Breaking News

Bamagujiya 51-52

End! End!! End!!!_

 

Tunda Habeeb yabar garin Abuja yabar Safeenah da Dr Amin da rikicin Beebah don gabaÉ—aya ta rikice musu cikin kwanakin batada wata walwala indai kaga tana dariya to ba’a sako mata zancen Habeeb bane da


zarar anyi mata zancen shi zata haɗe rai ta fara kumbura ga Safeenah da nacin magana ta rinƙa nuna mata damuwarta da lamarin Habeeb kenan har sai taga ta ƙosa tana shirin tashi tabar gurin sannan zata ƙyaleta.
Abin da yake bawa Safeenah mamaki bai wucce yanda tasha kama Beebah tana kuka ko kuma cikin bacci taji tana ambaton sunan Habeeb É—in ba amma kuma a zahiri idan akayi mata batunsa sai walwalarta ta É—auke, to yauma kamar ko yaushe tana zaune a É—aki ta gama yima Ayyana kwalliya tana taje mata gashinta taji Muryar Safeenah na cewa.
“Ashe bakine damu a gidan sannunku da zuwa” duk da batasan su waye ba Saida gabanta ya faÉ—i haka tadai maze taci gaba da yiwa Æ´arta wasa a haka Safeenah ta shigo ta sameta fuskarta wasai alamun farin ciki tace “Kizo kinada manyan baÆ™i a parlourn baÆ™i” bata jirayi abinda zata ce ba duk da taga alamar cewar a tattare da ita ta juya ta fice bayan ta karÉ“e Ayyana a hannunta, jiki babu Æ™wari haka ta miÆ™e ta É—auki mayafinta ta yafa ta fice daga dakin ta nufi É—akin baÆ™in gabanta naci gaba da faÉ—uwa.

 

Tura ƙofar tayi ta shiga tare da sallama idanunta ya sauka kan Jumme dake zaune gefenta mahaifinta ne riƙe da Hudais sai Kilishi dake dauke da Ayyana, tsayawa tayi turus tanajin wani faduwar gaba na shigarta tare da bin iyayen nata da kallo ɗaya bayan ɗaya.
RiÆ™o hannunta akayi ta juya ta dubi wanda ya riÆ™e hannun nata ganin Habeeb ne ya É—aganta gira tare da janta har zuwa inda mahaifan nata ke zaune tana isa ta zube a gabansu da sauri jikinta na rawa tana wani irin kuka ya Æ™wace mata data kasa sanin na meye farin ciki ko nadama? Tabbas tayi farin cikin ganin iyayen nata sun taso takanas dominta, sannan nadamarta ta tsayin watanni ta dawo mata sabuwa tabbas da tabi umarnin Mahaifanta ta nuna jajircewarta da bata fuskanci wani wulaÆ™ancin ba tasani yan É—akin da mijinta yafito da mahaifiyarsa sun sota sun kaunaceta da kaunar da mijinta yake yi mata, duk da tasan cewa bata isa kaucewa kaddararta ba tunda Allah ya Æ™adarta Habeeb shine uban Æ´aÆ´anta to ko bataso sai ya zama mijinta amma tayi wasarairai da Æ™imarsu…..
Cikin kukan me taÉ“a zuciya ta buÉ—e baki tace “Jumme Baba nasani na cusa baÆ™in ciki da damuwa a zuciyarku duk da cewar kunyi É—awainiya dani tundaga samuwata har zuwa girma na, a lokacin da zan nuna muku tabbas kuÉ—in iyaye ne na kwarai duk da rashin hasken musulunci a cikin rayuwarku baisa kunyi wasarairai da tarbiyya ta ba, kawai sai Æ™addara ta jefomin shi cikin rayuwa ta har naji a raina gara na barku dana barshi, inason Habeeb nasani shima yayi domin Ni yayimin halaccin da maza masu irinsa sunyi Æ™aranci a duniya saboda Ni ya amince ya rasa komai daya mallaka ta bangaren mahaifinsa Æ™arshe kuskuren mu mu biyu ya haifar min da damuwar da har na mutu bazata goge ba, ko sanda bana cikin musulunci ban kaunaci zina ba na Æ™yamace ta na tsaneta har kawo lokacin da Habeeb ya zama mijina, kwatsam waini Habeebah saboda son zuciyar kishiyata kishiyar surukata da iyayen kishiyata yasa sukayi amfani da Æ™iyayyar da mahaifin mijina yakemin aka barratani da mijina a lokacin da nake buÆ™atarsa aka rabani da É—ana da nake kallonsa a matsayin gata na…”

 

