Breaking News

Bamagujiya 33-34

 

★★★~~~★★★~~~★★★

 

Abu kamar wasa Saida Beebah tayi kwana goma sha uku a asibitin sannan ta samu ƙwarin da aka sallame ta, a zaman nan nata babu wani daga gidan sarautar da yazo dubata in ka ɗauke Hajiyan soro da tazo


itama don ta fahimci kowa ma a gidan fushi Habeeb yakeyi dashi ne kuma ta fahimci da gaske ya damu da damuwar yarinyar fiye da yanda ya damu da kansa sannan zuwa lkcn anyi walƙiya a cikin gidan sarautar duk wanda ya isa yasan Habeebatullah matar Habeeb ce mai martaba ne har yanzu zancen baije masa ba yaketa sha da gwiɓa.
Wani abu da yaso ya ja masu samun saɓani da Kilishi lkcn da aka sallami Habeebah daga asibiti fir yace bazata koma Emirates House ba gdansa zata wucce domin kuwa baiga dalilin da zaisa Khausar ta tare a cikin gidan daya gina da sunan Beebah ita kuma taci gaba da zama a inda ba don ita aka tanadeshi ba.
Kilishi taƙi yarda shikuma ya kafe itakam data gaji hakanan ranta badon yaso ba ta raka Habeeba har Prince area inda gdan nasa yake ita kanta Beebah bata amince da wannan hukuncin ba saidai batada mafita tunda Kilishi ta amince haka zata hƙr shikam ransa har kunne zuciyarsa fari tas haka suka shiga gidan yana riƙe da hannun Beebah da gabaɗaya jikinta babu ƙwari.

 

Kilishi ce tayi sallama babu kowa a parlourn farkon sai ƙamshi da yaketa fitarwa na amarci Beebah ta lumshe idanunta ta sauke kan wani babban hotonta da sukayi kwanakin baya lkcn bikin naɗin Maje Dutse, neman gurin zama takeyi ya hanata ya ja hannunta ya buɗe wata ƙofa suka shiga parlour ne madaidaici da aka kashe masa manyan kudade wajen haɗashi sai wasu ƙofofi biyu dake facing juna a cikinsa.
Kilishi ya kalla yace “ya kikaga gurin Kilishi?” Ajiyar numfashi tayi ta zauna tace “gurin yayi kyau Habibu ina Khausar É—in?” Nandanan fara’ar kan fuskarsa ta É—auke ya bagarar da zancen da cewa “Da alama kinajin yunwa Wyf ki kwanta naje kitchen na dafo Miki Indomie” murmushi Hajiya Kilishi tayi ta miÆ™e tace “sai ayita hÆ™r da kai zuciya nesa zaman mata biyu Habeeb sai ansa lura saboda abokan adawar junane ko dariya babu wacce keso taga kayiwa wata fiye da wacce kayi mata, to nidai ina horon ka da adalci domin shine hanyar tsiranka”
MiÆ™ewa tayi tayi musu sallama ta fice ya rakata ya dawo har yanzu baiji motsin Khausar ba bai wani damu ba ya shige kitchen ya fara dube-dube yayi Sa’a ya tarar da shinkafa da wake ga salat da cucumber da Bama an haÉ—a an yanka masa kwai gefe kuma ga soyayyen nama nan ya taÉ“e baki yasan bai wucce baÆ™i zatayi ta girka musu ba ya kuwa É—auki flat ya zubawa Beebah ya haÉ—a mata komi ya É—auka ya nufi part É—in nata tana zaune inda ya barta ya zauna yana hilatarta da hira taÆ™i kulawa saboda har yanzu zuciyarta bata sauka dashi ba.

