Breaking News

Auren Shehu Book 1 Page 13

Auren Shehu

13

Da taimakon direban da ya kai Ammy Wanda dawowar sa kenan aka sa Malam cikin mota.

“Ba mu san me ya same shi ba, mun tarar da shi kwance a bandaki cikin wanan hali da ku ka gan shi yanzu, diyar sa ta fadi sunan asibitin da za a kai shi, wani turanci ne wallahi ya kwanta min”


Cewar Usman wanda shi ke zaune bayan mota, kan Malam kwance bisa kafarsa, ya na maganar ne cikin kokarin tuna asibitin da Halitta ta fada masa.

“Toh ai zaifi wata daga cikin iyalan na shi su fito a tafi asibitin da su, Hajiya ba ta nan ne?”

Daya daga cikin daliban Malam ne ya tambaya cike da damuwa.

“Eh haka zai fi, Hajiya ba ta nan, bari a kira daya daga cikin ‘ya’yan na sa”

Usman ya fada ya na mai duban Jauro da Isa da niyar daya daga cikin su ya taimaka ya kira su Halitta. Ganin haka Jaura ya kada baki ya ce

“Dan cirani wannan kuma ai aikin ne kai da ka ke sirikin gidan, mu masu gadi ina mu ina shiga gida haka? Maza shiga ka kirawo matar ka a tafi”

Wani mugun kallo da Usman ya harbi Jauro da shi ya sanya shi saurin wucewa ciki ya na fadin

“Toh ni jan idan ka me zai min, dan ka zama surikin Malam ba zai ba ka lasisin aikan mutane kamar yaran ka ba, ka dai ci darajar masu daraja!”

Maganganun da Jauro ya ke ne ya dan ja hankalin wasu daka cikin daliban Malam har suna musayar kallan juna, dama suna da labarin abin da ya faru daren jiya. Idan Usman ya damu da lafazan jauro sam be nuna ba, kallan Malam ya ke ya na fadin

“Sannu Malam, Allah ya ba ka lafiya, Allah ya ma ka afuwa”

Jim kadan Jauro ya dawo Halitta biye da shi, hijabin da ta saka tare da nikabin da ta saka be boye hawayen da ke zuba daga idanun ta ba dan kuwa har ya dan jika nikabin.

“Matar ta ka ta ki fitowa sai kanwar ka”

Cewar Jauro ya na mai nuna halin ko in kula da kallan da Isa ya bi shi da shi. Cikin azama Halitta ta shiga gaban mota ta na mai rufo kofa, direba wanda dama shi ma tuni ya zauna a nashi guri ya sakawa mota key, Isa da sauran dalibai suna mai yiwa Malam addua aka rufowa Usman kofa. Tuni Jauro ya bude gate, direba na mai tashin mota cikin gaggawa su ka dauki hanyar asibiti.

Tun da su ka dauki hanyar asibiti Halitta ke gwada numbar Ammy duk sanda ta kira amsa daya nakurar ke bata, na
‘numbar da ta kira a kashe ta ke, ta sake gwadawa anjima’

Har su ka kusa isa asibiti ba ta sami numbar Ammy ba, sai na kanwar Ammy wacce ita ma din Kano ta ke aure. Bayan Halitta ta sheda mata abin da ke faruwa na game da rashin lafiyar Malam ta tambaya ko Ammy ta je gidan ta? Cike da mamaki da damuwa ta ce ba ta je ba, a tambayi direban da ya tafi ina ya kai ta, sai a sannan wannan azancin ya zo wa Halitta. Bayan ta aje wayar ta ke tambayar direba ina ya aje Ammy? Direba ya ce shi dai tasha ya aje ta.

Isar su asibiti likitan da ke duti ya mu su karbar gaggawa ta hanyar sawa Malam robar shakar numfashi ta hanci da baki, sannan aka kwantar da Malam kan gadon da ke offishin sa. Halitta kadai ya amincewa zaman Office din sa’ilin da ya gama duba Malam ya ke tambayar ta ko ya shiga matsanincin damu ne? Allah ya takaita da ya fadi wani bangare na jikin sa be dena aiki ba, Halitta ta amsa da “uhum” kawai ba tare da ta iya ba shi cikakken amsa ba.

Sai da aka samu jikin Malam ya dan lafa sannan aka mayar da shi dakin kwantar da masu jinya, Amma har lokacin robar bada taimakon numfashi ne a bakin sa. Usman na mai duban Halitta ya furta

“Shin kin sanarwa Hajiya kuwa?”

