Breaking News

Auren Shehu Book 2 Page 3

*Khadija Sidi*
Auren Shehu 2

3

 

Allah yayi dare gari ya waye, carar zakara tare da kukan shanu, gami da guje guje da ihu da yara ke yi ne ya sanya Zainab sanya hannayen ta bisa kunnuwan ta, tare da


runtse idanu, ga wani zugin azama da take ji a kafafun ta, haka kuma kan ta ya mata nauyi. Tun tana jin komai tamkar cikin mafarki, har ya fi karfin kunnuwan ta ya kai ga sanya ta bude idanu a hankali. Maimakon ta ga silin da fanka sai ganin karare ta yi jere reras, idanun ta ta rufe a karo na biyu ta na mai fatan farkawa daga mafarkin da ta ke. Ko da ta sake budewa ta ga dai har lokacin rufin kara idanun ta ke gane mata ta shi zaune a firgice ta na mai bin bukkar da idanu, bukka ce maidaidaciya wacce aka gina da jar kasa mai dauke da yayin ciyawa da rufin kara. A kideme ta kai kallan ta ga in da ta ke kwance, sai a sannan ta lura da gadon kara mai dauke da matacciyar katifar da ta ke zaune kai. A hankali ta ke karewa bukkar kallo tundaga ledar da ke shimfide kasan bukkar, har zuwa koren akwaitin karfe da ke aje gefe kusa da katan kwaryar da aka rufe da wani fefe, sai butoci guda biyu, na roba da na karfe.

“Mafarki na ke!”

Cewar Zainab ta na mai duban kayan da ke jikin ta, sam ta kasa tuna sanda ta sanya shi, abun da za ta tuna kadai shi ne sanda ta ke karatu cikin dare ba kayan ba ne jikin ta. Ta na jinjina kai ta kara fadin

“Da na gama karatu bacci ya sace ni, shi ne na ke mafarki! Da kabari kato ake yin shi da sai na ce mutuwa na yi, bari dai na koma bacci ko Allah zai sa na farka!”

Ta na maganar ne yayinda ta koma ta kwanta tare da rufe idanun ta. Jim kadan taurin gadon karen ya dame ta, haka ma hayaniyar yara da ta ke jiyowa daga waje ya sa duk yanda taso ta koma bacci ko Allah ya sa ta tashi ya gagara. Tsaki ta ja ta na mai tashi da sauri da niyar ta fita ta tsawatarwa ma su hayaniyar, ko da ta taka kafarta wani raradi ne ya ziyarci kwakwalwar ta har sai da ta koma ta zauna da sauri tana fadin

“Wayyoo Dady!”

Sai a sannan ta lura da yanayin kumburi da kafafun ta su ka yi. Hakan ne ya karasa ta tsorata da halin da ta tsinci kan ta ciki. A haka ta yi karfin hali ta tashi ta na mai takawa da kyar wanda duk sanda ta taka sai ta cije lebe har ta kai ga assabarin da aka saka bakin kofar daki, hannun ta biyu ta saka ta daga shi nan ta yi tozali da abin da tun da ta zo duniya ba ta taba gani ba, kanta ya zuye ya na mai sarawa ganin bukkai ba adadi, gabas da yamma kudu da arewa, Rugace ta gargajiya tsantsa in da jama’ar wajan mata da yara ke kai kawo cikin kwanciyar hankali.

