Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Zafin Kai 46


46
Koda DD ya shigo kaantes karfe goma Sha Daya,
Parking yayi ya fito Kai tsaye part din dd babban ya nufa inda kusan kowa na gidan Yana can a Palo suna jiran fitowar likitan Dayake Kansa da nurse Daya.

Yana shigowa dukkaninsu suka dawo da kallansu akansa ya qaraso fuskarsa fresh da alaman ya samu isashen hutun Dayake buqata na hayaniya da hidimar yau.

Kai tsaye gurin ummensa dake kallansa cikin nutsuwa da kulawa ya nufa ya tsaya gefenta tareda Dan zagayota da hannunsa Daya Yana Dan babbugawa ahankali alaman komai zai tafi daidai batareda yayi magana ba.

Zaunawa sukai tsawon wasu mintina suna Jira kafin likitan ya fito ya tabbatar musu da dole zasu tafi da dd babban asibiti Koda awanni ne yayi idan ya dawo daidai sai a dawo dashi gida idan Kuma Basu amince ba ya gayyato sauran likitocin asibitinsu suxo a ringa dubasan a gida.

Kai tsaye dad kaante da DD sukace sun amince din Dan haka babu Bata lokaci Akai Kiran ambulance ta asibitinsu akazo aka dauki dd babban Akai asibiti dashi.

Bayan tafiyar dashi DD kaman hannun ummensa yayi ya kaita har cikin bedroom dinta ya zaunar da ita ya fice yabisu Asibitin a motarsa.

Bayan tafiyarsa fitowa tayi ta nufi dakin Zeenah da benazir da Amnah suke ciki harma da Zeenah din.

Zaune suke Bena na bawa Amnah Madara babu kuzari ko walwala a tareda ita.

Zeenah kuwa tana toilet gurin wanka.

Shigowa ummen tayi tana kallan Amnah tace

“Daman tana Shan Madara ne Benazir?

Ahankali benazir din ta Dan gyada Kai cikin sanyi da nutsuwa tace

“Eh madaran Daman kawai take Sha sbd ba ruwan mamah yaqi zuwa.”

Qarasowa gefen gadon Umme tayi cikin damuwa sosai da tausayawa ta zauna tana cewa

“Shine tintina baa fada mana ba da sai ayi wata dabarar da breast milk din zaixo,.Amma gaskia Hakan madaran zallah kawai bazai isheta ba.”

Karbanta ummen tayi tana goge mata baki tissue tana Jin tausayin Amnah din na rashin Nono gashi yanzu har anyi kusan sati uku da haihuwa bare ayi wata dabarar.

Fitowan Zeenah daga wanka yasa ummen kallan benazir dake zaune Kai a qasa tace

“Kiyi hakuri ki kwana a Nan din yau gobe zaa gyara Miki naki dakin ne a canja Miki komai kafin a saka ranar tarewan ki idan kin Dan Saba da Nan din Kuma Dawood din sai yaje Zurich ya dawo saiki tare gaba Daya kinji?

Ki sake jikinki inshallah zakiji Dadin zama damu hakama Amnah.

Ahankali hadiye Wani numfashi Mara qarfi ta Dan dago batareda ta iya kallan ummen ba ta gyada Kai tana Bude baki cikin nutsuwa da sanyi tace

“Nagode.”

Murmush Mai sanyi itama ummen ta saki cikin mutuwan jikin halinda suketa samun kansu aciki.

Miqewa tayi tareda Kwantar da Amnah din zata fice tana cewa

“Zeenah Kinga ga Amnah Nan da benazir kada ki saki ac da yawa sbd benazir na Bata gama jego ba hakama baby Amnah sanyin zai mata yawa ki kula sosai.”

Ficewa tayi tana sake jadaddawa Zeenah wadda taketa cewa to sbd itama tasan bama zata saki ac din sosai ba.

Bayan fitar Umme Zeenah kallan benazir tayi bayan ta gama sauyawa Amnah kaya tayi mata Shirin bacci tace

“Ki Kwantar da ita kema kina buqatan gasa jikinki sbd wannan hidiman dole akwai gajiya.”