Kai ta girgiza masa, murya dashe tsabagen kukan da ta sha ta amsa da

“Wayar ta ba ya shiga, kuma ban san in da ta je ba bare na kira su”

Shiru ne ya biyo baya na wani dan lokaci, daga bisani ya nisa tare da fadin

“Dare na yi, ina ga zai fi a mayar da ke gida ko? In ya so kya dawo da safe kila kafin nan an sami Hajiya….”

“Ni ah ah nan zan kwana gun Dady”

Halitta ta katse shi cikin nuna kafiya. Usman na kallan ta cike da tausayi ya sake fadin

“Ki yi hakuri ki tafi, jinyar namiji sai namiji, ba za ki iya…..”

“Ba namiji ba ne, Dady na ne fa!”
Ta fada ta na mai fashewa da kuka. Shiru ya mata na wani dan lokaci, har ta yi kukan ta ta gama. Sai ji ta yi ya na kiran direba, cike da umarni ya ce da direba

“Maza ka mayar da ita gida….”

“Ni ba zan je ba ai na fada…”
“Shhhhh za ki je yanzu ma kuwa…”

Yanda yayi maganar ne cikin ba da umarni ya sa da ga Halitta har Direba tsayawa su na duban shi, ganin haka ya dan sassauta murya tare da fadin

“Malam ba zai ji dadi ba idan har ki ka zauna a nan, kuma kin ga ai farin ciki da samun lafiyar shi ki ke fata ko?”

Kai ta gyada masa kamar karamar yarinyar. Cikin rarrashi ya furta

“Yauwa diyar halak, Allah ya mi ki albarka. Yanzu sai ki tashi ku tafi ko?”

Ga mamakin Direba sai ga Halitta ta tashi, bayan ta sake duban Malam, ta kalli Usman ta ce

“Ka kulan min da shi, Zan dawo da safe”

“In Sha Allah”
Ya amsa mata a takaice. Hakan nan ba a san ran ta ba su ka bar asibitin. A hanya ta yanke hukuncin kiran yayar babbar Malam Hajja Dudu wacce dama ta san da auren Zainab da Maigadi da Malam ya daura. Nan ta fada mata halin da ake ciki na rashin lafiyar Malam, tare da tafiyar Ammy. Ta na mai salati da sallalmi ta yiwa Halitta alkawarin baro Maiduguri da asubar fari.

Da misalin karfe goma Halitta ta isa gida, ta tarar da Falmat zaune cikin zulumi, ganin ta taso da sauri ta na tambayar jikin Malam. Halitta ta amsa mata da sauki, ko ta sami Ammy a waya? Falmat ta ce ba ta same ta ba, Amma bari ta sake tambayar Zainab. Ta wuce dakin Zainab ganin ta yi dai dai ta na baccin ta cikin kwanciyar hankali da ke dama akwai bashin bacci kan ta ya sanya Falmat dawowa falo, Amma ta kasa fadawa Halitta Zainab din bacci ta ke, ta yi karya Zainab din ma ta ce ba ta same ta ba.

Iya ce ta shigo jin sun dawo, ita ma tun tafiyar su Halitta asibiti ta ke zaman jiran su. Bayan ta tambayi jikin Malam, tare da ko an sami Ammy ne ta yiwa Halitta tayin abinci, Halitta ta ce mata ta koshi sam bakin ta ba dandano. Da haka ta shige dakin ta, alwala ta yi ta yi sallar ishai tare da yiwa Malam addua, Allah ya kawo sauki cikin lamarin sa.

Washagari da sassafe Halitta da Falmat su ka nufi asibiti, Zainab kyememe ta ki bin su cewar ta ba ta so ta je ta ga wannan dan Boko haram din da Malam ya ce ya daura mata aure da shi. Sai da su ka isa sannan Usman ya tafi ya bar Malam tare da su Halitta da direba. Jikin Malam kam a iya cewa da sauki na bahaushe amma har lokacin ya na jin jiki, haka kuma be fara magana ba bare ma ya ci abincin da Halitta ta girka masa.

Kamar wasa Halitta ta gwada wayar Ammy sai gashi ta shiga, ta na kuka ta ke fadin

“Ammy kin tafi kin bar mu ga Dady nan kwance a asibiti rai a hannun mai duka….”

