Breaking News

Bamagujiya 3

Page 3*

★★★~~~★★★~~~★★★

Tunda ya fara mgnr suke kallonsa yana ida faɗin abinda yake faɗi ya juya yayi tafiyarsa wani kayan takaici wanda akace yana sonta da ƙawancen har yasha kwana yama riga tafintan nasa barin gurin taɓe baki tayi tayi gaba suna tafe babu me cewa wani Saida suka kusa rabuwa Lantai tace.



“Nifa lamarin Æ´an birnin nan ya fara bani tsoro musamman akanki Bibo meye kuma Æ™awance tsakanin namiji da mace?” Kawar dakai tayi tace “to basai yayi da gyatumarsa ba tunda shi bashi da É—a’a aiko mahaukaci yasan wannan ba daidai bane”
Shigewa tayi gdansu Lantai ta wucce nasu gdan, tana shiga tayi watsi da komai ta shige dakinsu ta faÉ—a kan shimfiÉ—a ta kwanta tare da lumshe idanunta wannan wanne irin mutum ne? Meye yake nufi da Æ™awance tsakaninsu? Tambayar data kwana da ita a ranta kenan har wayewar gari tada tashi wanke fuskarta tayi suka gaisa da uwarta ta nufi wajen gyatuminta ta ishe shi zaune yana shan kunu ta zauna suka gaisa tace “inason dama zanje gona ne” dubanta yayi duba irin na tsanaki yace “gona kuma?” Meye zakiyi a gona?” Sunkuyar da kanta tayi Æ™asa tace “Sallau jiya yake cewa da Jumme ciyawa ta É“ata yabanyar gonarka idan ba’a cireba zatayi É“arna wannan tasa naga ya kamata naje nagani koda abinda zan iyayi” jinjina kai yayi yace “shikenan kije Allah ya tsareki”

 

Ƴar ƙaramar dariya tayi ta miƙe ta fita saboda murna ko sallama batayiwa Jumme ba ta bar gidan ta nufi gonar tanata yan waƙoƙinta.
Tsakanin gonar da cikin gari akwai nisa sosai amma sabo yasa basa ganin nisan haka taci gaba da kurÉ—awa tayi nisa sosai daidai wata itaciya ta rinÆ™a jiyo Æ™amshi me kwantar da zuciya tana dosarta Æ™amshin na Æ™aruwa harta isa jikinta, gabanta ya faÉ—i “Wayyoh!” Tana mgnr tana ja da baya ga mamakinta sai taga yayi murmushi ya taso daga gurin yace “kin tsorata ko?” Wata ajiyar zuciya ta saki me Æ™arfi jin dirin saukar muryarsa har cikin lakarta.
Sake matsowa yayi yace “Ina zaki?” Yana mgnr yanakai hannunsa ga buhun dake saÉ“e a kafadarta, batayi Masa gardama ba ta sakar masa ya fara dubawa yana kallonta Saida ya gama dubawa tsaf koda baisan amfanin kayan ba alama ta nuna masa gona zata hakan yasashi É—agowa yace “gona?”

 

 

Da sauri a Æ™oÆ™arinta na ganin ya barta ta tafi ta É—agansa kai yaja fasali ya karyar dakai yace “zan iya rakaki inason na iya aikin gona….” Zaro idanu tayi tare da kunshe dariya ya zubanta idanu har Saida ta saita kanta yace “meye ya baki dariya?” TaÉ“e baki tayi tace “ba haÉ—i saniya da tallan kilishi” da sauri ya dawo da hankalinsa gareta yace “sabida me?” Gaba tayi taci gaba da tafiyarta tana cewa “ko cikin malalata akwai gwarzo kaikam ko riÆ™on lauje bazaka iyaba bare noma”
Murmushi yayi yabi bayanta yace “iya magana kamar Æ´ar mahauta kuma haka zaki koyamin ba”

 

Tsayawa tayi tare da haÉ—e fuska tace “Idan muka tafi gona tare zakasha wahala kuma mutanen garin mu zasuje su faÉ—awa Jimo Ciwake harma su Æ™ara da sherri ka taimakeni ka barni naje nayi abinda ya fito dani”
Fuzge buhun hannunta yayi yayi gaba batare da ya sake cewa da ita komai ba dole tasa ta rinÆ™a binsa da sauri tana cewa dashi “bakaji ba kagafa akwai nisa jikinka bai saba da wahala ba banaso kasha wahala…..” Tsayawa yayi ta iso gareshi ya kai hannu zai riÆ™ota tayi saurin ja baya tace “Aa haram giya a gdan Mallam kada ka kuma taÉ“ani jiya daka taÉ“ani Saida Jumme ta kusa ganewa da kuwa ta gane da tuni na zama tarihi don jefani za’ayi cikin ruwan wankin zunubi kuma zunubin nan bazai barni na tsira ba”

