Daurin Boye 46
46
Misalin sha daya na safe yana tsaye gaban dressing mirrow din dake dakin yana daura agogon hannunshi,yayin da taje zaune daga gefe tayi kyau cikin material doguwar riga da mayafinsa,yatsun hannunta take
murxawa,tayi nisa sosai cikin tunani,batasan da wacce fuska zata kalli khalipha ba saboda munana zatonta da tasoyi a gareshi,sai gashi rayuwarsu ita dashi din taso tayi kamanceceniya,anya kuwa zata samu wani kaman khalipha a rayuwarta?,anya kuwa ba dace bane wanzuwarsa cikin rayuwarta,ya fuskanci fiye da abinda takeso ya fuskanta,batajin akwai sauran abinda ya rage kuma,jarumi ne tun quruciya kawo girmansa,zaki ne da yake iya fuskantar duk wani qalubale dake gabanshi,mai qaqqarfar xuciya,kaifin hankali jumuri da juriya.
D’as d’as taji ya murza yatsunsa saitin fuskarta wanda hakan ya sanyata dagowa da hanzari hakan ya tabbatar masa lallai tayi nisa cikin duniyar tunani
“Madam tunanin me kike kuma haka?” Kai ta kada tana fidda qaramin murmushi daya fitar da dimple din fuskarta gami da dauke idanunta daga kanshi,saboda wani kyau da yayi cikin suit din daya tsuke a ciki
“So ya jikin naki?”
“Da sauqi” ta furta da muryar mai sanyi
“Ma sha Allah”
“Sauko muci abinci” sai tadan noqe kadan tana kallonshi,baibi ta kanta ba ya bude komai ya zauna dirshan a qasa yana lanqwashe qafafunsa,sai a sannan ya dubeta da lumsassun idanunsa wanda kullum suke cike da wani irin kwarjini,kasa musa masa tayi,sai ta janyo jiki ta sauko qasan itama tayi irin zaman da yayi,cup biyu ya hada tea ya zuba komai kuma cikin plate daya
“Bismillah” ya furta yana watsa mata kallonshi bayan ya saka chips a bakinsa yana taunawa a hankali,a sanyaye ta sanya hannu ta dauki ruwan tean din ta soma kurba a hankali,nashi cup din ya aje bayan ya zagaye hannayenshi a jikin cup din ya zuba mata idanunshi,yana son yasan dalili ko ya zaluqo abinda ya sanya kulli yaukin yake jin sabbin feelings game da ita,ya sani dai cewa da fari tausayinta ya soma ji,daga bisani sanyinta da yanayinta ya soma yi masa kama dana hajar,a yanzun kuma bazai iya tantance komai ba,baisan dalili ba baisan me yasa ba,bashi da amsar duka tambayoyin dayakewa kanshi.
“Zuwa yanzu ina fata kin gamsu da cewa ba yaudararki koda siffa biyu khalipha yazo miki ba,sannan kin fahimci khalipha shi dinma ba kowan kowa bane,irin rayuwar da kikayi shima ya dan dana ya kuma fuskanci makamanciyarta,ina fata na wanke dukan wani shakku da tarin tambayoyin da kike dashi a kanmu?” Ya qarashe maganar yana qoqarin kallon qwayar idanunta,dan qaramin murmushi mai gajeran zango tayi,saita kasa cewa komai taci gaba da kurbar shayinta
“Kinga na gaya miki gaskiya….koki tashi tsaye ki karbi mijinki ko su qwace miki shi” ya fada cikin idont care manner,ba don kuma hakan bane har zuciyarsa,saidai yayi hakanne saboda ya gwadata,hakanan ta samu faduwar gaba da kalamanshi,tana son ta kalleshi,tana son ta tambayeshi ya dauketa ne amatsayin mata,tana son jin ya canza mata matsayine daga wanka ya bata a baya amma ba zata iya tambayar tashi ba kada ya zaci wani abu.
Cokalin hannunshi ya karkada cikin cup din tangaran din dake hannunshi,wanda shi ya bada sautin daya dawo da hankalinta kanshi
“Daga yau ina buqatar amsar duk wata tambaya ko magana dana miki,shurun kin nan bana buqatarsa alright?”
