Breaking News

Auren Shehu Book 2 Page 15

 

AUREN SHEHU 2

Kamar yanda Ammy ta mata alkawari babu wanda ya kara tunkarar Zainab da maganar zubda ciki, hakan ya sa ta dan sami kwanciyar hankali, musamman da Anty Sauda ta hada na ta ya nata ta koma Maiduguri.


Cikin sati daya Usman ya hade kayan sa, bayan ya shawo kan su kawu Iliya da kyar sun yarda ya sake barin Rugar Shehu. Ana saura kwana uku ya tafi aka daura auren Muhamad Bello da Raqeba. Iyalle ce ta karbi rukon Cangwai duk da a zahirin gaskiya sun gano ba diyar Usman ba ce, rashin Rahila da Tanko ya sanya dole su hakura su zauna da ita.
Muhamad Bello ne da kan sa ya raka Usman har Yola gidan Alhaji Ibrahim Balla kamar yanda ya yi alkawari. Ya karbi bakwancin Usman hannu bibbiyu musammam da ya ga harkar cigaban da ya zo da shi. Cikin gidan gonar sa ya bawa Usman masauki na musammam, cewar shi zai iya zama kafin ya bude ido shi ma ya sami na shi.

Alhaji Ibrahim Balla magidanci ne mai kimanin shekaru hamsin da biyar a duniya, matar shi daya haka kuma dan sa daya tilo kamar tsoka daya a miya, amma hakan be sa ya sangantar da dan na shi ba wanda ake kira Umar. Ya tashi da tarbiya, dattako dadin dadawa kuma ga gata, ilimi wayews da ado tamkar dawisu. Umar saurayi ne mai shekara talatin da biyar a duniya, kasancewar ya karanta health economics a Fannin digiri ya koma yayi development studies a masters ya sa ya zama shi ne jagaba wajan habbaka sana’ar mahaifin na sa, wato sana’ar gidan gona.

Cikin kankanin lokaci Alhaji Ibrahim ya lura da halayyar Usman, da kuma amanar sa, hakan ya sa zuciyar sa kwadaita masa hada shi da dan sa Umar wanda kusan duk abin da ya shafi gidan gonar shi ke tafiyar da shi. Ga kuma ilimin Isalama da ya tabbata Usman na da shi wanda ya ke da yakinin lalle Umar zai amfana sosai, da wannan ya yi kokarin kulla abotan Usman da Umar, duk da kuwa ya san in dai aka zo fannin wayewa hali ya sha bambam.

In da Allah ya kawo abin da sauki, sai ya hada jinin Umar da Usman, yanda ado da wayewar Umar ke burge Usman, shi kuma Usman kamala da ilimin addinin Usman ke burge shi, musamman da ya ji ya na larabcewa da wasu daga cikin abokan sana’ar su da su ke Larabawa, sannan duk wani muhadara da majalisin malamai Usman na kokarin zuwa wani lokaci har gayyatan Umar din ya ke. Kullu yaumin Umar na kokarin jan Usman jiki kamar yanda mahaifin sa ya ba shi umarnin, duk dai Usman na dan janye jikin sa ba dan komai ba sai gudun kar ya kwafsawa Umar, duk wata harka da ya shafi shiga cikin mutane sai Usman ya nemi ya janye jiki, har sai Umar yayi da gaske kafin ya yarda ya bishi. Duk wanda kuwa ya kuskure ko kallan banza ne ya yiwa Usman lalle kuwa a ga fushin Umar.

***

Hutun Halitta wacce ita ce mai debewa Zainab kewa ya kare, Sudais ya ce lalle ta hado nata ya nata ta koma Saudi ba zai iya zuwa Nigeria ba kamar yanda ya mata alkawari ba saboda yanayin aiki da ya yi yawa.

Da yamma likis Halitta shirye tsaf, sanye cikin bakar doguwar riga, suna tafe suna hira Zainab ta raka ta har mota in da Ammy da Falmat ke zaune suna jiran ta su kai ta Airport. Har ta zauna ta dubi Zainab wacce ke tsaye ta na duban ta. Sanye da hijab ruwan dorawa da ya kai mata har kasa, gaba daya ta sauya ba walwala ba farin ciki, kullum cikin damuwa ta ke har ta kai ya fara nunawa a jikin ta.

“Dan Allah Yakura ki rage damuwa ko dan cikin da ki ke dauke da shi”

Cewar Halitta cike da damuwa. Ta kara da.

“Zan mi ki addua in Sha Allah……”

“Idan har irin adduar da kuka min ne har Allah ya sa na dawo gidan ba na so, da ba ku min ba da yanzu ina tare da miji na…”

Jin haka Ammy ta kauda kai gefe. Falmat cikin ran ta cewa ta yi ‘aha dama zancen kenan Yakura ta zama sai ka ce mayya!”

