Breaking News

Auren Shehu Book 2 Page 16

AUREN SHEHU 2

Finale…

“Ammy I’m not expecting visitors, Dan Allah ki ce mu su ba zan gan su ba”

Cewar Zainab ta na kokarin gyara diaper din Shehu. Tun da Ammy ta fada mata ta yi baki, ta ce su shigo ciki mana, ta ce da ita ai maza ne, ta yi mirsisi ta ki tashi. Ammy na duban ta ta kara fadin


“Ki yiwa Allah da manzan shi ki tashi ki je ki ga su waye Yakura, barka fa su ka zo mi ki”

“Toh Ammy me zai sa baki maza su zo nema na saboda Allah da manzan sa, har ki na ce da ni Anty Sauda ta ce daga gani ‘ya’yan manya ne, Ni ina ruwana da girman iyayen su! Ban san su ba, ban zuwa kuma”

Rai bace Ammy ta furta
“A matsayi na na mahaifiyar ki na baki umarnin ki tashi ki je ki ga ko suwaye! Ba kuma na san musu!”

Zainab na jin haka ta shuna baki. Ta mike Tsaye ta na gunguni. Doguwar rigar atamfa ce jikin ta, dake jikin jego ta kara cikowa ta koina ta murmure. Dankwalin atamfar ta daura irin wannan daurin da ake kira ture ka ga tsiya, ta ja mayafi ta yafa a kafada. Ganin ta na kokarin daukar Shehu Ammy ta furta

“Ki bar shi mana tun da bacci ya ke”
Ta na mai aza shi kafada ta ce

“Ah ah ai na zaci barka su ka zo yi, na je ma yan barka ba jinjiri?”

Ba ta tsaya ta saurari amsar Ammy ba ta yi waje fuu kamar wacce za ta tashi sama.

Usman kuwa tunda su ka zauna ya tsurawa kofa idanu duk da Umar ne zaune daidai kofar. Umar na kokarin masa hira amma ina hankalin sa ba ya jikin sa, yayi nisa baya jin kira.

Sallamar ta da shigan ta falon lokaci daya ne, idanun ta kan Umar ya fara sauka, in da shi kuma Usman ya shiga duban ta cikin rudani. Idan aka dauke yanayin tsiwar da ta shigo da shi, da Kuma tsayin ta komai na Zainab ya canza, dama tunda Zainab dirarriyar mace ce, Amma yanzu sai ta zama irin matan nan da aka fi sani da zaratan mata, kamar wacce makerin dare ya kyara. Baban abin da ya saka shi cikin rudani shi ne yanda ya ga alamun kumburi kafar ta, da kuma yanda alamun jego ya bayyana dukkanin gabobobin jikin ta, dadin dadawa ga jinjiri kwance kafadar ta.
Ba kunya ta gama karewa Umar kallo tas, ta tabbatar ko mai kama da shi ba ta sani ba, ta na kokarin kallan Usman ta karasa ciki, fadi ta ke

“Sannu da zuwa, gashi kuma ni ban san ku ba bare na san a dangin wa ku ka zo min……..”
Cak ta tsaya ta na duban shi kamar yanda shi ma idanun sa ke cikin na ta. Idanun da har ta koma ga mahaliccin ta ba za ta taba mantawa ba. Baki ta bude da niyar magana, bayan sakanni ta sake rufewa, ji ta ke tamkar mafarki ta ke, sai kuwa ta lumshe idanun ta na dab wani dan sakanni, sannan ta sake budewa. Mai kama da Usman din nan dai be bace ba, sai ma tasowa da yayi ya nufo ta. Kallan sa ta ke tun daga sama har kasa, shigar da yayi ya sa ya kara kwarjini kai ka ce wani basarake ne ko kuma wayayyen dan kasuwa wanda ya ci ya tara. Ba ta dada gasgata abin da zuciyar ta ke fada mata ba, sai da ya tsaya gaban ta, ya kalle ta, sai ya kalli jinjirin da ke kafadar ta da lokacin be samu ya ga fuskar sa ba, cikin yanayi mai wuyar fasaltuwa ya furta

“Abu……”

Zainab ta runtse idanun ta dan tun daga kwakwalwar kan ta, har zuwa yatsun kafarta ta ji kiran.

