Breaking News

Cuta ta Dau Cuta 9

*_Typing_*

 

 

 

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_


 

_ _

 

_Shafi na tara_

……Da ɗai-ɗai suka dinga isowa gidan. Hakan ya sake ɗaga hankalin mata dake cike da gidan ana jajantawa. Dan duk yanda akaso suyi bayani kasancewar an san sunje can gidan haka ya gagara. Baba ne kawai ke iya maimaita kalmar, “Akwai matsala. Gidan Jazool babu lafiya ƙwarai da gaske”.
Zugum-zugum akai kowa na sauraren baba cikin ƙara tsorata da jimantawa. Sai da suka samu nitsuwa kusan ta awa ɗaya sannan suka bada labarin abinda ya faru. Yanda Yaya Mujee ke siffanta sunga Alimah tamkar irin horror ɗin nan ya hargitsa zukatan mutane. Yanda wasu suka firgice ma sai ka ɗauka da su aka gano. Yaya Inusa da baice komai ba tun ɗazun cikin damuwa ya ce, “Baba dole ne fa a nema iyayen yarinyar nan akan lokaci. Dan abinda na fahimta gidan nan na Jazool akwai aljanu, kuma da alama sun shiga jikin matarsa”.
“Gaskiyarka Inusa dole aɗauki mataki da wuri kam, dan barin yarinyar can a wannan halin ita kaɗai akwai tashin hankali. Bari muga a lalubo mahaifin nata”.
Kowa dake wajen ya gamsu da zancen Baban. Yayinda tausayin Alimah da JJ ya sake mamaye zukatan kowa. Sam Baba ya kasa samun number ɗin mahaifin Alimah, dole ya yanke hukuncin idan sun idar da sallar la’asar zaije shi da Yaya Mujee gidan su Alimah ɗin.

