Breaking News

Duk Karfin Izzata Book 2 Page 13

Book 2

*Episode 13*

…….sai 6pm Hiyana ta lallaÉ“a ta zagayo ta koma chikin gida a babban palon kasa tachi karo da yaya khalid, zai koma part nasu, sugunnawa tayi har kasa “yaya khalid ina


wuni” “me ya fitar dake waje sister? Shiru ta É—anyi tana tubanin abun da ya dace ta faÉ—a masa “Bgs ne ya miki wani abun ko? Dan naga hawaye a face naki” Chikin sauri ta girgiza kai tana faÉ—in “aa yaya Khalid ba shi bane” kallon ta khalid yay fara yi from head to toe, kawar da kai gefe yayi chike da bakin chiki yace “ok jeki yi wanka ki chanza kaya kizo part nawa ki sameni kuma kizomin da wayar ki” sai lokachin ta tuna ashe tana da waya, jiki ba kwari ta mike ta haye sama, tana tafiya tana tunani, wai shi yaya prince ai na ya keson na sa rai nane ya kashe ni ma ya huta kawai na gaji nagaji sa irin azabtar dani da yake wayyo Allah dan isar ka ya Allah ka kawomin É—auki, da wannan tunanin ta shiga palon su, zaune saman sofa mai zaman mutun 3 ta samu Fahad yana sanye da jallabiya fara yana latse latse a waya, tsugunnawa tayi har kasa “yaya Fahad ina wuni” sai lokachin ya É—ago ido kallo É—aya ya mata ya kauda kan shi gefe chike da bachin rai ya mike har wani huchi yake kamar wani zaki ya nufi betroom na Bgs batare da yache da ita komai ba.

kwanche saman gadon ya same’sa idon sa a lumshe, kallo É—aya Fahad ya masa ya gane bai yi barchin ba, chike da fushi ya fara magana “yaya prince ka dubi girman Allah ka tausayawa sister wai dan Allah me ta maka ne da har ka tsaneta haka pls ko dan farincikin Ammi da Abba ka rinÆ™a tausayin sister, ina kakeson yarinyar nan ta sa ranta dan Allah dai, ko so kake watarana zuchiyar ta ta buga ne? ba ni kakewa ba amma duk sanda kayi mata wani abun jinake zuchiyara kamar zafa fashe, ji nake kamar zan mutu, nasan kana son mu baka son É“achin ran mu kana kauchewa duk abun da zai samu bachin rai, to kasani fa wlh idan kayiwa sister wani abun gaba É—ayan mu ji muke kamar zamu mutu dan É“achin rai, mu muna sonta muna kaunar ta, munason farinchikin ta kamar yadda mukeson na Auta, karka manta fa wlh ina da tabbacin Ammi tafi son Hiyana sama da yadda take son Auta, wlh ko dan Ammi dole naso yan uwana, lokachin da aka aura min Amrat ban son ta amma dana fahimchi yaran nan sune farincikin Ammi, sai na hakura na rungumi matata Allah da ikon sa kuma chikin Æ™anÆ™anin lokachi ya dasamin son ta a rai na, dan Allah yaya prince ka bawa sister kulawa ko dan Ammi, da Abba ina da tabbacin hakanne kawai burin da ya rage musu a rayuwa pls yaya prince ba dan kowa ba dan Allah.

Ba tare da ya bude ido ba yawa Fahad alama da hannu akan yazo, ba musu yaje ya zauna a gefen sa
Wani wawan mari ya sakar wa Fahad É—in a kumatu tare da mikewa zaune ya wato idon sa waje, chike da É“achin rai ya fara magana “kayi girman da zakazo ka tsaya a kai na kanamin magana haka ko? Chikin sanyin murya da danasanin Fahad yace “kayi hakuri yaya prince bachin rai ne yasa hakan amma am so so sorry ba zan sake ba” shiru Bgs yayi bai sake magana ba “yaya prince dan Allah ina neman wata alfarma” zuba masa ido kawai Bgs yayi batare da yayi Magana ba, “dan Allah yaya prince kabar sister ta dawo É—akin ka wlh ban son ganin ta a palon nan kuma kaga tana da tsoro sosai” shiru yayi na tsawon 2mins kafin yace “me ya samu É—akin na ta? Da sauri Fahad ya kara juyowa da kyau yana fuskantar shi dan jin yadda Bgs É—in yayi magana chikin sanyi murya da alama zasuyi nasara “yaya prince ai ton lokachin da ta kalli snake a É—akin take tsoron shiga” zuro dogayen kafofin sa kasan fadon yayi ya miÆ™e batare da yace da Fahad komai ba ya nufi wajen hutawan sa dake chikin É—akin, shiru Fahad yayi yana addu’a a chikin zuchiyar sa Allah ya É—ora su a kan Bgs Allah ya sa ya yarda hiyana ta dawo É—akin sa, Almost 30mins yana zaune daga Æ™arshe dai ya mike ya fice daga É—akin chike da sa ran zasu iya yin nasara awan nan karon dan, yadda yaji yaya prince yayi magana a hankali.

