Breaking News

Auren Shehu Book 1 Page 9

9

 

“Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun! Allahumma ajirni fi masibati haza wakallifna minha!”


Lafazin da Malam ke ta nanatawa kenan ya na mai kawar da kai daga kallan Zainab. Sai da su ka tabbatar ya tsaya sosai da kafafun sa sannan su ka sake shi, kamar wanda be da lada a jiki haka ya juya ya nufi cikin gida, shi kan shi tafiyar kawai ya ke ba tare da ya san ya na yi ba, haka kuma be fasa furta “Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun” dan kuwa tun da ya zo duniya be taba tsammanin zai ga rana irin ta yau ba.

Ganin Malam ya shige ciki Jauro ya sami damar kallan Usman ya ce

“Toh munafuki ka tona ka ji dadi ko? Dan bakin ciki ai sai ka zuba ruwa a kasa ka sha! Ga dai halin da ka sa bawan Allah!”

Shiru Usman ya ma sa gaba daya hankalin sa kan Yakura ya ke, musammam da ya ga ta daura hannayen ta biyu a ka ta na rusa kuka mai ratsa zuciya. Kirjin sa cike da tausayin ta ya matsa kusa da ita da niyar mata magana, kan ya kai ga bude baki ya furta komai ta daka masa tsawa cike da tsana ta ce

“Dallah kar ka matso kusa da ni munafukin banza munafukin hofi, na tsane ka, na tsane ka tun randa na fara dora idanu akan wannan muguwar fuskar ta ka, Allah ya isa tsakani na kai!”

Ta wuce ciki fuuuu, in da Jaura ke kara goyan bayan abun da ta fada ta hanyar yiwa Usman shagude. Isa wanda gaba daya ya rasa ta cewa ne ya matso kusa da shi, ya dan taba kafadar Usman, sannan ya wuce dakin su na Maigadi, zuciyar sa cike da al’ajabi.

Yanda ya shigo falon afujajan, fuska fal hawaye ga salati ya na futa daga bakin sa ne ya ruda su Ammy da Halitta wanda har lokacin ba su san wainar da ake toyawa a waje ba, su dai suna nan cikin tashin hankalin rashin samin Zainab a dakin ta.

“Malam lafiya? Me ke faruwa? An yi Rashi ne?”

Zama yayi dirshen a kan carpet, kai ya ke jinjinawa yayinda ya fashe da kuka mai karfin, ya na kuka ya ke fadin

“Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun”

Daga Ammyn har su Halitta su ma din kukan su ka sa, Dan kuwa ganin kukan Malam ba karamin tashin hankali ba ne. Ammy na kuka ta ke fadin

“Malam me ya faru Yakura ta mutu ne?”

Duban ta ya ke da idanun sa da su ka yi jajur, tsabagen bacin rai jikin san har rawa ya ke, murya na kakkarwa ya ce

“Da wannan mummunar ranar gwara ranar mutuwar Zainab! Har ki na tambaya ko ta mutu? Wato kin ma san da fitar ta? Ki na nan shashashar uwa diyar ki na haura katanga ta fita yawan banza ki na tambaya ta ko mutuwa ta yi?”

Ammy na mai girgiza kai ta ke fadin

“Ban da masaniya idan ba dazu da na duba bata nan ba, wallahilazim kamar yanda ba ka sani ba…..”

“Ina amanar da na baki? Yau na yi dana sanin yawan nisa da ku da na ke yi! Yau na yi danasanin tura Yakura jami’a can uwa duniya! Yau na yi dana sanin rashin aurar da su da wuri da ban yi ba! Kun cuce ni! Yanzu ace cikin ku duka babu wanda ya san wannan halin da Zainab ke aikatawa ba? Har Mai gadi da yan unguwa su sani amma ku da kuke tare da ita ba ku sani ba?”