Matan sanye da rigar saki irin na fulani mai hade da zani, in da wasu su ka sanya fari, wasun su shudi ne jikin su, duk da akwai dankwali kan su, sun saki jiki rabashe rabashe su na hidimar su, daga mai share na su bangaran bukkar, sai mai kwasar manshanu daga cikin kwaryar nonon da ta tatso tare da taimakon yara mata guda hudu wanda ba su fi shekara goma sha uku ba, can gefe kuwa mata ne guda shida wanda dudu ba za su haura shekara ishirin ba amma gaba daya cikin su ya sake saboda wahala, musammam kirgin su wanda ya ya kwanta sharkaf kamar tsumma, sun zage dantse wajan dakan geron fura. Kusa da su mata biyu ne zaune daga gani ka san kishiyoyi ne, suna cin abinci hannu baka hannu kwarya, daya daga cikin su dauke da yaro akan cinya ta tana ba shi nonan da tsabagen yanda ya kwanta kai ka ce tsumma ne. Daga can gefe kuwa tsoffine guda biyu zaune suna koyawa yara mata guda biyu da ke zaune gaban su sakar riga, wanda za su kimanin shekara goma. Sai kuma yara maza da ke wasan langa sun yi kacaca tsabagen wasan bazan da su ke yi cikin kasa. Sai kuma

Yaran ne su ka fara ganin Zainab wacce ta saki baki da hanci ta na kallan sarautar Allah. Shirun da yaran su ka yi ya ja hankalin iyayen su ka ankare da Zainab. Kamar yanda ta bude baki ta na kallan su haka su ma su ka bude baki su na kallan ta cike da mamaki. Sun ji labarin Shehu ya dawo da Kado Rugar Shehu, wanda har aka mu su kashedin kada wanda ya yarda yayi wani yare cikin Rugar face fulatanci, musammam ga Kado, Amma sam ba su taba tunanin irin wannan kadon Shehun su ya kawo Ruga ba.

Kallon Zainab su ke tun daga dankwalin da ke kan ta, zuwa doguwar riga mara hannu da ke sanye jikin ta, surar Zainab, da kuma yanayin fatar ta da ya fita daban, duk da yawancin su farare ne, ita baka ce amma yanda fatar Zainab ya ke subul subul ya na sheki kadai abin kallo ne.

Tuni su ka fara kuskus a junan su, in da yara su sa tafi suna fadin

“Kado! Kado! Kado”

Hakan ne ya sanya Zainab sakin assabarin da sauri cikin faduwar gaba, ta na dingishi jikin ta har rawa ya ke ta komo cikin bukkar. Cikin yanayin tashin hankali ta ke kara duban bukkar, gani ta ke kamar za ta ga wata alama da zai bayyana mata halin dimuwar da ta tsinci kan ta ciki.

Ganin jikin wani abu kamar akwaitin ta leko ta karkashin gado ya sanya Zainab ta karasa gaban gadon da dingishi, dan gaba daya ji tayi zafin kafar ya dena damun ta. Cikin zafin nama ta janyo akwatin, ganin nata ne da gaske ta ji wani dan sanyi cikin ranta yayinda ta bude da sauri ta na mai mamakin yanda aka yi akwaitin ya je in da ta ganshi ta zuge zip din akwatin, haka kuma kayan ta da ke ciki ya bata mamaki dan kuwa ba za ta iya tuna sanda ta jera kayan cikin akwatin ba.

Ciki ta yi kacibus da wayar ta, da murnar ta ta dauko wayar, hannu na rawa ta kunna ganin a kashe ta ke. Allah Allah ta ke ya gama kunnuwa ta samu ta kira waya ko Allah ya sa ta sami mafita, amma ko da wayar ta kunnu ta shiga cikin wajan kira sai taga anbuga mata waya a adadi, kuma duka miskul ne, kiran Ammy ya fi sau goma, haka ma na Falmat da sauran yan ajin su. Sakon waya kuwa su ma ga su nan birjik.