 

Zubanta idanu yayi yace “wanne zunubi kenan?” TaÉ“e baki tayi tace “ai babban zunubi ne namiji ya taÉ“a jikin mace a nan garin idan har hakan ta faru to duk inda tayi za’a rinka jin warin maza a jikinta kuma zaija mata Æ™yama da tsangwama wannan dalilin zaisa taÆ™i auruwa domin babu wanda zai É—auki karya yakai gidansa a matsayin uwar Æ´aÆ´ansa”
Murmushi Habeeb yayi yace “Al’adarku nada kyau da tsafta kamata yayi ace baku kuke da wannan tsarin ba mu musulmi mune zaifi cancanta da mu kasance a haka domin ubangijinmu ya hanemu da kusantar zina” daga wannan basu kuma mgn ba sukaci gaba da tafiya har suka kai gonar Habeeb ya tsaya yana kallon gonar ba wata babba bace amma tayi kyawun yabanya da ta burge shi.

 

Tsinkayo muryarta yayi tana cewa “kaje ka zauna ga bishiyar mangwaro can tunda ka nace Saida ka biyoni” miÆ™a mata kayan hannunsa yayi batare da yayi furuci ba bai kuma bi umarninta ba, ganin abin nasa na yine yasata wuccewa ta fara aikinta tanayi yana kallon yanda take tafiyar da komai yana gane irin ciyawar da take cirewa da haka shima yakai hannu ya fara tayata.
Ba ƙaramin mamaki ta shiga ba da taga ko ita data saba aikin bata kaishi kwazo ba ta ɗago tasa gefen zaninta ta sharce gumi ta zubansa idanu tana mamakin inda ya iya aikin gona da kuma yabawa kyawun surarsa tabbas yakai kyakkyawa na gaske duk da ba fari bane amma yanada wani sihirtaccen kyawu da hasken fata na tsabar hutu da jin daɗi da yake bayyana kwanciyar hankalinsa.

 

ÆŠagowa yayi ya zubanta idanu tayi saurin kawar da kanta tare da basarwa ta sunkuya tana tattare kayan tana cewa “naga abubuwan mamaki a iya yau dana zauna dakai naga kana isa waccan Æ™oramar kana wanke jikinka kana dungura goshinka Æ™asa meye hakan yake nufi…. ”
Cikin mugun mamaki Prince Habeeb ya Kalli Bibo tare da kafeta da manyan idanunsa, yanzu ita a nufinta batasan sallah ba? Mamakinsa ya kawar da cewa “koda yake a ina zata sani?”
Tayata tattare kayan yayi yace “Kada kiyi gaggawa da sannu kuma a hankali zakisan komai game dani tunda kin yarda da abotarmu” miÆ™ewa tayi da sauri tana girgiza kai tace “Aa Nifa ban yarda da wata Æ™awance ba….” Hannu yasa saman bakinta ta É—ago ta dubeshi idanunsa nakan fuskarta yace “kar kija da Æ™udurina inason abota dake kuma ta Æ™ullu daganan har zuwa lkcn da zan bar garin nan naku kiji a ranki a koyaushe kuma a kowanne yanayi zamu kasance a tare Habeeba bana nufin cutarwa gareki saidai ke kin kasance Æ™addarata”

 

“Ƙaddara” ta faÉ—a tare da É—agowa da sauri, bai tsaya bata amsa ba saima gaba da yayi dole tasa ta bi bayansa suka nufi cikin gari duk inda suka wucce hankali akansu yake har suka je Æ™ofar gidansu taja ta tsaya shima ya tsaya sun jima a tsaye ganin bashida niyyar furuci sai kafeta da yayi da manyan lulu eyes nasa yasata juyawa tana cewa “Na gde ka huta gajiya”
Shigewa tayi ciki yabi bayanta da ido abubuwa da yawa na ayyanuwa a ransa waÉ—anda ya kasa tantance yuwuwarsu ko rashin yuwuwarsu koda yake Hausawa sun ce da tsoro ake cire saa shikam zuciyarsa na rawa akan abubuwa da dama amma dai zai jarabba kalar tashi nasarar yagani idan yanada rabo.
Da wannan tunanin ya isa masaukinsu Najeeb daya gaji da kiran wayarsa har ransa yayi Æ™una ya tareshi da cewa “Ina kaje?” Tambayar ce ta bashi haushi ya zabga masa harara ya nufi cikin gdan gdane me kyau nesa da cikin gari kaÉ—an ginin zamani dakunansu harda A C ga babban inji da aka sanya musu me bada wuta kowanne lkc sannan duk wata kalar kayan jin dadin rayuwa sun siya sun zuba a gdan a taÆ™aice dai idan ka shiga gdan bazaka gane a Æ™auye kake asalin Æ™auye irin Tsaunin gawo ba.