 

Abincin kawai taja ta fara ci tana jin daɗinsa sosai rabonta da taci abinda yayi mata daɗi haka harta manta, aikuwa taci abincin sosai sannan ta miƙe batare data kulashi ba ta nufi ƙofa ɗaya cikin ƙofofin dake cikin parlourn, ta kuwa yi saa ta buɗe nata ta mayar ta rufe tanabin dakin da kallo tashin farko wani ɓangare da aka jera akwatuna guda goma sha takwas ta fara bi da kallo sannan ta sauke idanunta kan gadon da aka gyara shi yaji kayan ƙawa yayi kyau na sosai.
Ajiyar zuciya ta sauke lkcn da taji ya bude dakin ya shigo ya mayar ya rufe ya kamota jikinsa ya janye tare da kallonsa da kallon akwatunan lumshe idanu yayi ya sake janyota jikinsa ya haÉ—ata da jikinsa sosai cikin sanyin murya ta bawan da yake neman tuba gurin ubangidansa yace.
“Kiyi afuwa a gareni Wyf ki daina yimin rowar kalaminki ko mara daÉ—i ne ki rinÆ™a furtamin zan jure wlh nasan kallon da kikemin ki daina zargina ba laifina bane babu yacce zanyi ne amma kinsani duniya ta sani ke nakeson……” Rufe masa baki tayi ta dago manyan idanunta zatayi mgn ya toshe mata bakin da cewa “Karki ce don Allah babu amfani mu rinÆ™a jayayya Beebah wasu hakan sukeson gani ki manta da komai muyi rayuwa me daÉ—i kinga mun samu Æ´anci inason mu raini bbynmu da kulawa”

 

Ƙwacewa tayi taje ta kwanta yayima Kofar key ya rage kayan jikinsa ya haura gadon tayi saurin tashi ya cafke ta ya haÉ—ata da Æ™irjinsa ya É—ora lips É—insa a goshinta ta saki masa wani kuka da ya sanyashi saurin janyewa ya zubanta idanu tanata Æ™oÆ™arin Æ™wacewa sake matseta yayi yace “Ke wai ya kikeso nayi ne Wyf wannan wanne irin kishi ne daya hanaki tsayawa ki fahimceni ki bani dama mu tunkari abinda ke gabanmu?” Magana takeson yi ya hanata dama saboda ya lura sai ya saita mata tunani akansa da gaske sannan zasu daidaita idan ita taÆ™i fahimtarsa waye zai fahimceshi bayan ya É“ata da kowa akanta Mai Martaba har baki yayi masa lkcn da yaji lbrn Habeeba matarsa ce itace bamagujiyar daya hanasa aure, sunyi baram baram har yana iÆ™irarin janye masa tallafi idan bai rabu da itaba shi kuma ya amince ya ajiye masa komai daya shafeshi ya yarda ya rayu da ita, yanaji a ransa indai da ita to bashida wata damuwa.
Hajiya Kilishi ita kaÉ—ai ta rage masa kuma ita ta haneshi yanke igiyar aurensa akan Khausar tunda ita ce ta tona masa asirinsa itace burmawa cikinsa wuÆ™a, duk da yasan komai daÉ—ewa gsky zatayi halinta amma yaso ace shine ya tone komai in yaso komai za’ayi ayi lkcn ya shirya.
HaÉ—e bakinsu yayi suka rinÆ™a kokawa tana kuka tana tureshi shikuma yaÆ™i barinta kuma yaÆ™i rarrashinta Saida ya rabata da komai na jikinta yaja musu bargo babu abinda ke tashi sai shassheÆ™ar kukanta tanayi masa magiya shikuma yaÆ™i sauraronta tunda ya fahimci itama bata sauraron uzurinsa Saida yayi hani’an sannan ya É—aga yana ajiyar zuciya.

 

