Breaking News

Bamagujiya 43-44

 

Cikin Æ™unan zuciya É“arin jiki da tashin hankali ta miÆ™e tsaye idanunta na ganin duhu ta nufi wardrobe domin É—auko kayanta tasa Hajiyan Æ™ofa tace “Matsiyaciya ubanme kikazo dashi da zaki É—auka? Ina haka akazo dake a cikin tsumma zaki wani buÉ—e


wardrobe kinga maza zo kama hanya kafin dare yayi Miki” lumshe idanunta tayi ta juyo ta dubesu ta girgiza kai zuwa yanzu furucinta ya Æ™are batada wata kalma da zata iya furtawa domin kare kanta tabbas komai nisan gona dole zaaje kunyar Æ™arshe wannan shine dalili na farko da yasa taji a ranta zata iya rabuwa da Habeeb rabuwa ta har abada.
Ƙofa ta nufa tana shirin fita ta juyo ta dubi Hudais dake bayan Baba Larai kawai sai taji wani kuka ya Æ™wace mata ta matsa takai hannu zata kwanceshi, Baba Larai batayi mata gardama ba ta kwanto mata shi Hajiyan Æ™ofa tayi saurin karÉ“eshi tana cewa “Allah ya kiyaye ya Æ™ara raÉ“ar jikin wannan annamimiyar matar maci amanar Æ™auna kekam kin cika butulu…..” Wani kallo tabi Hajiyan Æ™ofa dashi ta juya ta fice da sauri Hajiyan soro na Æ™wala mata kira amma bata juyo ba saboda Zuciyarta ta riga ta gama Æ™eÆ™ashewa batajin daidai da second É—aya zata iya Æ™arawa cikin wannan ahlin gara ta fita kamar yanda suka shirya tozartata dayi mata Æ™azafi.

 

Abin takaici da mamaki wai maigadin da komai a gidan ita keyi masa shine ne cewa da ita “Ummah tagai da Assha” wai harda cewa yake “aje aci gaba da tallan Burkutu…..” Ko tana cikin hayyaci itan ba ma’abociyar kula kowanne shirme bace bare yanzu da takejin jiri na É—aukar ta bata iya gane komai kawai daÉ“a Æ™afarta takeyi ko ina.
Batayi aune ba batasan meye ke faruwa ba kawai saiji buɗe idanu tayi taganta a gadon asibiti hannunta da ƙafarta nannaɗe da bandeji, ta rinƙa raba idanu tana kallon asibiti da wani irin yanayi na rashin tabbaci.

 

Ji tayi ance mata “sannu!” Ta karkata akalar idanunta kan wanda ke mgnr cikin yanayi na rashin madafa ta zubansa idanu tanason tuno inda ta sanshi shi ta kasa tunawa ganin yana nufota yasata janye injin idanunta daga kansa ta zubawa selling idanu, hakan ya bashi damar matsowa har inda take ya zubanta idanu a hankali yace “inane yanzun keyi Miki ciwo?”
Shiru tayi masa brain nata na tariyo mata dalilin faÉ—awarta wannan halin ta yunÆ™ura zata tashi da sauri mutumin ya riÆ™e ta tare da Æ™walawa wata nurse kira suka taimaka mata ta tashi zaune ta dubesu cikin rashin hayyaci tace “kwanana nawa anan?” Kallon juna sukayi namijin yace “biyu” cikin tashin hankali tace “Na shiga uku É—ana Hudais ina yake a wanne hali yake yanzun?” Babu me amsar wannan tambaya tata domin basusan komai game da itaba har gara ma Dr Amin shi yanayiwa yanayinta kallon sani amma ya rasa gane inda yasanta, kalmar ta É—aya ta sanyashi jin wata faÉ—uwar gaba ta É—arsar masa.

