Breaking News

Amatulmaleek 79

 79

*INA MATA,MANYAN MATA,MATAN DASUKA SAN KANSU,MATA MASU DARAJA,MATA MASU BUQATAN GYARA DA KULAWA DA KANSU???*


*SHIN KUNSAN SHAHARARRIYAR ME MAGANIN KUSAN DUKA MATSALOLIN MATA DASUKE FAMA DASU HARMA DA WASU DAGA CIKIN NA MAZAN WATO MEERAH HERBS* 100% Natural herbs💯🔥👍

*Amarya,budurwa,uwargida,bazawara da duk ma macenda take buqtaan gyara da ingantattun kaya karki wuce kayan Meerah Herbs sbd mun tabbatarda ingancinsu kafin tallata muku💯👍*


MAGANIN SANYI 

MAGANIN NONO 

MAGANIN HIPS 

MAGANIN SLIMMING 

MAGANIN NANKARWA

GYARAN AMARE

SET MAIJEGO

MALLAKA 

SUBULU DA MAYUKA NA GYARAN JIKI

TURAREN WUTA

MATSI

MAGANIN NI'IMA

BACK TO VIRGIN SET

INFECTION FLUSHER


08142800199

07068558096*************

Amatu na fitowa wanka a natse ta zauna ta goge jikinta tareda Shafa Mai da turare ta Saka Riga da wando na bacci masu santsi da tsada ta Saka huka mara nauyi ta ziro slippers ta fito Dan Jin shiru gidan da Kuma ruwan datake buqata ta Bude kofar dakin ta fito tana Jin qamshin dayake shiga hancinta Yana Sakata mamakin jinsa sbd tasan bame yiyu bane Jin wannan qamshin a gidan nan Kuma a daidai wannan lokacin.


Tsakiyan palon take sake kusantowa tareda Bude Baki cikin sautin muryanta me nutsuwa ta qwalla kira Kiran Karima.Tinda ta ya jiya Karan Bude kofar bedroom da rufewa ya dago kansa a natse ya zubawa hanyar dayaji motsin idanuwansa Dake galabaice da buqatan ganinta harta fito daga hanyar bedroom din tana shigowa palon dakyau idanuwansa akan cikinsu Dayake gabanta ya koma Yana Jin Yana sake macewa akanta kowane lokaci da zai ringa Dora idanuwansa akanta.


Bata lura dashi ba Saida ta kawo kusan gab dashi idanuwanta suka sauka akansa cikin sauri ta tsaya cak tareda yar razana sbd Bata taba tinani ko tsammanin ganinsa ba Tako Ina a gidan.


Juyawa tayi ta Kalli kofar kitchen tareda kallan hanyar bedroom din anty Farha kafin ta Dake Dan janyewa gefe daga gabansa tana dauke kallanta akansa shikuma Yana sake zurfafa nasa kallan akanta tareda miqa hannunsa Daya cikin sanyi da nutsuwa yayi mata sallama Yana sake miqa mata hannun idanuwansa akanta.


Bata Kalli hannun ba ta Dan koma gefe daga nesa kadan dashi ta zauna a natse tareda dagowa ta gaidasa kaman yanda take gaidasa a Baya Babu sakewa Babu alaman sabo ko wata shaquwa da kulawa.


Hannunsa data bari a gurin kaman ma Bata Gani ba ya kalla tareda dawo da hannun Yana kallanta ya amsa gaisuwar tareda tasowa ya dawo inda take ya zaune sosai jikinsu na haduwa ya kamo hannunta Daya a sanyaye ya Bude Baki yace


"Girman laifin Ashraf yakai har haka ne?

Hukunci Zaki masa?

Ba Zaki sassauta ba ko kadan ne?


Hannunta Daya kama ta zare ahankali cikin nutsuwa batareda ta dago ta kallesaba ta girgiza masa Kai kawai ahankali alaman ba komai datakewa fushin.


Tsayawa yayi kallanta sbd gaba Daya ma taqi kallansa hakama taqi nuna fushin nata ko bacin ran nata yasan yanda zai Bata hakurin ya rarrasheta.


Miqewa tayi tana kokarin tafiya kitchen ta dauko abinda ya fito da ita ta koma daki,tana taku Daya ya riqo hannunta tareda sauke numfashi da ajiyan zuciyan masu sanyi jikinsa na mutuwa ya miqe tsaye a hankali ya dawo gabanta ya tsaya cikin kulawa ya janyota jikinsa tareda ya Bude Baki da Wani irin sauti mara hayaniya ya furta


"m sorry"


Rintse idanuwanta tayi ahankali tana Jin radadin zuciyarta na raguwa sedai Kuma batajin zata iya barin ya Ragu din tinawa da quncin data shiga akan shariyarsa.


