Breaking News

Bamagujiya 9-10

Last Free Page 9-10*

★★★~~~★★★~~~★★★

 

Bai koma gda ba sai yamma koda ya fito daga ma’aikatar yayan nasa tasu ma’aikatar ya nufa amma abin arziki ya kasa hassalawa sai juyi da yake a kan kujera wayar Beebah


yaketa kira taki tafiya duk damuwa tabi ta cunkushe masa zuciya sai bayan magrib ya nufi gdan babu wani karfi a jikinsa saina imani wanka yayi yana shirin fita Masallaci sallar Isha wayarsa tayi ruri ya ganin number Mai martaba yasashi haÉ—a nutsuwarsa ya daga Mai martaba yace “in ka dawo kazo inason ganinka” amsawa yayi tare da fita yaje yayi Sallah sannan ya nufi kiran na Mai martaba ya shiga da sallamarsa yana zaune saman shimfiÉ—un Kilishi da farin tabarau a idanunsa ya amsa sallamar Habeeb ya nemi guri ya zauna yace.
“Allah yaja kwana gamu mun amsa kira” É—agowa yayi yayi masa murmushi ya miÆ™e ya saita zamansa yace “Am dama wani babban uzurine ya taso munason zamu haÉ—a gwiwa da wani campany dake Japan domin haÉ“akar masana’antunmu” jinjina kai Habeeb yayi yace “hakan yayi Allah ya taimakeka hakan zai kawo ci gaba Æ™warai” murmushi Mai martaba yayi yace “shiyasa nakeson ka Habibullah to dama ba komai bane yasa na kiraka campanyn sun buÆ™aci a tura mutum É—aya daganan domin yaje yayi course na yanda ayyukan suke kasancewa kamar yanda suma zasu turo nasu wakilan don faÉ—aÉ—awa juna fasaha.
Na duba naga babu wanda ya dace da wannan tafiya saikai duba da kwazonka da basirar ka saboda haka kaje ka fara shiri nan da sati biyu zaka tafi in Allah ya yarda….”

 

Tunda Habeeb yaji Æ™udurin Mai martaba gumi yake karyo masa yasan tabbas da manufa cikin wannan shiri, a sanyaye ya É—ago ya buÉ—e baki zaiyi mgn Mai martaba ya É—aga masa hannu yace “banason kace komai kaje Allah yayi maka albarka shekara É—aya ne babu yawa idan Allah ya amince kafin lkcn zan sama maka matar data dace dakai na aura maka na turota tunda na fahimci yanzu hankalinka ya hadu kana buÆ™atar auren” a kasalce yace “Habeeban fah ranka ya daÉ—e….” Shiru mai martaba yayi masa shi kuma ya kasa tashi jikinsa har rawa yake saboda tashin hankali bai iya jurewa ba yace “Na rantse da Allah bazan iya zama da duk wacce zaka aura min ba Allah ya taimake ka indai bazaka amince nayi jahadin janyo Habeebah daga duhun kafirci zuwa hasken musulunci ba idan bazaka amince min na rayu da abinda raina da zuciyata suke muradi ba to ina roÆ™onka da kayi hkr ka barni na Æ™arasa rayuwata ni kadai kamar yanda na shirya yinta a baya….”

 

Tsawa Mai martaba ya daka masa yana huci yace “Ni Habeeb Nine nake faÉ—a kake faÉ—a harma na zartar da hukunci kace baka amince ba lallai ya tabbata ka girma kakai shiyasa har kake jayayya dani akan kafira, to na rantse da Allah kaji dai kuma ka sani bana saurin rantsuwa akan lamarin rayuwa to nayi akan wannan yarinyar indai kaga ka aureta to kodai ka canza uba ko kuma bana numfasawa, tashi ka ficemin a daki kafin na nakasaka”
Tsuma jikin Habeeb yakeyi saboda É—imuwa da gigita rantsuwar mahaifinsa tayi mugun girgiza shi Shikenan ta faru ta Æ™are Mai martaba ya gama yanke hukunci yanzu babu bakin da zai iya fahimtar dashi ya gane….”

 