Zaune saman sofa a palo ya samu hiyana ta takure waje guda da alama sanyi takeji, “sister tashi kije É—akin ki ki chanza kaya” chikin rawar murya tace “yaya Fahad wlh tsoron É—akin nake ji bazan iya shiga ba” shiru yaÉ—an yi kafin yace “ok É—auki kayan naki muje na rakaki part É—in yaya Aiman sai kiyi wanka a chan ki chanza kaya” ba musu ta mike ta É—auko wasu riga da sket masu shegen kyau black colour, ta nufoshi gaba yayi ta bishi a baya, har part na Aiman.

Zama Fahad yayi saman sofa a palo san nan yayiwa Hiyana nuni da betroom din yace taje tayi wanka yana jiranta a nan, dan ya lura tsoron part É—in take.

Jikinta sai kerma yake ta shiga betroom É—in Aiman wani makeken hoton’sa ta fara chin karo da shi a gefen gado yana sanye da jeans da t-shirt ya É—aura rigan aikin sa a sama kayan yana É—an murmushi, ganin hoton Aiman ba karamin tayarwa Hiyana hankali yayi ba, nan take hawaye suka fara zarya akan fuskanta, tana kuka tana bin É—akin da kallo karaf idon ta ya sauka kan wani makeken Frame mai kyau gaske wadda ke É—auke da hoton Bgs yana tsaye da kakin sojoji ya rike Ak47 a hannun sa, ba karamin kyau yayi ba fiskar nan tashi kamar kullun babu alamar annuri ko kaÉ—an,kurawa hoton ido tayi tana ta kallon sa tana goge hawaye ta, 15mins ta É—auka tana kallon hoton kafin ta wuche ta nufi toilet a gurguje tayi wanka ta fito, shiryawa tayi chikin riga da sket din ta nufi gaban mirrow ta tsaya tana kallon kanta

Ba karamin kyau kayan suka mataba sun fito mata da ainihin suran jikin ta,

kai kallon ta tayi kan kirjin ta gaba ɗaya rabin boobs nata awaje kasan chewar wuyar rigan babban ne sosai gashi kayan sun manne da jikin ta sun matse ta sosai, tsaki ta ja ta sanya hannu ta tara kyakkyawar lallausan bakin gashin kan ta a tsakiya ta daure ta kitse bindin gashin ta watsa shi baya wadda ya kai har karshen bayan ta, kunyan fita hakan take ji gashi hijabin Amrat ya jike kuma yayi datti sosai, shiru ta tsaya a ɗakin almost 10 mins tana tunanin yadda zata fita da kayan nan a hakan ma wai ta zaɓo kayan masu ɗan fasali kenan, data ga dai tsayuwa ba zai tsinana mata komai ba sai ta, dauki kayan ta da ta chire ta kare kirjin ta dasu ta kama hanyan fita tana tafiya gaba ɗaya a takure take har ta fito palon

Yadda ta bar Fahad haka ta fito ta same’sa yana zaune yana latsa waya, jin Sallamar tane yasa ya É—ago kai kallo É—aya ya mata ya kau da kai tare da mikewa yayi gaba yana faÉ—in “to muje” bayan sa tabi hannun ta rike da kayan da ta chire ta kare kirjin ta dasu, part nasu suka koma.

