Breaking News

Auren Shehu Book 1 Page 10

Khadija Sidi

 

Cikin daji mai suna santali wanda ya ke arewa moso gabashin mararrabar Nigeria da Nijar ne Rugar Shehu su ka yada zango. Babu laifi akwai ruwa da ‘yayan itatuwa wadatacce hakan ya sanya su jimawa a dajin. Rugar Shehu ba su da wani yare face


fulatanci, ka?an daga cikin jama’ar rugar wanda su ke fita suna cudanya da hausawa ne ke jin hausa.

Babu laifi mahaifina ya yi aure aure da yawa, duk a dalilin neman magaji kasancewar duka matan sa ‘ya’ya mata su ke haifa masa wanda da sun kai shekara goma sha uku zuwa sha biyar ake mu su aure. Sai da ya haifi ‘ya’ya Ashirin duka mata, har ya fitar da rai dan kuwa shekaru sun ja ya bawa arbain baya, sannan Allah ya amsa masa ya azurta matar sa ta hudu wacce dama ita ta fi kuwa karancin shekaru da haihuwar da namiji.

Murna gun mahaifina ba a magana dan har kyautar shanu biyu mace da namiji yayiwa unguwar zoma da ta karbi haihuwar. In da mahaifina ke murna samun magaji, Dan uwan shi wanda ya ke cikin ummansa, shi maihaifina ya sha nono ya bar ma, babban abin bakin ciki ya zame masa dan kuwa ya ci burin kujerar da mahaifina ke kai, rashin magajin mahaifina shi ne babban takobin da ya rike.

Kamar yanda Baffa Mudi ke bakin cikin jaririn da aka haifa, haka ma sauran matan gidan su ka nuna bakin ciki karara, dan sam babu wacce ke hubbasa wajan taimakawa mai jego, haka ta yi jegon ta sai dai ‘ya’yan ta mata ko kuwa dai mokota su agaza mata, idan kuwa an ga sauran matan kusa to lalle mahaifina ke kusa, ana yi ne dan ganin idanun sa. Haka a daddafe sati ya zagayo, ranar suna aka sanya min suna Usman, mahaifina ke kira na “Magaji” wannan kalma ta zamo tamkar wuka a kirjin Kawu Mudi.

Baffa Mudi ne dan uwa daya tilo da su ke ciki daya da Mahaifina, su biyu kacal Mahaifin su ya haifa a duniya. Matar Baffa Mudi daya, haihuwar matar shi goma sai dai biyar daga ciki sun rasu, biyar kadai ke a raya, duka mata ne. Bayan an haife ni da sati biyu matar Baffa Mudi ma ta haifi dan ta namiji, yaro ya ci sunan Mahaifina amma ana kiransa da Tanko.

Gata da soyayya karara da mahaifina ke nuna min ba karamin bakin jini ya jawowa Iya ta da ni kai na ba. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, ana jifa da surkulle domin halaka mu, Allah kuma na kare mu.

Tun kafin na cika shekara biyu a duniya na yaye kai na na ki nono, Wanda hakan ya nunawa Iya ta alamun cikin da ta ke dauke da shi. Murna gun mahaifina ba a cewa komai, shi dai fatan sa Allah ya maimaita a haifa ma sa da namiji. Cikin da Iya ta ke dauke da shi ya sanya Mahaifina dakatar da canza shekar da ake da niyar yi duk da kuwa ruwa da kayan itatuwa sun ja baya. Wannan ya bawa Baffa Mudi damar yiwa mahaifina zagwan kasa ta hanyar hore mu su kunne akan wannan hukuncin da mahaifina ya dauka saboda a cewar shi hakan na nuna rashin adalcin Shehun rugar. Da ya ke jama’ar rugar Shehu amintattu ne, kalilan ne su ka dauki zugan Baffa Mudi dan haka hakan sa bai cimma ruwa ba, Nan dajin Santali Iya ta ta sake haifo dan ta namiji, da mako ya zagayo aka sanya masa Muhammadu Bello.