Bayan idar da sallar la’asar suna shirin wucewa gidan su Alimah kira ya samesu daga asibiti cewar JJ fa ya farka a wani yanayi. Dan a yanzu haka ma rirriƙe ake da shi. Dole su Baba suka saki zancen zuwa gidan su Alimah suka tafi asibiti. A yanayin da suka sami JJ kam abun akwai tausayi, ga likitoci sun tabbatar da su basuga komai a tattare da shi ba. Brain ɗinsa lafiya lau take. Hakama fatarsa babu wata damuwa amma ga wasu irin ƙananun ƙuraje sun maidashi butsaaa babu ƙyawun gani tamkar jikin kada. Su baba da suka fahimci komai a yanzu roƙonsu sukai kan su masa allurar barci kawai zasu wuce da shi gida. Dan sun gano bakin zaren shafar aljanu ce. Wannan shine dalilin dawo da JJ gida aka nemo malamai suka rufu a kansa.
An masa addu’oi sosai duk da yana barci, sai aka kuma yanke shawarar bari har sai ya tashi. Har dare babu alamar JJ zai farka. Dan takai amma fara tsorata da barcin nashi. Ga su Baba ana idar da magrib suka fantsama gidan su Alimah, sai dai sun sami gida a garƙame da kwaɗo, da sukai tambaya kusan mutum uku suka sanar musu ai wannan gida ya kai shekara huɗu a rufe tun bayan rasuwar masu gidan, hasalima a yanzu ƙarƙashin kulawar ƴan sanda yake. Matuƙa kansu baba ya kulle, sai dai rashin lokaci ya sakasu yanke shawarar ajiye wannan batun har safiyar gobe suka nufi gidan JJ domin ceto Alimah tare da malam nan dan a barota da gidan. Dan malam ne suka bada shawarar a fara zuwa a ceto yarinyar da safe sai a nema iyayen nata saboda dare ya riga ya fara. Haka dole badan Yaya Mujee yaso ba suka nufi gidan JJ. Sun sami gate ɗin gidan yanzu a rufe. Iya ƙoƙarin suga sun buɗe hakan ya gagara. ALLAH ya taimaka akwai extre kay a hannun maƙwafcinsa, dan haka ya ɗakko. Da yawansu suka shiga gidan kasancewar mazan anguwa duk sun dawo, sai dai suna gama shiga ƙofar gate ta tafi da kanta ta datse ji kake gammm!!!. Gaba ɗayansu babu wanda gabansa bai mahaukacin faɗi ba. Dan duk a birkice suka juyo suna kallon ƙofar gate ɗin. Yayinda masu ƙarfin hali suka ɗauki addu’a a bakunansu.
Cikin ƙarfin hali maƙwafcin JJ ya ce, “Iska ce ta rufe ƙofan, dama tanayin hakan tun ana aikin gidan”. Wasu sun ɗan ji mutsuwa, yayinda wasu dai sun haƙurane kawai dan ganin sunada yawa. Akwai wuta a gidan tako ina dan anguwar suna samun wutar nepa sosai. Cikin gidan suka nufa kowa na addu’a. Baba da malaman ne a gaba, sai ƴan anguwa da masu son ganin ƙwaf da suka biyosu daga can gida. Basu sami Alimah a inda suka bartaba ɗazun, sai dai inda ta zauna duk jini ne, sai kuma sawun ƙafarta da tambarin jinin ya tafi har hanyar back door na kitchen. Hankalin kowa ya tashi da ganin jinin nan, amma cikin ƙarfin hali haka aka ɗuru cikin falon kowa na karanta addu’a.
Bbaaammmm!! Kake jin ƙofa ta datse kanta anan ma. A yanzu kam ai babu batun yarda da cewar iska ce ta rufe. Kusan gaba ɗayansu suka kalli ƙofar falon hankali a tashe. Bammm!! Ta Back door ɗin itama ta bada sautin rufewa harda ƙarar saka sakata. Yanzu kam rawar jiki ɗan gaske kowa ya fara, musamman ma ƴan son ganin ƙwaf ɗin nan da mazan anguwa. Malaman nan kam sun fara karatu cikin ƙarfin hali. Tsitttt babu wani abu da ya sake motsa kansa a gidan, zamaka iya ɗauka hatta iskar dake kaɗawa ta tsaya ne itama. Farrr-farrr wutar gidan ta fara rawa. Cikin sauri suka fara dunƙulewa waje guda, masu tsoron tsiya a cikinsu har fitsari ya cika musu mara, masu ƙarfin hali na taya malaman nan addu’oi. Ɗifff wutar ta ɗauke gaba ɗaya, duhu mai tsanani da ko tafin hannunka baka iya gani ya mamaye gidan duka. Sai ga mazajen fama na rungumar juna masu guntun fitsari na fara ɗiga…..

taɓ bara na fece alkur’an. Yo ƴan maza na cikin wanga yanayi mu ƴan mata sai muyi yaya, ai fecewar kawai ta ragemun tunda ni mai ɗaukar rohoto ina iya tashi sama kamar jirgi.

_________★★★★

*_Aslm hajiyata miye matsalar gashinki? Rashin tsawo ne ko cunkushewa gareshi ko kuma baqi kikeso yayi da santsi ne? Ga garin itatuwa na kawo maki mai fito da gashi har har gadon baya cikin sati biyu kacal._*

*_Sannan na kawo maki back to virgin wanda ko haihuwa nawa kikayi zaki matse cikin qanqanin lokaci ki koma kamar budurwa, har oga sai ya rasa gane shin wani aure yayine ko canza mashi mata akayi._*

*_Daɗin daɗawa kuma ga saiwar breast wanda zata gyara maki boost ɗinki cikin qanqanin lokaci ki koma kamar budurwa abinki…..hmmm hajiyata wani abun sai kin gwada zakiyi man godiya……ke dai tuntubarni ta wannan number ɗin domin qarin bayani 09032237835._*

