Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Auren Shehu Book 1 Page 7

7.

Majalisar tasu wacce ta ke kusa da gidan Malam ya isa, Ya tarar ta cika yanda ya so, Dan haka zuciyar sa wasai ya ce

“Na zo da labari da ?umi ?umi, wannan jaridar sabuwa ce kal!”

Cikin kaguwa su ji labarin daga me cewa

“Siyar mana”


Sai wanda ya ce

“Ba mu mu sha”

Sai da ya sami waje ya zauna, cikin nuna gwaninta ya ce

“Yau da ido na na ga mace ta hauro daga gidan Malam………”

“Ahab! Toh wannan sabon abu ne? Har wani labari da dumi dumi? Toh ai idan wanan ne na sha gani malam!”

Daya daga cikin samarin ya katse shi. Uku da ga cikin su da sam ba su taba ji bare su gani ba kuwa baki su ka ruke, cike da mamaki guda ya ce

“Kai Uzairu ka ji tsoran Allah! Da kai ma Khalifa! Gidan Malam fa ka ce! Wannan ya tashi daga karya sai dai a kira shi kazafi!”

“Mtsw kai ne a gun ka sabo, kai Uzairu fada mana sabon abu ba wannan ba Alhaji”

Cewar daya daga cikin samarin da shi dama ya taba gani shi ma. Shi kuwa Uzairu da ya kawo gulma gwiwar sa ce ta yi sanyi, dan kuwa sun sace masa gwiwa, cikin so ya burge ya ce

“Ba nan kawai abin ya tsaya ba, wani namiji ne ya ruko kugun ta, gaban ido na su ke ta badala, tun suna daga waje har su ka shige mota, Allah ya kadai ya san me su ke aikatawa ciki dan kuwa gilashin baki ne wuluk….”

“Kai auzubillallah ko ma wacece wannan ba ta da ala’aka da Malam! Ba jinin Malam ba ce!”

“Eh toh ko ma wacece dai daga gidan Malam ta ke, dan kuwa a kulli yaumin in za ka gan ta fuskata rufe ta ke da wannan abun da su ke rufe fuska da shi tsabagen munafunci! Kai ni har da asuba na sha gani ana dawowa da ita!”

Cewar Uzairu ba tare da ya kula da tashin hankali da sauran samari da su ke masoya Malam su ka shiga ba. Daya daga cikin su wanda har lokacin ya kasa yarda da abin da ya ke ji ne ya ce

“Kai Uzairu, tsakani da Allah ban ji dadin wannan magana ta ka ba, Bai kamata ba, shin yanzu ina amfanin wannan kazafi haka?”

“Oh toh kazafi ne ma?”

Uzairu ya tambaya cikin nuna bacin rai.
“Eh kazafi mana, yanzu idan mun je za mu ga abin da ka fada zahiri?”

Uzairu na susa kyeya ya ce
“Ai sun bar wajan……”

“Ai dama ba nan za su zauna ba, amma da za ku zauna waccar rumfar ta kusa da gidan Malam har dare ya raba ko ma asubar fari kila ku ga an zo an sauke ta”

Cewar Khalifa wanda ya ke maganar ko shakka babu. Daya daga cikin su wanda dama dan adawar Malam ne sakamakon rashin jituwa da ke tsakanin mahaifin shi da Malam ya ce

“Allah dai ya biya, ka ce yau za mu yi kwanan waje, dan kuwa sai mun ga abin da ya turewa buzu nadi!”

“Ni ma dai Habibu, za mu kasa mu tsare sai mun ga mai kan uwar daka!”

Cewar Uzairu da dama haka ya ke so, ya sami wanda zai taya shi dan kuwa dai muddin bai gano wacece ba hankalin sa ba zai kwanta ba. Su kuwa samari biyu wanda su ke ganin hakan bai dace ba saboda darajar da Malam ke da shi, tashi su ka yi su ka bar wajen, sauran na bin su da habaici kila Malam ya mu su alkawarin kujerar makka ne.