Sai da Bello ya dan yi kwari sannan aka tasanma barin dajin Santali, nan mu ka niki gari, mu ka hada kwan mu da kwarkwatar mu, mu ka shigo Nigeria, mu na tafe muna tare da shanun mu su na kiwo, duk in da dare ya mana mu yada zango. Duk yanda mu ka so kiyaye shanun mu kar su shiga gona, yau da gobe sai sun shiga, dan haka ko da yaushe cikin fada mu ke da manoma, wani sa’in har a kai da bata kashi. A haka Allah ya isar da mu wani yanki da ke cikin kungurmin dajin falgore. Bayan dube dube da Maihaifina yayi na surkulle ya ce a kafa bukkar rugar Shehu a nan dajin. Cikin sati daya aka kafe dajin nan kaf ya zama babu mahalukin da ya isa ya dumfari rugar Shehu da kowani barna ko mugun nufi.

Toh rayuwar ruga dai haka mu ke yin ta, babu wutan lantarki, babu asibiti, babu makaranta babu ko wani irin taimako daga gwamnati dan kuwa idan ba dai wani tarzoma ta hado mu da manoma ba gwamnati ba ta waiwayan mu bare ta ba mu agaji, dan haka ban san wani abu wai shi boko ba. Ina da shekara hudu a duniya matar Baffa Mudi ta kara haihuwa, ta haifi diya mace wacce aka sa mata suna Ummakaltime, ana kiran ta Cangwai.

Kasancewar mahaifina shi ne Shehun rugar dama shi ke koyar da yara da samarin ruga karatu wanda ya hada da kur’ani, littafan addini, sai kuma rubutu da karatun ajami. Soyayyar da ke tsakanin mu, da Kuma ganin ni ne magajin shi wanda ya ke sa ran zan zama shehu ya sanya shi ya fara ba ni ilimin surkulle tun ina dan shekara takwas a duniya, duk yanda ya so ya jawo Bello jiki a koyar da mu tare hakan ya gagara saboda lalurar bebantaka da ta sami Bello sanda ya na da shekaru biyar a duniya.

Ba na manta ranar ta kasance wata juma’a ne aka tashi da rashin ladanin Rugar Shehu, bayan an masa sutura, aka kai shi kushewa aka rufe mu ka dawo gida mu tadda Bello na ta kurari da kuka, juyin duniyar nan an yi ya fadi abin da ke damun shi, amma ya gagara sai dai gwalangwalanto, wanda hakan shi ne karshen maganar sa kenan duniya.

Sanda na cika shekara goma na fara kora shanu nawa na kai na, Mahaifina ya ba ni mace da namiji wanda su ke aure, cikin shekaru kalilan su ka hayayyafa sosai Allah ya albarkaci kiwo na sai gani da shanu har guda koma, sanda na cika shekara shabiyar a duniya shanu na tuni sun kai ishirin.

Ba yaban kai ba, tarbiya da kuma yanayin karatu da na ke samu daga wajan Mahaifina ya sa na fita daban daga sauran matasan rugar mu, idan ka dauke Baffa Mudi da iyalan sa babu wanda ba ya girmama ni a rugar Shehu. Sam ba ma ga miciji da Tanko dan Baffa Mudi, dan kuwa yayi kauran suna wajan fiti na da neman fadan manoma, hakan nan babu gyara babu dalili ya ke kora shanu cikin gona su yi barna su bata amfanin gona ba dan komai ba sai dan neman fitina. Da ta fara fitinar mutane ne Mahaifina ya Umarci Baffa Mudi da yayi wa Tanko magana, ko dai ya canza hali, ko kuwa ya bar masa rugar baki daya. Maganar da ta kara kawo rashin jituwa tsakani na da Tanko kenan, har ta kai ba ya amsa sallama idan na masa.