“Toh” ta furta,sai yaci gaba da kallonta,tayi laushi sosai akan sanda suka taho daga gida da kuzarinta harda tsokanar fada wa rahama,yana ganin tana da buqatar shan iska,saboda haka a take cikin ranshi ya soke tafiyarsu anjima da yayi niyya,saiya buda wayarshi ya tura saqonni sannan.ya rufe ya miqe tsaye yana duba agogon hannunshi.
“Hudu dai dai ki shirya zanzo ki rakani waje waje” tana daga zaune ta daga idanunta har ta kalleshi tana jin faduwar gaban kada dai yace gidan ummi zasu koma,yanayin yadda ta kalleshin sai daya dan sanya bugun zuciyarshi qaruwa,saboda yadda idanun nata suka sake haske da girma
“A dawo lafiya” tace dashi sanda yake fita,ya amsa mata cikin kulawa sannan yaci gaba da takawa har ya fice
Tana kammala sallar la’sar ta isa gaban mudibi ta tsara kwalliya mai kyau da burgewa,tayi kyau cikin atamfa riga da skert wanda kalarta take mai duhu,dalili kenan daya sanya ta sake mata kyau ta haska fatarta mai haske da qyalli,tsaiwa tayi gaban mudubin tana kallon kanta,duk da cewa ranta akwai damuwa amma bai hana kwalliyarta yin kyau da tasiri ba,ita kanta tasan zuwa yanzu ado da kwalliya yabi jikinta,ya zame mata jiki,koda inda zata ko babu ba zaka rasata cikin kwalliya ba.
Tunda ya shigo yake kallonta,komai nata yayi masa kamar tasan ra’ayinsa da tsarinsa game da kwalliya,har ya kammala shiryawa ta tsone masa ido,wannan karon shima cikin shadda ya shirya,cikakkiyar shigar kanawa zam,badai iya sanya sutura ba dama,yana gaba tana binshi a baya zasu fice daga dakin ya juyo cikin wani irin zafin nama,hannunta ya cafka yadan rage tazarar dake tsakaninsu har tana jin saukar numfashinsa,kamar mai rada yace
“Bazan iya daurewa ba,kinyi kyau humairaaah” ya fada saitin kunnenta wanda hakan ya sanya tsigar jikinta tashi,kunya taji ta kamata bugun xuciyarta na daduww,saitayi hanzarin sake ja baya gami da zare hannunta daga nashi,kai ya girgiza mata ya nufarta kamar kuma wanda aka umarta saiya tsaya cak sakamakon tuna wani abu da yayi ya juya ya fice,sai dataga fitarsa sannan ta bishi a baya.
Wata tafiya ce ta alfarma cikin rakiyar motocinsa wanda bata sani ba biyoshi sukayi daga kano ko dama yana da wasu a nan lagos,tafiya suka yi mai dan dama kafin su iso bakin wani beach,wajene mai kyau da tsari,tun daga saukarsu ya burgeta,tana zaune a mota sai da yayi mata magana sannan ta fito,su biyu suka dinga takawa suna zagayawa bakin wajen,wanda daga qarshe suka qare a boat,su biyu ya biyawa saboda haka iyasu ya dauka,ya biya dukka awannin da zasu kashe cikin ruwan.
Iskar dake tasowa daga cikin ruwan mai dadi ce da kuma wani irin sanyi mai armashi,idanunta ta lumshe tana sheqar iskar har cikin zuciyarta take sauka da sanyinta tana wanke duk wata damuwa da qunci da yayi saura a ciki,wani lokaci idan wani jirgin yazo giftasu fallatsin ruwan kan tashi har kan fuskarta saboda tana daga gaba gaba,har lokacin idanunta na lumshe sanyin ruwa yayi mata yadda takeso,murmushi ta saki sanda ta tuno wani scene data gani cikin film din da khalipha ya dage sai ya tayata gani,yadda masoyan ciki suka gabatar da wata zazzafar soyayya cikin jirgin ruwa,saita fara imagination wanda ya sanya murmushinta fadada.