Kukanne yaci Æ™arfinta daÆ™yar ta buÉ—e bakinta tace “nasani haƙƙinku ne wlh badon banason Habeeb ba amma na zaÉ“i yi muku biyayya wannan karon matuÆ™ar zaku yafemin kuskurena na baya da rudin Æ™uruciya yasani aikatawa kuyimin afuwa ku yafemin don….”
Rufe mata baki Jimo yayi yana murmushi yace “Kayyah Bibon Baba wannan ai ya zama shuÉ—aÉ—en labari Æ™addararki ce kamar yanda Liman ya fada mana ina zamukai rabon WaÉ—annan yaran Habeebah dakin matsa ma wajen yimin biyayya da tuni ba labarina akeyi ba kila da tuni Æ™asa ta jima da rufe idanuna kece da hÆ™r Bibo da ban hau dokin zuciya ba da baki wulakanta ba kuma da da haka ta faru mu zaki nufo mu share Miki hawayenki nikam na yafe Miki tun ranar da hasken musulunci ya ratsa Zuciyata Habeebatullah kije ki rayu da mijinki da yaranki cikin aminci kuma na tabbatar kafin Ni mahaifiyarki ta jima da yafe miki”

 

Kwantar da kanta tayi saman cinyar mahaifinta taci gaba da rera kukanta na farin ciki tana gdy ga Allah da ya ƙadarta mata ganin wannan rana itakam da basu yafe mata ba da batasan ya zatayi da rayuwarta ba.
Ji tayi an kama gashinta anja ta É—ago tare dayin murmushi ashe Hudais ne ta miÆ™a masa hannu ya taho jikinta ya kwanta luf yana sauke ajiyar zuciya ta dubi Kilishi tace “Kilishi dama a gurinki yake ba a matar babansa ba?”
Murmushi Kilishi tayi tace “babanshi ai bashida mata tun washegarin ranar da kika bar gidan itama ta bari gara kema kullum muna hasashen dawowarki itakam ta tafi kenan yanzu haka ma tayi aure shekaran jiya ta tare a gidanta” ajiyar zuciya ta sauke dama tasan auren Khausar da Habeeb wataran dole zai Æ™are don da gaske Habeeb yake Khausar bata tsarinsa amma bataso ace itane sanadi ba.

 

Ranar yini akayi ana hirar yaushe gamo iyayenta kamar su mayar da ita ciki Safeenah sai hidima takeyi da baÆ™i tsakanin Beebah da Habeeb kuwa Saidai kallo kawai Allah yasani tasan baiyi mata komai ba amma ta Æ™udurce a ranta matukar ba Mai Martaba ne ya amincewa zamansu matsayin ma’aurata ba to ta hkr dashi itakam ta daidaita da nata iyayen shima tanaso taga ya samu daidaito da mahaifinsa a washegari suka É—auki hanyar Dutse harda Beebah tunda suka taho gabanta ke faduwa bata fatan ace su sauka a gidan sarauta saboda komai zai dawo mata sabone.
Ga mamakinta sai taga sun nufi wata babbar unguwa ta manyan attajirai an buÉ—e musu wani get sun shiga yayi parking suka fito shine yayi musu jagora har cikin gidan yana nuna musu ko ina Saida ya gama nune nunensa sannan ya juyo ya dubi Habeebah yace “gidanki ne da zaki rinÆ™a sauka idan kinzo hutu daga London saboda ina tunanin nan da 2 weeks zamu tafi” Saida taji wani dam a Æ™irjinta tayi masa wani mugun kallo sannan ta kawar dakai anan sukaci sukasha kukunsa ya shirya musu komai Saida suka gama sannan ya É—ebesu suka nufi tsohuwar unguwar su shima tsohon gidan cikin watanni biyar zuwa shidan ya gyara shi sosai ya sake masa kayan cikinsa Saida suka gama dubawa sannan ya dubeta yace.

 

“Wannan kuma nakine halak malak Habeebah bansan dame zan saka miki soyayyarki gareni ba sannan bansan dame zan goge Miki tabon mikin da akayi Miki a duniya kawai saboda a rabani dake ba wlh tallahi Habeebah tun kafin bayyanar gaskiya Ni nasan bazaki taÉ“a aikata abinda akace kin aikata ba kuma Kilishi ma da su Hudah sun shaideki akan hakan, mun riga mun yanke hukunci Baba da Jumme zasu zauna cikin wannan gidan saboda wata hatsaniya da tasa suka baro garin Tsaunin gawo dalilin karÉ“ar addinin Musulunci da sukayi”
Tunda ya fara maganar take kallonsa idanunta na zubar da hawaye tana girgiza masa kai har Saida ya gama sannan tace.
“Bana bukatar komai daga gareka Habeeb Ni burina naga kun daidaita tsakaninka da mahaifinka yaci gaba da sonka da janka a jikinsa kamar yanda yake yi a baya burina ya karÉ“eni matsayin suruka nasani inasonka saidai so bazai rufe mana idanu a karo na biyu mu kara yin abinda zamu zo yaci gaba da bibiyarmu har jikokin mu ba, nasan kafini sanin girman haƙƙin mahaifa akan Æ´aÆ´ansu….”