“Abu……”

Ya sake kiranta ya na kokarin ruko ta, Zainab ta ja da baya da sauri ta na mai girgiza masa kai. Murya na rawa ya furta

“Na sani Abu, na san ban kyauta mi ki ba, ban mi ki adalci ba…….”

Juyawa ta yi da sauri za ta fita, sai a sannan Usman ya ga fuskar takwarar shi, wanda ganin sa sai da ya zauna dirshen kasa.

Umar ne ya taso ya tsugunna gaban sa tare da taba kafadar sa. Usman ya dago da sauri ya dube shi, gaba daya ya manta da zaman shi a falon. A hankali ya furta

“Da na ne…..na zalinci Abu Umar”

“Ba da niya ka yi ba, za ta fahimce ka, za kuma ta yafe ma ka…..”

Cewar Umar yana kokarin karfafa gwiwar Usman. Zainab kuwa da ta shiga ciki ta tarar da Ammy, Anty Sauda, da Hallitta zaune falo ko takan su ba ta bi ba, ta shige dakin ta yayinda hawaye ke gudana daga idanun ta. Kallan kallo su ka shiga yi, kowanne na tunanin ko lafiya? Kafin daga bisani Ammy da Halitta su ka bi bayan ta, Anty Sauda ta yi zaman ta cewar ta koma menene ita dai ta na daga nan.

Ammy da Halitta sun yi juyin duniyar nan akan Zainab ta fada mu su dalilin kukan ta, Amma ta ki, sai kai da gwiwa da ta hada ta na rera kuka mai sauti, in da Shehu da ke kwance kusa da ita ya ke taya ta da na shi kukan.

Ganin ba za su sami abin da su ke so kusa ba Halitta ba ta dau Shehu ta mikawa Ammy tare da fadin

“Ammy bari dai na bi sahun bakin da ku ka ce sun zo gun ta, babu mamaki sakon mutuwa su ka zo mata da shi”

“Eh gaskiya, maza bi bayan su, Allah ya sa dai ba su tafi ba”

Da saurin ta ta fita. Anty Sauda na tambayar ko lafiya? Ta ce mata ta na zuwa. Cikin falon Dady tadda su zaune in da Zainab ta bar su. Kallo daya ta yiwa Usman ta gane shi. Fuskar ta dauke da emotions iri daban daban ta furta

“Me ya sa Usman? Me ya sa sai yanzu ka zo? Me ya makarar da kai har haka? Kar ka fada min duk watannin nan ba ka farga da kuskuran da kuka tafka ba sai yanzu?”

Be taba tunanin wani daga cikin dangin Zainab za su iya ganin shi su kyale ba tare da sun masa wankin babban bargo ba, Amma duka tunanin na sa ya manta Malam na da diya kamar Halitta, wacce har abada ba za ta taba canzawa ba. Ya na mai duban ta cike da godiya ya ce

“Na yi kuskure mafi girma kanwa ta… Shin ko za ku iya yafe min?”

“Yafiyar mutum daya ce mafi muhummanci a gare ka, shin za ka zauna ne nan ka na dana sani, ko kuwa ka shirya gyara lamarin ka da iyalin ka?”

Cewar Halitta ta na mai duban Usman. Wanda ya tashi cikin azama ya na fadin

“A shirye na ke kanwata”

“Toh bisimillah”

Nan su ka bar Umar, Halitta na tafe Usman na biye da ita, a bakin kofar ya dakata Halitta ta shiga ta ce da Ammy ta dan shirya za ta shigo da bakon da ya zo.
Har ya shigo ya tsugunna gaban ta ba ta gane shi ba, be sa ta cikin rudani ba sai da ta ji ya bude baki ya ce

“Hajiya ban san da wani ido zan kalle ku ba, ban san da wani baki zan ba ku hakuri ba……”

“Waye wannan wai Halitta?”

