.
Ba dan ta yarda ba ta bishi sai dai dan yayi mata alkawarin cewa ba zai cutar da ita ba.
Mota suka shiga ya ja suka bar gidan………, garin babu haske shi yasa bata gane unguwar da suka shiga ba sai ganin ta tayi a wani gida suna isowa yace ta fito.
Cikin gidan ya nufa da ita…….kasancewar akwai solar a gidan shi ya bata daman ganin ko ina sai take jin kamar ta san gidan amma decorations d’in ya banbanta da wanda take tunanin gidan ne.
Har matakalan bene suka taka suna isowa dai-dai bakin wani k’ofa yayi dailing number ya saka wayar a kunnen shi” hello mun iso muna bakin k’ofa……….ka fito please.
Muryar da taji a wayan ne ya tsinkar mata da gaba ta juyo ta aika mishi da kallon shine ko?
Kai ya gyad’a mata ba alamar eehhh ba tare da yace komai ba.
K’arar bud’e k’ofa suka ji Nana ta zuba ido ta ga wanda zai fito, she shocked sosai da fuskar da ta gani a gaban ta,………tunanin  fuskar ne ya fad’o mata a rai, sai yanzu take kanin fuskar tayi matching da wanda take gani a gaban ta……………Mene dalilin wani buri ne yake da shi akan ta da rufe ta a guri d’aya?
Lallai akwai lauje cikin nad’i bata tsammaci ganin wannan fuskar a matsayin ammintacce ba………….

*eedatou*

*💫SHINNING STARS WRITERS ASSOCIATION*

”’The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers.”’

https://m.facebook.com/110896360504039/photos/a.110896457170696/110898470503828/?type=3&source=45

🍇🍇🍇 *UNCLE DATTI*🍇🍇🍇.
”’JIKINA YAKE SO!”’
*WRITER OF*
*1.MAGANIN MATA(DAMUWA)*
*2.WAYE MACUCI?*
*3.RAYUWAR SUMAYYA*
*4.UNCLE DATTI(JIKINA YAKE SO)!*

©
*eedatou✍🏻*
”’Follow and ✅ote me on Wattpad”’: *eedatou*

Masu neman littafin daga farko don Allah ku yi hakuri yawan ku ya sa banzan gama  biya muku bukatu ba duk yawan typing da aikin gidaba zai bari na samu daman tura muku ba.

No comments