Jin kaman ana shirin rungumota ta baya ya sanyata saurin waiwayawa,khalipha ne tsaye hannayensa goye a bayansa yana kallonta,ya bude baki zaiyi magana wayarta ta dauki tsuwwa,saita juya tana dubawa,aliyace ke kira,latsawa tayi ta kara a kunnenta,dai dai sanda a sake jin ya matso gab da ita fiye da da,don a yanzun ko qwaqwqwaran motsi tayi zata iya fadawa jikinsa,hakan yasa ta hadu tsam ta hada hankalinta waje guda,saidai hakan bata samu ba,don duk yayin da ruwan yayi wasa da jirgin saita gogi jikinsa,hakanne ya sanya ta danna handsfree ba tare data sani ba
“Bakya jina?” Tajiyo muryar nan ta aliya
“Ina jinki sashen,ya gida yasu mama”
“Lafiya lau sashen,na shiga ta wajenku na tadda baku nan,tace min kunyi lagos?,hala amarci aka tafi shahh hh….” Ta qarashe maganar da sigar zolaya tana bayyananniyar dariya,kunya ce ta kama aysha,saurin katse aliyan tayi,duk da tasan idan aliya ce tayi ta banza saita gama amayar da abinda ke cikinta
“Banason iskanci aliya meye haka ne?” Dariya ta sake yi
“Au na manta fa yayanki ne ko?,to ai ba laifi yayanma ai girma ne,amma dai abi a hankali kada komawa wudil ya gagara”
“Dama abinda kika kirani ki gayan kenan aliya koko me?” Ta fada tana dan hade rai kaman tana gabanta,don ji take kamar ya jefa wayar cikin ruwan dake gabanta tsabar kunyar da aliya ke bata,gashi tana iya jiyo yadda khaliphan ke turo kai da alama kunnensa yakeso yaji abinda aliyan ke fada sosai,dariya ke taso masa yana danneta ganin yadda mode din ayshan ya sauya,bai manta abinda mahmoud ya gaya masa ba kusan hakan yace mishi ana ya gobe zasu tafi,da alama bakinsu daya
“To aini kaman qarar ruwa nakeji,ciki kuka kwana ne?”
“Sai anjima,ki gaida mama da kyau” aysha ta fada tana shiriin katse kiran
“Ayyah sashen kiyi haquri,nikam kira nayi na baki saqo wajen boss….abokinshin nan wallahi ya fiya matsa lamba da yawa”
“Zan gaya masa,ki gaida mama bana ji sosai” ta fada tana katsewa saboda kada aliyan ta baarota,don tasan kadan daga aikinta ta fadi maganarta,kuma ita babu ruwanta ita zata bari da jin kunya.
“Mu haka muke,bama kama abu da wasa,idan muka soma sai mun cimma gaci,jarumtarmu a nan take” ya fada yana nuna saitin zuciyarshi da yatsa,saita zame jikinta dake tsakanin qarfen jirgin da khalipha daya katangeta ta baya,kamar hadin bakintana tsaka da takwa don barin wajen kiran hanan ya shigo,shima tana zaune kan wani dan tebur da aka ajiye musu coffe da kayan motsa baki zata soma amsawa taji an zare wayar daga hannunta,handsfree ya maidata sannan ya aje saman teburin ya zagaya kujerar dake fuskantarta ya zauna bayan ya harde hannu ya zuba mata idanunshi,hakanan ta dake ta soma amsawa
“Anya lafiya ko ayshat,kodai wani ya riqe mana ke ne?” Idanunta dan fiddo
“Haba mana hanan,kada muyi haka dake mana ya zaki fadi haka” dariya ta sanya cikin nishadi
“Ah to ni na sani,kinsan soyayya ba abinda bata haifarwa,sauyawar hali da tsarin rayuwa na lokaci guda….wai da hakan zata faru kuwa da nafi kowa murna”
“Me yake faruwa a makaranta?”
“Labiba ta shigo dazu nemanki,tace jibi kuna da C.A” idanu ta zaro don shaf ta mance labiban ta gaya mata dr mahadi ya fadi cewa zaiyi CA din cikin sati duk da bai tsaida rana ba
“Ya salam,ina hanya in sha Allahu”
“To Allah ya kawoki lafiya,kinga matar nan ma tabi mijinta taje tayi bulunbuqui da ita” tasan sarai da maman hunaifa take
“Ba ruwana,maman hunaifa ta waje na ce”
“Hademin kai zakuyi kenan?,zaki dawo ki sameni” ta fada tana dariya dariya da haka sukai sallama.