Ammy ta katse shi cikin kin gasgata zuciyar ta. Ta na nuna shi da dan yatsa ta sake furta

“Kar dai wannan maci amanan maigadin nan da Malam ya dau diyar cikin sa ya basa amma karshe ya saka mana da sharri”

Jin haka Anty Sauda ta ware idonu zuciyar ta daya ta furta

“Haba ke kuwa Hajja Aleesha, duba ki gani fa da kyau! Ina ke ina hada wannan wayye kamulallen mutum mai daraja ta wannan tsinannen almajirin….”

“Haba Anty Sauda, kada ki manta wannan da ki ke magana akai shi ne mahaifin dan da Yakura ta haifa, in da kara ba kya zagi uban dan Yakura ba”

Jiki sanyaye Anty Sauda ta ke kara duban shi, wato lalle da gaske shi ne mijin Yakura? Toh dama karya ake da aka ce shi maigadin gidan Malam ne, ko dai dama bad da kama yayi tun asali dan masu hali ne ya zo mu su a almajiri. Shi dai Usman ya sunkuyar da kai, zai iya jure duk hukuncin da za su dauka matukar ba za su hana shi iyalin sa.
Anty Sauda na sosa kyeya ta ce

“Uhum toh gaskiya dai ina ga dama tun farko akwai kuskure, ai ni da na san wannan aka aurawa Yakura da sam ban tada hankali na ba. Hajja Aleesha ai ina ga zai fi a bari ya shiga ya sami Yakuran can su sasan ta…”

“Sasan ta me?”

Ammy ta katse ta a fusace. Ba ta gushe ba ta kara da

“Babu wani abin sasantawa! Da tana so su sasan ta da ba ta shigo ciki ta na mana kuka kamar wacce aka aikowa sakon mutuwa ba! Ke kin san wacece Yakura! Ka sace min diya! Ka kai ta dokar daji! Ka katse mata karatun ta! Sai da ka tabbatar ka bata mata rayuwa sannan ka sako ta mota tsabagen zalinci! Tun da ta dawo ba mu kara gane kan ta ba, ta zame mana tamkar bakuwa, a haka ta yi renon ciki, sai da ta haihu za ka wani kwaso jiki cikin manyan kaya ka zo gare mu? Ka ga mun ma ka kama da matsiya ta? Ko kana tunanin za ka yaudare mu da wayewa ne….?”

Hawaye ke fita daga idanun Usman, cike da nadama ya furta

“Wallahilazim ba haka ba ne Hajiya, ba wannan ba ne munufa ta, na yi kuskure kuma na yi nadama, ku yafe min. A shirye na ke na dau duk wani hukuncin da za ki yanke, Amma kar ku raba ni da Zainab, wallahi ba zan iya rayuwa babu ita ba”

“Toh tantabara! Ai watannin da ka korota ba rayuwa ka ke ba ko? Gawa ne kai duk wannan lokacin hala? Tashi ka fitar min daga gida! Tashi ka fita!”

Cewar Ammy cikin daurewar Fuska. Nan su Halitta ta su ka shiga ba ta baki. Amma Ammy ta juya mu su baya. Haka kuma duk magiyar duniyar nan yayiwa Ammy da ta bari ya gana da Zainab ba, ya kuma dauki Shehu, Amma ina Ammy ta riga ta hau sama. Haka ya karaci hawayen sa ya fito ya tadda Umar jikin mota ya na jiran sa. Yanayin da ya ga Usman ya sa ko tambayar halin da ake ciki be yi ba, kawai mota su ka shiga in da Umar ya tada ya juya kan motar. Bakin gate Jauro ya cigaba da mu su fadanci har sai da Umar ya fito da kudi ya danka masa. Ya na godiya ya daga mu su hannu har su ka fice. Bayan tafiyar su abokin Jauro ke tambayar na shi kason, Jauro ya hana, cewa ya ke

“Kai me ya hana ka zuwa ka karbi na ka? Ka na ganin mota mai numfashi, da kuma irin manyan da ke jan motar amma ka yi fuska! Toh wallahi raban da na ga mota irin wannan ta shigo gidan nan tun Malam na da rai!”