Sashin Hajiya Kilishi ya nufa da ƙannensa biyu mata da suke ciki ɗaya da sauran matan gdan duk suna babban falon suna kallo yazo ya shigesu ya nufi ɗakin mahaifiyarsa ya faɗa kan gadonta saboda mugun sanyin da yaji yana keta ƙashinsa yaja bargo ya rufa.
Kallon kallo sukayi Hajiya Zulai ta dubi Hajiya Kilishi da Hajiya Hauwa tace “Salma?” Dubansu Kilishi tayi tace “Naam Zulai” Hajiya Hauwa ce tace “Soja Æ™alau kuwa?” Numfasawa tayi tace “da alamun ba Æ™alau ba wato É—ebowa yayi da zafi aure yakeson zaiyi kuma ba musulma bace yarinyar da yakeson aure, nikam na fahimceshi kuma na bashi goyon baya to amma fah tunda mai martaba bai fahimta ba babu wanda ya isa ya fahimtar dashi”
MiÆ™ewa Hajiya Zulai tayi ta nufi É—akin tace “Babana komansa daban banda rigima irinta tarar aradu daka inashi ina kafira matsayin mata….” Tana faÉ—in haka ta bude dakin ta shiga yanda taji gadon na rawa yasata nufarsa da sauri ta yaye bargo tace “Innanillahi Ni Zulaihatu Babana meye hakan kuka kamar wani Æ™aramin yaro….”
Tashi yayi zaune ya kama hannunta yace “Don Allah ku ceci rayuwata ku faÉ—awa mai martaba zanje Japan É—in amma ya barni na auri Beebah Hajiyan soro bazan iya taÉ“uka masa komai ba indai ya rabani da Beebah nasan itama bazata iya rayuwa babu Ni ba”

 

Numfashi taja tace “Akan mace kakeson kashe kanka dubi fa yanda kake rawar sanyi Habeeb yanzu waye kake tunanin zai iya tunkarar mahaifinku yace zai fahimtar dashi?”
Hajiya Kilishi ce ta cafe da cewa “kaje inda ya umarce ka kayi masa biyayya insha Allahu zaka dace idan kace zakaja yaja kaine zaka faÉ—i Æ™asa” zama sukayi sunata rarrashinsa shikam banda zafin jiki ma babu abinda suke Æ™ara masa kafin wane wannan zazzaÉ“i me zafin gaske ya lulluÉ“eshi Hajiya Kilishi ta shiga damuwa tabbas bada wasa Autan mazan nata ya É—auki lamarin ba da gaske yakeyi don duk abinda yasa a ransa har yakai masa jinya to ya isa kallo.

 

Ranar sai ɗakin tabar masa bayan likita ya duba shi baccin wahala ya ɗauke shi zuciyarsa taƙi samun sukuni
Washegari da asuba ya duba wayarsa ya zabura ya tashi zaune yana latsa wayar bugu biyu ta daga cikin muryarta me cike da gajiya da kasala tace “Tunda ka tafi nake kiran ka naji ko kun sauka lfy bana samu É—an birni ina fatan lfy kake…” Wata gwauruwar ajiyar zuciya ya sauke yace “kamar bakida lfy meye yake damunki?” Kukan da ta kwana ta nayi shine ya dawo mata sabo tace “banasonsa wlh tsohone idan suka auramin shi kashe kaina zaiyi É—an birni kai nakeso….”
“Wa?” Ya faÉ—a da Æ™arfi yana miÆ™ewa daga gadon cikin kuka tace “Sarkin Mahauta….”

 

MiÆ™ewa yayi daga gadon yace “Wa…waye yace zai bashi ke waye….” Kashe wayar tayi yayi bin duniya ta kasa É—agawa aikuwa ba’a wayi gari dashi a gdan ba ya nufi tasha ya hau mota saboda bazai iya tuÆ™i ba shata ya É—auka har garin Tsaunin gawo bai zame ko inaba sai gdan Dagaci a Æ™ofar gida ya tarar dashi sunashan hantsi ya mike da sauri ya tareshi suka gaggaisa yace “Ina Beebah?” Sunkuyar dakai Dagaci yayi cikin kunya yace “Tana ciki wani abu ta faÉ—a maka?” Iska ya furzar yace “waye wanda suka bawa ita?” Gabansa ne ya faÉ—i yace “Mai Tukuba ne nasan kasanshi a zaman da kayi a garin nan don ko zaman yini É—aya kayi a garin nan indai ka shiga cikin mutanen garin nan zagaji sunan me tukuba É—aiÉ—ai yarinyar data zama bazawara a garin nan da bashine ya mayar da itaba a yanzu haka matansa na aure sha tara a gidansa Bibo itace ta Ashirin yau da yamma yace zai kawo komai na aure a É—aura zai É—auketa su tafi rani nayi iya yina na kasa yanada manya a karamar hukumar nan yanada bokaye sannan yanada kuÉ—i kaga dole na sakar masa iko….”

 

Numfasawa yayi ya dubi agogon hannunsa 12:12pm ya dago jajayen idanunsa yace “akwai masallaci a garin nan?” Girgiza kai Dagaci yayi yace “Saidai Hayin Fulani” ajiyar zuciya yayi yace muje ka rakani”
Babu musu suka nufi hanyar da zata kaisu Hayin Fulani suna zuwa suka tarar anyi shimfiÉ—u a É—an Æ™aramin masallacin juma’ar Liman É—in dakansa ya fito ya taresu yana kallon Habeeb da mamakin abinda ya kawo shi musamman da yaji ance shine baÆ™on.
Karkacewa yayi masa bayanin komai da uzurinsa liman ya kalli na’ibi suka jinjina sukace “kaiko É—annan miye naka da auren É—iyarga ta Jimo kaje ka nemi wata mana ko a rugar nan ne baka mukayi”
Girgiza kai yayi yace “ita nakeso liman taimakon ta zanyi bayan soyayya akwai tausayi kanaganin wanda sukeso subawa aurenta yarinya Æ™arama nawa Habeebah take wlh Kona aureta saina raineta kafin ta gama haÉ—a hankalinta sone yayi mana gaggawa, liman ka yankan sadaki na biya a É—aura bisa tsarin addinin musulunci”