Cikin narkewar da batasan tayi ba ta langwabar da kai tana duban khalipha,kallon data masa sai ya zama kamar da manufa tayi,gaba daya ya kashewa khalipha jiki,yasan me takeson cewa makarantarta,da qyar ya bude bakinsa yace
“Baki da damuwa”.
Sun jima kafin subar nan,daga nan dinma wani wajen suka qara nufa,sai da sukaje waje uku kafin su koma hotel.
Washegari da daddare ma ya sake daukarta suka fita,wani katafaren shago dake saida tufafi irin na igbo da yoruba ta rakashi,sai ya nade hannu yace ta zabi duk abinda taga ya dace,ga zatonta yana nufin shi zata zabarwa,haka tayi ta maza ta zaba mishi kaya masu kyau da quality,harshi kansa mai shagon ma mamakin tasan kan kayanne?,murmushi kawai tayi,inda daga qarshe ta daukawa anni wasu kaya da suka burgeta sosai,dubanta kawai yayi baiga abinda ta dauka ba,saiya karbi accnt num din wajen ya musu transfer fiye da kudin siyayyarsu,tana gaba yana biye da ita a baya,ya bude mata murfinm motar cikin jin nauyin yadda yake matan ta shiga ta zauna,don ko yaranshi bai bari su bude matan shi da kanshi yake hakan,sai daya rufe murfin motar sannan ya koma cikin shagon.
Tsahon mintina goma cikakku aka sake kawo wata ledar sannan ya shiga aka tada motar suka bar wajen.
Nesa dashi kadan ta kwanta,saboda tana tuna yadda suka kwana jiya,batasan yadda akayi ta kwana a jikinsa ba,saida suka tashi sallar asuba sannan ta ganta cikin jikinsa kanta kwance saman qirjinsa,hakanan shima ya shirya yana dan dubanta,gefe daya shima ya kwanta idanunsa lumshe,yana tuna baccin da sukayi mai nauyi jiya wanda ya jima rabonshi da bacci mai nauyi irinsa,da haka bacci ya kwashesu.
Qarfe sha daya na safe suna tsaye cikin airphort,aysha na gefan khalipha,tayi kyau cikin baqar abaya,kusan shigar baqi tayi komai nata har gilashin fuskarta,wanda hakan ya sake bayyana kyau da hasken fatarta,kota ina khalipha gani yake kamar kowa ma kallonta yake saboda kyan data yi masa,dalili kenan daya sanya yaranshi suka karesu a dabarance ta yadda ayshan ba zata fuskanci me yake nufi ba,daidai lokacin da asma’u itama ke tsaye cikin tashin hankali suna sa’insa da daya daga cikin ma’aikatan wajen,kano takeson komawa a yau amma ana gaya mata cewa ticket ya qare,tana jin kuma ya zama dole ta koma a yau din,sakamakon kayanta da abba ya auno mata daga china donta fara business da suka zo,tazo clearance amma tag number dinta ya fadi,kuma ta tabbatar koda kayanta zasu fitan sai taci wuya,shi yasa take gaggawar komawa ta sanar da abba,don ta saka rai da kayan,hakanan ta gama bazawa qawaye da sauran jama’a,kada mu su rainata su dauka qarya take.