Idan kuwa batun amana ne sau dayawa jama’ar rugar Shehu na bani amanar Shanun su duk sanda su ke da uzuri, cewar su duk rugar Shehu ni kadai zan kora shanun jama’a na kiyaye mu su kamar yanda zan kora nawa, kafin ka ce menene tuni na kasance kamar mataimaki gurin Mahaifina wanda shekaru sun ja sosai, hidimomi da dama ba ya iya yi, duk yanda Baffa ya so ya ja ragamar shehuntakar kuma Mahaifina ya ki sakar masa, sai dai ya sanya na wakilce shi, cewar sa tunda ina da nutsuwa zaifi na fara gwada mulki tun ya na raye.

Ba zan manta da wata ranar labara ba, lokacin ina da shekara goma sha bakwai, na dawo daga kiwo Mahaifina ke fada min shawarar da su ka yanke na daura min taubashiyata, daya daga cikin ‘ya’yan Baffa Mudi, wato Cangwai. Cangwai dai yarinya ce mai hankali da nutsuwa, wajan kyawu ma babu laifi, idan aka dauke kiyayyar da mahaifin ta ya ke min sam bata da laifi, dan haka na yi na’am tare da godiya da wannan hadin.

Iya ta kuwa nunawa ta yi sam ba ta yarda da wannan hadin ba, a cewar ta ba hadin alkhairi ba ne, yanda Baffa Mudi ba ya kaunar mu me zai sa ya so ya kulla wannan kulli haka? Sai da rai ya baci sosai tsakanin ta da Mahaifina, ni na zaunar da ita, na nusar da ita ce komai nufi ne na Allah, muddin ba ma nufin kowa da sharri to kuwa Allah ba zai bari a jefo mu da sharri ba, ta kwantar da hankalin ta, khairan in Sha Allah.

Da haka da haka aka daura min Cangwai. Daya daga cikin bukkokin da ke wajen gidan Shehu mu ka tare cikin yarda Allah. Bayan sati daya da auren mu Cangwai ta fara laulayi, Iya ta ce ta fara lura da cikin da ta ke dauke da shi, za ta yi surutun yayi wuri na ce da ita babu komai ni da iyali na mun yi tarayya tun a daran fari, dan haka ba wani abu ba ne dan ta na dauke da juna biyu.

Abu dai kamar wasa cikin kankanin lokaci cikin Cangwai ya bayyana sosai, Ni kai na na kanyi mamakin shin watanni nawa da auren mu da har abu zai fito sarari haka kamar kwarya? Gashi mu ba asibiti ba bare bokan ture ya duba ya fada min adadin watannin cikin.

Dangantakar mu ya sanya ban yi kokarin neman warware wannan sarkakkiyar ba, na rufa asiri mu ka zauna haka, ko da wasa ban taba nuna mata wani damuwa ko bambamci ba, ina kula da ita kwatankwacin yanda na ke ganin Mahaifina ke kula da Iya ta, sai ita ce ma da na ga kamar ta na cikin damuwa, duk sanda na so na ji dalilin ta kan ce min babu komai.

Iyar ta kullum ta na hanyar gidan mu, haka ma Baffa Mudi, ni kuwa sam ban taba kawo wani abu cikin rai na ba. Cikin wannan halin mu ka kai wata shida tare da Cangwai. Wata ranar lahadi da daddare na dawo daga hirar dare na tarar Cangwai ba ta bukkar mu, na yi tsammanin ta zagaya bayan gida, ni kuwa dama na debo gajiya sai na yi kwance bisa gadon karar mu bacci na diba na sama sama

Ban yi cikakken minti goma da kwanciyar ba kamar daga sama na ke jiyo muryar su, a bakin kofar bukkar na ji mahaifiyar Cangwai na tambayar yaushe zan dawo. Cangwai ta ba ta amsar da sai can cikin dare ai wajan hira na je, Bukkar su ka shigo, Cangwai na niyar kunna futular acibalbal Iyatar ta ce ta bari saboda ba ta san jama’ar gidan su san da zuwan ta.

Ina shirin mu su gyaran murya dan su san da ni kenan na ji Iyar Cangwai ta ce

“Ba dai ki tona mana asiri ba ko?”