“In Sha Allah zan mi ki adduar mafi alkhairi a rayuwar ki”

Cewar Halitta. Zainab ta kada baki ta ce

“Usman ne mafi alkhairi Halitta”

Halitta na mai murmushin yake ta furta

“In dai shi ne toh Allah zai warware komai Yakura, bi’izinllah”

“Allahumma amen, Allah ya tsare ya sauke ku lafiya”

“Ameen ameen, ma yi chatting, ko da yake ke fa ko wayar ma ba ki da shi bare na chat, ki taimake ni Yakura, kira daga Saudi tsadi, ki samu yar waya sai mu ke gaisuwa ta social network, ki taimaka”

Zainab na murmushi ta bata amsa da

“Yar ana ce zai yi tunani akai”

Da haka su ka yi sallama jikin kowa a sanyaye.

***

Watannin Usman uku suna kasuwanci tare da Umar Balla. Hidimar da ke gaban sa be sa ya manta Zainab daidai da sakan daya ba, da ita ya ke tashi da ita ya ke kwanciya cikin ran sa. Wani sa’in sai yayi da gaske ya ke iya jure rashin ta. Har Umar ya kai ga ganewa akwai damuwar da ke tattare da shi, amma ko da ya tambaye shi dalili ce masa yayi babu komai kawai yakan dan yi tuntuntuni ne akan Rugar Shehu da kuma yanda zai bunkasa Rugar a sami cigaba.
Tafe su ke cikin motar Umar, kan hanyar dawowar su daga Mambila in da su ka je su ka yi cinikin shanu. Umar wanda ya ke baki, be da tsayi sosai amma kuma ba a kira shi gajere ba, haka kuma kyawun sa na ba yabo ba fallasa, sanye ya ke da kanana kaya, bakin wando da jar riga mai gajeran hannu. Usman da ke gefan sa sanye da wannan shigar ta sa da ya saba, riga yar shara, da rawanin sa da ya koma yi tun bayan tafiyar Zainab. Hankalin Umar kan kwalta ya furta

“Ni kuwa da za ka bi shawara ta Usman da fili za ka siya babba ko da kuwa a wajan, ka gina gidaje ciki in ya so ka kwaso duka jama’ar Rugar ta ka, ku yi zaman ku ciki ”

Cikin kaguwa Usman ya furta

“Shin ka na ganin haka me yiwuwa ne? Kai mutane na fa ba kamar na ku ba ne, zaman bukka ya fiye mu su zaman binni da wahalar ta, Ni dai da ka ganni nan ni ke da kwadayin birni…”

Dariya Umar yayi jin furucin Usman, dan kuwa ya san har ga Allah ya sosa masa in da ya ke masa kyakayi. Kana ya ce

“Ina ce so kake ka bunkasa Rugar ta ku? Ka na tunanin wannan tsarin da Shugaban kasa ya ke so ya aiwatar mai yiyuwa ne? Ko ba ga yanda kudanci da wasu bangare na arewacin kasar nan ke sukar tsarin ba? Ka ga wannan Ruga settlement din ba abu ne mai faruwa nan kusa ba, Amma kai a karan kanka za ka iya kwatantawa ta ka Rugar, tun da babu laifi Allah ya ba ku arziki na dabbobi kwarai da gaske, da kuma taimakon yan kasuwa na nan Nigeria da kuma na kasashen waje wanda za su sa hannun jari a tada hanyar arziki mai girma, ina mai tabbatar maka za ka shahara kwarai”

“Kai wannan maganar ta ka ya sa ni tunani Umari, wa ya ga jama’ar Rugar Shehu kusa da birne!”

Umar na dariya ya furta

“Kai ba ma kusa da birni ba, idan ma cikin birni ka ke so ka kawo su ai ba abu ba ne mai wuya, dama naira ce wuyar, kuma Allah ya hore, ana nan ana nan sai ka aure matar birni, dama ana ta min maganar ka, ana ta kawo sakon gaisuwa fa”

Gaban Usman ne ya fadi, yayinda da Zainab ta fado zuciyar sa. Cikin kokarin waskewa da maganar aure ya furta

“Wace matar birni ce za ta so bagidaje dan kauye Irina? Ai mata sun fi son wayayyan mutum”

Umar na duban sa ta wutsiyar ido ya ce

“Wai kullum aka yi magana sai ka ke kawo wayewa wayewa wayewa! Wai kai wata irin wayewa ka ke magana?”
Zuciyar Usman daya ya furta

“Wayewa ai shi ne boko, ka ga kai da ka ke dan boko Umari hatta shigar ka daban ta ke, yanayin ka daban kai komai na ka ya fita daban ba kamar ni dan daji dan Ruga ba, wanda ko aji ban taba shiga ba bare a kai ga jami’a, ko zo a kashe ka da turanci ba ban sani ba….”

“Da larabci fa?”
Umar ya katse shi ya na mai take mota ganin ya sami sararin hanya.