Jin wayar na kugin neman chaji ne ya sa Zainab dena duba kira da sakonnin da aka tura mata, ta shiga kokarin kiran Ammy kafin wayar ta mutu, Nan ma wani tashin hankali ne ya ziyarci idanun ta, domin kuwa wayar nunawa ta yi ba za ta iya kiran kowa ba sanadiyar rashin sabis, haka kuma wajan da ke nuna alamar sabis a wayar ma ya dauke gaba daya, a sannan Zainab ta dada jaddada kalmar ‘babu sarki sai Allah’

Zufa na ketowa daga goshin ta rufe akwatin, hannun ta ruke da wayar ta tashi tsaye ta na dingisawa ta sanya silfas din da ke aje kusa da akwatin na ta, ta ja akwatin yayinda ta bude assabari ta fito waje, cak ta tsaya ganin yanda yaran nan da iyayan su duka su ka baro abin da su ke, su ka yi da’ira bakin kofar bukkar Shehu kamar masu jiran tsammani.

Babban abin da ya kara tsorata Zainab shi ne yanda su ka karu dan kuwa har na gona sai da yaran nan su ka je su ka kira su zo su ka ga Kado a dakin Shehu. Zainab na mai ja da baya cikin dakiya da rashin nuna tsoro ta ce

“Ban san ko su waye ba! Ban san wata duniya na ke ba! Ban kuma damu da na sani ba! Roko na daya dan Allah….ku nuna min hanyar da zan koma tawa duniyar! Kada ku cutar da ni…..”

Inda Iyayen yara su ka zubawa Zainab Idanu ba tare da sun tanka mata ba, yaran kuwa matsawa su ka yi kusa da ita suna kokarin taba akwatin ta, Zainab ta matsar da shi cike da kyamkayamin yara, ba ta ankara ba daya daga cikin yaran ya kai hannun sa kan wayar da ta har ya na taba hannun ta, cikin tsawa Zainab ta furta

“Stay away from me stupid boy kawai mara kunya da tarbiya! Sai na ci uban ka wallahi!!!!”

Yaro yayi baya da sauri haka ma sauran yan uwan sa, wanda daga baya su ka sanya dariya su na mai tafa hannu sanadiyar karar rashin chajin da wayar Zainab ta yi ta na mai kawo wuta. Zainab na girgiza kai ta ce

“Innalillahi wainnailaihi rajiun!”

Ta na ja akwaitin ta ta nufo iyayen yaran in da su kuma suka fara ja da baya, yara kuma ba su fasa shafa akwatin Zainab ba, inda ta ke kokarin hana su ta hanyar jijjiga akwaitin, ce mu su ta ke

“Dan Allah ku taimaka, ku min magana ko na sami sauki”

Ga mamakin ta sai ji tayi sun fara mata magana amma da fulatanci, a fusace Zainab ta ce

“Dallah ku yi min hausa ba na jin yaren da ku ke min! Sokwaye kawai!”

Maimakon ta ji hausan da ta ke bukatar ji, sai ma dada yara mata su ke cikin yaran fillo. Hakan ya sa Zainab fusata, ta na jan akwaitin yayinda ta ke dingisawa ta bi hanyar da ta ji ta kwanta mata ta na tafe yara na biye da ita suna tafa hannun ganin yanda Zainab ke jan akwaitin ta mai taya ne ya fi burgesu, tafi su ke suna fadin

“Kado! Kado! Kado! Kado”

Haka kuma masu kiriniyar cikin su ba su fasa kokarin taba akwati da wayar Zainab ba, haka su ka mayar da ita tamkar zararriya yayinda hawayen bakin ciki ya cika fal idanun ta. Fadi ta ke

“Madness! Mad people everywhere! Wallahi zan ci uban ku! Shegu ‘ya’yan asara!”

 

Usman kuwa tun sassafe ya tafi fadar shi da ke can gefan bukkokin Rugar Shehu. Zaune ya ke da dattawan gari da kuma matasa, kasancewar shi ne ranar zaman fada na farko tun tafiyar Usman ya sanya babu wanda ya je kiwo ko gona, kowa ya hallacci zaman. Maganar Zainab kowa ke son ji daga bakin Zainab, Amma shakkar Usman ya sa su kasa bude baki su tambaye shi.