Mutuwar zaune na yi jin amsa Cangwai na cewa

“Ah ah Iya, Amma wallahi a tsorace na ke, gani na ke kamar fa ya san ba cikin shi ba ne, dama Baba ya sani ya bari sai da na zo gidan na sami cikin halak, ai ya fi……”

Wani irin zufa na ji ya na keto min, Ashe dai duk yanda na so kar na zargi baiwar Allah nan ashe hainta ta su ka yi. Babban abin taikaici shi ne amsar da iyar ta ta bata, cewar ta

“Ke yiwa mutane shiru! Wa ya ce mi ki Baban na ki ya na so ki haifa masa jika da wannan la’anan nan yaron? Ko kin manta dalilin da ya sa ki ka tare da sangami har ya mi ki ciki?”

“Sangami”

na maimaita cikin rai na, Sangami na daya daga cikin fitattun matasan da ke wata ruga kusa da rugar Shehu, mahaifin sa yayi suna kwarai wajan tarin shanu, haka kuma abokin fitinar Tanko ne. Iyar Cangwai ba ta gushe ba ta kara da

“Kar ki manta yarjejeniyar da aka yi tsakanin Mahaifin Sangami da na ki, na farko dai ki samu ki haife dan nan, wannan wawan mijin na ki da Shehu su gama azazzabin samin magaji, sai a sheka su barzau, kin ga kenan burin Mahaifinki na zama Shehu ya tabbata, ke kuwa mu aurar da ke ga Sangami, tare da bawa baban shi rabin shanun rugar Shehu kamar yanda aka yi alkawarin matukar ya taimaka aka dauke Shehu da magajin su daga doran kasa, shi wancan beben dan na sa da mu ka lakasa tun shekarun baya be Isa ya aiwatar da komai ba, ina Bebe zai iya shehuntakar ruga? Ina ya ga bakin magana?…..”

“Usman mutumin kirki ne Iya, ba ki ga yanda ke mutunta ni ba, ya na kula da ni…..”

Cewar Cangwai cikin nuna damuwa, cikin hantara Iyar ta ta ce

“Ke rufawa mutane baki! Ko dai kin fara son shi ne?”

“Ah ah”

“Toh idan kin fara sai ki zaba ko shi ko uban ki! Dama abin da ya kawo ni kenan! Na ja kunnan ki! Sakarya kawai na ji kin tona mana asiri uban ki ne a rana ai”

“Zan kiyaye!”

Da wannan Iyar Cangwai ta tafi, Cangwai ta fita ta dan taka mata. Jiki sanyaye na tashi zaune, dan tashin hankali na ma rasa abin yi bare na motsa. Zuciyar ta daya ta dawo, ashanar da na mata tsaraba da shi sanda na fita kiwo ta kesta haske ya gwauraya daki hakan ya bata damar ganina zaune na doka tagumi fuska fal zufa kamar wanda ke zaune gaban wuta.

A razane ta ke dubana yayinda jikin ta ya dau kyarma, saura kirin ta wulgar da acibalbal din da ke rike a hannun ta Allah ya sa na tashi da sauri na riko shi. Gefe in da mu ka saba ajiyar shi na aje. Ina mai bata baya dan sam ba na kaunar ganin ta, na ce

“Me ku ka yi ku ka nakasa kanina Bello?”

Murya na rawa da alama ta fara kuka ta amsa min da cewa

“Dan Allah kar ka tona min asiri, ka rufawa Mahaifina asiri na maka alkawarin kare lafiyar ka da mahifin ka….”

“Ba wannan na tambaye ki ba!”

Na katse ta cikin tsawa, juyowa na yi na karasa gaban ta, hannaye na biyu bisa kafadar ta ina mai jijjiga ta ba tare da na yi la’akari da tsohon cikin da ta ke dauke da shi ba na ce

“Me ku ka yiwa kanina ya dena magana?
Ko ki fada min ko na halaka ki da cikin shegen da ki ke dauke da shi nan take kafin na je na riske azzalumin uban na ki”

Yanda ta ga na rikide cikin kankanin lokaci ya sanya ta kara tsorata da lafazan da ke futowa daga baki na, tana kuka ta ke fadin

“Lokacin da abin ya faru ina da karancin shekaru, Amma dai na san surkullen da aka yi masa da tare da gawa aka hada aka birne, yanda gawar ba za ta kara magana a duniya ba, haka shi ma Bello ba zai sake magana a duniya…….”