___________★★

Sati biyu ta cika a tsakanin Dafeeq da Kainaat. Yayinda ɓangarorin biyu kowa ke nasa shirin. Sai dai duk yanda Dafeeq ya ɗauki al’amarin ƙarami game da tunkarar Khadijah da zancen zai ƙara aure hakan ya gagara. Duk da yanzu ta tattarashi ta ajiye bata masa magana akan komai da zai zo da shi gidan amma sai yaji ya kasa tunkararta da batun. Ya fara zuwa aiki, yayinda nauyin cefanen gidansa ya koma kan Kainaat a yanzu. Kullum cikin kawo musu kaji da kayan daɗi yake, ya baza ɗunkuna na alfarma tsakanin yadika da shaddoji. Ita kanta Khadijah ya mata kala goma masu tsada. Sabon gida ne dai basu kai ga komawa ba, amma mota tuni Kainaat ta koya masa da kanta a yanzu haka ma ita yake hawa.
Hankalin Khadijah a matuƙar tashe yake, kullum sai tayi kuka amma tsoro ya hanata sake tunkarar Dafeeq akan wannan sabon yanayin da suka tsinta kansu a ciki. Duk da yana fahimtar halin ƙuncin data saka kanta bai taɓa zaman lallashinta ba. Sai dai yana cin abincinta, yana kuma biyan buƙatarsa a jikinta duk da ita batajin wani shauƙin hakan a yanzu. Yakan fita gida da safe sosai, baya dawowa sai sha ɗaya, wataran ma sai sha biyu. Daya dawo yay wanka yaci abinci zaice ya gaji suje su kwanta. Dole take bin umarninsa, ya sameta ya mora ya hau barcinsa. Itako bata iya runtsawa, dan sosai take kewar Dafeeq ɗinta na da. Wanda baida lokacin kowa da komai sai nata, kullum suna manne da juna. Hatta da aiki yakan makarane a kullum kafin ya fita. Sannan idan ya dawo gida baya sake fita sai salla, da an idar yake dawowa gida su cigaba da sha’aninsu cike da farin ciki da farantama juna. Hatta aikin gida tare sukeyi, wankin kayansu da fita zuwa gidan baba hakimi. Wataran ma haka nan zai ɗauketa suje su zagaya gari suyi ƴar sayayyar kayan ƙwalam dinsu ko suci a can su dawo gida. Wanka idan har yana gida tare sukeyi. Amma yanzu duk babu waɗan nan tattalin da soyayyar. Iyakarsa cin abincinta da kuma sauke gajiyarsa. Dariyarsa ma ta gagareta gani, idan ta nuna damuwa ko’a fuska yace ita ta cika matsala. Tasan fa da da yanzu akwai banbanci, yanzu yana aiki uziri ya masa yawa kaza-kaza. Bata da bakin magana, dole take haɗiye komai sai ya fita taci kukanta. Ga kaɗaici na cimata zuciya, sam kayan alatun da yake faman zube musu a gidan baya wani birgeta, ita saima ta yini bataci abinci ba. Duk ta fige ta fita a hayyacinta. Shiko yana mulmula uwar ƙibarsa fatarsa na ƙara wani fresh.