Zaune su ke kan tabarma karkashin katuwar bishiyar mangaro da ta yi mu su lema, Usman sanye cikin farin yadi da farin rawani wanda shi ya banbantashi da sauran jama’a da ke sanye da kayan saki, a matsayin shi na Shehu.

Ana tattaunawa ne akan sabbin tsari da dokokin da Usman ya kawo wanda za su shafe wanda su ke yi a da, sun hada da wajabta sanya mayafi ga duk wata mace baliga, dena shiga sassan da ba na iyalin ka ba kai tsaye ba tare da neman iso ba, dena koyar da karatun surkulle in da za a musanya shi da karatun qur’ani zalla.

Tun daga nesa ya hango ta tafe, yara da iyayen su biye da ita, haka shi ma Muhammadu Bello wanda ke zaune gefan Usman ta hannun dama ya hango ta, tun daren jiya ya ke fargaban tashin Zainab, ilekuwa sai ga abin da ya ke tsoro na faruwa. Usman na mai aje takardar da ke hannun shi ya tsaya cak yana tsimayin karasowar ta, haka ma sauran yan fada wanda su ka lura da inda hankalin Shehun na su ya tafi, su ma su ka zubawa sarautar Allah idanu yayinda Zainab ke dada matsowa gare su.

Tun da ta hango mutane zaune zuciyar ta ke Allah Allah ta karasa gaban su kila ta samu masu hankali ciki, idan har ta damu da zugin azabar da kafarta ta ke mata, ba ta nuna ba, sai dai dinkishin da take yi ne zai tabbatar da azabar da ta ke ciki. Ganin wani zaune tsakiyar mutanen, da kuma yanda shigar sa ta banbanta da na su ya tabbatar ma Zainab da shi ne shugaban Rugar, cikin fatan neman doki ta karasa. Zuciyar ta daya ta fara kokarin kutsawa ta cikin tarin mazan domin karasawa ga Shehu ta na fadin

“Ku matsa dallah! Malam matsa dallah!”

Duk da ba dukanninsu ne su ka fahimci abinda ta ke fada ba, ganin yanda ta tasar mu su da sauri su ka dara mata hanya, suna mai binta da kallo cike da mamaki har ta kai ga gaban Usman, idanun ta kan yaran da tun da su ka iso gaban Usman kowa ya nutsu kamar ba su ba ne su ke mata tafin atile ba, Zainab ta ce

“Kai ne shugaban wannan shedanun yaran da mahaukatan Iyayen su…..”

Juyowa da ta yi ta kalli Usman wanda lafazan Zainab ba karamin tunzurashi yayi ba, ya tashi tsaye haka ma sauran yan fada su ka yi yunkurin tashi amma ya musu alama da hannu da su zauna. Zainab na girgiza kai ta ke nuna shi da dan yatsa, tsayin shi, fadin shi, da idanun shi ne ya kara tabbatar mata da Usman din ne, Abu na farko da ya tsirga zuciyar ta shi ne zaton ta ya tabbata, Usman ya cika dan garkuwa da mutane, gashi ya dauko ta duk da ta kasa tuna yanda aka yi . Cikin faduwar gaba ta saki akwatin hannun ta yayinda ta zube kasa, ta zauna dirshen ta na duban kasa tamkar mai nazari.

Yanda Zainab ta firgita da ganin shi, da kuma yanayin da ganin na shi ya sanya Zainab ciki ba karamin faranta ran Usman yayi ba dan a tunanin shi ta karaya ne. Jin Zainab ta furta

“Ya aka yi ka kawo ni nan? Menene dalilin ka na kawo ni nan?”