Tas na dauke ta da mari kafin ta kai da karasa maganar ta, ta yi baya sauran kiris ta fada na riko ta da sauri cikin danasanin marin ta da na yi, dan kuwa tun da na zo duniya ban taba dukan wata diya mace ba, face Cangwai.

“Dan Allah ka yafe min, kada ka halaka ni, zan hade kaya na, na bar rugar Shehu ba zan sake dawowa ba har abada”

Takaici ya sa na kasa magana, kallan ta na ke cike da tsana karara cikin idona. Mun kai kusan minti biyar cikin wannan halin kafin na sake ta, rai na na kuna fice da bar mata Bukkar gaba daya gudun halin zuciya.

Bukkar Mahaifina na nufa, ganin babu alamar haske ya sanya na sake shawara, na juya na fice ba tare da na dubi bukkar Iya ta ba, dan kuwa ba na jin zan iya tunkarar ta da wannan maganar ta tashin hankali cikin dare haka. Can turkar shanu na na je, Nan na kwana amma ban runtsa ba, yanda na ga rana haka na ga dare, sai da asuba ta yi sannan bacci ya fara dauka ta, ban kai ga runtsawa ba korarin Bello da ya zo ya na tashi na ne ya katse min baccin.

Yanda ya ke maganar ya na mai nuni izuwa gida ya sanya ni kara tsanar Baffa Mudi, kiri kiri ya nakasa yaro karamin dan kawai san mulki da san zuciya, ban san sanda na fara zubar da hawaye ba, shi kuwa Bello da yayi tunanin sakon da ya isar min ne ya sa ni hawaye tuni ya fara kokarin lallashina, ya na mai dafa kafada ta, kafin daga bisani ya fara jan hannu na.

Sai a sannan na fahimta lalle akai wani abun tashin hankali da ke faruwa a gida, da sauri na tashi, ko silifa ban saka ba. Bello na janye da hannu na mu ka isa gida. Mutane ne fal bakin kofar gidan wasu na alwala wasu kuma tabarma su ke shimfidawa, ganin Baffa zaune dirshen a kasa ga Tanko gefe ya na matsar kwalla, jama’a na ta min sannu da sai hakuri ya sanya na karasa cikin gidan da sauri.

Cikin gidan ma tashin hankali na tarar, kuka da kurarin mata ne ke tashi, haka ina tsallake mata na isa ga bukkar Iya ta, Nan na iyi idu biyu da gawar Cangwai kwance, gefe kuwa Iya ta ce ri?e da jinjirar da ta haifa, cikin dare rai yayi halin sa bayan ta haifi diyar ta mace. Kalaman Cangwai ke dawo min sanda ta ke rokan karda na halaka ta, za ta hade kayan ta tabar Rugar Shehu ba za ta sake dawowa ba, ?ana sanin barin ta ita kadai da tsohon ciki ya mamaye ni, haka tsananin tsanan Baffa Mudi da shi kan sa mulkin da ya ke kwadayi har ya kai ga saka diyar shi cikin halak.

Bayan an shirya Cangwai ana shirin a fito da ita, sai ga Baffa Mudi ya shigo, ya nemi a bar masa gawar zai gana da ita kafin a fito da ita. Tun da ya kebe da gawar hankali na ya kasa kwanciya. Ya dan jima ciki kafin ya fito ya ce za a iya fito da ita.

