Zafin Kai 98
*****
Nafisat dake kokarin gama Shirin Amnah takai ta dakin Aunt Zeenah ta kwana acan wayarta tayi haske ta saki Amnah din tana dubawa taga Daddyn Amnah dinne Wanda tinda Bena ta Bata yake Dan kiranta wasu lokutan sbd ‘yarsa yaji lafiyarta kokuma idan tayi bacci sbd zazzabin dare Datake na rashin mamanta.
Amnah ma dake Dan Jin bacci tana ganin sunan daddynta jikin wayar Nafisat taji ta warw
are da murna ta karbe wayar ta dauka tana ambatar sunansa cikin tsananin farin ciki.
Wani kyakyawan murmushin farin ciki ya sake da ajiyan zuciya Yana cewa
“Daddy’s Angel meya hanaki bacci har yanzu?
Cikin farin ciki da tsananin murnan Jin muryansa tace
“Daddy nayita jiran Kiranka ne fa,
Baka kirani ba,
Daddy Kuma bakanan Ina kaje??
Murmyya sake Yi Yana kallan Bena data dago ta kallesa tana Dan sahirtaccen murmurshi farin Jin muryar babynta.
“Angel tafiyan gaggawa ya kamani Kuma na kwanta Dan zazzabi Amma yanzu na ji sauki,and I have a beautiful surprise for you my angel…..
Katsesa tayi cikin tsananin murna itama da cewa
“Daddy Nima inada wonderful news da zan baka me girma da Dadi sosai fa.”
Kallan Bena yayi sbd yasan zata fada masa mummynta ta kirata ne,
“Ok my love Ina Jinki fara fadan naki”
“No daddy sai Ina ganinka zan fada Maka sbd inason ganin naka murnan,ni bakaga nawa ba Amma aunt Z da Umme sun Gani harma da dad kaante.”
Kashe wayar tayi tareda dauko iPad dinta dake kunne Daman tana kokarin saka kiransa nasa Kiran ya shigo da sauri ta koma kan gadon mummynta ta zauna tsakiya tareda dauka take hoton daddynta ya bayyana shi kadai Bena ta koma gefen sumayyah tabarsa.
Bayyanar Amnah kan wayarsa ya saka sumayyah da tin dazu muryanta kawai suke ji zuciyarta ta Dan buga kadan sbd yau ne Karo na farko data ji muryar ‘yar data Haifa.
Hakama yau ne Rana ta farko data ganta a mutum,dazu Bena ta nuna mata hotinansu yanzu Kuma gata suna Kallo tana magana da daddynta cikin farin ciki.
Cikin farin ciki tace
“Daddy ai kace idan mummyna Bata dawoba mutuwa zakayi bazaka iya rayuwa ba ko???
Tsit palon yayi Naseer ya gintse dariyarsa Yana dannewa,
Shi Kansa Bilal da sumayyah D din suka kalla Wanda yayi shiru Yana satar kallan Bena wadda tayi qasa da Kai tana boye nata murmushin itama.
Gyaran murya yayi ahankali kafin yace
“Angel shine news din??
“Aa daddy ka tsaya kaji,
Ai haka kafada ko??
Sake kallan Bena yayi ya dawo da kallansa kan Amnah din yace
“Eh hakane bama na fada bane kawai shine zancen.”
“Yawwa to daddy baka rasa mummyna ba,bazaka mutu ba,. mummy na ta kirani dasu munyi magana da ita zata dawo,
Na fada mata Abinda kake fadamun bazaka iya rayuwa ba mummy ba zaka mutu,itama tace tayi missing naka sosai,tace itama Kaine rayuwanta tana sonka sosai….”
Naseer ne ya katseta da cewa
“Amnah kaante yau babu gaisuwa ko Neman uncle Naseer ba.”
Sai alokacin ta lura da Naseer din ta saki dariyan murnan ganinsa Shima tana Tona masa nasa asirin na soyayyarsa da Aunt Zeenah dinta.
DD kuwa idanuwansa ya zubawa Bena wadda takejin kaman qasan gurin ya Bude ta shige sbd kunya.
Kallan Daya jifanta dashi ya sakata kasa dagowa Saida taji kallan Yana kashe jikinta da yawa ta dago ta Dan kallesa ya kashe mata Ido Daya tareda miqa hannu ya kama nata Yana furta kalman thank you a hankali.