Sai data Dan sauke numfashi a zuciyarta kafin ta dago idanuwanta masu rudasa ta kallesa cikin sanyinta kafin ta janye jikinta gaba Daya tana Dan dauke idanuwan nata akansa ta Bude Baki tace meyasa yake cewa sorry ita Babu komai fa daya mata.


Hakan data fada ya sakashi sake shiga damuwa Dan maganan yakeso suyi Amma tana toshe masa hanya.


Kitchen ta juya ta tafi ta dauko ruwanta ta fito har lokacin Yana tsaye hanyar dakinta take kokarin nufa ya sake takowa ya kamo hannunta tareda rungumota ta Baya cikin sanyi yace


"Please LA""


Shiru tayi batace komaiba 

Ya sake zagayota da hannuwansa Yana fora hannuwansa akan cikinta Yana shafawa Yana Jin kaman ya Bude kirjinsa ya Sakata cikin zuciyarsa ko zuciyan ta samu sassaucin azaban Sonta take ji.


Ajiyan zuciya ya sauke hannunsa na kan cikin a sanyaye tace


"ASH is really sorry"


Hannunta ta Dora akan hannunsa ahankali Wanda Hakan ya Sakasa Jin sanyi da Wani irin nutsuwa sedai kafin ya Bude idanuwansa yaji ta janye hannunsa daga cikin nata tana janyewa gaba Daya daga jikinsa ta juyo batareda ta kallesa ba ta sake maimaita masa ba komai ya Dena damuwa da maganar.


Wannan Karan kusan abinda yake ranta na fushi ya Dan bayyana tareda hawayen da suka ciko idanuwanta masu radadi duk yanda taso dannewa da boyewa.

Ganin fushin datai Yana son bayyanar masa ya Sakata wucewa kawai bedroom dinta ta shige ta rufo kofar sbd batason yasan tana cikin quncin abinda ya mata Dan Bata buqatan basa Daman wanke kansa.


Hanyar data bi ya zubawa idanuwansa da suka sauya take sbd ganin hawayen Idanuwanta sun rikita masa lissafi.


Baya keta iyakar da Bata kamata ba da Babu abinda zai hanasa shiga dakin ya sameta Amma ba gidansa bane ko da tana matarsa bazai iya shiga kuryan ba.


Zaunawa yayi cikin tareda daukan wayarsa yana Sake Kiran wayarta Amma taqi dagawa Dan haka ya rubuta mata Sako Amma still ba reply ba motsinta.


Shiru yayi kansa na daukan nauyi kaman yanda zuciyarsa tayi nauyin.


Bazai iya sanin zaman awa nawa yayi ba a palon har sai da su anty Farha suka dawo itama anty Farha din tayi mamakin ganinsa shi Daya a palon Dan haka suna shigowa ficewa kawai yayi.


Yana fitowa harabar gida mr Jameel Dake tsaye kaman an dasashi a inda yake sbd abinda Farha ta masa Yama rasa inda zai Saka ransa,

Kallansa ASH yayi da idanuwansa da sukai Dan ja Shima ASH din ya dago ya kalla da nasa idanuwan kowannensu na kokarin boye damuwarsa.


Sai da safe Mr Jameel yayiwa ASH din bayan sun shiru kowa ya rasa abin fada.


Mota ASH din yaja yabar gidan ya kama hanyar gida.


Mr Jameel ma tada tasa motar yayi ya nufi gida.


ASH na Isa gidan Kai tsaye shigewa bangarensa yayi Daman Kuma dare yayi tinda kusan goma ta wuce.Husnah da daddaren Haydar ne yazo da kansa suka ci abinci tare sbd idan ba Wani ya tsayu akanta ba ba lallai ta iya cin abincin ba sbd har lokacin tana cikin damuwa da sanyin jiki.


Maamah kuwa Abdul ne yaci da ita mum Aisha kuwa da aka sallamo tana daki a rufe Babu Wanda yasan halin datake ciki.


Su kawu kuwa a matse suke da su koma kauye amarci kawai suke Jira su fara darza.Bayan ficewan ASH anty Farha dakin Amatu ta nufa Kai tsaye ta Bude tana ambatar sunanta ta ganta zaune tsakiyan gadonta idanuwanta sunyi jajir da alama kuka tayi sosai sbd Radadin abubuwan da suka dawo mata na wahalan datasha a wannan Dan lokacin da ciki.