Ganin da gaske suke saidai ta bi jirgin gobe ya sanyata cikin bacin rai da qunaquni ta soma takawa zata bar wajen,duk abinda ke faruwa khalipha na ankare,gab da zata gotasu ya dan taka kadan ya matsa inda zata iya ganinshi
“Mrs dan gote” ya fadi hannayensa harde a qirjinsa kamar yadda yake al’adarsa ce,waiwayowa tayi taga wace matar dan goten,sai suka hada ido da khalipha,ta fuskanci da ita yake don ita yake kallo yana murmushi,gabanta ya fadi,kwarjininsa suka cikata,wani kyau taga ya qara mata fiye da yadda ta sanshi a baya
“Ki nemi taimako wajen madam,kamar akwai kujera daya data rage sai tasa a baki kawai” ya fada cikin idont care tune,hararashi taso yi saboda wani takaici daya taso mata,kamar ita zata nemi taimako wajen aysha Allah ya sawwaqe,aisai ta rainata ma,har abada bata jin zata iya yin hakan,sai kawai ta soma takawa zata bar wajen,dai dai sanda idanunta ya hango mata aysha dake zaune idanunta kan wayarta,gabanta ne ya fadi ta tsura mata ido tana kallonta kafin daga bisani ta dauke kai ta wuce,tana fita ta kira abba,saidai ya gaya mata zaiyi iyakar iyawarsa,baida mutane a wajen amma zai gwada,kashe wayar kawai tayi cikin bacin rai,asara ce tasan zasu tafka ta koda kayan sun fito,bata da wani babba data sani da zai shige mata gaba saidai abban,kuma shima yadda yake mata bayani kamar abun zaija lokaci.
Zuciyarta ta bata shawarar ta koma wajen khalipha,to amma itakam gaskiya bata son tayi abinda mutuncinta zai zube,don haka sai ta koma can wani waje da zata iya hangosu,idanunta na gano mata aysha,ta dubi securityn dake tare dasu,haushi da baqinciki gami da takaici ya dinga sakko mata,ba shakka aysha ba itace ta cancanci wannan matsayin ba,ita asma’u ita ta dace dashi,ayshan da batasan dadin komai ba,batasan wani gata ba,bata san so ko qiyayya ba,bata damu da komai ita ta samu wannan bigiren daya kamata ace ita ke ciki?,aysha da masu irin hamid suka dace,ya akayi ma wai ta hadasu ne da khalipha?,ya akayi bata qyaleta ta zabi wani daban da kanta ba,anya ma ba ta san cewa waye ainihin khalipha ba?,anya ba bincike tayi a kansa ba shi yasa tayi laqwas ta qyale har akayi auren?.
Tana zaune tana karanta wannan wasiqar jakin har lokaci ya fara nisa,ta duba agogon wayarta,ba shakka.nan da wasu mintuna jirgin da zai nufi kano zai tashi
“Kije kawai asma’u,ai itama tasan kinfi qarfin roqar duk wani abu daga gareta,koda kin roqa dinma aiku kuka fara mata alfarma kafin tayi muku,banda ku da tunu yanzu qila tana can cikin wani mawuyacin halin da ba’asan ma wanne iri bane,kai gaba daya ma auren nata ai kece silarshi,da wannan shawarar da zuciyarta ta bata ta miqe ta doshi inda aysha ke zaune khalipha na dan tsaye daga bayanta yana amsa waya,bayan ya gama ya tsaya siyen ticket qwaya daya daya rage ta internet.
Tana gab da isowa wajen aysha ta daga kanta saboda gajiya da tayi da danna wayar,tayi haka ne saboda nauyin kallon da khalipha ke binta dashi,sam baya jin kunyar ma yaranshi dake tsaye a wajen,murmushi ta jefi asma’un dashi cikin fara’a tace
“Ah,anty asma’u?,kema kin shigo legos kenan?,hala keda ya hamid ne?ku bata wuri sisterna ce” tayi magana dasu wanda ada basu da niyyar matsawa,fuska a dinke ta qaraso wajen,sai taji kaman ayshan tana sane da tace tare da hamid suke magana ta gaya mata a fakaice
“Zuwa nayi na tafi da kayana da nayi order daga china,so an samu dan minor problem kuma hamid bai qasar bare yayi magana a sakar min,so ban sani ba ko mijinki nada wanda zaima magana akan hakan saboda yau nakeson komawa gida”murmushi ta saki ganin yadda take magana kai tsaye cikin isa isa,amma kona komai tasan ta isa dinne shi yasa harta tako ta nemi alfarma a wajenta,tasan halin asma’un tsaf ciki da bai,ba kowane zata nemi alfarma a wajensa ba saboda tsabar jin kanta da takeyi
“shikenan minti daya” ta fada tana miqewa,a hankali take takawa inda khaliphan ke tsaye yana danne danne da waya ahannunsa,yayin da asma’un ta bita da kallo tana qarewa shigarta kallo,ko hasidin iza hasada yaga aysha yasan ta canza,yanzu classic aysha ce,ba irin ayshan daka sani a baya ba,gefanshi ta qaraso wanda kaman yana ankare dama da tahowarta din yana jin tsaiwarta ya waiwayo yana dubanta bayan ya zuba mata dukkan idanunshi da sukayi mata nauyi,batasan me yasa yake tasiri haka a kanta ba,saita dan sadda kai
“Asma’un kika zo nemawa alfarma?” Ya tambayeta ta wata irin siga da bata gane meye cikin ranshi ba,bata ankara ba taji ya saqalo hannunta cikin nashi cikin wani salo ya soma takawa tilas tabishi.