 

“Habeeb tambayarka nakeyi ina kaje….” Juyowa yayi ya kafeshi da idanunsa wanda ba kowa ke jure sanya Æ™wayar idonsa cikinsu ba ya tako gabansa yace “Ni kamar ni kake tambaya ta ina naje kamai dani wani Æ™aramin yaro ne ko kamai dani mahaukaci da kake gadi na?”
Yayi mgnr yana zare Æ™afar wandonsa, harara Najeeb ya watsa masa yace “ka kuwa É—aukowa kanka abinda zai dameka banga uwar da ta É—auki hankalinka akan wannan yarinyar mara addini ba da har ka zaÉ“i zubar da mutumcinka akanta…..”
Tsawa ya daka masa yace “Wlh tallahi ka Æ™ara faÉ—ar wata kalma mara kyau akan Habibah saina….”
“Sai kayi me? an faÉ—a mara addini kayi duk abinda zakayi sakarai da idanunsa yake rufewa idan yaso abu kamar babu wani abu bay…..” “Najeeb….” Ya faÉ—a tare da É—aga hannu zai daukeshi da mari me kuma ya tuna saiya fasa jikinsa yana tsuma yace “Ficemin daga É—aki kafin na illataka…”

 

Hayaniyar tasu ce tayi yawan da har ta fito da James daga É—akinsa koda bayajin Hausa yasan lallai koga yanayin fuskokinsu ran maza ya É“aci ganin yanda Habeeb ke tsuma yana ruwan bala’i yana nunawa Najeeb hanya yasa James kama hannu Najeeb suka fice yana cewa “Kuma ka rubuta ka ajiye wlh indai ina raye zamu koma Dutse wlh saina rusa duk wani shirinka baka isa ka auro mana Arniya mara addini ka kawo mana cikin zuri’armu ba wawa kawai da baya lissafa rayuwa wannan abinda kake shirin aikatawa ai ya cika abin kunya ace duk matan da muke dasu a Family saika fito waje wajen ma ka rasa wacce zakaso sai BAMAGUJIYA to saika aura mu gani ai….”
A hassale yace “Idan Allah yayi saika hana ai É—an hana ruwa gudu kawai Ni na taÉ“a jin wannan jaraba kun dameni na kawo matar aure na kawo wacce nakeso nakasa samowa yanzu kuma lkc yayi kwatsam ta faÉ—o rayuwata amma kaine na farko da zakayimin hassada to barima kaji Ni kuma naci alwashin ko zan rabu da kowa da komai saina auri Habeeba…..”
[3/31, 7:39 PM] AM OUM HAIRAN: *BAMAGUJIYA*
*(HOT LOVE AND DESTINY)*

NA

*FAUZIYYA TASIU UMAR*
*OUM HAIRAN*

 

*Tsokaci*
Labarin BAMAGUJIYA labarine me dauke da manyan darrusa da jigogi masu muhimmanci, zakuji salonsa daban da sauran salo please kuyi hkr kubini a sannu kamar yanda kuka bini a Juhud Gidan Uncle Ruwan jira insha Allahu zan warware muku zare da abawa.

 

*Jan kunne*
Allah daya bazan dauki zagi cin mutumci a wannan karon ba babu wacce nayiwa dole ta karanta littafin nan bana son shisshigi da katsalandan cikin lamura na domin bana shiga lamarin kowa kowa yasan wannan, harkar gabana nakeyi.

 

*Sanarwa*
Kamar yanda kuka sani ne ba wani sabon abu ba littafan OUM HAIRAN na kudine zaifi ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali, bana Miki/maka fatan kaci haƙƙin daba naka ba domin nasan Allah bazai bari ba musamman yanzu da zamu shiga wata me alfarma.
Ki biya ta waÉ—annan hanyoyin acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko ku turo katin waya MTN ta WhatsApp number na kamar haka 09013718241. Normal group 300, Special 700.

No comments