Usman ya tsaya ya na duban ta kamar yanda sauran jama’ar su ka zuba mata Ido. Ganin be da niyar amsa mata ta tashi a fusace dan masifa ma mancewa ta yi da kafar ta, sai da ta taka kafar ta cije lebe cike da azaba, ta na dingisawa ta karasa gaban Usman hannu a kugu take magana cike da tsiwa

“Dan ka na dan garkuwa da mutane ba wai zanji tsoran ka ba ne! Tun ranar farko da na dora idanu kan ka na san kai wanene! Dady ka yaudara har ka masa rufa ido ya kasa gane kalar ka! Haka Anty Sauda da Ammy su ka ki yarda da ni akan a min katangar karfe tsakanina da mugu irin ka! Nawa ka ke bukata? Nawa ka ke bukata ka mayar da ni gidan mu?? matsiyaci kawai!”

 

Ganin yanda Zainab ke yiwa Shehun su magana cikin tsawa da tsiwa ne ya sa matasa tashi tsaye cikin fushi suna mai yiwa Zainab ihu, da harshen fulatanci su ke fadin

“Karyar ki ta sha karya kado! Ki tuba ko kuwa muna tasar miki da bugu”

Ganin haka Zainab ta yi baya a tsorace kamar mai shirin ranta a na kare. Usman ya daka mu su tsawa cikin harshen fulatanci, ya ce

“Kada ku kuskura! Mata ta ce! Ni kadai na ke da ikon hukunta ta!”

Gaba daya su ka runsunar da kai sannan su ka koma wajan zaman su suka zauna, hakan ne ya bawa Zainab damar cigaba da tsiwa duk da cikin ranta ta gama tsorata da Usman, tsoran ne ba ta san nuna masa gudun kar hakan ya bashi damar cutar da ita, cikin karfin hali ta furta
“Ihun ku na banza ne dan ba ku bani tsora! Ku tambayi dan uwan ku ku ji yanda ya sha dakyar hannun sojoji!”

Usman ya kai kallan sa ga Muhammadu Bello, wanda ya kawar da kai gefe yayainda ya tuna kashin da ya sha a barikin soja. Cikin danne zuciya Usman ya mayar da kallan sa ga Zainab, wacce ba ta gushe ba ta cigaba da fadin

“Wallahi tun kafin na sabar maka ina mai baka umarnin ka yi duk yanda ka yi na wayi gari a nan ka mayar da ni makaranta! ba na san iskanci ban da lokacin batawa jarabawa na ke Idan ba haka ba sai na lahira ya fi ka jin dadi, kai ba kai ba har wa’annan yen koran na ka”

Ta karasa maganar ta na mai nuna jama’ar wajan da dan yatsa.

Cike da isa Usman ya koma wajan zaman shi ya zauna kamar ba da shi Zainab ta ke magana ba. Daya daga cikin dattijawan ne ya kada baki cikin harshen fulatanci ya ce

“Shehu ka gafarce ni, wannan mata taka sam ba ta da tarbiya, ba ka tunanin zaman ta a wannan Ruga za ta iya lalala ta mana tarbiyar yaran mu da matan mu?”

Sauran dattawa su ka goyi bayan shi ta hanyar jinjina kai. Wani ya kara da

“Shehu duk matan da ke Rugar nan, ga ‘ya’yan mu amma ka rasa wacce za ka aura sai Kado? Wacce ba ta san darajar Shehu ba bare na al’ada ba? Ji fa yanda ta tsaya kerere gaban mu muna dattawa, ba kunya bare tarbiya”

Shehu na murmushi ya mayar musu da amsa cikin hausa ya ce

“Ba a san rai na aka daura min ita ba, sadakar ta mahaifin ta ya bani! Tabbas ba ta kai darajar matan Rugar Shehu ba, dan haka kada ku damu tamkar baiwa ta ke a Rugar nan”

Yanda Zainab ta kai hannu baki ta na kallan shi tamkar wacce ta ke shirin burma masa wuka, ya sa Usman canza harshe, dama yayi hausan ne saboda ta san abin da ya ke fada, ya na murmushi yayinda mazan wajan daga samari har dattawa ke kallan Zainab cike da mamaki, matan wajan kuwa dariya su ka sa bayan Usman ya dada maimaita musu cewa sadakar Zainab aka bashi, haka kuma ba takai matan rugar su daraja ba. Cikin ihu kamar mai shirun rufe shi da duka ta ke fadin

“Ka yi hausa mana! Idan ba munafunci ba ka yi yaran da na ke ji! Ni ba sadaka ba ce! Ba zan taba zama matar ka ba! Ni ba baiwar ku bace! Bloody fool! Ka mayar da ni na ce!”