 

Tunda ta fara maganar yake kallonta har ta gama yayi murmushi yace “hakane kema kince wani abu saidai ki sani Mai Martaba jikinsa yayi sanyi tun lokacin da naje na nuna masa hotunan Ummi na na sanar dashi kin haifa min Æ´a mace a ranar yake cemin naje na dawo dake É—akinki komai ya wucce a manta da duk wani abu daya faru dama shi tunda abin ya faru yake tuntuntuni akan abin sai gashi yaron da kansa yazo ya Æ™aryata kansa batare da wani ya takurasa ba yace sashi akayi yazo a daidai lokacin aka shirya plan na yanda za’a gayyato Mai martaba yazo ya kamaki da kansa,
Idan baki gasÆ™ata abinda na faÉ—a Miki ba yanzun mu wucce gidan sarautar kiji da kunnenki…..”

 

 

“Basai kunzo ba Ni nazo” sukaji an faÉ—a a bayansu juyawar da zasuyi sukaga Mai Martaba tsaye da dogarawansa jikin Æ™ofa ya tako fuskarsa dauke da murmushi har gaban Beebah ya riÆ™o hannunta yace “So da yawan lokaci munayin hasashe baibai da daidai mukan hasaso abinda yake saÉ“anin gsky sai zukatanmu su tafi akansu har su rinÆ™a tursasamu akan cewa wannan abin shine daidai, na hasashi kuskure na tafi akansa nayi jayayya da abinda ubangiji ya hukunta karshe nayi zaÉ“i sabanin na ubangiji na takura masa Saida ya karÉ“a bisa shawarwarin Ƙanina Lukman da Hajiyan Æ™ofa ashe duk a keken É“era suka É—ora ni yanzu gashi Ni da idanuna yayanku Ahmad ya É—aukeni ya kaini wani hotel na kama Khausar da hannu na da maza tana shaye-shaye turr da wannan asara da taÉ“ewa Habeebah duk da an daÉ—e ana faÉ—amin Khausar ba sa’ar auren Habeeb bace bantaÉ“a yarda ba sai ranar kuma abin mamaki harda yaron da akace kece kika gayyato shi don buÆ™atar kanki saboda Kinga mijinku bayanan daganan na tabbatar duk wani abu daya faru makirci ne akayi amfani dani don shiga tsakaninki da mijinki Habeebah kiyi hÆ™r ki rayu a gdanki tare da Æ´aÆ´anku kamar yanda nakewa kowacce Æ´a dana haifa fata”

 

Sosai Habeeb yaji daÉ—in yanda mai martaba ya wankesa ya sani ba don Allah ya kawosa yayi bayani dakansa ba da babu kalmar da zai yi amfani da ita wajen fahimtar da Beebah,
Shida mai martaba da Kilishi ne suka tafi inda suka bar Beebah da iyayenta sunata mamakin karamcin surukanta sunata hirarsu ta yaushe gamo nan suke faÉ—a mata mutuwar Baba Uda taji mutuwarsa sosai har hawaye tayi.
Rayuwarta me takeyi ita da iyayenta saboda Kilishi ta hanata komawa gdansa tace ta bari tayi arba’in ransa baiso ba hakanan ya hkr ya haÉ—a nasa ya nasa ya wucce London.
Yanda Habeeb ya mayar da hankalinsa wajen kula da iyalinsa abin ba’a cewa komai bayan tayi arba’in ya harhaÉ—a masu nasu ya nasu suka É—auki hanyar birnin London daga wannan lokaci komai ya wucce rayuwa ta saitu kamar babu wani abu daya taÉ“a faruwa komansa Beebah komai ya tashi yi da ita yake shawara, ga yaransu dagwai dagwai gwanin ban sha’awa Saida Ayyana ta shekara Biyar sannan Beebah ta sake haihuwar yaronta namiji yaci Sunan Mahaifin Beebah wato Muhammad kasancewar bayan musuluntarsa cewa yayi akirasa da Muhammad.

 

_Tammat bih hamdullah_

 

_Wannan littafi Mai farin jini nan na kawo karshensa kuskuren dake ciki Allah ka yafe mana ba don halinmu ba Allah ka bamu ikon amfana da abubuwan amfanin cikinsu._

No comments