“Yanzu dai ba za ka bani ko sisi ba?”

“Ko asi ban ba ka”

Cewar Jauro yayinda ya wuce abin sa ya na lissafa adadin dadin da zai ci da kudin sa.

*****

Har su ka kai hotel din su babu wanda ya tanka. Bayan sun yi fakin ne za su rabu Umar ya dube shi ya ce

“Kar ka damu Usman, komai zai daidaitu”

Murmushi Usman ya masa, sannan ya wuce ciki ba tare da ya iya ce masa komai ba. Umar ne ya masa order abinci ya sa aka kai masa har daki. Ganin yunwa na neman halaka sa ya sa ya dan caccaki abincin, Amma sam ya kasa sukuni bere ya runtsa, sai juyi ya ke akan gado. Ko da ya duba agogo ya ga sha biyu sai ya ta shi wuf, jallabiya ya sanya saman singiletin jikin sa, dakin Umar ya nufa kai tsaye.

Zainab kuwa tun tafiyar Usman ta shiga wani hali, zuwan shi ya fama mata ciwan da ta ke tunanin da ya fara warkewa. Ammy ce ta yi ta bata baki, ta kuma mata alkawarin kar da ta damu in dai Usman ne ba zai kara saka kafa gidan ba, ta masa korar kare. Maimakon ta ji sanyi cikin ran ta kamar yanda Ammy ke zato, sai ma dada saka ta cikin hali mai wuya ta yi.

Kwance ta ke bisa gadon ta, ta tsurawa Shehu ido amma a zahiri tunanin Baban sa ne ya addabi zuciyar ta. Tambayoyi kala kala ke yawo cikin kan ta, Shin me ya same shi har ya canza haka? Ya aka yi ya iya shiga irin na wayayyu haka? Me ya kawo sa wajan ta? Shin ya zo ya tafi da ita ko kuwa dai ya ji labarin ta haihu shi ne ya zo ya raba ta dan ta?

Tsigar jikin ta ne ya tashi yayinda ta ji makogaran ta ya bushe. Ta tashi ta yi, ta na neman ruwan da ta saba ajewa a dakin ta rasa, dole sai fita ta yi ta nufi kitchen neman ruwan sha.

Tun fitowar ta daga dakin ya lura da ita, yanayin duhun falon be sa ya kasa gane Zainab ba. Ta gaban shi ta gifta amma sam ba ta lura da shi har ta isa kitchen din. Hakan ya bashi damar shigewa dakin da ta fito daga cikin.
Ganin an bar kofar kitchen din wangale ba sakata bare a sa mukulli ya sanya ta jan tsaki. Ta yi saurin karasawa ta ja kofar ta rufe. Sai sannan tsoro ya kamata, ta yi saurin daukar ruwan gora ta shige ciki kamar wacce za ta arta a na kare.

Jin tahowar ta yayi sauri aje Shehu, ya koma bayan kofa ya tsaya. Ko da ta karaso ta ga kofar da ta rufe da hannun ta shi ma wangale, da gudu ta karasa ciki wajan Shehu, daukar shi ta yi ta na mai duba lafiyar sa, ta ga dai lafiya lau ya ke, sannan hankalin ta ya dan kwanta, babu mamaki tsabagen tunanin da ta ke yi ne ya sa ta yi zaton da ta fita ta rufe kofar. Kara aje Shehu ta yi, hannun ta dauke da ruwan da ta dauko ta karasa kofar dakin ta ja ta rufe. Nan su ka hada idanu, ta bude baki za ta saka masa ihu yayi saurin janyo ta jikin sa tare da hade bakin shi da na ta ya fara kissing din ta. Tun ta na kokarin kwacewa har jikin ta yayi sanyi ta yi lamo ta na ganin ikon Allah, kafin daga bisani ita ma din ta fara mayar masa da martani.