Yana shiga palo ya wuche betroom na su ita kuma hiyana ta zauna saman sofa, ta kame jikin ta waje guda, dan ji take kamar babu kaya ajikin ta a haka har barchi ya fara É—aukan ta gyarawa tayi ta kwanta ba jimawa barchi yayi awan gaba da ita

KHALID

wunin yau gaba ɗaya Zahra ta wuni ne tana kuka khalid yayi rarrashi har ya gaji taki yin shiru taki chin komai tun safe ga zazzaɓi da ya rufe ta, Sosai Khalid ya shiga damuwa, ya rasa meke masa daɗi
……..zaune yake gefen gado yayi tagumi ya rasa meke masa daÉ—i, Zahra na kwanche saman gadon tana kuka kasa kasa, chikin shesshekar kuka tace “yaya Khalid” chikin sauri ya juyo tare da haurawa saman gadon ya karisa in da take, hannun ta ya kama chikin nashi murya kasa kasa Kamar mai raÉ—a yace “am sorry my wife kiyi hakuri kinji? Chikin dashewar murya tace “yaya Khalid ka dai na damuwa kaji bana son ganin ka kayi shiru kana tunanin nan” “my wife in dai baki dai na kukan nan ba baki chi abinchi ba, ba zan dai na damuwa ba” “to yaya khalid kamin tausa dan ko ina chiwo yake min idan na samu sauki zan chi abinchin kaji? Chikin sauri ya fara yimata tausa yana faÉ—in “yanzu nan ma ina gama yimiki tausan nan zaki samu sauki sai na baki abinchi da kai na ko? Kakalo murmushi dole Zahra tayi ga hawaye na bin gefe da gefen fuskar ta tace “to amma iya tea kawai zan sha” “ok to ko tea din ma yayi bari na kawo miki” batare da ya jira amsar taba ya sauko daga gadon ya nufi, waje.

Jim kaÉ—an ya shigo hannun sa É—auke da kyakkyawar cup, mai É—auke da tea mai zafi gefen gadon ya zauna tare da ajiye cup É—in a saman drawer gefen gadon, hannu yasa ya É—ago ta ya É—aurata kan chin yar sa, ya É—auki tea É—in ya fara bata a baki, a hankali hankali take dan sha har ta shanye “in karo miki wani ne? “Aa yaya Khalid ya isa haka wannan ma da kyar fa na shanye” batare da ya sake magana ba ya ajiye cup É—in a saman drawer, san nan ya miÆ™e tare da ita a jikin sa suka haura saman gadon.

Kwanchiya yayi, tana manne a kirjin’sa, a hankali yake shafa bayan ta yana mata raÉ—a a kunne tun Zahra na share sa har ta fara biye masa suka chigaba da zubawa juna kalaman love.