Benazir da batasan me zata ce ba hakama bazata iya musantawa sai ta Kwantar da Amnah din ta nufi bayan Zeenah datace ta biyota toilet din ta taimaka mata da sabbin abubuwan amfani.

Duk quncin rayuwar dasuka taso aciki da rashin gata da rufin asiri Allah Bai taba saka musu kwadayin rayuwar datafi karfinsu ba hakama sunada nutsuwarsu a duk inda zasu samu kansu shiyasa data shiga bathroom din Mai kama da wata duniyar daban Bata daga hankali ko Damar da kanta ko Jin tana shaawar tsayawa kallan Abinda yake toilet dinba,wankan ma kasawa tayi ta Saida ta jima sosai tana Kukan data rasa Kona meye kafin tayi wankan ta fito sbd idan batayiba ta fito Kila su baa kwanciya a gidan sai anyi wanka ancire datti komai kankantarsa.

Qaton towel din da Zeenah ta Bata shi ta dauro ta fito jikinta rufe da Wani sbd Bata Saba fitowa ahakan ba.

Koda ta fito Zeenah ta rage hasken dakin sosai Wani qamshi da sanyi kadan ne ya gauraye dakin ni’iman qamshi na ratsa kowane numfashi da zaka ja a hancinka.

Kaya ne Zeenah ta nuna mata Riga da wando masu tsayi da kauri sosai da taushi suna qamshi Mai sanyi tace ta saka.

Karba tayi ba musu ta koma toilet ta Sako ta fito sbd bazata iya tsayawa musawa a rayuwar datasan kaman anriga an siyota ne Dan haka batada Wani zabi bayan yin kusan duk Abinda aka umarceta batareda ta tsaya azabtar da kanta ko batawa Wainda take zamansu lokaci.

Tana sakawa Zeenah ta nuna mata inda zata kwanta babu musu tazo ahankali ta kwanta kaman mara lafiya a rakube ta janyo Amnah cikin jikinta tana rintse idanuwanta tana Jin zuciyarta na Neman karyewa da tinanin a wane hali Anne take ciki a wanna Daren da zata kwanta ita Daya babu ko Daya acikin ‘yayanta.

Zeenah bata jima ba bacci Mai nutsuwa ya dauketa,
Ita kuwa benazir har kusan karfe Biyun dare bacci Bai ziyarci idanuwanta ba sbd radadin rashin sanin halin da Annenta take ciki.

Amnah ce ta motsa daidai karfe uku Dan haka ta tashi zaune ahankali ta sauko gadon jiki ba qarfi ta hada mata Madara da komai da aka aje musu akan bedside.

Madaran ta Bata ta sauya mata pampas harma da Riga sbd sanyin madaran Daya Dan taba rigar kada sanyi ya shigeta.

Tana gamawa ta Kwantar da ita Takoma itama kaman me tsoron kwanciyar ta kwanta tareda rufe Idanuwanta wannan Karan Bata jima ba baccin ya dauketa sama sama.

Rashin baccin datai da wuri ya saka Zeenah kyaleta dataga tasamu baccin sai qarfe 7 ta tada ita tayi sallah.

Zeenah komawa bacci tayi ita Kuma Amnah tasake bawa Madara tanason mata wanka tana jiran Zeenah ta tashi ta Basu ruwan zafi Dan haka ta zauna kan dadduman datai sallah rungume da Amnah data koma bacci itama.

Tana zaune har qarfe Tara na safe lokacin Zeenah ta tashi ta sauko gadon tana kallan benazir din da mamaki tana shafa wuyanta Dan ya Dan sake tace

“Bena a zaune kikai baccin safen ne?”

Girgiza mata Kai benazir din tana cewa

“Ban koma ba Amnah na bawa Madara”

Toilet Zeenah ta wuce tana cewa

“Duk da hakan ya kamata ace kin koma baccin safe sbd samun Qarin lafiya.

Brush tayo ta fito tana kallan benazir dake jiranta tayiwa Amnah wanka.

Komawa sukai ciki ta Tara mata ruwan zafi Dayake Bata Saba ba a roba suke mata a can gida
Itama Kuma Zeenah din kwata kwata batama San ya akewa babys wanka ba Dan haka dole kusan tare sukaiwa Amnah wanka sbd kasawan da benazir tayi ita Daya anan din.