 

ÆŠagowa Liman yayi yace “Duk da inajin tsoro bazanÆ™i É—aurawa ba amma hanzari kace ita yarinyar ba musulma bace kaga kenan akwai jumurÉ—a abinda zaifi indai ta amince zata aureka to ta yarda ta musulunta auren zaifi sauki…”
Gumi ya share yace “zata musulunta daga baya nidai a É—aura É—in shine me wuyar” baÆ™in nacinsa yasa dole Dagaci ya karbi waliccin Bibo na’ibi ya karÉ“i na Habeeb aka É—aura wannan rikitaccen aure akan sadaki saniya biyu kamar yanda al’adar Waliyyin angon take.
Wayyoh zo kuga murna gurin Habeeb har sujjada yayima ubangiji na cika masa burinsa da yayi, ya manta da duk wata kwantacciyar Æ™ura da É—aura wannan aure zai tayar ya manta da rantsuwar mahaifinsa ya manta da alwashin da yaci akansa muddin ya auri Habeeba, ya manta da Æ™udurin Mahaifanta da sukaci alwashin saisun kasheshi sun kashe Bibo muddin ya matsa akan aurenta……
Sai a lkcn abubuwa suke ta dawo masa yayi zugum zuciyarsa ta kasu biyu wani sashi farin ciki wani sashi É—inbin damuwa, Dagaci ne ya katse shirun da cewa “Mal Balaji tunda dai wannan aure ya É—auru Habeebah matar Habibu ce to zaifi ya É—auke matarsa subar garin nan don tabbas maganar zata fasu kuma indai har ta fasu batare da yabar Æ™auyen nan namu ba to kuwa ko zai fita zai fita cikin rashin hayyac….”
“Kwarai kuwa munafiki zai fita cikin rashin hayyaci domin kuwa bazamu bawa abar dogaro kunya ba kamar yanda muka alÆ™awarta zamu kasheshi mu kasheta sayi auren a lahira na rantse indai nine Buba Sarkin Noma to yau saina raba wannan yaron da rayuwarsa bai isa ya auri jikanya ta ba macuci masu shanye jinin bil’adama……”

 

Wani sara ya kaiwa Habeeb daidai lokacin da Habiba ta kwace daga riƙon da yayi mata ta hankaɗe Habeeb suka zube can baya tare sai gashi a ƙasa ita kuma tana kwance a samanshi.
Idanunta ta buÉ—e cikin idonsa ya sakar mata wani murmushi yasa hannunsa ya riÆ™e weast É—inta ta kwantar da kanta luf a Æ™irjinsa dagashi har ita wata nutsuwa ce take kwarara a Æ™asan zukatansu….
Babu wanda yasan meye yake faruwa saida sukaji Liman yana cewa “Buba Aure ne mun riga mun É—aurashi Habiba ta tabbata matarsa kada kuja da ikon Allah shine ya hukunta wannan aure kuma babu wanda yasan rabon dake tsakani wannan….
Dakata nace ka dakata Mal Liman kun hana mu taÉ“ashi amma fah ka sani idan har kukaga yabar Æ™auyen nan to warware auren nan kukayi….” Janyewa Habiba tayi a jikinsa zatayi magana Uda ya kai mata bugu Mal Liman ya janye ta ya turata gdansa ya dubi Habeeb yace shiga ciki akwai zauren baÆ™i ka jirani”

 

Zaku iya samun littafin nan ta website na arewabooks ku karanta cikin sauÆ™i ga waÉ—anda karatu keyi musu wuya a WhatsApp, ko kuma ku sauke app na arewabooks a wayoyin hannunku ga link É—in domin shiga ta website ku biya ku karanta cikin aminci

https://arewabooks.com

 

*Share please*
[4/13, 8:45 PM] AM OUM HAIRAN: *BAMAGUJIYA*
*(HOT LOVE AND DESTINY)*

NA

*FAUZIYYA TASIU UMAR*
*OUM HAIRAN*

https://youtube.com/channel/UCZ5Vt2–iGyJfTwItSzAnGg

*Paid book*
Kunata cewa promo ɗin dana baku yayi kaɗan to gashi nan na ƙara daganan zuwa jibi zaku sameshi a 200 PC 500
Ki biya ta waɗannan hanyoyin acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko ku turo katin waya MTN ta WhatsApp number na kamar haka 09013718241 ƴan Niger kuma zaku tuntuɓi wannan number don biyan kuɗinku +227 95 04 58 22.

 

No comments