Gaban asma’un suka tsaya sannan ya soma magana cikin muryarshi mai cike da izza da kwarjini
“Kin nemi alfarma but bata hanyar data kamata ba,yanayin yadda kika yi mata magana baiyimin ba,baya ga haka ma banajin yaron oga zai iya komai akan hakan,dadai ogan nashi yana nan wataqila saiya roqa miki shi,ko kawai ta jirayi dawowar mai gidan nata,may be ma he can do morethan i can” daga kai aysha tayi da sauri tana kwabe fuska tana dubanshi tana girgiza kai,sai yaga tayi mishi kyau sosai,girarshi ya dage mata alamin baiga wani kuskure da yayi ba,yatsansa ya saka yadan taba girarta data tattareta waje daya can qasa yace
“You r beautiful” sai ta saki fuskar tata daga tattaretan da tayi ta koma yi masa kallon mamaki,tuni asma’u dake zaune wani abu ya yunquro mata,sun wani tsaya gabanta suna mata soyayya sai kace kansu aka saukar da wahayinta,dadin abun tun kafin ayi d’aran akai kwand’i,yaushe ma suka fara son junansun,taso ta miqe tabar wajen bayan ta gaggaya musu magana saidai kuma ta tabbatar idan tayi hakan ta barar da damarta,tasan da biyu khalipha ke gaya mata magana saboda babu kalar wulaqancin da itama bata yi masa ba.
Murya can qasa kamar mai rada aysha tayi masa magana don batason asma’u taji
“Kayi mata wannan alfarmar domin girman Allah” wata kasala sosai sautin furucinta ya haifar masa dashi,wanda hakan ya sanyashi lumshe idanunsa ya bude duka lokaci guda
“Taci darajar aisha” kunya taji tadan kamata saita basar,wayarshi ya ciro
“Morning boss” daga daya bangaren kakkaurar muryar ta cika wayar khaliphan
“Morning ahmad mun tashi lpy”
“Lpy lau boss….boss kayi wuyar gani,koda yake manya dama haka kuke irinmu saida haquri kafin mu samu ganinku” murmushi khaliphan ya dan fidda mai sauti
“Kullum qorafinka kenan,bayan daka tashi nemana kasan yadda za’ayi ka hadu dani ai…..ba wannan ba,akwai wata yarinya…..ya sunanta ma yake?” Ya qarashe da low tune yana duban aysha da alama tambayarta yake ta gaya mishi,kunya ta sauko ta rufe ayshan,yana nufin yace ya manata sunan asma’un?,saita gaya masa kawai tana dakewa,bata yarda ta dubi asma’un ba ta share kawai,bayani ya masa bai qarasa bama ahmad din ya tsaidashi kan cewa ba matsala,yanzu za’a duba kayan nata ai tafi qarfin komai,dai dai sanda ya qare wayar lokacin tashinsu yaui,saboda haka ya maida wayar aljihunsa yana cewa
“Saiki gaya mata ta wuce ta tafi gida….mtsweeww,kome mijinta keyi oho” taji duk abinda ya fada,duk yadda ranta yakai ga baci haka ta hadiye,don a yadda ta karanci khaliphan tsaf zai fasa abinda yayi niyya,wanda hakan yana dai dai da tayi asara ne kota jira har daddy yayi mata cuku cuku,hakanan ta miqe tabi bayansu
[3/8, 9:04 AM] Binta Mustapha:
Post a Comment for "Daurin Boye 46"