Maiduguri Nigeria

Ahzan ne zaune saman karfet a betroom din mum É—in sa yayin da mum ke saman gado suna hira
“Ahzan kana ganin hakan shine dai dai? “Eh mum ya kamata mu taimaka mata” “amma Ahzan abun ne da ban mamaki anya Dr walid bai yi kuskure ya baka result na wata ba, a mai makon na Ummi dan ni dai ban ga alamar Ummi na bukatar aure ba” “mum baki ji Dr yace yanzu ne abun ya fara kamata ba idan ta kara 1 week ba tare da an mata aure ba, shine abun zai bayyana karara kuma kinga idan hakan ta faru ba zanji daÉ—i ba” “Ahzan Hanan fa zata girmi Ummi sosai dan yadda nake ganin Ummi ba zata wuchi 16 years ba kawai tana da wadatatchen halittace, ni anawa ganin idan ma hakane to chiwon hanan ya kamata ya fara kamawa ba Ummi ba” “mum kowa da kike gani a duniyar nan da irin tasa kaddarar, ai wanna chiwon bai bi ta shekaru ba” “hakanne Ahzan kana da gaskiya to shikenan zanyiwa dadyn ka salim magana” “to mum amma fa karki sanar da kowa batun chiwon nata dan kar su fara magana akai” “ai wannan abun kunya ne baki ba zai iya faÉ—i ba” “yauwa my mum san nan kinji Dr yace kar a wuche 1 week baa mata Aure ba idan aka wuche za’a samu matsala, ba Æ™aramin tausayi yarinyar ta bani ba shi yasa ma na yanke shawarar Auren ta kawai, dan in shere mata hawayen rashin iyaye” “In Sha Allah zaka samu ladan hakan” “Allah yasa my mum, amma mum yana ga baki shirya zuwa wajen aiki ba jiyama fa baki jeba lfy” “wlh Ahzan gaba É—aya jikina a mache ne bana iya komai sai kwanchiya kawai” shiru Ahzan yayi yana tunani a ranshi “kai gaskiya maganin na aiki da kyau am sorry mum ba zaki iya komai ba kwakwalwan ki ma bazata yi aiki ba bare kiche babu irin wan nan chiwo a duniya, dole sai abun da na tsara miki shi zaki yi, bazaki iya fita ko nan da tsakar gida ba har sai an É—aura Aure na da Ummi dan karki bata min shiri nasan kina fita zaki samu lbr ana neman Ummi dan haka babu in da zakije sai bayan Aure, shima dady salim yanzu zanje nayi maganin sa dan idan yazo kawai ya amince da zanchen Aure na da Ummi, babu wan da zai zo gidan nan da sunan yazo biki salon suga Ummi, su tonamin asiri Auren sirri za’ayi
“Ahzan tunanin me kake? Da sauri ya dago kai tare da mikewa ya nufi hanyar fita daga É—akin yana faÉ—in “babu wani tunanin da nake mum ina tausayin yarinyar ne kawai” ya kai karshen maganar tare da ficewa daga É—akin, gyara kwanchiyar ta mum tayi a saman gadon ta ta lumshe ido ta chigaba da barchinta da ta fara.

KANO

da sallama É—auke a bakin sa Aryan ya shigo fada, kallo É—aya Abba dake zaune kan kujerar sarauta ya masa ya kau da kansa gefe dan bai san ganin Aryan a chikin wannan hali kwata kwata, saman kujerar kusa da Abba yaje ya zauna “Aryan yaushe ka dawo? “Yanzu na dawo Abba” “to ya ake chiki Allah dai yasa diyanar ce” “aa Abba ba ita bace, wadda suke magana a kanta wai mahaukachiya che wani ya buge da mota to kaga ita kuma ai ba mahaukachiya bace shiyasa ban ma bi ta kan maganar tasu ba ina jin hakan nayi dawowata kawai” “eh lallai Aryan na yarda kana chikin matsananchin tashin hankali wadda yasa baka iya tantanche abubuwa” juyowa Aryan yayi da kyau yana kallon abba kafin yace “Abba me yasa kace haka? “Eh mana Aryan idan ba kana chikin tashin hankali ba, ai da ka daÉ—e da gano in da diyana take” da sauri Aryan ya kara waro idon sa waje yana kallon Abba “ta yaya kenan Abba kamin bayani” “lokachin da farida ta kira tana sanar mana da diyana ta bata kai kayi picking call din amma tashin hankali ya hanaka kaji bayanin da farida tayi kafin É“atar diyanar” “Abba pls tell me wani bayani kuma tayi!? “Chemaka tayi diyana ta tafi babu É—ankwali babu mayafi babu ta kalma ta bar wajen, to kaga bazaka nemi diyana a chikin masu hankali ba sai dai a dubata a sawun marasa hankali, idan kayi tunani mai yuwuwa wayan chan mutanen suna da gaskiya domin babu yadda za’ayi suga hoton diyana su che itache kai kuma ka che ba ita bace ko da blue eyes nata zaka iya ganeta chikin sauki kawai dan ayanzu baka da nitsuwa ne, shiyasa Amma abun da nake so da kai yanzu ka tattara nitsuwar ka waje guda, ka dawo asalin Kga da na sani kayi aiki da kwakwalwan ka dan samun nasara ina taya ka da addu’a tare da fatan awanan karon kayi nasara”

a sukwane Aryan ya miÆ™e ba tare da ya sake magana ba ya nufi hanyar fita fada, taku yake da sauri sauri, wayar sa ya chiro, ya kunna hasken screen É—in ya duba time 7pm contact ya shiga sauri sauri ya fara kiran layin Shahram, kira É—aya Shahram ya É—aga chike sauri da bada umarni Aryan yace “ka sanar da commissioner ya rikemin wayan nan mutanen, san nan ka shiryamin tafiya gobe karfe 7 ina son tai mana a Maiduguri” yana gama faÉ—in hakan batare da ya jira amsar Shahram ba ya katse kiran part na Ammi ya nufa