Taja masa tsaki tare da jan blanket ta rufe jikinta tana ƴan ƙunƙuninta shidai bai kulata yayi wanka ya shirya ya fice tare da ja mata ƙofar.
Ta daÉ—e tana juyi kafin ta Æ™arfafa kanta ta tashi tayi wanka tayi sallar la’asar ta rinÆ™a jiyo hayaniya a babban parlourn itadai ranta bai bata ta fita ba tayi zamanta a parlourn ta tana kallon wani series Film da ake haskawa a MBC Bollywood wayarta tayi ruri ta janyota ganin numbersa yasata ajiyewa taci gaba da kallonta tana nan kwance taji an buÉ—e Æ™ofar an shigo ta É—ago kanta sukayi ido biyu da Æ™annen mijin nata su miemie Miemie ce ta iso gareta tace “Sannu Aunty Beebah ya jikin ya fetus É—in mu?” Tashi tayi zaune a gajiye idanunta akan Khausar da Allah ya sani Beebah ko kaÉ—an batason ganinta.
Ganin itama Khausar É—in idanunta akanta yake yasata kawar da nata tare da cewa “Alhmdllh Mimi ya amarci ku baku tare bane naga kuna yawo?” Murmushi miemie tayi tace “Wlh kinsan itama Khausar rikicin aurenki yasata tarewa babu shiri kinsan ita matar cushe ba daraja ta cika ba….”

 

Jin ƙanwar mijin nata na ƙoƙarin cin mutuncinta a gaban kishiya kishiyarma Beebah yasata juyawa ta fice badon ta rasa abin faɗa ba saidon tuna kashedin da mijin nasu ya kirata yayi mata.
Cikin ranta tana raya matakin daya kamata ta É—auka akan wannan wulaÆ™anci da akeyi mata akan macen da bata fita komi ba zama tayi ranta na suya ta rasa meye yasa dangin mijin nasu suka rabu biyu wasu suna Æ™in Beebah wasu suna Æ™inta, ajiyar zuciya tayi ta kwanta tana kwancen duk sun shigo sunyi mata sallama amma banda Miemie haka suka tafi itakam Miemie gurin Beebah aka barta sunata hirar su har dare Mijinta yazo ya É—auketa ya kaita gda, bayan sallar Isha ne Beebah taji tanajin yunwa ta mike ta fito ta nufi kitchen É—in dake babban parlourn ta shiga, komai akwai a cikinsa hakan ya bata damar daukar doya ta fere tayi fatenta da wake da busasshen kifi ta zubo a flat tana shirin fitowa taji an shigo ta É—ago sukayi ido huÉ—u ta sunkuyar da kanta ganin yanayin fuskarsa babu walwala yasa tsoro shigarta cikin in…ina tace “Sas…sannu da shigowa” ajiyar zuciya yayi ya karÉ“i abincin ya É—auki juice din data dauko ya fita daga kitchen É—in cikin tsoron yanayinsa tabisa a baya suka wucce Khausar tsaye a babban parlourn tana danne-danne da waya.

 

Babu wanda yace da ita itama babu wanda tacewa suka wucceta ta bisu da kallo tare da taÉ“e baki, suka shiga ciki ya mayar da Æ™ofar ya kulle yace “Waye yace kiyi girki?” Kujera ta zauna batare da tayi masa mgn ba ya matso gabanta yace “tambayarki nakeyi” cikin alamun Æ™osawa tace “Ji nayi inason yi” yanayin data bashi amsa yasashi ajiye mata flat É—in ya zauna kusa da ita ya É—ebo yakai mata bakinta ta karÉ“a ya sauke ajiyar zuciya yana bata yana kallonta tayi Æ™asa da idanunta yaja numfashi tare da kiran sunanta, ta É—ago idanuwanta da suka cika da Æ™wallah yasa hannu ya tallafe kuncinta yace “Idan kikaci gaba da kukan nan zaki iya sawa zuciyata ta buga Please Wyf kiji tausayina ki daina kinji?”
ÆŠaga masa kai tayi alamar eh ya É—ora bakinsa a nata yace “Ina zamuje honey moon?” Kwantar da kanta tayi a Æ™irjinsa a hankali damuwarta na yayewa tanajin wani farin ciki da nutsuwa na shigarta, tabbas ta amince Habeeb shine duniyarta bazata iya barinsa ba….
Tunanin ya katse mata da cewa “Idan ina tare dake dukkan wata damuwa tawa takan É—auke na nemeta na rasa Wyf muyiwa juna halarci rayuwa mu rayu dake mu mutu tare wlh kinyimin halaccin da babu wata mace da zata sha gabanki a duniyata ke ko a lahira nasani kina saman kowacce mace cikin matana”