Kukan Shehu ne ya dawo da su daga cikin hayyacin su, Usman yayi baya da sauri yayinda ita kuma ta karasa wajan sa, cikin ran ta tana godewa Allah da ya kwace ta daga hannun Usman. Usman jingine jikin bango, cike da so da kauna ya ke duban ta yayinda ta dauki dan sa cikin tattali da rarrashi. Ba ta damu da ya na wajan ba ta sanya masa abin da ya ke bukata a baki, Shehu yayi saurin cafkewa ya shiga zuka dama abin da ya ke jira kenan. Yanda ya ga ta dan runtse idanu alamar ta ji zafi ya sanya shi motsawa kusa da ita da sauri ya na fadin

“Sannu Abu, da zafi ko?”
Sai a sannan ta tuna ashe fa ba mijin ta ba ne, ta yi saurin jan mayafi ta rufe kirjin ta, Manyan idanun ta ta watsa masa cike da harara ta furta

“Malam me ya kawo ka gidan nan tsakar dare haka? Yaushe ka fara haura katanga? Me ya kawo ka daki na?”

Daf da ita ya zauna hakan ya sa ta dada muskutawa domin ba da tazara a tsakanin su. Hakan ya kara sa Usman dada matsawa kusa da ita, ita ma din ta kara matsawa, haka su ka ta yi har ya kure ta jikin bango.

“Wai menene! Zan ma ka ihu wallahi!”

“Toh in kin min ihu an zo an gan ni dakin mata ta sai menene?!”

“Wacece matar ta ka? Idan ma kana shirin dawowa da ni wallahi gwara ma ka fidda rai! Ka riga ka sake ni, I don’t care daya ne ko uku, babu ni babu kai”

“Saki kuma? Ni Usmanu na sake ki? Toh abin na ki kuma ya koma sharri ne Abu?”

Takaici ne ya sa ta kasa magana. Ganin ba ta da niyar tanka masa ya sake furta

“Yanzu dai menene shedar sakin da na mi ki fisabilillahi?”
Tashi ta yi a fusace har nono na fita daga bakin Shehu, ya dan saka kuka amma ko ta kan sa ba ta bi ba sai da ta dauko takardar da ya bata, ta aje masa, ya fi takardar da idanu. Cike da tsiwa ta kara da

“idan ka gama dubawa za ka iya fitar min daga daki!”

Takarda ya dauka ya buda, ganin abun da ke ciki ya sa shi dariya, tabbas zatan shi ya tabbata. Ganin yanda ya ke dariya ya sanya ran Zainab kara baci. Musammam da ta ji ya furta

“Shin ko sau daya kin bude takardar nan kuwa Abu, ko kuwa dai tsabagen ba a iya karanta ajami ba ne?”

Ba ta so ya san ba ta taba budewa ba saboda kar ya gane tsabagen tsoran yawan sakin da ya mata ya sa. Dan haka ta ba shi amsa da

“Na karanta mana da ban karanta ba ta ina zan san sakin da ka min?”
Ta karasa maganar tana mai dora Shehu bisa kafadar ta, domin ta samu yayi gyatsa. Idanun shi na mata dariya ya bude ta takardar ya ce

“Toh kuwa Abu sai dai wata takarda ki ka karanta ba wannan ba, dubi wannan da kyau ki gani, ban sani ba ko kin san yanayin rubutun Malam, Allah ya jikan sa da rahama, wannan rubutun shi ne duk da dai jinya ta sa be fita sosai ba”

Hannu na rawa Zainab ta karbi ta kardar, ko shakka babu rubutun ya fi kama da na dan koyo, kalma biyu ne kacal jiki, sai da ta nutsu da kyau ta gane menene ciki

“Zainab…… Amana….”