Hankali kwance Usman ya ce

“Ni na kawo ki nan? Ko kin ga sanda na dauko ki? Ki tuna yanda aka yi ki ka zo sai ki koma da kan ki, matukar ba haka ba ki shirya zama karkashi na a matsayayin miji ke kuma baiwa ta…….”

“Ba za ka taba zama miji gare ni ba! Uban kuturu yayi kadan! Ni ce baiwar ta ka? Ka san dawa ka ke kuwa? Da na zauna karkashin ka gwara na kwanta kabari!”

Ta katse shi a fusace, ta na mai daukar akwaitin ta ta furta

“Fine zan nemi hanya ta da kai na, Amma dukkan ku ku kuka da kan ku! Sai kun dandana gudar ku!”
Ta fara jan akwaitin ta, wayar ta dake ta kukan neman chaji ta duba ko alamar sabis ya dawo, fadi ta ke

“Wawaye jahilai kawai! no wonder aka ce a guji iskancin bakauye! Kun ci sa’a network di na ya dauke da ban ma tsaya musayar magana da almajirai irin ku ba, ka yi da diyar halak”

Ko da ta karasa wajan yara da iyayen su mata, sai su ka ki dara mata hanya, a fusace ta ce

“Dallah ku matsa min na wuce! Duk karnin manshanu ku ke da warin rana! Ga warin talauci! Kai wannan masifa har ina! Kazamai kawai!”

Ganin da gaske ba su da niyar matsawa ya sanya ta juya ta kalli Usman

“ka fada mu su su bani hanya ko na ci kaniyar su wallahi!”
Usman ya kawar da kai gefe ba tare da ya tanka ba, Bello ne ya taso ya ce da mata da yaran su bata hanya ta wuce cikin harshen fulatanci sannan su ka buda mata hanya, sai a sannan Zainab ta gan shi da kyau, ta gane shi ne kanin Usman da aka kamo. Ta na duban Bello ta ce

“Halan ba ka bashi labarin kashin da ka sha ba ne shi ya sa be daddara ba! Toh tun wuri ka masa bayani idan ma giyar wake ya sha gwara ya wattsake! Sakakkaru kawai!”

Tana gama maganar ta ja akwaitin ta. Bata kula da kugin yunwa da cikin ta ya ke mata ba, bare ta tuna da sallar asubahi da ke kan ya, ta na takawa da kyar ta doshi wata yar siririyar hanya da take tunanin shi zai fitar da ita hanyar da zai sada ta ga titin barin Rugar Shehu, nan kuwa bata san dokar daji ta kara nufa ba. da sauri Bello ya dawo wajan Usman ya ce

“Ta tafi fa Shehu, hanyar da ta dosa hanya ce da zai kara batar da ita cikin dokar daji, ka ga yanda ta ke tafiya da kyar, gashi akwai hatsari sosai cikin dajin kasan bata daya daga cikin mu, halittun dajin ba su san da zaman ta ba kada ta je ta hakala, ba za ka dakatar da ita ba?”

Usman na duban mata da yara ya ce kowa ya koma harkokin sa, haka kuma ya gyara zama in da ya ba da umarnin su cigaba da tattauna abin da su ke tattaunawa kafin zuwan Zainab. Ganin haka Bello ya san Usman be da niyar amsa masa, dan haka shi ma ya koma wajan zaman sa, zuciyar na da tunanin dangantakar da ke tsakanin Zainab da Shehun su, da kuma halin da Zainab za ta iya shiga cikin dokar daji.

 

No comments