Duka su Biyun sun gama jiqa kayansu Dan haka Zeenah ce ta fito da Amnah tace Benazir din tafara wankan kawai.

Bata jima ba ta gamo wankan da sabulun Zeenah da qamshinsa ya cika toilet din ta fito ta karbi kayan da Zeenah ta miqa mata na wata dagowan Ashape din embellished English super exclusive purple.

Undies data Bata dasu takasa kalla sbd su Basu Saba da panties irin haka ba gajerun wandina suke sakawa Suma hande idan taje siyowa wasu ma kaman na gwanjo,
hakanan ta saka da sauri kada Wani ya shigo dakin saidai rigar sai takejin kaman ta kamata daga saman tinda Bata Saba saka kaya irin Hakan ba.

Tana gamawa ta zauna ta shirya Amnah wadda tafara Kuka tin tanayi a hankali har tafara Yi sosai duk ta rikita benazir din wadda Daman duk a cikin damuwa da rashin kuzari take.

Umme ce ta shigo bedroom din Jin kukan Amnah din Dayake Neman cika koina.

Shigowar Umme ya saka Benazir sunkuyar da kanta qasa cikin sanyin jiki tana sake rufe kanta da dankwalin kayanta tinda Zeenah bata Bata mayafi ba gashi ita batama San Ina aka Kai nata kayan ba bare ta dauko ciki.

Cikin nutsuwa da girmamawa ta Bude baki a hankali ta gaida Umme.

Amsawa ummen tayi cikin kulawa tana cewa

“Meya faru ne?
Kin Bata madaran kuwa?
Ko kun kwana cikin sanyi Mura ya shigeta ne??

Kasa magana benazir tayi sbd batasan me zata ce ba tinda itama batasan me Amnah din kewa Kuka ba.

Kallanta Umme tayi tace sake hada mata madaran ki kawo mugani.

Ficewa tayi dakin da Amnah tana jijjigawa cikin kulawa da kauna.

Rintse idanuwa Benazir tayi sbd kanta Dayake Neman daukan zafi.

Madaran ta hada ta tsaya dakin ta rasa ina zata dosa sbd Bata Saba wannan free rayuwan dasuke tinanin tayi a gidan ba.

Zeenah ce ta kalleta bayan ta saka doguwan riga mara nauyi tace

“Follow me.” Gaba tayi tana latsa wayarta data kunna lokacin benazir ta biyota a baya kaman mara lafiya sbd rashin kuzari da sanyin jiki.

Wani mahaukacin palon Daya gama Jin komai na Jin Dadin da kake buqata a zaman duniya suka fito komai da koina yagama daukan sanyi da qamshin kwanciyar hankali da nutsuwa.

Duk inda ta saka tafin kafarta sanyi ya shigeta sai ta rintse idanuwa ahankali tana qanqame madaran Amnah Dayake hannunta.

Dakin Umme Zeenah ta Isa da ita ta Bude suke shiga Benazir din ta tsaya daga kofa
Zeenah kuwa gurin Ummen ta nufa tana Kiran sunan Amnah dake Kuka har lokacin.

Dagowa Umme tayi ta Kalli benazir din tace

“Qaraso kawo abata mugani idan ba Wani abin yake damunta.”

Takowa tayi ahankali ta qaraso ta tsaya daga gefe ta miqawa Zeenah madaran Umme ta amsa tafara Bata cikin sa’a kuwa ta amsa tanasha da sauri.

Gama Bata Akai Umme ta gyara mata jikinta da kanta ta Kwantar da ita take tayi bacci tana sauke ajiyar zuciya ahankali.

Kusan dukkaninsu ajiyar zuciya suka saukar Suma kafin benazir ta silale ta fito ta Maida kanta dakin Zeenah ta zauna qasa a darare zuciyarta ba Dadi Dan batasan Tayaya zatai rayuwa a Nan dinba Kuma,
Duk da alqawarin data daukanwa Anne na zata Kwantar da hankalinta tayi rayuwa me nutsuwa to Amma ta Ina? Tayaya?.
#MAMUH#
#DBENA
#MARRIAGE

Post a Comment for "Zafin Kai 46"