Hankali na ya kasa kwanciya dan haka, kafin a kai da fito da ita na ce da su su dakata, Iyar Cangwai ta ce ban isa ba, tun dazu me ya hana na zo na mu yi sallamar karshe sai yanzu? Iya ta da sauran kishiyoyin ta ne su ka sa baki, haka ba a san ran Iyar Cangwai ba na shiga dakin. Ranar na yi abin da ban taba tsammanin zan iya ba, Yanda gaba na ke faduwa da hawayen da ke kwaranya daga idanuna be sa na fasa kunce suturar da aka yiwa Cangwai ba, hannun ta na hagu na yi arba da wani abu dunkule an daure shi da bakin kyalle, na yi sauri na sunce, daga waje ina jiyo Iyar ta na kuka da kururuwan na ki fitowa a tafi a rufe Cangwai.

Cikin azama na tura abun cikin wandan saki na, hakan yayi daidai da shigowar Iya ta, ganin na bude Cangwai ta hau ni da fada, tare da taimakon ta mu ka yi sauri mu ka rufe ta, cikin kankanin lokaci aka sallace ta, mu ka je aka rufe ta.

Cikin dare na sami Iya ta zaune dakin ta rike da jinjirar da Cangwai ta bari, ganina ta yi yunkurin bani yarinyar, Amma na ki karba. Hakan ba karamin tunzura Iya ta yayi ba, a zatan ta zafin mutuwar Cangwai ya sa na tsani jinjirar da ta bari. Nan kuwa kwashe komai na sheda mata, har da abinda aka kunsa hannun gawar Cangwai.

Mamaki da takaici ne ya rufe iya ta, kuka ta ke cike da takaicin zaluncin da aka yiwa Bello. Tare mu ka kunce abin da na ciro daga hannun gawar Cangwai, laya ce mai dauke da sunana da sunan baro baro da rubutun ajimi, an rubuta

“Kamar yanda gawar nan ta bar duniya, haka za ka bace a doran kasa Usman , kamar yanda wanan gawar ta ba za ta taba shakar iskar duniya ba, haka kai ma na za ka taba zama Shehun Rugar Shehu ba Usman”

Ko da na gama karantawa Iya ta ba karamin tashin hankali da rudani ta shiga ba, da kyar na samu na kwantar mata da hankali, na kuma umarce ta da kar ta shedawa Mahaifina halin da ake ciki, ta bari mu sami mafita a tsakanin mu, dan kuwa halin da Baffa Mudi ya nuna zai aikata komai dan ya cima burin shi na san rai da san duniya.

A wannan daren Iya ta ta yanke hukuncin da ya sa yayi sanadin bari na gida har na ke zaune tare da ku a yau, Iya ta ta umarce ni da na sakarwa Baffa Mudi Shehuntakar Rugar Shehu, ta Umarce ni da tunda a nashi tunanin ya birne gawar diyar sa da surkullen watsa ni uwa duniya, matukar ya ga ban tafi ba zai fahimci asirin sa ya tonu, ya kuma cigaba da kulla zalunci har ya kai ga cin nasara, da na bi uwa duniya ba a cikin hayyaci ba, gwara na tafi da niyar neman ilimi, dan haka ta na so na hada kaya na, na shiga arewacin Nigeria, duk gidan da na ga Malami na tabbatar na nemi ilimi daga gare shi, haka kuma duk sanda na canza sheka na sami hanyar sanar da ita ko da kuwa hakan ya na nufin ziyartar ta ta shigar batda kama, ita kuma muddin ta san in da na ke za ta turo min Bello duk sanda bukatar haka ya taso. Ina ji ina gani haka ta hade kaya na, ba tare da na yiwa Mahaifina sallama ba na baro Rugar Shehu na shiga uwa duniya…”

Usman ya nisa, ya na mai duba Malam ya kara da

“Hakan ba karamin ciwo ya yiwa Mahaifina ba, a tunanin shi mutuwar Cangwai ya sa na bi uwa duniya, tun ya na cigiya har ya sadakar ya fawwalawa Allah. Shekara goma sha biyu kenan da barin Rugar Shehu, kamar yanda Iya ta ta umarce ni, na kan ziyarce ta duk sanda na sami dama cikin bat da kama, haka kuma duk in da na ke tana da masaniya akai, ina barin mata bayanin wajan a rubuce, ta kan aiko Bello duk sanda bukatar haka ta taso. Allah yayiwa Mahaifina rasuwa bayan shekara uku da barin Rugar, yanzu haka Baffa Mudi ne Shehun Rugar”