Su Zainab kuwa kasancewar lokacin da su ka saba shiga club bai yi ba, yawo Mike ya wuce da ita, sai da su ka gama zagayen su sannan su ka zauna wani dan garden da ake sayar da kayan kwalama. Mike ya siya mu su abin jika makoshi da gashesshen kifi. Da kyar ya samu ta ci ta dan koshi, sannan ya sake tambayar ta abin da ke faru. Nan ta labarta ma sa komai. Ran Mike yayi matukar baci, ba tare da yayi la’akari da iyayen Zainab ake magana akai ba ya furta

“Why? Me ya sa ka? Wannan ai son kai ne! Shekarun ki ya wuce 18, kin wuce a mi ki dole! Ba wanda ya ke da wannan damar! Kar da ki yarda a yi mi ki auren dole kin ji ko? In sun takura mi ki you should take them to the court! Ni zan tsaya mi ki”

Fuska cike da hawaye ta ke duban shi, ta na mai girgiza kai ta ce

“No Mike you don’t understand, they’re my parent, ba zan iya ba, Daddy Malami ne, sananne kuma, imagine yanda zai ji idan na kai shi court……”

“Just listen to yourself! You should think about yourself, your happiness first kafin na kowa! Shi yayi tunanin wani hali za ki shiga in ya mi ki auren dole?”

Mike ne katse ta, ya na mai ruko hannun ta ya ce

“Zeee look at me!”

Ta dago manyan idanun ta ta na duban sa, cikin murya mai ratsa zuciya ya ce

“You’re beautiful, God you’re very very beautiful! ga ki yarinya! You have a long way to go in life, in ki ka bari aka mi ki aure I’m sorry to say it might be the end of everything, your freedom, your happiness and even your beauty musammam ki fara having children…..”

Zainab na girgiza kai ta ce

“Ah ah, ba na so Mike, ba na so”

“Then tell your Dad, ba ni ba, in kin je gida look him in the eyes and tell him, ki fada masa ba ki yi shirin aure yanzu ba, ki fada masa ba za ki auri dan abokin sa ba, ya bar ki ki yi rayuwar ki! Ya dena wani yaudaran ki da ke ce favorite child din shi, he should know by now kin girma, kuma kin san yancin ki!”

Shiru ne ya biyo baya, kafin daga bisani Zainab ta nisa, ta na mai goge hawaye ta ce

“Zan yi kokari na ganar da shi Mike, I promise you auren nan ba za a yi shi ba”

Cikin jin dadi ya ce

“Yauwa ko ke fa! Oya share hawayen ki, mu tafi ma mu ji dadin mu a club da fatan dai you’re wearing something sexy under this your agbada hijab”

Ya karasa maganar ne ya na mai bin jikin ta da kallo. Ba tare da ta nuna damuwa da irin kallan da ya bi ta da shi ba, Jin batun club ya sa ta duba lokaci, in da agogon ta ya nuna karfe shabiyu da minti 40. Tashi ta yi da sauri ta ce

“No ba zan iya dadewa a waje ba, kasan Daddy ya na nan Mike”

“Ohoooo! Ke da Dadyn nan na ki! Kin fiya tsoro wallahi! Idan ya na nan sai menene! Haba mana”

“Ba za ka gane ba”

“Try me, ganar da ni mana”

“Mu shiga mota, mu na tafiya ina ma ka bayani”

Haka ba yanda ya so shi ma ya taso su ka shige mota in da su ka dau hanyar gida.

Ammy kuwa har ta kwanta amma ta nemi bacci ta rasa, Zainab da damuwar da ta ke ciki ne ya sa ta kasa bacci. Da abin ya ishe ta ne ta tashi ta nufi dakin Zainab. Ko da ta shiga ta ga ba ta nan sai ta yi tunanin ko bandaki ta shiga, Nan ma ta buga kofar tare da kiran sunan ta. Shirun da ta ji ya sanya ta bude kofar yayin da gaban ta ya shiga faduwa ganin bandakin ma wayam Zainab ba ta ciki.