“Ah wannan Alhamdulillah ai har labari sai na baka da shi”

Kai Umari ya gyada, be gushe ba ya kara da

“Wannan larabcin da ka iya ya fi turancin da ka ke ihun ba ka iya ba, ilimin da ke da shi na addini ya fi wannan bokon da ka ke tunanin shi ne wayewa, da ilimin boko shi ne wayewa da tun lokacin manzo (SAW) za a fara boko, addinin islama shi ne wayewa, ba ka taba yin bokon ba ne, da ka yi da za ka gane cewa komai da ake koyarwa a bokon musammam na bangaran kimiyya akwai su cikin alqur’ani da hadisin Manzo (SAW)”

Usman na mai gyada kai ya furta
“Allahu akbar”
Umar ya kara da

“Wannan rudun da ka ke gani na duniya, ba wayewa ba ne, wannan ba komai ba ne illa zamananci, ka ga wannan shiga tawa da ka ke gani ya ke burge ka, nan da shekaru masu zuwa sai ka ga ana kiran sa da old fashion, ma’ana an bar yayin sa, zamanin sa ya wuce, Allah shi ne zamani Usmanu! Haka kuma mutane nawa ne ga su yan birnin kuma yan boko amma hakan be sa sun kasa shirme ko rashin azanci a rayuwar su ba? Soboda sun yiwa wayewa fahimta daban har ya kai su ga halaka. Haka kuma ita jami’a da ka ke gani, waje ne koyan rayuwa, waje ne in da mutane iri iri daga sassa daban daban ke taruwa domin koyan ilimin boko, toh amma daga karshe ba ilimin kadai ake koya ba, har da dabi’u na dan Adam, mai kyau da mara kyau sai dai wanda yayi dace, da kuwa ilimin addini shi ma ya na da gurbi irin yanda boko ya samu a zukatar bil adama da kuwa boko ya zama ba koman komai ba”

Umar ya fadi ya na mai kallan Usman. Ya kara da

“Ai kai ma wayayye na Usmanu, in kuma ka na so ne ka zama dan zamani zan maisheka dan zamani na koya maka shigar yar birni, Amma fa idan matan birni su ka sako ka gaba ba ruwa na”

Ya karasa maganar ya na dariya. Shi ma Usman din dariyar ya ke, nan kuwa be san Umar har zuciyar sa ya ke magana ba, dan kuwa daga lokacin ya sha alwashin wanke Usman tas ya mayar da shi dan zamani kuma dan birni.

*****
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, in da Zainab ke renon cikin Usman, tare da fama da son shi da tsananin kewar sa, har ta kai in ta yi sujjada ta kan roki Allah ya cire mata soyayyar Usman daga zuciyar ta, amma sai ya zama tamakar abin ma dada karuwa ya ke, dan haka sai ta hakura ta zubawa sarautar Allah ido. Halitta ce ta dage sai da Zainab ta sami waya, amma iyakar ta WhatsApp, bayan shi ba ta wani social network. Zainab the slay Mama ta zama salihar Dady a zahiri da badini, haka kuma ta na kokarin yiwa Malam addua sosai,

Bangaran Usman kuwa yanda Umar ya dage akan mayar da shi dan zamani ya sanya shi mika wuya wajan daukan darasi, ta suturun Usman ya fara, sai da ya tabbatar Usman ya ba da dukkanin kayan sa na ruga sannan tasa shi gaba ya masa ordering shaddu getzner na gani na fada daga SAFFAD Fabrics and more na Hajiya Safiyyah Ummu abdoul, . Rabin shaddu farare ne guda ishirin, sai kuma shudi, ruwan kwai, da kalar toka guda goma. Haka kuma ga material na maza da su boyel. Kanana kaya da takalma ne ya sa ka abokin sa mai shigo da kaya da Uk ya kawo masa. Tun Usman na kokawa akan kudin da Umar ya ke sa shi kashewa, sai gashi shi ma ya zo ya na alfahari da su bayan isowar kayan ya ga kyan su.

Dinki irin na zamani wanda yawanci irin na Umar din ne ya sa aka yiwa Usman, kai hatta roll on sai da Umar ya koyawa Usman yanda ake amfani da shi. A hankali ya ke kokarin fito da Usman gari duk da ba karamin fama ya ke sha da shi ba wajan saka kananan kaya, sai Usman ya ce masa shi wallahi ya na jin kan sa tamkar tsirara musammam idan rigar mai karamin hannu ce. Ran da kayan sa na Uk su ka iso ranar Umar ya zo har gidan gona ta tasa Usman a gaba lalle ya saka daya daga cikin su ya fito ya same shi ya na jiran sa cikin mota.

Umar na zaune cikin mota har ya fara tunanin sake komawa ciki ya taso kyeyar abokin na sa, sai gashi ya fito cikin kananan kaya, shudin riga mai haske, da shudin wando mai duhu, shi kan sa Umar be san sanda ya saka ihu ba ganin yanda kayan ya karbi Usman kwarai, fadi ya ke

“Yo mutumina! Lalle yau za mu dau magana!”

Cike da kunya Usman ya karasa gaban sa, sai a sannan Umar ya lura da silifas ruwan dorawa da ke kafar Usman. Ya na dariya har da kwarewa ya furta

“Toh Malam Shehu! Wannan silifas da ka sha haka ina zuwa?”

Usman na mai kallan kafar sa, da iya gaskiyar sa ya furta

“Yo menene toh? Silifa din ma ba ni sawa?”