Usman ya kare maganar cikin kewar Iyar sa da bakin cikin mahaifin sa ba tare da sun samu sun gana ba. Gaba daya falon babu wanda be tausayawa Usman ba, Musammam Halitta wacce har hawaye ta zubar saboda hakan. Cikin jimami Malam ya nisa ya ce

“Da farko dai ina ma ka ta’aziyar rashin mahaifin ka, da kuma matar ka. Ba kai kadai ka ci amana ta ba, hatta yar ciki na ta ci amana ta, idan kuwa haka ne na yafe ma ka duniya da lahira……”

Karar wayar Malam ne ya katse maganar da ya ke, ko da Malam ya duba ya ga makocin sa kuma daya daga cikin amintattun abokan sa ne Alhaji Sidi, ya daga wayar, bayan sun gaisa ya ce da shi ya jira ana zuwa. Bayan da ya aje wayar ya umarci Jauro ya je ya budewa Alhaji Sidi gate, ya shigo da shi ciki. Cikin himma Jauro ya fita, in da Malam ya dakata da jawabin shi har lokacin da Jauro ya shigo biye da shi Alhaji Sidi tafe.

Alhaji Sidi na mai bawa Malam hannu yayinda ya zauna kusa da Malam ya ke tambayar abin da ke faruwa cikin al’ajabi, Da safiyar nan ya ji dan sa ya shigo da wani labari hakan nan babu dadin ji, wai an kama wata yarinya ta na haurowa daga gidan Malam, shin menene gaskiyar maganar?

Murmushin yake ne ya maye fuskar Malam, hannun sa cikin na Alhaji Sidi ya ce

“Zan ma ka bayani Alhaji Sidi, Amma kafin nan na ji dadin zuwan ka har rai na, domin kuwa ina da bukatar shedu, zuwan ka ya cika min shedun na ke bukata”

“Shedu? Na me kuma Malam?”

Alhaji Sidi ya tamabaya cike da mamaki.

“Kar ka damu Alhaji, a sannu za ka fahimci komai, ina kai Usman matso nan kusa da ni”

Cikin shakku Usman ya taso ya zauna gaban Malam in da ya nuna masa. Malam na mai dafa kafadar sa ya ce

“Usman a daren jiya ka yi min abinda babu wani mahaluki da ya taba yi min cikin duniyar nan, ka rufa min asirin da diyar cikina ta so tona min a duniya, ba zan yi butulci akan jarabawar Allah ba, Allah ya jarabci annabin sa, annabi Nuhu AS ta hanyar dan sa, sa bare ni da ba ko wan kowa ba, Amma akwai alfarma daya da na ke so ka min….”

Ya karasa maganar ya na mai duban Usman. Cikin girmamawa da kaskantar da kai Usman ya ce

“Malam duk abinda ka ke so ni mai yi maka ne, wanda ya ba ka ilimi nan duniya ai ya ma ka komai”

Cikin jin dadin amasar da Usman ya ba shi Malam ya ce

“Ina so ka taimaka ka auri diya ta Zainab…”

A firgice Usman ya dago ya kalli Malam, haka ma Halitta da su Ammy, gaba daya falon babu wanda be girgiza da maganar Malam ba, Zainab kuwa ji ta yi gaba daya dodon kunnan ta ya toshe tsabagen yanda maganar ta doki kunnan ta. Cikin in’ina Usman ya furta

“Ma…l..am”

Alhaji Sidi kuwa mamaki ne ya sanya shi furta

“Me ke faruwa haka? Wata Zainab ka ke nufi ne haka?”