 

Hawaye ne ya rinÆ™a zubo mata wani na bin wani ta É—ago cikin kuka mara sauti tace “Don Allah ku taimaka min ku faÉ—amin halin da Hudais yake ciki inajin tsoron kada wani abu ya sameshi gashi mahaifinsa baya gari….”
Dafa gefen gadon Dr Amin yayi yace “Kiyi hÆ™r kinga yanzu bakida lfy Æ™afarki akwai ciwo sakamakon accident É—in da kika samu kuma abinda ke cikinki yana samun barazanar zubewa idan kika cika takurawa da tunani komai zai iya faruwa” batace masa komai ba kuma bata daina kukan da takeyi ba ta kwantar da kanta a cikin cinyarta can ta É—ago tace “Wai nan É—in wanne gari ne?” Nurse Zainab ce tace “Kina ne Abuja ko kinsan wani anan?” Da mugun sauri ta dago tace meye ya kawoni Abuja…..” Maganar ce ta shaÆ™eta saboda irin kallon da Dr Amin yake yi mata ta kawar da kai ta fara Æ™osawa da wannan mugun kallon nashi da ta rasa dalilinsa.

 

Kwanciyarta Nurse Zainab ta taimaka mata ta gyara Dr ya fita yana cewa Zainab a bata kulawa zanje gda na É—an huta idan na dawo za’a kwance wannan bandejin aci gaba da treatment din Æ™afar a kula sosai” jinjina masa tayi ya dubi Beebah yace “Madam ko kina bukatar a taho Miki da wani abu?” Baisamu arzikin ko daga hannu ba hakan ya tabbatar masa wannan duk inda ta fito miskilar gaske ce bai takura kansa da son sai yaji daga gareta ba ya juya ya fice yanajin wani irin yanayi me nauyi game da ita a zuciyarsa saidai shi da kansa gargaÉ—in kansa yake yi domin yanayi ya nuna itan matar wani ce ko kuma sakin wani ce.
Da wannan mutuwar jikin ya isa gdansa ya buÉ—e ya shiga yayi parking ya fito ya nufi kofar da zata sadashi da asalin cikin parlourn gidan ya buÉ—e ya shiga babu kowa a parlourn don haka kai tsaye ya nufi sama acan ya jiyo hayaniyar yaran ya isa ya bude dakin nasu sunata wasansu suna ganinsa sukayo kansa suna “Oyoyo Dad” kama hannunsu yayi yana musu yar gajerar dariya yace “Ina Mom É—inku?” Ƙaramin ne ya karyar dakai yace “Yau Mom hutu takeji tace kada mu dameta” yasan Æ™iriniyarsu shiyasa ya saki hannunsu yace “Ok kuje kuyi alwala bari nayi wanka nazo muyi jam’in sallar Azahar” shigewa ciki yaran maza guda biyu sukayi da gudu yayi murmushi ya nufi É—akin uwargidan nasa ya buÉ—e tana kwance a gado tana latsa waya tana ganinsa ta tashi tanayi masa murmushi ta tarosa tayi hugging nasa tare da kissing Æ™irjinsa tace “your are welcome my jannati” shafa kanta yayi yace “Welcome sweeter ya fama da Æ™iriniyar yara?”

 

Rausayar dakai tayi tace “Sun dameni habeebty shiyasa nace suje suyi playing games su barni na huta” Safeenah kenan macen gaske ta samu lambar yabo wajen iya kula da miji matsalarta É—aya baÆ™in kishi ko kaÉ—an bata Æ™aunar taga wata mace ta raÉ“i mijinta wannan yasa bata Æ™aunar duk wani abu da zaisa mijinta yaji a ransa ta cancanci yayi mata kishiya, ta gwammace ko zatasha wahala itadai tasha indai zata rayu da Dr Amin É—in ta ita kaÉ—ai, wannan kenan.
Jansa tayi har bathroom sukayi wanka suka fito yaje sukayi sallah su da yaransu sannan suka zauna cin abinci sunacin abincin zuciyarsa na gurin petiant É—insa yarinyar ta tsaye masa a rai, yanason jin dalilin barowarta gda shikam yanayinta yana nuna masa duk inda ta fito babban gidane batayi masa kama da matar yara ba.
To yau É—in ma bai iya bawa Safeenah labarin petiant din tasa da baisan sunanta ba sai ita ce tace “Nikam Sweeter ya labarin yarinyar da kace tsautsayi yasa ka bigeta a Kano Amma ka kawota asibitinka saboda ka bata kulawa?” Numfashi ya sauke yace “har yanzu babu wani labari game da itan saidai yanayi yana nuna itaÉ—in matar wani ce Inma mutuwar aure tasa ta baro gidanta ko kuma wata babbar damuwa to koma dai menene inason ta kara samun sauÆ™i sai muyi magana a nutse”
Jinjina kai tayi tare da cewa “To Allah yasa muji alkhairi” amsawa yayi da Amin ya miÆ™e yace “inajin bacci zanje na É—an kwanta hudu ki tasheni” itama miÆ™ewa tayi suka tafi É—akin tare suka kwanta suna Æ´ar hirarsu ta ma’aurata har bacci ya É—auke su.