“Ka ga wannan magana ta ka sai ka canza Alhaji, kar a ga gaye iya gaye amma in ya bude baki sai aji maganar yar Rugar Shehu”
Usman ya kai masa duka, Umar ya kauce ya na dariya, ya kara da

“Haka kuma tsakanin ka da silifas dan Usumanu sai dai a bandaki, wallahi babu in da zan kara zuwa da kai da silafas kafar ka!”

“Sai na yi zamana! Kai ni fa da na san haka za ka uzzara min da ban ce ina san wayewar nan ba!”

Umar na dariya ya wuce ciki ya na mai furta

“Zamananci dai ko, na fada ma ilimin addanin musulunci shi ne wayewa, wannan da ka ke koya zamananci ne, gishirin zaman duniya”

Usman na duban shi har ya shige ciki, cikin ran sa ya na mamakin yanda ya saba da Umar sosai, dan tun da ya ke be taba yin aminci da abota da kowa ba kamar Umar, cikin kankanin lokaci su ka saba da juna sosai kullum su na tare, haka kuma Alhamdulillah harkar gidan gona ta karbe shi, haka kuma shawarar Umar da ya bi shi ma da alama za ta bulle masa. Ya siyar da shanu fiye da dari biyu da hamsin daga cikin shanun sa, da kudin su ka yi cinikin wani katan fili duk da dai yayi wajan gari kadan amma babu laifi wajan da kwanciyar hakanli da kuma tsaro kasancewar yayi kusa da daya daga cikin check point na sojoji, in da dama nan su ka yada zango kusan na dundundin.

Umar ya fito dauke da daya daga cikin sau cikin da aka turowa Usman. Da kyar Usman ya yarda ya saka. Haka su ka fita ya na masa mitar ya takura masa, shi fa takalmin nan ya matsa masa. Asibitin hakurin da ya ke zuwa ya kai Usman, ga mamakin sa sai gashi dentist din da su ka gani ta ce Usman ba ya bukatar wanke hakori, hakoran sa are so perfect, sai dai Umar ne ke bukata. Ko da Umar ya koka sai Usman ya murmusa kana ya ce

“Kai ne fa Umar ka fadakar da ni cewa addinin mu shi ne wayewa, Manzo (SAW) ya ce ba dan kar ya takurawa al’umar sa ba da ya ce su dinga asuwaki kafin kowacce alwala. Ka ga ban san brush da wannan abun da ku ke shafawa kai ba, Amma na san aswaki da Manzo ya koyarda da mu, shi ya sa baki na ke da tsafta da haske”

Umar na gyada kai ya furta

“Hakkun ka yi gaskiya, Amma kuma wannan karan za ka kara da zamani, idan mu ka gama da asibitin nan za mu biya shopping mall mu siyo su brush da abin goge bakin ka ga sai ka kara wasai ko?”

Darawa Usman yayi, kafin ya kara magana Umar ya kara da

“Ka bari fa Usmanu, yanda ka zama gaye din nan sai fa mun yi da gaske, dan wallahi ba ka bina bashin rantsuwa matan da za su fara binka sai Allah, musammam ga ka da dukiya, fata na dai kada ka yi zaben tumun dare, na kuma san kai mai sani ne, ka ji tsoran Allah ka kuma roki Allah ya kare ka daga kaidin shedanun mata, ya kuma ba ka mace ta gari…..”

“Amen summa amen”

Cewar Usman, cikin ran sa kuwa Zainab ya ke hangowa. Tunanin ko ta cigaba da rayuwar ta yanda ta ke a da ya ratsa zuciyar sa, be san sanda ya furta

“Innalillahi wainnailaihi rajiun! Allahumma ajirni fi masibati haza wakallifni khairan minha!”
A tsorace Umar ke kallan sa ya na tambayar lafiya? Me ya faru. Shi kuwa Usman bakin kishi ne da ya taso ma sa ya turnuke kirjin sa ya sanya shi salati. Amsawa Umar yayi da babu komai, kawai ya tuna wani abu ne. Yayi saurin barin wajen gudun kar Umar ya gane halin da ya ke ciki, dan kuwa sirri irin na Usman ya sa har yanzu be taba bawa Umar labarin Zainab ba.

*****
Sanda cikin Zainab ya cika wata tara chif, ya rage saura sati biyu EDD din ta ya cika Halitta ta dawo Nigeria. Ganin yanda Zainab ta bude ta zama katuwa zama da kyar ta shi da kyar Halitta ta sako ta a gaba da tsokana, duk dai ita ma din dauke ta ke da na ta yaron cikin wata uku cif.

Wata ranar lahadi da yamma likis, Zainab da Halitta sun dawo daga strolling, Halitta ke raka ta kusan kullum safe da yamma. Su ka tadda Anty Sauda zaune gaban Ammy ta hada kai da gwiwa ta na ta sharbar kuka. Hankalin su ba karamin tashi yayi ba dan kuwa a tunanin su ko General ne ya mutu. Muryar Halitta na rawa ta furta

“Anty Sauda lafiya? Ammy lafiya? Wani abu ya sami Genaral ne?”