“Diya ta ta ciki na, ka ga wannan bawan Allah da ke zaune gaba na? Shi ne kadai zai iya rayuwar aure da waccar yarinyar asiri na ya rufu, dan kuwa ya rufa min asiri a yau fiye da tunanin ka! Wannan dalilin ya sa na yanke hukuncin daura ma sa ita ta zame masa halak malak ko mutuwa na yi na san na fita hakkin ta”

Jin haka tuni Zainab ta fashe da kuka mai tsuma zuciya, fadi ta ke

“Dan Allah Dady ka yafe min kar ka yanke wannan danyan hukuncin a kai na, dan Allah Ammy ki sa baki, dan Allah Halitta ku taimaka min, Alhaji ku sa baki”

Hawaye ke zuba daga idanun Halitta daya na bin daya, kiri kiri ta na ganin mahaifin ta na shirin mata yankar kauna tsakanin ta da masoyi abin kaunar ta. Cike da kishi Jauro ke duban Usman, da ya san Malam zai yanke hukuncin haka da shi ma ya ce Zainab matar shi ce, yanzu gashi Usman da ya zo ya tarar da su cikin gidan ya sami garabasa kara zube.

“Malam dan Allah kada ka yanke hukunci cikin gaggawa haka, Yakura jinin ka ce, kada ka bata rayuwar Yakura”

Ammy ce ke magana cikin magiya. Idan Malam ya ji Ammy toh sam be nuna alamun da shi ta ke ba. Ya na duban Usman ya ce

“Kai na ke tsimayi Usman, shin ka karba? Za ka iya auren diya ta?”

A hankali ya daga idanu ya kai kallan sa ga Zainab wacce ta ke kuka mai fitar da sauti, har ga Allah be taba jin wani abu na so game da ita ba, bare yayi tunanin aure zai shiga tsakanin su. Yanda ta ke kallan sa ne ya sa shi saurin kau da kai gefe

“Usman?”

Malam ya kira sunan sa da kakkausar murya.

“Na’am Malam, na yarda na amince, sai dai matsalar abu biyu ne”

“Ina sauraran ka Usman”

“Banda kudin sadaki, haka kuma banda muhallin da zan iya aje mata Malam”

Jin haka Malam ya dara tare da fadin

“In dai wannan ne matsalar ka toh Alhamdulillah, na tabbatar ka haddace Riyaadul Saliheen?”

Cike da girmamawa ya gyada kai alamar eh.

“Toh Alhamdulillah, na yanke maka wannan littafin a matsayin sadakin Zainab, ina so ka koyar da ita wannan littafai, batun muhalli kuma ga BQ nan babu kowa da ciki, zan sa a gyara maka ku zauna, Allah bashi idan ka yi na ka sai ku tashi ku koma can ko?”

Baki bude Ammy ta ke duban Malam har ya kare jawabin sa, ba ta taba tunanin Malam zai iya kaiwa matuka wajan wulakanta ta da yaran ta ba sa sai a yanzu.

“Innalillahi wainnailaihi rajiun yau! Innalillahi wainnailaihi rajiun! Innalillahi wainnailaihi rajiun!”

Salatin da Zainab ke yi kenan cikin kuka, dan kuwa ji ta ke kamar rayuwar ta ce ta zo karshe. Halitta ma kukan ta ke haka ma Falmat wacce tausayin yar uwar ta ya maye zuciyar ta. Alhaji Sidi na mai gyaran murya ya ce

“Malam ran ka a bace ya ke, ka tuna yanke hukunci cikin fushi…..”

Hannu Malam ya daga masa, ganin haka Alhaji Sidi yayi shiru. Kana Malam ya ce

“Malam Usman dama kai namiji ne, kai kan ka mai kar?a ma kanka aure ne a kaidar shari’a ka isa ka karbarwa kan ka aure, ga shedu uku nan, Jauro, Isa da kuma abokina Alhaji Sidi, dan haka idan ka shirya sai a hanzar ta a daura auren ko?”

Kai Usman ya gyada abun ya zo masa kamar almara. Haka kuwa Zainab ta na ji ta na gani Malam ya daura mata aure da Usman, akan sa dakin koyar da ita littafin Riyaadul saliheen. Ana shafa fatiha Zainab ta zube mu su nan sumammiya.Auren Shehu

No comments