Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Duk Karfin Izzata Book 2 Page 20

Book 2

Page 20

 

_______A gigice hiyana ta farka daga nauyayyar barchin da ya take juyawa tayi tana yan waige waige hannu ta sanya a saman lips nata da ɗan karfi tace “daman


duk wanan kiss da yaya Prince yamin ma farki ne,ina ma wanna daɗɗaɗar mafarkin ya zama gaskiya ya Allah ka nunamin ranar da yaya Prince zai min kiss” ɗago ido tayi tana bin ɗakin da kallon chikin sauri ta diro kasa daga saman gadon dan tana tabbacin yanzu yaya Prince ya dawo, lallaɓawa tayi ta leƙa wajen hutawar sa chan ta hangosa zaune ya manna waya a kunne da alama waya yake chikin sauri ta juyo ta dawo chikin ɗakin ta ɗauki hijabin ta ta sanya ta fice waje ta nufi kitchen, dan shirya masa abinci

Shi kuwa oga zaune yake yana waya da Aryan
“Ykk Aryan? ya jikin su Aunty Amarya? Daga ɗayan bangaren Aryan yace “Suna lfy nakira na sanar da kai ne zan wuce yola yanzu” shiru Bgs ya ɗan yi kafin yace “aa ba yau ba kuma ba gobe ba zanyi bincike a kai kafin na baka izinin zuwa yanzu dai ka chigaba da bata magani da wanchan wawan ke bata,kafin na tattara bayanai” “amma Bgs kasan fa wannan maganin idan yayi yawa zai ja mata wata matsalar ko” “Aryan baka da zaɓi just kayi abun da nache kawai” yana gama faɗin hakan ya katse kiran dai dai lokacin da hiyana ta kariso wajen hannun ta ɗauke da try abinci

Saman table ta aji masa abincin ta ɗau plate ta fara serving nashi bayan ta cammala komai ta ajiye masa saman table ɗin ta matso masa da table ɗin gabansa,tsugunnawa tayi a gaban na sa daga ɗan gefe chikin raunanniyar murana tace “yaya Prince dan Allah ka kiramin Ammi inason in tambayeta an gane diyana ne,wayar da yaya Khalid ya sai min card ɗin ciki ya kare” shiru yayi bai yi magana ba sai ma ɗaukan spoon da yayi ya fara chikin abinci sa,

shiru shiru bai yi magana ba ita kuma tana tsugunne a gaban sa ko kallon in da take bai yi ba har ya kusa kammala chin abin chin chike da kunan rai ta miƙe da gudu ta bar wajen tana hawaye,ko kallon ta bayyi ba ya chigaba da chin abincin sa

Saman katafaren gadon sa ta faɗa tare da sakin wani marayar kuka, tana zanchen zuci wai yaushe ne yaya Prince zai chanza a rayuwar sa mutun kamar ba mutun ba baka taɓa gane me yake so me baya so, yana bala’i son su yaya Fahad amma har yanzu ya kasa gane kamar yadda yake son yan uwan sa kowama haka yake son nashi, wlh ina da tabbacin na fishi kaunar yan uwana sune duniyata sune komai nawa wai ni yaushe ne bakin ciki zai kare a rayuwa ta, ya Allah kamin zaɓi mafi alkhari kamin zaɓin da ya dace da ni, ya Allah ka karemin yar uwata a duk in da take a faɗin duniyar nan, tabbas ina ji a jikina diyana na raye sai dai aduk lokacin da na tuna tana raye nakanji gabana na faɗuwa ya Allah kasa ba chikin wata musibar ta faɗa ba,

Sai da tayi kukan ta mai isarta sannan ta miƙe ta nufi toilet ta wanke fuskar ta tayi wanka ta fito ta sake shiryawa chikin wata shegiyar doguwar riga mai bala’i kyau rigar ta kamata sosai rigar bata da hannu launin pink color an mata kwalliya da wasu duwatsu farare masu kwalli daga guiwar rigar har zuwa kasa an tsaga ta ta gaba

