Breaking News

Bamagujiya 47-48

_Ban amince a juyamin littafi ta kowacce siga ba_

 

Jinjina kai da girman lamarin Engineer Wali yaci gaba da yi can Habeeb yace “kasa na faÉ—a maka damuwata kuma kayimin shiru Shikenan tunda bakada abin faÉ—a kaje kaima kubarni na mutun in hankalinku zai


kwanta….” Katseshi Wali yayi yace “Not ka gane Friend ina tunanin rayuwa irin taku ta gidan sarauta meyesa bakuson bare a cikinku ne meye yasa kuke yanke hukunci da son rai Wallahi duk da cewa bantaÉ“a ganin Maman Hudais ba amma zuciyata bata amince zata aikata wannan abinda akace ta aikata ba haba shi Mai Martaba hankalinsa ne ya gushe ko kuwa rufa ido akayi masa yarinyar da batasan kowa ba sai kai da Ahlinka yarinyar da kai da kanka Saida kukasha Æ™warbai kafin ta amince dakai har ku fara gudanar da Sunnah da ita yarinyar da kowa ya sani ko Æ™awa bata taÉ“ayi ba sannan batada fitina kullum cikin nutsattsen yanayi take Habeeb wato kayi gaggawa daka datse igiyar aurenka dake kan Æ™anwarka Khausar inada yaÆ™inin ita tasan komai kuma bazai wucce shiri da tuggunsu ba”

 

 

Numfashi ya sauke yaci gaba da cewa “Kai akaso a dasawa kokwanto tsana da Æ™yamar Maman Hudais sai aka ga wannan bazai yiwu ba domin bakai ka dasawa kanka yarda da soyayyarta ba shine aka juya lamarin kan Mai Martaba ta yanda zaka tabbatar da abin shiri ne

Meye ya kawo Mai Martaba gidanka a wannan lokacin kuma meye yasa ba’a bari anji abinda ita Beeban zatace ba sannan meye yasa ba’a kiraka ba domin sanar dakai a daidai lokacin? To duk waÉ—annan abubuwan abin dubawa ne amma bamu da lokacin dubasu kawai ta ina kake tunanin zamu fara neman yarinyar nan?”
TaÉ“a Æ™ofar akayi hakan ya dakatar da hirar tasu Engineer Wali ya tashi ya buÉ—ewa Dr Al’Amin ya shigo yana duban Habeeb sukayi musabaha ya dubi Wali yace “Bro wake ba lafiya?” Kallon Habeeb Wali yayi yace “Gashinan abokina ne da nake baka labari munyi karatu a Oxford dashi ya fara karantar harkarku mahaifinsa Sarkin Dutse yasa ya juya zuwa É“angaren mu kaganshi nan ciwon soyayya ne ke wahalar dashi ko kunada maganin matsalar?”
Murmushi Dr Amin yayi yace.

 

“TurÆ™ashi lamari ya É“aci kenan ciwon so akwai wahala Nima gashi ina neman faÉ—awa a karo na biyu duk da dai inata kwaÉ“ar zuciyata kada ta shigar dani inda bazan fito ba” yana maganar yana gwada BP É—insa ya dubeshi da sauri yace “Ya Salam Engineer ka rage wannan damuwar kaga yanda BP naka yayi sama kuwa?
Gaskiya ka rage damuwar komai zai wucce insha Allahu girgiza kai yayi ya sharce hawayen dake Æ™oÆ™arin zubo masa yace “Kayi aikinka kawai babu wani abu da zai iya rabani da wannan damuwar sai dalilinta” daga haka bai kuma cewa komai ba Dr Amin ya gama rubuce rubucensa ya bawa Wali ya juya yana cewa “Ka kula da kanka Please akwai yanayin hauhawar jinin da ka iya haifar da komai Allah ya shiga lamarin” amsawa Wali yayi suka fita tare har asibitin suka sayi maganin sannan ya juyo yana mamakin yanda yayan nasa bashi labarin yanda akayi ya sami petiant É—in tasa da ya dauki kulawar duniya ya É—orawa.