Dakin Halitta ta nufa jikin ta na rawa ta na mai fatan ko dai Zainab din kasa bacci ta yi, ta koma dakin Halitta ko Falmat duk dai ta san abu ne mawuyaci. Ta tarar idanun Halitta biyu, kallo ma ta ke a kan laptop. Cikin rawar murya ta ce

“Halitta ina Yakura?”

Gaban ta yayi mummunar faduwa jin tambayar Mahaifiyar su, a zahiri kuma cewa ta yi

“Ta na dakin ta mana”

“Ah ah ba ta ciki, daga nan na ke, ba ta shigo nan ba?”

Halitta na girgiza kai a sanyaye ta ce

“Ba ta shigo ba, kila ko ta na dakin Falmat…..”

Da sauri Ammy ta juya ta fice, dakin Falmat ta nufa, ita ma Halitta tasowa ta yi ta bi bayan ta, ta na mai kokarin kiran Zainab amma wayar ta ki shiga. Sun tarar Falmat ta yi dai dai ta na baccin ta har da munshari, ganin babu Zainab babu alamar ta hankalin Ammy ya fara tashi matuka. Cikin zafin nama ta fara tashin Falmat, da kyar ta samu ta bude idanun ta, cikin magagin bacci ta ke kallan Ammy.

“Ke tashi da Allah! Ina Yakura?”

Jin tambayar da aka mata take ta wastsake ta ce

“Yakura kuma Ammy? Ba ta dakin ta?”

“Mtsw da ta na can da zan zo ina tambayar ki ne? Ba ta shigo nan ba?”

“Rabona da ita tun sanda na shiga dakin ta kiran ta mu ci abinci, kun duba kitchen? Kila yunwa ya tada da ita ta je kitchen neman. ….”

Ammy ba ta bari ta karasa ba ta juya ta fita da sauri, kitchen din ta nufa, Halitta da Falmat biye da ita, hatta store da dakin baki sai da su ka duba, babu Zainab babu alamar ta. Falo su ka dawo, Ammy wacce ta fara fita hayyacin ta tsabagen firgici sai ga ta tana duban bayan kujera, idanu cike da kwalla, murya na rawa ta ce

“Oh ni Aleesha na shiga uku ina Yakura ta shiga da tsohon daren nan? Malam! Kila ta na bangaran Malam! In kuwa ba ta nan gwara na tashe shi na sanar ma sa tun wuri Yakura ta bata! Toh ko sace ta aka yi! Na shiga uku wayyo Allah na!”
Ganin yanda ta zabura za ta wuce bangaran Malam Halitta ta yi saurin dakatar da ita ta hanyar fadin

“Ammy dan Allah ki tsaya ki kwantar da hankalin ki, kar ki tashi Daddy Yakura ba ta bangaran shi, ba sace ta aka yi ba, da kafar ta ta fita……”

“Ki na nufin guduwa ta yi saboda za a mata auren nan? Wayyo Yakura da ba ki yanke wannan danyan hukuncin ba! Mun sanya diyar mu cikin wani hali, ya Allah ka kare mana ita! Halitta kin san za ta gudu ya aka yi ki ka bari ba ki fada min ba”

Ammy ce ke simbatu ta rasa abin da ke mata dadi sai kai kawo ta ke. Falmat kuwa kallan su ta ke a tsorace dan kuwa har lokacin ta kasa fahimtar abin da ke faruwa. Ammy na mai goge hawayen da ya fara fita daga idanun ta, ta ce

“Kai bari na shedawa Malam Yakura ta gudu, Yakura ta sa kafa ta gudu da tsohon daren nan tsagen ba ta son auren da ya kulla”

“Ammy na ce kar ki fadawa Daddy, Yakura ba guduwa ta yi ba! Za ta dawo! Ki kwantar da hankalin ki dama ta saba fita!”

Daga Ammy har Falmat Halitta su ke duba cike da mamaki, wacce kallan da su ke mata ya sanya ta farga da subul da bakan sa ta yi

“Me ki ke nufi ta saba fita?”