Salati Ammy ta ke yi daga dayan bangaran, cike da damuwa ta ke tambayar me ya faru? Me ya sami Malam? Nan Halitta ta kwashe komai ta fada mata, ta kare da

“Dan Allah Ammy ki tausaya mana ki dawo..”

Ammy wacce jikin ta ya gama sanyi ta yiwa Halitta alkawarin dawowa da sun isa Yobe, dan kuwa ta na hanyar Maiduguri amma sun kusa isa Yobe. Da wannan su ka yi sallama. Halitta ba ta jima da aje wayar Ammy ba sai ga Hajja Dudu, tare Uwargidan Malam Hajja Kilishi, sai kuma babban dan Malam wanda ake kira Gana. Tun asubar fari su ka dau hanyar Kano.

Ganin halin da Malam ya ke ciki tuni Hajja Kilishi ta fashe da kuka ta na mai tambayar musabbabin halin da Malam ke ciki. Daga Halitta har Falmat ba su so zuwan Hajja Kilishi ba, dan kuwa sun san ran Ammy ba karamin baci zai yi ba muddin ta zo ta tarar da ita.

Haka su ka wuni a asibiti, an samu Malam ya fara magana sama sama haka kuma ya dan ci abinci. Da yamma Usman ya dawo, ganin dakin Malam cike, ciki har da Zainab wacce tun ta hango sa ta ke watsa masa harara ya sa yayi jim kamar zai koma. Halitta ce ta masa iso ta hanyar fadin
“Usman shigo mana, ya za ka koma”

Cike da yar kunya ya shigo, ya tsugunna har kasa ya gaishe da Hajja Kilishi da Hajja Dudu. Su ka amsa ba yabo ba fallasa, Gana ya bashi hannun su ka gaisa. Hajja Dudu ce ta tambayi Halitta ko wanene Usman. Kafin Halitta ta ba da amsa Zainab ta yi carab ta ce

“Maigadin mu ne”

Gudun kar Halitta ta fadi dangantakar auratayya da Malam ya kulla tsakanin su, Nan kuwa ba ta san labari ya riga ya iske mu su. Maganar da Hajja Kilishi ta yi ne ya tabbatar mu su da hakan na cewa

“Ko shi ne sirikin namu mijin Zainab?”

Ras! Gaban Zainab ya fada, ta na mai dauke kai ta hadiyi yawun bakin ciki.

“Eh shi ne”

Cewar Halitta wacce amsar da ta bawa Hajja Kilishi ya mata nauyi matuka a baki, ta na mai danne kishin da ya taso mata ta kara da

“Shi ne ma ya kwana da Dady jiya”

Dukan su kallan Usman su ke, kan sa ke sunkuye. Jin amsar da Halitta ta ba su ya sanya ya dan dago kai ya na mai duban Zainab ta wutsiyar idanu. Ganin haka ya sanya Zainab watsa masa harara cike da tarin tsana.

“Allah sarki, sannu Allah ya ma ka albarka, ba a banza Malam ya ba ka auren diyar sa ba, ka cika dan halas, yanda ka rufa mana asiri Allah ya rufa na ka duniya da lahira”

Cewar Hajja Dudu wacce tun shigowar Usman ta yaba da hankali sa. Zainab kuwa ji ta ke kamar ta tashi ta fita a guje tsabagen tsanar Usman da ta yi. Jin Usman ya mu su sallama ya ce zai koma tunda Gana ya na nan ne ya sa Zainab dan samin sauki cikin ran ta.

Bayan tafiyar shi su ka shiga tattauna auren Zainab, in da Gana ke nuna rashin dacewar auren a nashi ganin auren zai iya zama wani barna maimakon gyara a rayuwar Zainab, in aka yi la’akari da yanayin wayewar Zainab da kuma ilimin ta. Ya ce zai yiwa Malam magana a san yanda za a yi a warware wannan aure tun kafin ya haddasa wata matsalar gaba. Maganar ba karamin dadi ta yiwa Zainab ba, duk da dai Hajja Dudu da Hajja Kilishi sun nuna rashin goyan baya akan hakan.