“Ba gwara wani abu ya same shi ba da cin fuskar da ya min! Ni General zai ci Amana?”

Jin haka Zainab ta samu waje ta zauna cike da mamaki, shin dama akwai ranar da Anty Sauda za ta kuka da General? Mutumin da ta ke ikirarin ta gama da shi ko tsinke ta aje be isa ya tsallake ba sai da izinin ta. Zainab ba ta yi mutuwar zaune ba sai da ta ji Anty Sauda ta furta

“Wai Genaral ya rasa wacce zai auro min sai yar aiki! Da ilimi na! Da wayewa ta! Da arziki na amma ya auri yar aiki na? Wata jaka yar kauyen kayayau! Har ya na ikirarin matukar ba zan iya zama ba toh kofa bude ta ke!”

Jikin Halitta yayi sanyi kwarai, haka ma Falmat wacce shigowar ta kenan ita ma ta tsinci maganar. Ammy kuwa ta dade da kasa magana tsabagen al’ajabi. Zainab ce kadai ta furta

“Tooooh yar kauye fa Anty Sauda? Ki na nufin yar kauye dai kamar miji na Shehu?”
Ta yi maganar da manufa biyu wanda in aka dauki Anty Sauda babu wanda be fahimci in da Zainab ta dosa ba, Anty Sauda ta furta

“Irin su fa tsinannun tsintattun mage! Kuma ita ma din bafulatana ce waya sani ma ko Rugar su daya shi ne ya min shune tsinannun! Sai na yi maganin su! Wallahi bokan ta ya mata karya yanda na sha wahalar mallakar Malam sai ba ta isa ta zo da ruguje min ba! Yarinya ce fa kankanuwa! Ga ta bagidajiya! Kin san mazan nan daga na barta ta na masa girki saboda business ya dan fara hawa kai na, shi ne ta yi amfani da damar ta ta masa barbade….”

“Assha kin ga inda kuskuren na ki ya ke Anty Sauda, wayewa da ganin ke kin isa ya sanya ki ka bari wacce ki ke tunanin bagidajiya ce kuma yar kauye ta aure mutum mai daraja kamar General! Kenan akwai lokacin da wayewar ba ta amfani…!”

“Yakura!!!”
Ammy ta dakawa Zainab tsawa, in da Anty Sauda ta saki baki ta na duban ta. Zainab ta dubi Ammy ta furta

“Ammy kar ki hana ni magana! Ranar wanka ba a boye cibi! Ina ga nan Anty Sauda ta zauna ta gama kare min tatas! Har fadi ta ke ilimi na da jami’a ta be amfana min komai ba na rasa wanda zan so sai dan kauye! Da ke da na shiga jami’ar ko wayewar ita ce mizanin auna darajar dan adam ko azanci na dan adam! Ita ya aka yi ga shekarun, ga wayewar, ga arzikin ga ilimin amma ta yi sakaci irin wannan? Da wayewa, ilimin boko ko shiga jami’a shi ne mizani azancin dan Adam da wayyayu dayawa ba su halaka ba! Da yan kauye dayawa ba su cigaba ba! Wannan abun da ya faru da ke kukan kurciya ne Anty Sauda!”

Kuka Anty Sauda ta saka, fadi ta ke

“Ni Yakura? Ni ki ke gasawa maganganu haka? Na dade da sanin ba ki da kunya amma ban taba tunanin za ki iya shafawa idanun ki toka ki gasa min cin kashi haka ba!”

“Yakura ki bata hakuri! Ba ki kyauta ba!”

Cewar Ammy cikin tsawatarwa. Sai da ta yunkurin tashi da kyar, ta dubi Anty Sauda ta ce

“Allah ya ba ki hakuri tunda Ammy ta ce na baki hakuri, Amma sam ban yi dana sanin maganar da fada mi ki ba, rayuwa dai is a circle, na dade da gane haka ina kuma fatan ke ma za ki gane”

Ta wuce ciki ba tare da ta damu da kukan da Anty Sauda ta ke yi ba, bare fadan da Ammy ta bita da shi. Nan ta ke Anty Sauda ta ja jakar ta tace ta fasa zama gidan Ammy. Sai da su ka yi da gaske sannan ta hakura, ta ce amma Ammy ta mata tsakani da mara kunyar diyar ta. Ita kan ta Ammy mamakin yanda rayuwa ta juya ta ke, Halitta da Zainab wanda da ba sa ga maciji ne yau su ka zama tamkar aminan juna, Anty Sauda da Zainab wanda su ka saba kullawa su kunce babu wanda ya sani ne yau kuma ba sa ga maciji. Lalle kam rayuwa na da ban mamaki.

Tun kafin EDD din Zainab ya cika, ana sauran sati guda Zainab ta tashi da nakuda, wuni daya ta yi cur ta na yi sannan Allah ya sauke ta lafiya ta haifo dan ta namiji mai kama da Shehu sak tamkar yayi kaki ya tofar. Ita kan ta Zainab da aka daga mata shi sai da gaban ta ya fadi kasancewar shi jinjiri be sa ta kasa ganin Usman a fuskar sa da komai na sa ba.