Qarasowa anty Farha tayi tana rarrashinta tareda Bata hakuri akan ASH din ta sauko Hakan tinda yace ayi hakurin.


Shiru kawai Amatun tayi sbd haryanxu bataji zuciyarta ta sassauto akansa ba.


Hakanan anty Farha tayi rarrashinta da ban hakurin ta fito ta wuce dakinta 

Ita Kuma kwantawa tayi duk da baccinta ya qaurace tin dazun.Washe gari da zazzabi Amatun ta tashi sbd kukan datai da daddaren dakuma rashin samun baccin Daren Dan haka ko data tashi sai ciwon Kai yazo kafin daga baya zazzabin.


Dr beeba anty Farha ta kira sai gashi Dr beeba din Tai kira Mr Jameel ta sanar masa sbd ASH ya Bada umarnin komai Daya danganci Amatu da cikinsa ya ringa sanin komai koma Menene.


Ganin ba shine ya kirata akan taxo Amatun ba lafiya ba yasa ta kira ta sanar kafin ta tafi din.


Mr Jameel na Jin Hakan ya taho mansion din Dan dama Yana Shirin tafiya can dinne sbd su kawu dasu mum Aisha da zasu wuce Yola.


Yana isowa kusan komai na tafiyansu ya kammala su kawu har sun fito mum Aisha da maamah ma kusan duk sun fito lafiyayyar motar mansion dince zata kaisu Yola.


Mum Aisha jiran kawai takeyi su Isa yolan subar Nan ko kallanta kawu ashiru yayi saita Saka Yan Sanda sun makantar dashi Dan kudinsa na sadaki harda qari Mai yawa zata basa ya saki auren ya qara gaba.


Maamah kuwa abinda ta sani shine zata koma gida ne ta zauna Amma ba Wani zaman auren da zatai da kawu bello sbd tasan ko gurin Sakata baidashi.


Husnah tayi kuka sosai na tafiyan maamah din hankalinta ya tashi ta yanda zata zauna ita Daya a gidan yanzu ba kowa.


Yanda ta daga hankalinta ne Haydar yace su shirya gaba Daya su rakasu maamah din Yola su biyo jirgi gobe su dawo.


Dayake Daman da Abdul zaa tafi tin farko sai tafiyar ta qara yawa Jin su Haydar dinma zasu tafi.


Mr Jameel ya sanar da ASH Dr beeba ta sanar da Amatu ba lafiya Dan haka bayan sun fito yayi sallama da su tareda sallaman su kawu da abinda ya wuce tinaninsu suka ringa Godia hakama su mum Aisha da maamah sanyi jikinsu yayi da sabbin motocin Daya Basu kowaccensu daddaya bayan yasan a kauye zasu zauna Ina gurin bin mota ma bare Janta.


Har lokacin Husnah a tsorace take da Dad din nata ta kasa zuwa inda yake duk da ta zama matar Abdul idan ba ganin tayi su uzaifa sun bar gidan ba hankalinta baa kwance yake ba.


Shine ya fara ficewa mansion din tareda Mr Jameel dayake jansa zuwa gidan Farha.


Shiru sukai Mr Jameel na drivern yanason ya tambaya Yaya ake rarrashin mace ta sauko daga fushi a gurin Mr Jameel Amma Kuma dai ya fuske ya kame batareda ya tambayar ba zai sake gwada sa'arsa yau yagani idan little Abeedan zata sauko.


Suna Isa Dr beeba ta riga ta Isa tana gidan Dan haka anty Farha ce da kanta ta fito tayiwa ASH din jagora bayan ta gaidasa cikin girmamawa batareda ta Kalli ko inda Mr Jameel yake ba tareda su.


Suna shiga palon Dr beeba na fitowa daga dakin tareda gaida ASH tayi masa bayanin ba Wani matsala bane kawai rashin hutun bacci ne da yar damuwa wadda ya kamata ace ta cire daga ranta koma ta Menene.


Shiru yayi tareda yiwa Dr beeba din godiya a taqaice kafin ya Kalli dakin anty Farha tayi saurin yi masa ison Isa dakin duba Amatun sbd bazata Wani iya fitowa ba.

##MAMUH#*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee 

And

*_YANCI DA RAYUWA_*

By Hafsat Rano 

Na kudi ne

For more page ku biya

500 for littafi Daya

1k for duka books din biyu

 at👇

0022419171 access bank Maryam sani

09033181070

No comments