 

Komawa yayi tare da yima Habeeb bayanin magungunan ya karɓa ya zubesu Saida ya takura masa sannan yasha maganin yaci gaba da jinyar jikinsa tare da baza cigiyarta jaridu talabijin da rediyo duk da kasancewar Amin ɗan nacin karanta jaridu kwana biyun yanayin jikin Beebah da kuma rashin lokaci yasa baisan wainar da ake yi toyawa ba.
A haka Beebah Saida ta shafe kwanaki arba’in a asibitin tana jinyar Æ™afarta sannan taji sauÆ™i sosai lokacin kuma cikinta ya fara bayyana sosai abinka da itan ba doguwa bace sosai shi yasa cikinta baya É“uya watanni biyar kowa na iya ganinsa, Dr Amin dakansa ya yankar mata katin files na awo a asibitin sai lokacin ne ya fara tunanin ta yanda zaijewa da Safeenah maganar, koda ya tunkareta tayi masifar bashi mamaki yanda ta nuna ai babu komi ya kawota su zauna har zuwa lokacin da zatayi bayanin daga inda take ita da kanta take cewa dashi yarinyar ta bata tausayi daga ganinta wartako akayi daga gidan mijinta kodai asiri ko kuma bakin ciki ya hanata faÉ—ar daga nahiyar da take.

 

Yaji daÉ—i sosai a ranar kuwa Beebah ta dawo gidan da zama Safeenah nata bata kulawa musamman dataga cikinta ya fara tsufa haka tayita zolayarta hardai ta saki jiki sukaci gaba da rayuwarsu a gidan gwanin ban sha’awa babu hantara bare kyara duk da cewa zuciyar Beebah na gurin É—anta da mijinta amma haka take daurewa saidai idan kewarsu ta dameta ta shige É—aki tayi kukanta ta Æ™oshi idan Safeenah ta ganta ta rinÆ™a bata hÆ™r daÆ™yar Safeenah ta samu Beebah ta bata labarin abinda ya fito da ita daga gidan mijinta sosai Safeenah ta kaÉ—u da jin wannan mugun makirci ta tausaya mata taso ta faÉ—awa Dr Amin amma fir Beebah taÆ™i barinta ta rinÆ™a roÆ™onta tabarshi batason komawa gidan Habeeb akanta abubuwa da dama sun faru dashi gashi har mahaifinsa yanajin ta cancanci ya ari bakinsa ya saketa.
Ajiyar zuciya Safeenah tayi tace “Shirme ne kawai da É“acin rai ai Shari’a ce kawai take da ikon sakarwa mutum mata shima kuma sai idan ya amincewa hakan, Beebah har yanzu kinanan matsayin matar mijinki kawai dai basu iskar yanada amfani amma dai don Allah karki azabtar da bawan Allah ki daina cewa bazaki komawa aurensa ba yayi don ke basani kema kinyi dominsa kiyi hÆ™r ki bayyana masa inda kike ko ya samu sauÆ™in damuwa kada kiyi kisan rai”

 

Batajin wannan magiyar abubuwa da yawa suke sata ƙin saurarar Safeenah idan ta tuna ta rabu da komai saboda Habeeb ta rasa komai sabodashi ta zaɓeshi fiye da iyayen da suka kawota duniya tabarsu tabisa amma ta kasa samun mafaka a gurinsa ɗan da takejin shine raba gardamarta shima sun karɓe sun barta batada tsuntsu bare tarko.
Takanyi kukan nadama da tunanin ta yanda zata tunkari iyayenta.
Kwanaki sukayita tafiya cikinta na tsufa har ta shiga kwanakin haihuwarta kullum sai sun fita motsa jiki Allah kuwa ya kawo mata haihuwar da sauƙi a gida ta haifi yarinyarta mace cikin dare ita kaɗai a ɗaki.

 

Sai bayan haihuwar ta kira Safeenah ta sauko tazo taga abin mamaki ta koma da gudu ta taso Dr Amin dakansa ya gyara yarinyar suka gyara maijego Safeenah ƙin komawa saman tayi ta zauna a gurinsu.
Karon farko taji tanason sanar dashi abinda ya shafeshi wayarta ta dauka ta latso number sa ta rubuta masa gajeren saƙo kamar haka.
_“Inayiwa Mijina fatan alkhairi da nasara akan duk abinda yakeyi yanzu, ina mai farin cikin sanar dakai yau ajiyar ka ta fito mun samu Æ™aruwar Æ´a mace…..”_
[5/24, 8:42 PM] AM OUM HAIRAN: _*BMGJY Bonus 49-50*_

_Ku biya ta acct detail 3184512451 First bank ko kati MTN ta WhatsApp number 09013718241._
_Normal 300 PC 700_
_Ƴan Niger zaku biya 500f ta wannan number +227 95 04 58 22_

_Ban amince a juyamin littafi ta kowacce siga ba._

 

No comments