“Wallahi ban sani Malam, wallahi ban sani ba in ba dai yau da Halitta ta sheda min ba……..!”
Cewar Ammy wacce kafin ta kai aya Malam ya katse ta cikin tsawa ya ce

“Halitta ta sheda mi ki? Halitta kin sani ki ka boye min saboda tare kuke lalacewar ku ko? Tare ku ke cin mutunci na?”

“Wallahi Dady ba tare mu ke ba, ban taba aikata makamancin haka ba, tsoran halinda za ka shiga ya sa ban fada mu ku ba……”
Halitta ta bashi amsa cikin kuka. Murya kasa kasa ya ce

“Halin da zan shiga? Kin gwammaci yar uwar ki ta cigaba da aikata barna ta na sabawa Allah ta na bata min suna a gari akan halin da zan shiga? Maigadi da yan unguwa su na gani har ana taruwa kofar gida na domin a sheda fuskar fitinanniya cikin ‘ya’ya na! Zainab da na ke ikirarin ta fi kowa cikin ‘ya’yq na sai ga ta tsakar dare tsakiyar maza sun dage sai sun ga kowacece ake kawo ta a mota, ta na haurawa tsabagen lalacewa da wulakanci?????”

“Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun!”

Wannan karan Ammy ce ke salati, hakan yayi daidai da shigowar Zainab wacce dama ta dade ta na shawarar shigowa falon ko kuwa ta yi zaman ta waje. Ganin ta Ammy ta yi wuf ta damko ta tana mai rufe ta da duka, fadi ta ke

“Gwara na kashe ki Yakura! Gwara na kashe ki kafin ki kashe mu, haihuwa ba ta yi rana ba! Kashe ki zan yi na huta”

Ihu da kukan Zainab be saka an ceto ta daga hannun Ammy ba, Malam na mai kawar da kai ya ce

“Dukan ta da ki ke ba zai amfana mana komai ba, Zainab ta wulkanta ni, Ashe zan haifi diya irin ki Zainab? Ashe duk Kamala da na ke ganin ki da ita duk na munafunci ne? Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun yau na yi danasanin haihuwar diya mace irin ki Zainab, kin zalince ni, kin haince ni kin ci amana ta Zainab…….”

Kaucewa ta yi daga rukon Ammy, da sauri ta karasa gaban Malam, hannayen ta biyu ta sa ta ruko kafafun sa fadi ta ke

“Dan Allah Dady ka yafe min, Dady ka yafe ni, Dady ka yafe min na tuba, duk hukuncin da ka yanke kai na zan bi, zan auri wannan dan abokin na ka da ka ke so na aura, amma dan Allah Dady kar ka min baki…..”

Jin haka sai ga Malam ya murmusa, ya na mai share hawaye ya ce

” Ana idar da sallar asuba ku zo ku same ni a nan falon da na ke ba da karatu!”

Ya tashi cikin hanzari har ya na hambare Zainab ba tare da ya kula ba ya fice ya bar Zainab hannun Ammy, dan kuwa ba ta fasa jibgar ta ba har sai da Halitta da Falmat su ka tausaya mata su ka shiga tsakani. Ammy na haki tsabagen yanda ta daki Zainab ta ce

“Da sani na zaune ki tun ran da na haife ki da baki ja min wannan masifar ba!”.

******

Kamar yanda Malam be runtsa ba, haka iyalan sa su ka yi kwanan zaune. Ko da aka kira sallar asuba Malam be fasa fita ya ja salla a masallaci ba. Bayan an idar ne ya nemi ganin masu gadin sa duka ukun.

Zaune su ke falan da su ke daukar karatu, Malam zaune bisa doguwar kujerar sa, su Usman zaune gaban sa suna ta raba idanu cikin jiran tsammani. Jim kadan Ammy ta yi sallama, sanye ta ke cikin hijabi tun daga sama har kasa, kallo daya za ka mata ka tabbatar da matsanincin damuwar da ta ke ciki. Biye da ita Halitta da Falmat ne, suma din hijabin ne jikin su.