Sbd faranta ranta dole ya nuna mamakinsa da murnarsa sosai Yana Jin Dadin labarin data kawo masan akan Kiran mummynta da aka samu.
Suna gama murna tace masa shi Kuma meye nasa surprise din.
Numfashi ya sauke me sanyi fuskarsa cikeda farin ciki kafin ya miqawa Bena hannu ta kama ahankali ta taso ta dawo gefensa ta zauna tareda kallan Amnah cikeda so da kulawa tace
“My baby.”
Kasa yarda da idanuwanta Amnah tayi sbd tsananin mamaki da murna ta miqe tsaye tana cewa Nafisat tazo tagani.
Dole Nafisat tazo sbd Bata gardama ga duk buqatan Amnah.
“Anty Nafisat duba Mummy na ce tareda Daddyna ko???
Gyada Kai Nafisat tayi cikin mamaki itama tana dauke idanuwanta daga kan wayar.
Wani tsallen ihun murna ta sake Wanda ya saka Zeenah data tinkaro dakin duba shirinsu qarasowa da sauri ta shigo dakin.
Cikin murna da rigima tace wlh ita gurinsu takeso a kaita a Daren.
Zeenah ce ta qaraso da sauri tana kallan screen din iPad din cikin tsananin mamakin ganinsu a tare ta zauna tana nunasu da yatsa tana rasa abin cewa itama ranta fal da farin ciki me tsananin gaske.
Ganin Naseer ma a gurin ya sata sake shuga mamaki ta nunasa da yatsa zatai magana ya daga hannunsa alaman ta yafe masa.
DD ne ya Kalli Amnah Yana rarrashinta da cewa suna Nan dawo gobe ko jibi inshallah.
Rigima takeson Yi Dan haka firar ta koma rarrashi har aka samu ta hakura aka bar zancen sukai sallama cikeda kewa da kaunar ‘yarsu.
Daga Bilal har sumayyah babu Wanda ya iya cewa komai sbd dukkaninsu Basu dauka irin wannan so da kaunar me girman gaske ne ba a tsakanin Amnah dasu DD din ba.
Bayan gama wayar zancen Amnah data Tona asirin zuciyar mamanta ne ya tsaya a zuciyarsa Yana yawo bayan kallanta babu Abinda yakeyi sbd Wani sanyi da Dadin tareda farin ciki sosai kalaman suka sanyaya zuciyarsa,
Idan wannan yanayin Dayake ji Dan yaji daga bakin Amnah ne to Yaya zeji idan kalaman Kai tsaye daga bakinta ne ta furta masa su?.
Tin bayan gama wayar shi nasa jikin da kalmomi suka qare bayan kallan Bena Dayakeyi a natse cikin sanyi hannunta na cikin nasa babu Abinda yakeyi.
Ita kanta Satan kallansa takeyi Akai Akai fuskarta dauke da murmushi da farin cikin da zuciyarta ke ciki akan zancen nasa asirin zuciyar itama dataji akanta.
Naseer da Bilal ne kawai masu magana sai can sama sama ya Dan jefa kalma Daya a qataice har suka jima sosai.
Sai 12 da mintina suka fito har mota D ya Brown skin wife dinsa kaman yanda yake fada hannunsa na riqe da nata.
Hannunta yayi kissing a hankali tareda musu Saida safe ta shige motar ya rufe mata duka wuce ya juya zuwa ciki Yana dawo da kallansa kan Naseer Yana tayar da maganarsa da Zeenah da Amnah ta Tona.
Su Bilal kuwa Koda suka Isa gida daga momyn Abdul har Anne sun Dade da Nisa a bacci Dan haka Suma kowa dakinsa ya nufa.
Bena na shiga dakinta babu Abinda tayi bayan fitsari tazo ta kwanta sbd already Daman tayi komai na baccinta zata kwanta suka fita,
Kuma kayan baccine a jikinta Daman Dan haka tayi kwanciyarta da rigarsa a jikinta bayan qamshinsa babu Abinda take shaqa daga jikinta Dana rigar hakama zuciyarta cike da farin ciki da sanyi tayi bacci me Dadi.