Ko da aka miko sa hannun ta, ta na hawaye ta masa huduba ta saka masa suna Usman. Yanda ta ke yi ya sanya nurse din tambayar ta ko dai uban dan ya rasu ne? Zainab na duban Usman junior ta furta

“Eh ya rasu tun kafin na san ina dauke da cikin dan sa, Amma gashi Allah ya kara dawo min dashi, sai dai wannan karan jini na ne, tsatso na”

Cike da tausayawa nurse ta furta

“Allah sarki, Allah ya ji kan sa ya kuma raya dan sa”

Zainab ta amsa da “amen”

Babu wanda be yi murna da haihuwar Zainab ba, hatta Anty Sauda sai da ta aje fushin ta gefe da ta ga dan da Zainab ta haifa. yaro sak uban sa, kai ka ce balarabiya ta haifo sa. Jin Zainab ta saka sunan Usman ba Malam da kowa yayi zato ba sai da aka yi dan kananan maganganu. Zainab kuwa ta ce da dai ita ta haifo kayan ta, kuma Usman ta ga daman saka masa, za kuma ta kira shi Shehu, ta ga wanda ya ke da ikon canzawa dan ta suna.

Ranar suna aka sha shagali, Hajja Kilishi da na ta ayarin sun yiwa Ammy kara kwarai dan kuwa sai bayan suna da kwana biyu su ka tafi.
****

Bangaran Usman kuwa ya na can ya na hidamar kafa Rugar Shehu cikin saban gidan gonar da ya ke ginawa sam be san an masa takwara ba. Umar ya mayar da shi dan zamani, dake dama mutum ne mai ilimin addini gashi ya hada da zamananci nan da nan ya zama goge. Kullum cikin masa tayin aure ake, abokan sana’ar su ne, mata masu kawo kan su kai har ma daga bangaran Alhaji Ibrahim Balla, Amma kullum Usman cikin zillewa ya ke. Har Umar ya gaji ya fito ya tambayi Usman shin lafiyar sa kalau kuwa? Usman ya bashi amsa da kada ya damu, dake su na shirin zuwa Rugar Shehu domin taho da wasu daga cikin shanun Usman, ya ce ya bari idan su ka dawo zai masa bayanin komai. Da haka su ka dauki hanyar su na Rugar Shehu.

Amma ko da su ka isa Mambila, aka yiwa Umar bayanin tafiyar kasa da za su yi kafin su karasa Rugar Shehu nan yayi kememe ya ce ba shi iyawa. Usman dai ya je ya dawo shi zai yi tsimayin shi nan Mambila. Hakan ko aka yi, Usman shi kadai ya niki hanya har Rugar Shehu.

Ganin yanda Usman ya canza kasa gasgata zatan su na Shehun na su ne da gaske. Nan fa Usman ya zama abin kallo kamar yanda Zainab ta zama farkon zuwan ta Rugar Shehu, bambamcin dai shi wannan mamakin yanda Usman ya canza gaba daya ne ya rufe su. Kowa burin sa ya taba Usman. Shaddar da ke sanye jikin sa, hular kan sa kai hatta takalmin kafarsa abin kallo ne gare su. Cikin su har da masu fadin babu shakka cikin wannan injin kyera mutane da aka ce akwai a birni aka sanya Usman, ya zama dan birni tamkar kado.

Bayan komai ya lafa ya mu su bayanin abin da ya ke tafe da shi. Wato na mayar da Rugar Shehu cikin birni. Kamar yanda yayi hashashe, dayawa daga cikin su sun yiwa maganar mummunar fahimta, ciki har da Kawu Iliya. Amma ko da Usman ya tsaya ya mu su bayani mai gamsarwa sai su ka dan sauko, Amma duk da haka su ka ce bazai yiyu kowa yaye a bar daji ba. Duk sanda Usman ya gama shirin sa ya zo wasu daga cikin jama’ar Rugar su bishi, a fara ganin yanayin zaman da yanda zai kasance, idan har abu yayi kyau saura jama’a su bi bayan su, idan aka sami kishiyar haka kuma toh lalle wanda su ka bishi sai su dawo gida. Haka kuma shanu mallakan sa ne, ko da kuwa dubu zai kore zuwa birni ba zai talauta Rugar Shehu ba, dan haka babu mai tsayar da shi, adduar su dai kawai Allah ya idda nufi, ya kawo mu su alkhairi.

Kwanan Usman biyu kacal a Rugar Shehu, ana gobe zai koma Bello ya zo masa da sakon Raqeeba na ta na so ta gan shi. Usman ya ce toh bisimillah mana. Nan cikin bukkar shi ta zauna tare da mijin ta Bello. Usman na daga zaune can gefe yayinda zuciyar sa ta masa nauyi jin maganganun da ke fita daga bakin Raqeeba. Ta kwashe abin da ya faru tsakanin ta da Zainab, da kuma yanda ta tunzura ta har ta yarda ta hada baki da su Rahila ta fada mu su. Cike da nadama ta kare da

“Abu mai kaunar ka ce kwarai, sharrin shedan ya sa na aikata abin da na aikata amma sam babu laifin ta, laifin ta daya shi ne zafin kishi, dan sai a sannan ni kai na na gane Abu mai kaunar ka ce…..”