Halin da ake ciki be hana Halitta satar kallan Usman ta wutsiyar ido ba, ta na mai adduar Allah ya sassauta mata son da ta ke yiwa wannan bawan Allah dan kuwa ko an kai dubu shi kawai ta ke iya hangowa duk inda ya ke muddin ta sa kafa a wajan. Ganin Malam ba shi kadai ba ne ba ya sanya su ka sami waje can gefan Malam domin samin tazara sosai tsakanin su da su Usman.

Malam na shirin tamabayar ina Zainab sai ga ta nan kamar an cefo ta. Har lokacin hijabin da ta fita da shi ne a jikin ta, ta na shiga ta tsinci idanun ta cikin na Usman, hakan ya sa ta mummunar faduwar gaba tare da fargabar dalilin da ya sa Malam tara su tare da ma’aikatan sa maza, ta yi saurin dauke kan ta, kusa da su Falmat ta samu ta dan rakade. Malam kuwa ganin Zainab jiyayi wani ciwon bakin ciki ya tasar ma kahon zuciyar sa, idan akwai abin da ya tsani gani ya bi bayan Zainab. Gaba daya ta bata kan ta a idanun sa dan ji yake kamar ya sallama ta ya huta. Zaman ta ke da wuya Malam na mai kawar da tunanin da ya ke cikin zuciyar sa ya furta

“Na san za ku yi mamakin dalilin da ya sa na tara ku nan tare da iyali na, Amma kafin na aiwatar da komai, ina so na san shin bayan diya ta da take haurawa ta na fita yawan dare, ku na ji kuna gani amma ku ka ki fada min, wata amana ta ku ka ku ke ci?”

Ya na maganar ne idanun sa kan su Usman, in da duka su ka sunkuyar da kai, musammam Jauro wanda in ban da zufa babu abin da ke keto masa. Shiru ne ya biyo baya kafin daga bisani Isa ya nisa ya ce

“Allah shi gafarta Malam, na rantse ma ka da Allah ban taba cin amanar ka ba, wallahi tallahi ban da masaniya akan wannan lamari da ya faru a daren yau, Ni ma lamarin sabo ne a gare ni”

Ya kare maganar na sa cike da ladabi ya na mai tausayawa Malam dan kuwa damuwa tuni ta bayyana a tare da shi, lokaci guda tsuafar shi ta bayyana karara. Jauro na mai sakar zuciya ya sa hannu ya goge zufar da ke keto masa, jin Malam ya ce

“Malam Jauro! Shin ka na da masaniya a kai?”
“Ah ah Malam, lillahi wa rasulillahi ban da sani akan wannan lamari!”

Ya ba da amsa cikin sauri ba tare da ya damu da kallan da Usman ya ke masa cike da mamaki ba. Shi kuwa Malam Usman ya ke kallo ya na mai nazari akan shi, bayan wasu yan dakikai Malam ya furta

“Sai kai Usman, tun yaushe ka san da wannan barnar?”

Idanun Zainab da Halitta kan Usman yayinda ko waccar su bugun zuciyar ta ya karu, in da na Halitta ke bugawa cike da tausayi, so da kaunar Usman, haka na Zainab ki bugawa cike da gaba, tsana da kiyayyar da take masa, gani ta ke duk duniyar nan ba ta da makiyi da ya wuce Usman. Cike da ladabi Usman ya ce

“Ka yafe min Malam, ba a yi cikakken wata da sani na ba”

“Wani dalili ya hana ka sheda min”

Shiru ne ya biyu baya, dan kuwa Usman ya kasa budar baki ya bawa Malam amsa, sai ma sunkuyar da kan sa kasa da yayi. Malam ya ce

“Ka yarda ka ci amana ta?”