Shi Kansa DD kayansa kawai ya sauya zuwa kayan bacci masu Dan kauri ya Haye gadonsa ya kwanta ransa sanyaye da nutsuwa.
ADVERT
*_REALTASTE 247 CATERING SERVICES_*
*_ASLM ALAIKM_*
*_Yan uwa abokan arziki yan gayu masu bikin alfarma na manyan mutane da son fita kunyar kowane kalar luxury abincin larabawa da qasashen qetare, kuzo ga number 1 best catering services damuke dashi a arewa,_*
*_REALTASTE 247 CATERING SERVICES shine best Abinda muke buqata a gurin hidimar biki da duka Wani occasions na girma da tsari tareda fita kunya indai gurin girki masu tsafta da tsarin ne tareda verities masu dadi,_*
Bikin aure
Bikin haihuwa
Bikin birthday
Picnics
Parties
Walima
Receptions
Hatta a cikin gidanka idan baka buqatan girki zakai ordern abinci daga garesu a kawo Maka har gida cikin tsari da burgewa.
Hakama kalolin abincinsu da services dinsu sun hada da;
Indian biryani rice
Mandy rice
Chinese fried rice
Stir fried spagetti
Chinese noodles
Fried rice
Party jollop rice
Chicken kebab
Beef kebab
Grilled chicken
Chicken cutlet
Kafta
Shredded sauce
Salads
Hatta bangaren snacks masu kyau da dandano da tsari babu Wanda basayi muku kalan Wanda ranka yakeso.
Realtaste 247catering services
08034425662
Instagram@Realtaste 247 catering services
Location:kano,Kaduna and Abuja.
Ga masu buqata su tuntubemu a 08034425662
Mungode.
Karku bari ayi babu ku.
Washe gari Anne Bata damu ko gangancin tambayan yaushe suka dawo ba sbd zuwa lokacin a qanqanin kwana Biyun ta Dan fara fahimtar rayuwar sakewa da yanci tareda Abinda kaga dama akeyi a gidan ba takurawa,hakama ‘yayan nata kowacce tare ne take da mijinta Dan haka ba amfanin daga hankali ko shiga fargaba,ga Momyn Abdul tana iya kokarinta gurin fahimtar da ita rayuwar mutane masu kwanciyar hankali da wadatacciyar da Kuma yanda rayuwar duniyar mutane suke sabanin wadda sukai su a baya kaman dabbobi karkashin Ababa.
Breakfast sukai dukkaninsu a dining Banda Anne data zabi zamanta a daki tayi nata sbd ita dai Bata sakewa da yanda Bilal ke bin sumayyah da Kallo duk motsin kadan,
Kunya da nauyin abin takeji Dan haka take Dan nesanta kanta dasu yanzu,danma Batada gurin zuwa kokuma kowa bayansu,
Sune danginta sune komai nata harshi Bilal din Wanda takejinsa har ranta shi da mijin Bena wadda haryanzu ko Gaisawa ma Basuyiba tukuna sbd baayi haduwar da nutsuwar gaisuwar zataxo ba.
Suna gama breakfast dakin Anne taje ta kira dd babba dake son magana da ita ta Bata wayar sukai magana sosai a bakinsa takejin komai Daya faru Shima ya boye mata cewan Safnah kishiyar Bena datai duka wainna abubuwan Safnah ce ‘yarta sbd fadan baida amfani,tinda kullum tanawa Safnah da sameerah adduar samun rahaman ubangiji gwara a tafi a Hakan ko Safnan ta samu sassauci daga Allah.
Bayan gama maganarsu da dd babba Umme suka kira itama sun jima sosai suna gaisawa da Annen kafin suka tsaya kan Amnah da Zeenah da sun Dade suna magana kafin sukai sallama.
Shiru Anne tayi sbd Jin rasuwar hande da yanda tazo mata abin beyi mata Dadi ba Dan haka tabita da adduar samun hasken kabari, Ababa kuwa adduar samun lfy kawai tayi masa sbd basatan me zatace akansa ba.
Bena kuwa fitowa tayi ta nufi kitchen bayan tayi wanka ranar su uku ne a kitchen itada momyn Abdul suna sake nunawa sumayyah abubuwa da yawa kafin sukai girkin Rana cikin kwanciyar hankali suka gama.