Sai dab da magrib Ammy ta iso dauke da akwatin ta, dan ko gida ba ta je ba bare ta ji labarin zuwan su Hajja Kilishi wanda ganin ta ba karamin bakan ta mata rai yayi ba. Ta tarar Malam ya na bacci amma ganin Hajja Kilishi tuni ta fara kalallame shi, daga ya dan motsa sai ta zabura ta matsa kusa da shi cikin nuna kulawa. Ita kuwa Hajja Kilishi ta na daga gefe ta zuba mata Ido kawai. Cikin ran ta mamakin yajin da Ammy ta yi ta ke ji.

Ko da Malam ya bude ido ya ga Ammy sam be nuna wani farin cikin ganin ta ba, sai ma idan ya na da bukatar wani abu ya ce da Hajja Dudu ko Hajja Kilishi ta masa. Hakan ba karamin musgunawa Ammy yayi ba. Haka kuma duk yanda Ammy ta so kwanan asibitin Hajja Dudu ta yi kyememe ta hana, cewar ta gwara Gana ya zauna da Malam ai jinyar namiji sai namiji.

Bayan kwana uku Hajja Dudu ta koma Maiduguri, Ammy na ji ta na gani Hajja Kilishi ta tare mata a gida, cewar ta babu in da za ta je sai Malam ya sami sauki sosai. Duk yanda ta so ta tunzura ta ta koma ta ki, haka ta hakura. Wasa wasa sai da Malam yayi sati biyu a asibiti, kafin a sallame shi sai da likita ya jaddada hutu da kwanciyar hankalin da Malam ya ke bukata wanda hakan ne ya sanya Gana yanke hukuncin wucewa da Malam Maiduguri bayan ya ji cikakken bayanin abun da ya faru daga bakin Jauro, wanda be boye masa komai ba. Sai ga Gana mai kudirin samar ma Zainab yanci na mai gargadin ta matukar ta kashe mu su uba ita da uwar ta wallahi ba su yafe mata ba.

Sai da su ka dawo gida Gana ya hade kayan Malam kaf, ga mamakin Ammy Malam be yi musu ba, shi ne ma ya ke fadawa Gana kalar kayan da zai zaba masa, in da ya ke cewa ya fi san farare saboda tafsirin azumi ya gabato, sati biyu ya rage a fara.

Bayan Malam ya sallami su Halitta, tare da mu su alkawarin zai dawo bayan sati biyu kafin azumi ya kamkama, ya na mai duban Zainab ya furta

“Yakura kin dai san ke matar aure ce, cikin sati biyun nan da na ke kwance asibiti ban sani ba ko kin cigaba da halin ki na haura katanga ki fita yawan lalace, toh ki budi kunnuwan ki ji ni da kyau, wallahilazim matukar ki ka kara aikata haka ba za ki gama da duniya lafiya ba, Allah ya isa ban yafe mi ki ba….”

Dagowa ta yi a gigice ta na duban Malam, hakan ya sa Malam jinjina kai, ya kara da

“Ware ido ki kalle ni da kyau, ba dan da karar kwana ba da tuni bakin cikin ki ya kashe ni Yakura, toh amma Alhamdulillah Allah shi ne zai jibanci lamura na, ba za ki tuzarta ni ba! Ba ki isa ba!”

Jiki sanyaye Zainab ta furta

“Ba zan kara ba Dady”

“Idan ma kin kara kan ki za ki yiwa, kin dai san ke matar aure ce. Bayan haka daga yau idan ki ka sake kwana a dakin da ba namijin ki ba ba tare da kwakkwarar hujja ko dalili ba Yakura shi ma ban yafe mi ki ba”

Jin haka ta saki kukan da ta ruke shi can kasan magoro, fadi ta ke

“Dan Allah Dady ka kawo min dauki ka sauwake min wannan nauyi da ka daura min, wallahi ba zan iya kwana daki daya da shi ba Dady, dan Allah Dady”

Cikin halin ko in kula Malam ya furta

“Ki ka iya kwana gidan rawa bare dakin auren ki? Kai Gana kana ina? Maza zo mu tafi ko Allah zai sa na dena ganin wannan yarinyar!”
Zainab na gani Malam ya shige mota ya barta da nauyi mafi tsanani a rayuwar ta. Haka kuma Ammy wacce duk yanda ta so ta sauke girman kai ta bawa Malam hakuri ta kasa tsabagen kishin zaman Hajja Kilishi, gashi ta na ji ta na gan ta ci nasararr tafiya da shi.
_

*A gafarce ni, in Sha Allah zan sake posting kafin Sunday.*
_

*Khadija Sidi*
Auren Shehu

No comments