Da sallama a bakin sa ya shiga betroom na Ammi zaune take saman Throw pillow tana shan fura ganin shi yasa ta ajiye furar a gefe chike da kulawa ta amsa masa sallamar tare da tambayar yaushe ya dawo, sauri sauri yace mata “yanzu” Ammi zata sake magana ya rigata da chewa “Ammi ina son ganin drowar sa kayan yarinyar nan “diyana? Ammi ta tambaya tana kallon sa sosai “Eh ita inane wajen sa kayan ta yake? “Yana É—akin su kayan na chan yadda suka bari ba a taÉ“a ba” tun Ammi bata karisa maganar ba ya juya ya fice ya nufi É—akin su Hiyana, jakar da ya bawa diyana lokachin da ya dawo saudia ya É—auka ya fice daga É—akin, kai tsaye Part nashi ya koma

Yana shiga betroom nashi ya ajiye jakar saman mirrow ya nufi toilet dan yin wanka

Uk

8pm dai dai hiyana ta fito part nasu ta nufi kitchen already jourfree ya gama shirya abinchin Bgs dauka kawai tayi ta komo part nasu gaba É—aya a takure take dan ji take kamar tsirara take tafiya kayan sun kamata sosai, da sallama ta shiga betroom É—in yana zaune saman sofa yana waya da wajen aikin su ga dukkan alamu magana yake akan sojojin su da yan ta adda suka kama yana chikin bachin rai sosai, saman table dake gaban sa ta ajiye masa abinchi chikin sauri ta juya zata fita dan kar ya ganta ba hijabi muryan sane ta katse ta yace “ke zonan!? Chikin sauri ta dawo ta tsugunna a gaban sa ta sunkuyar da kai kasa dan kunyar kayan jikin ta takeji, alama ya mata da hannu akan tayi sarving nashi, da mamaki ta É—ago tana kallon sa, taga bama ita yaÆ™e kallo ba, chikin sauri ta É—auko plate ta fara zuba masa abinchin tana gama zubawa bata lura da hannun sa dake saman hannun kujerar ba ta É—ora plate din awajen saman hannun nashi, wani wawan mari ya sakar mata, tare da binta da harara chikin tsawa yace “get out” da gudu ta miÆ™e ta fice daga É—akin tana kuka, katse wayar da yake yayi ya ajiye wayar a gefe, chike da É“achin rai ya miÆ™e ya fice daga É—akin ya nufi waje, Hiyana na ganin fitar sa ta dawo É—akin ta kwashe kayan abinci gaba É—aya ta mai da kitchen tana dana sanin abun da tayi yau itache rana ta farko da yaya prince zai fara chin abun da ya fito daga hannun ta amma gashi saboda zumuÉ—i ta bata hakan, dawowa tayi saman doguwar kujera ta kwanta ta lumshe ido tana tunani har barchi yayi awawon gaba da ita

12:30Am

Bgs ya dawo chikin gidan kai tsaye part nasu ya nufa, dai dai zai shiga betroom nashi yaji mutun na numfashi da kyar da kyar kamar wadda aka shake, gashi palon akoi duhu wutan a kashe yake, kunna wutar wayar sa yayi haske ya gauraye wajen, juyawa yayi ya nufi in da take kwanche ta takure waje guda, sai rawan sanyi take, a hankali ya kai hannun sa saman wuyar ta jikin nata yayi zafi sosai kamar wuta hannu É—aya yasa ya dauke ta chak, ya nufi betroom nashi da ita

Jin mutun ya dauke tane yasa ta waro manya manyan blue eyes nata da kyar dishi dishi ta fara gani ta kasa gane wanene ya dauke ta kokarin kwache kanta take ta fara fisge fisge da iya karfinta, chike da jin haushin hakan ya…..

 

Masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kaimu浪浪

NEW TEAM
THE TALENT TROUPE WRITER’

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*


*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)

*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat….love)

*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)

The Talent Troupe Writer’s 

*DUK ƘARFIN IZZATA*

Story And Written
⬇️
*Star lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

No comments