Momyn Abdul ce ta jera komai a dining sukuma dakunansu suka wuce Dan sake wanka da sallar azahar da Akai suna Aiki.
Wanka tayi ta fito tafara yin sallah kafin ta shafa body oil na Neutrogena sama sama kafin ta shirya cikin Riga da skirt na atampa ta zauna tana duba sakonsa Daya shigo wayarsa cewan Yana hanyar isowa gidan.
Murmushi kawai tayi kafin ta fito taje ta sanar da Anne D Yana hanyar zuwa ze gaisheta.
Shiru Anne tayi tana kallan Bena kafin tace
“Kinsan fa mijinki sumayyah tace bature ne baya Wani Gane hausar sosai nikuma kinsan bansan ya zamu gaisa din ba.”
Kallan sumayyahn Bena tayi tana cewa
“Anne kyaleta harda sharri a zancenta Amma ai Yasan yanda zaku gaisa lfiya kalau fa.”
Dariya sumayyah tayi sbd ita kanta da dubara kawai take Dan magana da DD din sbd baturen gaske ne ba komai yake ganewa yanda su suke ganewanba.
Suna isowa Ashe tare suke da Bilal Dan haka Bilal ne yayi masa jagora har dakin Anne dake zaune da hijabinta data gama sallah tana kan dadduma zaune Bena na gefenta bakin gado zaune.
Suna shigowa akan Bena idanuwansa suka fara sauka take yaji Yana Neman rasa seti
Ta dauke kallanta daga Kansa sbd tana kallansa ze iya kwafsawa gaban Anne Dan haka taqi yarda ta juyo gefensa duk da tanajin idanuwansa akanta.
Zaunawa sukai ahankali ya dawo da kallansa kan Anne cikin tsananin girmamawa da kulawa yanajin sonta sbd Bena na tsananin sonta ya gaisheta Yana tambayarta lafiyanta.
Anne data batasan batada lafiya ba Yana tambayarta lafiyarta binsa kawai tayi da lafiya kalau taji sauki,
Fira Bilal ya fara mata Yana mata bayanin wasu abubuwan akan DD din tana amsawa cikin nutsuwa da Jin dadi shikuwa idanuwansa Akai Akai suna kan Bena daga karshe kasa hakuri yayi gaban Annen ya kira sunanta tareda tambayarta lafiyanta itama.
Anne dai shiru tayi Bata iya cewa komaiba saima rudewa Datake Neman Yi daga sauraren Bilal Wanda Shima Neman rudewa da nasa bayanin Dayake korowa yakeyi sbd DD din gaba Daya ba ruwansa komai nasa da gaskiayrsa yake yinsa baya boyen munafurci.
##MAMUH#
*_REALTASTE 247 CATERING SERVICES_*
*_ASLM ALAIKM_*
*_Yan uwa abokan arziki yan gayu masu bikin alfarma na manyan mutane da son fita kunyar kowane kalar luxury abincin larabawa da qasashen qetare, kuzo ga number 1 best catering services damuke dashi a arewa,_*
*_REALTASTE 247 CATERING SERVICES shine best Abinda muke buqata a gurin hidimar biki da duka Wani occasions na girma da tsari tareda fita kunya indai gurin girki masu tsafta da tsarin ne tareda verities masu dadi,_*
Bikin aure
Bikin haihuwa
Bikin birthday
Picnics
Parties
Walima
Receptions
Hatta a cikin gidanka idan baka buqatan girki zakai ordern abinci daga garesu a kawo Maka har gida cikin tsari da burgewa.
Hakama kalolin abincinsu da services dinsu sun hada da;
Indian biryani rice
Mandy rice
Chinese fried rice
Stir fried spagetti
Chinese noodles
Fried rice
Party jollop rice
Chicken kebab
Beef kebab
Grilled chicken
Chicken cutlet
Kafta
Shredded sauce
Salads
Hatta bangaren snacks masu kyau da dandano da tsari babu Wanda basayi muku kalan Wanda ranka yakeso.
Realtaste 247catering services
08034425662
Instagram@Realtaste 247 catering services
Location:kano,Kaduna and Abuja.
Ga masu buqata su tuntubemu a 08034425662
Mungode.
Karku bari ayi babu ku.
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Post a Comment for "Zafin Kai 98"