 

Hannu yakai ya shafa cikinta yayi murmushi yace “Zan kaiki Tsaunin gawo idan kin haifamin Bbyna nasan ganinsa zaisa su amince ba butulce musu kikayi ba Æ™addarar rabo tasa muka kasa control zuciyoyinmu har Saida muka mallaki juna Beebah inasonki”
Murmushi tayi wanda rabonta da tayisa har ta manta ta É—ago ta É—ora lips É—in ta kan nasa tayi kissing nasa tace “Nima inasonka Hero kawai idan na tuna…..” Shiru tayi walwalarta ta É—auke kuka na neman kwace mata yayi saurin girgiza mata kai yace “Me kike tunawa?” Da rawar murya tace “Bani kaÉ—ai nake ikon ka ba Hero bani kaÉ—ai ke mallakar ka ba wannan yana saremin gwiwa inajin kamar na mutu saboda baÆ™in ciki komai yakanyimin baÆ™i harda kai, Hero meye yasa dangin mahaifinka sukaÆ™i sona ne shima yaÆ™i sona? Meyesa bazasu karÉ“eni matsayin da mahaifiyarka ta karÉ“eni ba?”

 

Zubanta idanu yayi yana murmushi yace “Ke kaÉ—ai kike mallakar Price Habeeb É—inki Wyf Hero naki ne ke kaÉ—ai” girgiza kai tayi alamar rashin yarda ya tsuke fuska yace “Da gaske” murmushin dole tayi masa nan sukaci abincin ya É—auko ledar daya shigo da ita dadai ita ba ma’abociyar son tsire bace amma tunda ta samu cikin nan kullum sai taci hakan yasa baya gajiya da siyoshi aikuwa tana gani ta sauka ta É—ora kanta a cinyarsa tace.
“Idan na tuna da masoyi sai inji Æ™wallah nata kwarara……
Idan na tuna da masoyi sai inji tamkar In saka Æ™ara…..
Idan na tuna da masoyi sai inji mutuwa bamuda tazara…….”
NishaÉ—i abin ya bashi sosai ya sauko shima ya É—auka yakai mata bakinta yace “Nayi kewa… Nayi kewa…. Nayi kewar me mini hira…..” Dariya duka abin ya basu ta kwantar da kanta a kafaÉ—arsa tace “Kasan me?” Lumshe idanuwansa yayi yace “Me me kenan?” Dariya ta farayi tana rufe idonta ta zame ta fara ja da baya, sosai yake nishaÉ—i ya biye mata suka rinÆ™a zagaye parlourn daÆ™yar ya kamata ya matseta yace “saikin faÉ—a” Æ™ara tayi tace “Wayyo Boobs É—ina Hero mugunta ko ahhh wlh zan faÉ—a maka…”

 

 

Sakar mata nipples É—inta yayi yace “Uhm inajinki” turo baki tayi tace “Yaune kawai na É—an ji daÉ—i da kanayi kadan…..” Hannu yakai zai Æ™ara cafkarta ta kwasa da gudu ta shige bayan kujera yayi murmushi yace “Ina gdy da yabo yau zakiji yafi haka zo kici namanki na ka’ida kar yayi sanyi”
Zama tayi taci gaba da cin tsiren Saida ta Æ™oshi ta tura masa gabansa tace “Kuma na Æ™oshi gobe da safe kafin na tashi ka dumamamin shi” kama kunnensa yayi yace “Angama gimbiyata”
Da wannan suka tashi sukayi ciki tare sukayi wanka suka shirya kamar basu da wata damuwa suka kwanta sun raya daren cikin nutsuwar da cikinsu babu wanda ya taɓa samun irinta suka kwana manne da juna, ita kuwa Khausar tayi kwanan haushi, cikin kwanaki bakwai ɗin da yayi mata ko ɗaki basu taɓa haɗawa ba amma yau tanajinsa sunata nishadinsu da matar sonsa tabbas da aiki ja a gabanta.
[5/12, 8:10 PM] AM OUM HAIRAN:

No comments