Fuskar ta cike da hawaye ta dago ta na duban sa. Usman be gushe ba ya furta

“Wannan shi ne nasiha ta karshe da Malam ya bar min, Malam be manta lamarin ki ba duk da ya na gabar mutuwa, Ni kuma na masa alkawarin ni da ke mutu ka raba Zainab, ba zan taba sakin ki ba duk runtsi duk wuya. Na san ban rukewa Malam amana yanda ya kamata ba, Amma wallahilazim duk nema na, da kokarin ganin ni ma na zama wayeyye dan zamani ina yi ne ba dan kowa ba sai dan ke, a tunanina ba ki kauna ta, shi ne dalilin ki na hada baki da makiya na dan a kashe ni, kuma na san babban dalilin da ya sa ba ki kauna na ta saboda ni bakauye ne bagidaje…..”

Ta yi saurin katse shi ta hanyar dora yatsun ta bisa leban sa. Hannu ya sa ya kama yatsun na ta, ya yi kissing. Sannan ya tashi tsaye ya karbi Shehu daga hannun ta, babu mu su ta sakar ma sa shi ya kwantar da shi gefe sannan ya dada jawo ta jikin sa, ya yayinda ya zauna bakin gado ya dora ta bisa cinyar sa. Ya na mai goge hawayen da ke gangarowa daga idanun ta ya ce

“Na sani Abu, na san ki na so na, Rakeeba ta fada min ki na so na, ki na Kauna ta tun sanda na ke bagidaje na, shi ya sa ma na kasa jira na gama wayewar gaba daya, na falfalo da gudu domin neman yafiyar ki, ashe ina can an haifa min Shehu ….tsaya sunan wa ma ya ci be?”

Cike da kunya Zainab ta cusa kanta cikin wuyar sa. Usman na mai runtse idanu ya furta

“Idan ki ka cigaba da kalallame ni haka Abu zan fa baki kanin shehu a daren yau…!”

Jin haka ta yi saurin zame jikin ta daga na shi, yanda ya sa dariya ya fitar da sauti ne ta gane zolayar ta ya ke, ita ma din dariyar ta saka. Har sai da dariyar ta koma ta farin cikin yau gasu dai tare cikin so da kauna. Su ka yi mai isar su sannan Zainab ta furta
“Usman”

“Ummm”

Usman ya amsa ya na mai dada hanyo ta jikin sa.

“Ba kai ba, jinjiri na sunan shi Shehu Usman….”

Dago ta yayi ya na kallan ta, kallo mai narka zuciyar wanda ake yiwa. Idanun sa na shekin kwalla ya furta

“Duk bakin cikin da na sa ki ciki, ki na tunanin na sake ki amma ki ka sanyawa dan mu sunana Abu?”

Zainab ta gyada kai alamar eh. Ga mamakin ta sai gashi ya tada ita tsaye. Kana shi kuma ya durkusa har kasa, hakan ya sa ta yi yunkurin tada shi, Amma ya ki, cewa yayi

“Dan Allah Zainab ki yafe min, Dan Allah ba dan hali na ba ki yafe min, matukar ba ki yafe min ba toh wallahi ko dada sace ki zan yi sai dai na yi, Amma ba zan iya rayuwa babu ke ba Zainab”

Dadi kamar zai kashe ta, ta ma rasa abin cewa kawai sai rungume shi ta yi, hakan yayi daidai da shigowar Anty Sauda, Halitta, Ammy. Usman yayi saurin sakin ta cike da kunya. Ammy kuwa juyawa ta yi da sauri ta na fadin

“Kai yaran zamani! Wallahi Halitta kin cuce ni!”

Anty Sauda ma sim sim ta bi bayan ta, ya rage sai Halittt wacce bakin ta ke kunshe da dariyar mugunta, hakan ne ya sa Zainab fahimtar abin da ke faruwa, cikin tuhuma ta ce

“Halitta ke ce ko?”

“Ah ah fa, na dan ji hayaniya a dakin nan, tsoro ya kama ni dan kuwa na san ke da baby Shehu kun yi kadan ku yi making all those noises, shi ne fa na taso su su zo su ga ko lafiya..”

Ta karasa maganar ta na mai kashe mata ido daya.

“Kai yarinyar nan ba ki da mutunci wallahi!”