Ganin Usman ya runtse idanu ya sanya Raqeeba kasa magana, cikin neman agaji ta ke kallan Bello wanda tun da ta gano ta kamu da san shi ta fada masa abin da ta aikata. Bello ya gyara muryar sannan ya furta

“Ta yi kuskure, tun da ta fada min na nuna mata bacin rai na…..”

“Tun da ta fada ma ka? Ka na nufin ta ma fada ma ka amma ka kasa sheda min Muhamadu?”

Ya na kokarin kare kan sa ya furta

“Ah ah watan jiya ta sanar da ni, dama jira na ke….”

“Ya salam matar ka ta cutar da ni, ni Kuma na cutar da Abu! Har ka san wannan maganar amma ka kasa fada min? Watan jiya? Kasan kwana nawa na yi kullum da kewan Abu? Ka san dare nawa ya shude kullum da ita na ke mafarki? Kasan kwanaki nawa na yi kullum zuciya ta na kukan rashin ta? Haba Muhamadu Bello! Haba dan Allah!”

Cewar Usman yayinda ya tashi a firgice ya shiga hada kayan sa. Alama Bello ya yiwa Raqeeba da ta tashi ta tafi. Tsoran fushin Usman ya sanya ta kiran su Kawu Iliya. Su ka tadda Usman ya dau jaka har ya fito. Sun yi sunyi su bashi hakuri ya bari gari ya waye sai su tafi amma Usman yaki. Gani ya ke kowani sakan idan ya wuce ba tare da ya na hanyar Kano ba asara ne a gare shi. Dole suna ji suna gani su ka bar shi ya dau hanyar Mambila cikin daren.

Sai da gari ya waye tangararan rana ta hudo kai sannan ya isa Mambila. Nan ma abinci kawai ya ci sannan ya tasa Umar a gaba lalle su dau hanya Kano. Yanda dawo masa afujajan ya sanya Umar shiryawa su ka dau hanya ba tare da ya masa mu su ba. Tun da su ka dau hanya Usman ya je rama baccin da be yi daren jiya ba. Umar ya daga masa kasa har sai da su ka isa Jalingo, bayan sun yada zango hotel din da su ka saba sauka ya je har daki ya same shi.

Babban daki ne wanda ya kai matakin dakunan da alhazawa su ke kamawa. Bayan ya buga masa kofa ya bude masa, ya sake komawa ya yi zaman sa bakin gado, sanye da farar singileti da gajeran wando. Umar ya dube shi ya ce

“Na lura tun da ka dawo ba ka cikin hayyacin ka, me ke faruwa? Me za su yi Kano?”

“Abu zan dauko”

“Wacece Abu Kuma?”

Umar ya tambaya cikin nuna rashin fahimta. Nan Usman ya bashi wani bangare daga cikin rayuwar shi da Zainab ba tare da ya tona sirrin da ya shafi dakin auren sa ba. Kafadar shi Umar ya dafa sannan ya ce

“Sai yanzu na fahimci dalilin da ya sanya ka ki kula kowa. Lalle ni zan raka ka har Kano, Amma fa gaskiya ba za mu je haka yanda ka ke a burkice ba Malam! Sai ka nutsu ka kuma kwantar da hankalin ka!”

“Shin ka na ganin Zainab za ta yafe min?”

Umar na jinjina kai

“Matukar ta na san ka kamar yanda ka nuna min, za ta yafe ma ka Usman, dukkan ku kun yanke hukunci ne cikin rashin sani da gaggawa, duk ilimin ka, ita kuma duk wayewar ta be sa kun iya gujewa kaddarar ku ba, yanda za ka sani ajizanci ne na dan adam, shi dan adam ajizi ne Usman”

Kai Usman ya gyada kawai. Umar ya masa sallama, ya bar shi nan zaune ya na fargaban yanda zai tunkari Zainab bayan wata da watanni da tura ta gida.

Kamar yanda Umar ya ce, sai da ta tabbatar Usman ya nutsu sosai, sun kuma shirya zuwa gidan surukai da kyau sannan su ka dauki hanyar Kano, Usman ya so su bi jirgi, Amma Umar ya dage sai dai su tafi a mota. Daya daga cikin manyan motocin Alhaji Ibrahim Balla ya dauko dan har lokacin Usman be iya mota ba, bare ya mallaki ta kan sa, Umar kuwa ganin za su je gidan surukai da aka dade ba a hadu ba ya ga dacewar a je da babba harka yanda za su cika ido da kyau.