Ammy ta tambaya cikin tuhuma
“Babu komai Ammy, kawai ina nufin ko ina ta je ma za ta dawo….”

“Halitta!”

Ammy ta daka mata tsawa wanda ita kan ta Halitta sai da ta ji har zuciyar ta. Ammy ba ta gushe ba ta kara da

“Ba kya magana hakan nan kara zube, me ki ke nufi da sama ta saba fita?”

Baki na rawa ta ce

“Dama….. dama…dama wani sa’in ta na fita cikin dare, sai ta dawo da asuba, duk sanda mu ke ji kamar ana haurowa ta garden, ita ce……”

Tas Ammy ta dauke Halitta da wani gigitaccan marin da sai da ta ga wuta a idanun ta, ta na mai huci ta ke fadin

“Kun haince ni! Kun zalin ce ni! Kun cuce ni! Gani shashashar uwa, ina can ina bacci ku kuma ku nan kuna cutar da mu? Da ku ke hada baki ta na fita gidan uwarwa ta ke zuwa??”

Tunda Ammy ta fara magana Halitta wacce hannun ke rike da kuncin ta take girgiza mata kai, dan kuka ta ma kasa magana.

“Ba da ke na ke magana ba? Gidan uwar wa ta ke zuwa!”

“Ammy dan Allah ki yi magana a hankali kar da Daddy ya jiyo mu”

Cewar Falmat wacce ita ma din kukan ta ke.

“Idan ya ji sai me? Sai na fada masa diyar ta shi da ya fi yiwa kyakkyawan zato ce ke hada baki da kanwar ta, ta na haura katanga! Wannan masifa har ina ni Aleesha!”

“Dan Allah Ammy ki yi hakuri, wallahi tallahi ba hada baki mu ka yi ba, sam ban da masaniya da ya wuce fitar da ta ke, shi ma din gudin halin da za ku shiga ya sa na kasa fada mu ku, Amma ina kokari na wajan yi mata nasiha da kuma addua…”

Halitta ce ke magana cikin kuka. Hannu biyu Ammy ta dora aka, ba su kara firgita ta ba sai da su ka ga hawayen na kwaranya daga idanun Ammy. A tare su ka furta

“Dan Allah Ammy ki yi hakuri”

Tuni ta canza harshe to koma yare, ta na mai fadin

“Menene amfanin rufewar da ki ka yi? Yanzun kin min adalci kenan Halitta? Ki na gani yar uwar ki na cutar mu da mu Amma ki kasa fada min, nasihar ta ki da adduar ta ki amfanin me ta yi mana? Yakura ta cuce ni, ta cuci kan ta, ta cuci Malam! Ina waya ta? Ba ni waya ta!”

Wayar ta ta shiga nema, ganin wayar ba ta kusa ta dubi Halitta wacce ke rike da na ta wayar, ta ce

“Kira min ita, kira ta ta fa?a min gidan uwar wa ta ke!”

Hannu na rawa Halitta ta kara kiran wayar Zainab, ta ci sa’a ya shiga amma kuma har ta gama kara ta katse ba ta daga ba. Haka ta yi ta kiran ta amma ba a dagawa, ganin haka Ammy ta koma kan kujera ta na tunanin mafita, shin Malam za ta tasa ta fada masa halin da su ke ciki ko kuwa dai ta jira Zainab yanda za ta hukunta ta ba tare da Malam ya san halin da su ke ciki ba?

Su Uzairu kuwa a na su bangaran zama su ka yi a mararrabar gidan Malam su na jiran dawowar Zainab da Mike, saura da su ka gaji da jira cewa su ka da Allah in dan sun karaso su ma a yi mu su waya.
Ganin shiru har karfe daya babu alamar motar Mike Khalifa ya ce

“Baba kamar fa wannan mutanan ba za su dawo ba, Ni ma gwara na tafi na……”

Motar da ta dan haske su kadan kafin a rage hasken motar ta gifta gaban su ya sanya Khalifa shanye sauran maganar da ya ke. Daga shi har Uzairu bin motar su ka yi da kallo, illa kuwa mota ta ja ta tsaya dan gaba kadan da gate din gidan Malam, ta daidai garden da ta saba haurawa.