Cewar Zainab ta na mai jifan Halitta da filo, Halitta ta yi saurin kaucewa. Ta na duban Usman wanda tun shigowar su kunya ya sa ya kasa sukuni, ta ce

“Malam Usman bayan abin da ya faru yau zai fi kyau ka wuce da matar ka gobe, dan ko ban ji akwai wanda zai so ya kara hana ka…”

“Halitta!”

Zainab ta daka mata tsawa, in da Halitta ta yi saurin ficewa ta na mai rufo musu kofa. Ta na fita Zainab ta ce oya Usman ya zo shi ma ya kama hanya. Ta yaya ma ya shigo gidan? Ya bata amsa da
“sabon maigadin ku za ku sake kawai, duba ta biyar na bashi ya bude min kofa, abokina Umar na can ta bayan gida ya na jira na, ba zan tafi ba sai kin min alkawarin za ki bi ni mu koma Yola”

“Yola kuma? Rugar Shehu fa?”

“Rugar Shehu na ke so na mayar cikin garin Yola, irin wannan tsarin da Shugaban kasa ya ke da burin yi, labari ne mai tsayi, ki min alkawarin za ki bini tukun”

“Zan bi ka duk in da sa kafa Usman”

Cikin jin dadi ya janyo ta jikin sa, ya sumbace ta a goshi. Sannan ya sumbaci Shehu a kumatu tare da masa addua. Sannan ya fita suna kewan juna.

***

Epilogue

Sassanyar iskar damina da ke kadawa bai hana ta tsayuwa baranda in da ta saba tsayuwa duk yamma bayan ta kammala duk wani hidimar gaban ta. Ba komai ke sata tsayuwa wajan ba illa ta karewa estate din da mijin ta ya gina da sunan Rugar Shehu kallo ba, ba ta taba manta shekaru goma da su ka wuce, daren da Usman ya lallabo dakin ta bayan Ammy ta hana shi ganin ta ba. Ta na murmushi yayinda ta dora hannun ta bisa katan cikin ta haihuwa ko yau ko gobe ta ke tuna yanda Ammy ta sauko daga dokin fushin da ta hau bayan ganin su da ta yi rungume da juna. Ko da Usman ya koma washagari kin yarda su gaisa ta yi, ta dai ce ba ta yarda Zainab ta bi shi ita kadai ba, sai dai ya jira su yi arba’in, sannan su Anty Sauda su bi shi su ga muhallin da zai aje mata diya, haka kuma su gana da wasu daga cikin dangin sa. Kafin wa’adin Ammy ya cika Usman ya sha zarya tsakanin Kano da Yola. Daya daga cikin ziyarar ta shi ne ya bata labarin estate din da ya ke ginawa tare da Taimakon Umar da mahaifin sa. Da kuma tarin hannun jarin da su ke bukata domin tada Rugar ta zama wajan neman kudi da juya shi. Anty Sauda kuwa lallabawa ta yi to koma gidan General da kafar ta bayan ta ga muhallin Usman da irin tarin dukiyar da ya mallaka duk raina shi da ta yi, ta yi tawassali ga Allah ta gane mutum ba abin rainawa ba ne. Shi kuwa Jauro tunda bayan da ya gane Usman shi ma ya saduda, kullum cikin bin Usman ya ke da bukatun sa kai har ya kai ya na bin shi har Yola, da ke Usman mutum ne be gaza taimaka masa ba, har aiki ya bashi cikin estate din Rugar Shehu.

Sanda Usman ke mata jawab akan yanda su ke tsara Rugar Shehu, gani ta ke tamkar abu mawuyaci, Amma da yardar Allah cikin shekara goma Usman ya taka matsayi mafi girma wajan samin cigaba. Duk da su Kawu Iliya sun ki yarda su koma saban estate din kamar Yanda Usman ya bukata, sun ba da matasa da dama wanda su ne ke kula shanu wajan kiwo, haka kuma cikin su akwai manoma wanda ke noma a filin da aka ware na musammam.