Da ya ke tun asuba su ka bar Yola, kuma Umar ya taka motar sosai, karfe hudu a Kano ta mu su. Kai tsaye Prince hotel su ka wuce in da su ka kama dakuna biyu. Dan zumudi jikin Usman har rawa ya ke. Umar na duban sa cikin zolaya ya ce

“Wallahi in ba ka dena wannan rawar jiki da zumudi ba babu in da za mu je yau sai gobe”

Fuska murtuke Usman ya furta

“Sai in ga me hana ni fita! Da ka san yanda na ke ji Umar da ka tausaya min”

Umar na murmushi ya ce
“Ni ma zolayar ka na ke, maza ka je ka shirya, ka tabbatar ka kure a daka yanda ko Abun ta ka baza ta gane ka ba, bare masu gadin nan da ka ba ni labarin su”

Cike da farin ciki Usman ya bi bayan wanda zai nuna masa dakin sa, ya na mai bawa Umar amsa da

“Yau kuwa zan ba ka mamaki Umari, dan ko kai kan ka ba za ka gane ni ba”

Haka su ka yi sallama su na wasa da dariya. Usman be bata lokaci ba nan da nan yayi wanka. Wata danyar farar getzner wacce aka mata aiki da shudin zare dinkin babbar riga ya sanya. Bayan ya feshe jikin sa da tuare mai tambarin ‘Boadicea the Victorious’, ya dau hularsa da aka saka da manyan zare kalar aikin babbar rigar sa sai dai kuma akwai wasu kalolin da su ka ratsa jiki, hular ta sha wanki da kari ya sanya. Daga agogon hannun sa har zuwa takalmin kafarsa kudi ne. Shi kan shi da ya kalli madubi, mudubi sai da ya kara dubawa. Lalle kam sutura ita ce mutum!

A restaurant ya sami Umar ya na cin abinci, ko daga shigan Usman ba sauran jama’ar da ke wajan ba, hatta Umar sakin baki yayi ya na duban sa har ya karasa teburin da ya ke.

“Butar shayi mutumin nan ka hadu! Wannan ado duk na zuwa biko ne?”

Cewar Umar cikin zolaya. Kujera ya ja ya zauna, kana ya ce

“Ka yiwa girman Allah ka min adalci ka bar wannan abincin mu tafi, wallahi da ka san halin da na ke ciki da ka tausaya min Umar”

Baki cike da shibkafa Umar ya ce

“Adalcin shi ne ka bari na cika timbi na Alhaji, da dai ace zuwan dadi ne da sai na sa ran za a ba mu na dare, Amma hakan nan siddin mu taso tun daga Yola har Kano ka hana cin abinci? Babu wannan maganar”

Cikin kosawa Usman ya furta
“Sai ka ta ci ai, idan ka gama ina jiran ka a mota”

Ya tashi ya fice in da matan da ke wajan su ka bishi da kallo. Shi kuwa gaba daya hankalin sa yayi gaba, in ba Zainab ya sa a Ido ba ba zai sami nutsuwa ba.

Sai da Umar ya take tumbin sa sannan ya fito su ka dauki hanya. Ko da su ka karasa gidan Malam su ka yi hon, Jauro ya ga motar da ke fake bakin kofa tuni ya bude mu su gate ba tare da ya damu da ya duba su waye cikin motar. Umar ne ya fara fitowa bayan sun yi fakin farfajiyar gidan, da sauri Jauro ya karasa gaban sa ya ba fadin

“Barka da zuwa Alhaji, sannu da zuwa Alhaji”

Ganin dogan mutum fari sol, ga kyau ga kwarjini ga kuma sutura, ya fito daga motar, Jauro be sanda ya zube kasa ba cikin fadanci, fadi ya ke

“Allah shi ja zamanin ka, barka da zuwa”

Shi kan sa abokin aikin Jauro bude baki yayi ya na kallan sa, dan kuwa tun bayan tafiyar musu ya can ji gurbin sa, be taba ganin Jauro ya rikice kamar yau ba. Shi kan sa Usman ya san tabbas Jauro be gane sa ba. Ya na shirin tambayar in da Zainab ta ke sai ga Anty Sauda ta fito. Ganin mota mai numfashi fake farfajiyar gidan da kuma mazan da su ke tafe cikin motar tuni ta karaso ta na tambayar

“Baki mu ka yi ne? Ko wajan Falmat ku ka zo ne?”
Har kasa su ka tsugunna su ka gaishe ta, Anty Sauda na fadin

“Ku tashi, ai ba sai kun tsugunna ba”
Umar ne ya ce da ita wajan Zainab su ka zo. Duk yanda ta so ta buye disappointment din jin Zainab aka zo nema sai da ya dan nuna a fuskar ta. Ta kan ta ta yi mu su jagora har cikin falon Dady, sai da ta tabbatar su zauna sannan ta wuce ciki ta shedawa Ammy halin da ake ciki, ta kare da

“Wallahi matasa ne daga kin gan su kin ga ‘ya’yan manya, Amma na san rashin mutuncin Yakura yanzu sai ta watsa ma na kasa a Ido, na ga tun da ta haihu ta ke jin maganar ki da kyau, ko za ki lallba ta fita su gaisa?”

“Toh Yakura ce ai ba a mata abin arziki, bari na gwada sa’a ta, a ina ki ka ce ke?”

Cewar Ammy cikin fargaban abin da zai je ya dawo.

“Su na can falon Malam”
Ammy ta ce
“Toh bari na gwada”

 

 

 

 

 

 

 

No comments