***********

Kwanan Habeeb É—aya a Lagos hankalinsa ya dawo gida saboda yinin da yayi yana kiran wayar Beebah tana ring amma ba’a É—agawa, gashi duk wani wanda zai samu bayani ta gurinsa ya kira wanda ya É—aga ne zaice masa kawai ya dawo gida babu lafiya wasu kuwa basa É—agawa, lkcn da Najeeb da Hajiya Kilishi suka sanar dashi gidan babu lafiya dare yayi nisa don a kallah lokacin sha biyu ta wucce.
Dole tasa ya kwanan zaune sai wajen asuba ya samu bacci barawo ya ɗauke shi aikam babu shiri ya tashi saboda ko a mafarkin baiga alkhairi ba karfe takwas jirginsa ya daga sai Birnin Dutse yayi saa kuwa Najeeb na jiransa kai tsaye gdansa ya nufa dashi cike da tausayin halin da aminin nasa zai zama a ciki, shidai ya hakikance duk wannan abun da akace ya faru koda Habeeb kamawa yayi da idanunsa yanda yakeson yarinyar nan bazai taɓa yanke hukuncin da Mai Martaba ya yanke wa auren su ba.
Tun daga babban parlourn ya fara fuskantar tabbas gidan ba lafiya lau yake ba domin kuwa babu wata alama da take nuna an gyara shi yau, haka ya kutsa sashin Beebah yana Æ™wala mata kira amma shiru yanda yaga É—akin a hargitse kayanta duk a baje a kasa yasa gabansa faÉ—uwa ya juya ga Najeeb yace “Batada lafiya ne?”

 

Sunkuyar dakai Najeeb yayi ya riÆ™e kafaÉ—arsa da Æ™arfi ya jijjigashi yace “Ka sanar dani meye ya faru da Wyf bayan tafiyata?” Janyewa yayi yace “kazo muje cikin gida zakaji komai” to dake neman bayani yakeyi baiyi musu ba yace “nasan ma bazai wucce suna can ba” da wannan suka fita suka nufi gidan sarautar suna zuwa ya fita a motar ko parking Najeeb bai gama yi ba ya shige ciki yana Æ™walawa Kilishi kira, tana É—akinta tanaba Hudais madara taji kiran nasa gabanta ya yanke ya faÉ—i tasan yau hauka ne a gidan harsai anyi kamar ayi masa turu.
MiÆ™ewa tayi ta fita yana ganin Hudais a hannunta yace “Ina Wyf É—in take Kilishi jikin nata ne ya matsa ne?” Sunkuyar dakai tayi hawaye ya zubo mata tace “Tabbas Habeebu Wlh tallahi Habeebatullah bata cikin mutane masu dauÉ—a da zunubin zina amma kash abin tur da Allah wadarai anyi amfani da wani saurayi da kuma shaidar da maigadin gdanka ya bayar an kitsawa Mai Martaba Æ™arya da gaskiya akan cewa tun lkcn daka tafi London Beebah ke kawo maza gidanka sai jiya asirinta ya tonu Habeeb Mai Martaba yayima Beebah korar kare tare da aron bakinka ya datse igiyoyin auren dake tsakaninku, bayan haka kuma ya karÉ“e Ibrahim daga gareta, wlh tun jiyan da abin ya faru na baza mutane su lalubomin ita don na hakikance wannan Æ™azafi ne Æ™age ne……….
[5/19, 7:59 PM] AM OUM HAIRAN: _*B

No comments