Fili aka ware sosai in da ake kada shanun su yi shawagi da kiwo, wanda bayan an kada su turken su nan ake diban taki domin noma da kuma siyarwa gomnati a matsayin takin zamani. Bayan haka akwai wajan kiwan tsuntsaye kamar kaji, zabi, agwagwi, da dai sauran su. Haka zalika sauran kananan dabbobi ma ba a bar su baya ba. Hakan ya sa Umar ya samarwa Usman investors aka gina asibitin dabbobi cikin estate din, su na raba ribar 50-50 bayan sun samarwa dinbun jama’a job opportunities wanda ya hada da masu aiki a factory din sarrafa madarar shanu zuwa yogurt da fresh milk. Rugar Shehu ya zama daya daga cikin factory ma su samar da yogurt mafi inganci. Zainab ke koyar da matan matasan da aka taho da su daga Rugar Shehu, don gaba daya an hana su tatsar nono bare ma su kai da fita tallar fura da nono. Haka kuma Shehu ya gina yar karamar primary cikin Rugar, ya dauko malamai gwanaye ya na biyan su domin koyar da yara, ingancin makarantar ya sanya hatta jama’ar waje su ka fara kawo yaran su suna sa su cikin makarantar, hakan ya sanya Usman da Umar tunanin bude bangaran secondary da zarar sun yaye daliban primary na farko. Usman ya zama abin alfahari har a wajan gwamnatin jihar Yola saboda gudunmawar da ya ke bayarwa kwarai ta bangare daban daban wanda ya hada da killace jama’ar sa, sun dena yawan kiwo bare su shiga gonar wani, bare a zo ana tashin hankali. Rugar sa ta samarwa matasa dayawa aiki. Asibitin dabbobi da ya bude ya zama daya daga cikin ingantaccun asibiti cikin garin yola. Haka kuma ya yiwa Yola attracting foreign investors dayawa, ba larabawan ba ba turawa ba, wanda a da Umar ke bin su da yin ko za su za sa hannun jarin su cikin Rugar Shehu, yanzu su ne ke kawo kan su da bukatar yin haka. Haka kuma bangaran Malamtaka ba bar Usman baya ba, ya zama hamshakin malami kuma fitacce wanda ke da dunbin masoya cikin garin Yola da sauran garurruwar arewa.

Tsayuwar daya daga cikin motocin Usman kirar Range Rover ne ya ja hankalin Zainab. Usman ya fito sanye da manyan kaya, shudin shadda dinkin jamfa, hular sa a hannun gashin kan sa ya kwanta lublub tamkar hula. Shehu ne ya diro daga dayan bangaran, ta na ji Baban sa na masa fadan be hana shi dirowa daga mota kamar dan biri ba! Yayinda ya ke kokarin taimakawa kanan Shehu, Hassan da Husain su ma su ka fito daga motar.

In da Shehu ke da shekara goma a duniya, wata uku ya rage Hassan da Hussain su cika shekara shida a duniya. Hannun Usman rike da na yan biyu in da Shehu ya ruga a guje ya na fadin sai na riga ku zuwa gurin Mama. Su ka nufo ciki. Zainab na murmushi ta juya zuwa falo domin tarar su. Ta shiga falon Shehu ya karaso da gudu ya rungume ta, hakan ya sa Usman da shigowar sa kenan daka masa tsayawa fadi ya ke

“Ka sake ka kayar min da mata sai na lallasa ka Shehu!”

Hakan ya sa Shehu matsawa gefe da sauri. Dariya Zainab ta sa, kana ta ce

“Ayya mana Malam ina laifin shi dan ya rungume Maman sa?”

“Ba haka ake yi ba ai, a hankali zai rungume Maman ta shi kamar haka”

Cewar Usman ya na mai rungumo Zainab, duka yaran su su ke kallo. Usman ya ce

“Maza ku ma ku matso ku mata yanda na mata amma fa a hankali kar a buge gimbiya ta ta ciki”

Kamar dama jira su ke, da saurin su suka taho in da dukkan su uku su ka rungume kafafun Zainab cike da so da kauna.

Alhamdulillah.

No comments