Yau ya kasance laraba, saura kwanaki biyu a ɗaura auren Dafeeq da amarya Kainaat, dan haka ya yanke shawarar tunkarar Khadijah da batun nan dan baya so taji a waje. Tayi mamakin ganin ya dawo aiki da wuri. Dan ana idar da sallar la’asar ya shigo gidan. Wanka yayi yace ta kawo masa abinci. Bayan yaci ya ƙoshi yana mata ƙorafin ramar da tayi itako tana ɗan murmushin ƙarfin hali kawai batare da tace komai ba. Bai sake fita ba har akai kiran sallar magrib sannan, bayan yayi har isha’i ya dawo gidan da tsarabar kayan ƙwalama. Tsareta yay sukaci tare, ganin kamar ya fara dawo mata a Dafeeq ɗinta na baya taji ƴar nutsuwa harta saki jiki taci. Bayan sun gama wanka sukayi da brush, tayi mamakin jin yace da wuri zai kwanta, amma haka ta danne komai na wasi-wasi a ranta ta biye masa suka shige bedroom tun ƙarfe tara. Tana kwance a jikinsa shiru bayan ya gama biyan buƙatarsa taji ya sauke ajiyar zuciya. Kallonsa ta ɗan yi, kamar bazatace komai ba sai kuma ta nisa itama tare da sake shigewa jikinsa.
“Husby kanada damuwa ko?”.
Shiru kamar bazaice komai ba, bayan wasu sakanni ya sake sauke numfashi da fuskantar ta shima. A hankali ya ce, “Tabbas inada damuwa Khadijah, kuma a kanki ne.”
A zabure ta kallesa tana mai nuna kanta da waro idanunta. “Ni kuma dai? Dan ALLAH miyasa zaka shiga damuwa a kaina Dafeeq. Wlhy in dai abinda ya faru ne a kwanakin baya ni na ajiye komai, na kuma maka uziri, sannan ina farin cikin cigaban da ya samemu tunda nasan duk dan ka faranta minne. Fatana dai ALLAH ya cigaba da rufa maka asiri ta hanyar halak, dan bana fatan jikunanmu su zama a cikin jikunan da wutar jahannama zataci sakamakon ci daga haram. Bana zarginka bazan kuma taɓa zarginka ba in sha ALLAH”.
“Nagode da hakan. Sai dai ni ba’akansa nake damuwar ba. Dan nasan dai hakkin ciyar dake a kaina yake Khadijah. Sannan inada ƴancin neman arziƙina ko zuwa miki da sabon abu batare da shakkar karki tuhumeni ba. Abinda kawai na sani bazan taɓa aikata abinda nima zai wargazamin rayuwa ba akan neman abinda zan ciyar dake ko ƙyautata ratuwarki.”
Duk da maganganunsa sun mata wani iri haka ta danne harda sakin murmushin ƙarfin hali. Cikin son danne hawayen da suka cika mata ido ta ce, “Hakane”.
Tashi yay zaune fuskarsa babu alamar wasa, hakan yasa itama ta tashi zaunen da ƙyau. Sai da ya zuba mata idanu na wani lokaci tamkar mai nazartar ta kafin ya ce, “Khadijah!”.
“Na’am”.
Ta amsa masa cike da girmamawa.
“Mata nawa akace maza su aura a musulince?”.
Ƙirjinta yay wata irin muguwar bugawa har sai da ta ɗago a zabure ta kallesa. Ganin yanda ya tsareta da nashi idanun ta haɗiyi wani abu mai kauri a maƙoshinta tana maida idanunta ƙasa cikin rawar murya ta ce, “Huɗu”.
“Masha ALLAH” ya faɗa yana gyara zamansa. Batare da damuwa da yanayinta ba ya cigaba da faɗin, “To ALLAH ya karrama mijinki da zamowa cikin jerin maza da zasu ƙara aure, nima zan mallaki mace fiye da ɗaya kenan. Dan na samu wata baiwar ALLAH da muka dai-daita kammu har jibi juma’a ma za’a ɗaura auren in sha ALLAHU….”
Sosai jikin Khadijah ke rawa Kaff-kaff tamkar wadda aka kaɗama gangi, yayinda idanunta tuni hawaye ya ɓalle a cikinsu. “Aure kuma Dafeeq!”. Ta faɗa cikin suɓutar baki da rawar lips ga hawaye share-share. Fuska ya sake tsukewa tamau, cike da gadara ya ce, “Ban cika namiji bane?”.
Kanta ta girgiza masa da sauri. “A’a ba haka nake nufi ba. ALLAH ya sanya alkairi ya bada zaman lafiya”.
A gatsine ya ce, “Amin” tare da komawa ya kwanta ya juya mata baya. Hannu tasa ta toshe bakinta jin kuka na neman kufce mata. Sai dai duk da haka sai da sautinsa ya shiga cikin kunnen Dafeeq. Ƙaramin tsaki yaja batare da ya juyoba ya ce, “Malama bana son wata damuwa fa. Idan kin kwantar da hankalinki ma ita wadda zata shigo ɗin ba sa’ar yinki bace ba. Sannan bata da lokacin wani yin ƙishi-ƙishin banzan nan dan tanada aji ta kuma san abinda yake yi. Ya rage naki ki kwantar da hankalinki kici arziƙi kema cigabanki ne”. Daga haka ya juya yay kwanciyarsa.
Kasa daurewa Khadijah dake jin kanta na juya mata tayi, da sauri ta dira a gadon ta nufi falo……..✍️

_Humm Khadijah _

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*

No comments