“Alquran wannan motar ce, wabillahilazi!”
Cewar Uzairu ya na mai nuna motar da dan yatsa.

“In dai kuwa su ne maza kirawa so Munir da Habibu, su zo maza yau za su sha mamaki!”

Khalifa ne ke maganar in da shi ma ya ke kokarin kiran na shi mutanen dan kuwa yau sun sha alwashin gano ko ma wacece wannan yarinyar mai haura katangar gidan Malam.

Sam Mike bai lura da su Uzairu ba, bare ma ya san da zaman su. Bayan ya faka ya riko hannun Zainab, cikin bata kwarin gwiwa ya ce

“Na san za ki iya kwatarwa kan ki hakki Zee, please do it for us”

Karar wayar ta da ta fada hannun kujera ta ji, da kyar ta iya daukowa, da ta duba ta ga wacce ke kiran ta ya sa ta jan tsaki

“Mtsw wannan wawuyar yarinyar ba za ta sakar min mara ba ko!”

“Wacece?”

“Sister na ce, I’m sure ta shiga daki na ta ga ba na nan ne ya sa ta ke kira na, rabu da ita ba zan dauka ba, bari na yi sauri na haura sai na ce mata daga garden na ke”

Ta bashi amsa yayin da wayar ta katse, hakan ya bata damar ganin miss calls din Halitta har goma sha uku.

“Kai wannan ba dai mayya ba, bari na tafi kar ta jaza min masifa”

Ta na maganar ne yayin da ta fito da sauri ta mayar da murfin mota ta rufe, sannan ta zaga wajan Mike da niyar masa sallama, hakan yayi daidai da hango samari hudu da ko shakka babu gun su su ka nufo. Da ke garin da dan duhu daga Zainab har Mike ba su iya tantace wasu irin mutane ba ne. Hantar Mike tuni ta kala, cike da tsoro ya ke duban Zainab da ga cikin mota ya ce

“Su waye wannan?”

“I don’t know, ban sani ba, I don’t think it’s safe, bari na koma mota mu bar wajan kawai”
Cewar Zainab dan kuwa ta tsorata ainun, ta na kokarin bude motar Mike ta koma ciki, ga mamakin ta sai gani yayi ya tada motar shi, ya ce

“No Zee, kar ki shigar min mota, babu mamaki set up ne daga Baban ki, dan a kama ni, gani Christian, I can’t go with you, I can’t risk it!”

Yanda ya figi motar da yanda samarin su ka bi motar a guje kamar za su iya kama motar ya sanya Zainab kaduwa, ta yi shahada ta sheda babu sarki sai Allah, dan kuwa ko da Mike ya tsarewa samarin nan kan ta su ka dawo, ganin haka ita ma sai ta gwada yin abin da Mike yayi, ta juya za ta arta a na kare, ba ta kai ga wuce gate din gidan su ba su ka cimma ta, in da su ka zagaye ta, yanda su ke mayar da numfashi, Daya bayan daya ta ke bin su ka bin su kallo, dan tsoro ta kasa furta komai.

“Ke wacece? Ki bude fuskar ki Malama! Duk abin da ki ke mana a unguwa muna sane da ke! Kuma yau din nan sai mun tona mi ki asiri!”

Cewar Uzairu wanda ya fi kowa za kewa. Ganin an bude gate din gidan Malam tuni hankalin su ya koma can, musammam Zainab wacce jikin ta har rawa ya ke. Haushin karnuka ke tashi daga cikin gidan dan kuwa karar tashin motar Mike da Kuma guje gujen v ne su ka fito a tare hannun su ruke torchlights.

 

Post a Comment for "Auren Shehu Book 1 Page 7"