Usman yayi shiru ya na mai dada sin da kai. Malam na mai kara jaddada tambayar sa ya ce

“Ka yarda ka ci amanar gadin da na ba ka? Ka yarda ka cutar da ni?”

Usman na mai girgiza kai ya ce

“Na yarda Malam”

“Ka amince da duk hukuncin da zan yanke akan ka, ko da kuwa na korar ka daga gida na ne? ko kuma hana ka cigaba da aikin gadi a gida na daidai ne? Ka yarda adalci ne?”

Wannan magana ta Malam ba karamin dadi ta yiwa Jauro ba, dama tunda Usman yayi azarzabin rufawa Malam asiri gaba daya bakin ciki da kishin Usman zai zama numba daya gun Malam ya kama shi, Amma ko da ya ga reshe ya juye da mujiya tuni zuciyar shi ta yi kal, shi dai fatan sa kar Usman ya shedawa Malam har da hadin bakin shi Zainab ke samin damar fita, gwara Malam ya kore shi kowa ya huta.

Halitta kuwa idanun ta ne ya ciko da kwalla, musammam da ta ji ya amsa da

“Na yarda Malam!”

Tuni ta fara kukan zuci, Dan ta san halin Malam ya iya yanke hukunci cikin fushi, sam ba ta so ya kori Usman ko da kuwa zai dawo yayi dana sani. Shiru ne ya biyu baya, kafin daga bisani Malam ya nisa tare da fadin

“Menene dalilin ka na rufa min asiri bayan ka bari ana barna a bayan ido na?”

Shiru Usman ya kasa amsawa, Malam be gushe ba, ya kara fadin

“Shin wani abu na ma ka da na cancanci wannan abu biyu daga gare ka? Cin amana da kuma rufin asiri? Ka ci amana ta, daga baya ka zo da rufin asiri? Ka na da wata manufa ne na yin haka?”

Usman na mai girgiza kai ya ce

“Ina neman yafiyar ka Malam, dan Allah ka min yafe min, ban da wata manufa da ya wuce kare mutuncin ka da gujewar tashin hankalin ka, na yi kuskure, ka yafe min”

“Kai wanene?”

Malam ya kara masa tambaya mai rikitarwa. Cikin nuna rashin fahimta ya ce

“Ni Usman ne, ban taba tunanin cin amanar ka, ko kuwa zaluntar wani daga cikin iyalin ka ba”

Malam na mai duban shi cikin nazari ya ce

“Iya binciken da na yi akan ka kai bafulatani ne dan cirani, ka fito daga wata ruga da ake kira Rugar Shehu, bayan abin da ka min a yau ya sanya ina tsoran zamantakewa ta da kai, dan kuwa idan har za ka iya ganin diya ta cikin halaka haka ka kawar da kai, to ko shakka babu za ka iya halaka ni kai na! Wannan ya sa na ke son jin cikakken tarihin rayuwar ka, wanene kai, da wata manufa ka zo gida na?”

Maganar Malam ta sanya zuciyar Usman rauni, cikin kokarin kare kan sa ya furta

“Allah ya sani ban zo da cuta ba tun ranar da na sa kafa ta gidan nan, haka ma yanzu da na ke zaune gaban ka. Kamar yanda ka sani tun a baya, Sunana Usman, Usman Tanko, na zo ne daga rugar Shehu, in da maihaifina shi ke da sauratar Shehuntakar rugur, Ya gada ne tun kaka da kakan ni. Ba mu da takamamman wajan zama, dan haka yawo mu ke daji daji, mukan yada zango a duk dajin da Allah ya nufa, muddin akwai ruwan da shanun mu za su sha, haka ciyawa da da harawar da za su ci. Babban abin da Rugar Shehu ta yi suna akai kuwa shine surkulle dan haka ba ma zama a daji sai an yi surkulle an kafe dukkannin dajin kaf ciki da waje ya zama mallakin mu…………..”

 

 

*Khadija Sidi*AUREN SHEHU

10.

No comments