gaban mirrow taje ta tsaya tana kallon kanta tsaki taja ganin yadda ta zama kamar wata karuwa ji take kamar taje ta damko Zahra ta mata shegen duka hannun ta na kerma ta ɗauki wani perfume dake wajen ta ɗan sanya a jikin ta kaɗan wai dan karya ji kamshin ya gane, drawer wajen mirrow ta buɗe tana yar dube dube hannun ta sai kerma yake alamar tsoro, wani kyakkyawar hoto ta chikaro da shi awajen jikin ta har bari yake wajen saurin ɗauko hoton sai tagama ashe hotunan biyu ne ba ɗaya ba, tasha ruwan mamaki lokacin da idon ta ya sauka kan face ɗin matar dake chikin hoton matar kamannin su ɗaya da hiyanar kamar an tsaga kara matar na tsaye a kasar wata katuwar bishiyar kuka tana riƙe da kwaryar nono, jikin ta sanye da kayan fulani riga zuwa chibiya da sani an mata manya manyan kitso guda biyu wadda gashin nata ya zubo har kan chibiya bakin kirin sai sheki yake kwata kwata matar bazata wuche 17 years ba, sosai hiyana ta kurawa matar ido tana son sanin wacece wanan mai mugun kama da ita haka,shiru tayi tana tunani to ko dai Ammi ce lokachin da take yanmata dan tasan idan ba Ammi ba ba wacce yaya Prince zai ajiye hoton ta awajen sa ganin tunani da take ba zata samu amsa ba yasanya ta ajiye hoton ta ɗauko ɗayan, ba karamin mamaki ta shigaba lokacin da idon ta ya sauka kan ɗayar hoton, gaba ɗaya Family su Ammi ne awajen tabbas hiyana ta san wasu daga chiki musamman Innar ta dake tsaye kusa da Ammi a lokacin kurawa tsohon da ke tsakiyar su ido tayi tana kallon sa yana ɗauke da yar yarinyar da baza ta wuchi shekara 2 ba murnushi hiyana tayi lokacin da ta gano chewa itace kan kafar tsohon nan domin tana da hoton ta tana karama dawo da kallon ta tayi kan tsohon ta zuba masa ido, na ɗan lokacin kafin ta fara bin su ɗaya bayan ɗaya da kallo, bata san lokacin da hawaye ya fara bin kuncin taba lokacin da idon ta ya sauka kan fuskar bappa dake tsaye yana ta murmushi, kallon sa take kamar ta kira shi ya amsa jin motsi takun Bgs ne ya sanya tayi sauri mayar da hoton ta goge hawayen ta chikin sauri ta juya zata barwajen dai dai lokacin shi kuma ya shigo kallo ɗaya ya mata ya kawar da kai gefe,ya wuche chikin ɗakin da sauri itama ta wuce ta ɗauki hijabin ta, ba tare da ta ɗaure gashin taba ta sanya hijabin ta wuche ta nufi wajen hutawar dan ta kwashe kayan abincin da yaci

Bayan ta kwashe kayan abincin ta mayar kitchen ne ta dawo ta gyara wajen tana gamawa ta dawo chikin betroom ɗin tana kokarin wuchewa palo sexy Voice nashi ya daki dodan kunnen ta “come here” chikin sauri ta juyo ta nufoshi yana kwanche saman gado, tana kokarin tsugunnawa a kasa yayi saurin nuna mata gefen sa da hannu ba tare da yayi magana ba, in da ya nuna mata ta zauna miƙewa yayi zaune shima suna fuskantar juna

Chikin sanyin murya ya fara magana “already an gane yar uwar ki tana gida” ai hiyana bata san lokacin da ta miƙe ta rungume sa tana dariya ba tana faɗin “wayyo Allah na Alhamdulila Alhamdulila” shiru yayi abun ma mamaki ya bashi sai da tayi dariyar ta mai isar ta sanna ta ɗago kai kallon face nashi ba karamin tsoratata yayi ba bashiri ta sake sa ta koma ta zauna a gefe ta nitsu ta manta ɗazun fa mafarki take yanzu kuma gaskiya ne, kara ɗaure fuska yayi sosai chikin izza ya fara magana “idan kika sake min irin haukar nan sai na ɓallaki ki nitsu kiji abun da zan che miki first menene sunan ki? Nitsu ta karayi chikin sanyin murya tace “hiyana”ɗan sakin fuskar sa yayi kaɗan kafin yace “what about your sisters Name” “diyana itace mai bina sai lamrat mai bi mata sai amrat auta” shiru yayi ɗan yi kafin yace “What about Your mother? Narai marai tayi da ido tana kokarin kuka,hannu ya ɗaga mata alamar kar ta kuskura ta fara masa kuka a nan ba tare da yayi magana “wacece maman ki yar ina ce? kuma aina take yanzu?chikin dakiyar zuchiya ta fara magana “ta rasu tun ina yarinya amma bayan rasuwar ta da jimawa bappa ya bamu lbr ta kuma yace zai ajiye mana wani sako ko bayan ranshi idan muka girma mu binciki ɗakin sa zamu samu sakon akan innar mu sakon yake tafiya”
“Ok mahaifiyar ta ku yar ina ce? “Bappan mu yace mana ita yar sudan ce” shiru yayi kafin yace zaki iya tuna a sudan a wani gari? Girgiza masa kai tayi kafin tace “aa bai faɗa mana awani waje bane mu dai yace mana ita yar sudan ce” “tana da yan uwa a nan Nigeria ne?shiru hiyana ta ɗan yi kamar mai tunani chan kuma ta girgiza kai tana faɗin “aa bata da kowa” shiru yayi bai sake magana ba sai chiro wayar sa da yayi ya fara kiran Aryan video call, bugu ɗaya Aryan ya ɗaga

Wani Cool murmushi Aryan ya saki lokacin da idon sa yayi masa tozali da hiyana zaune gefen Bgs yana son ya yi magana akan hakan amma yasan halin Bgs yanzu yana magana zai iya korin ta awajen

“Aryan ina yarinyar nan take? Chewar Bgs
da gangan Aryan yace “wace yarinya kuma” yana magana ya guntse dariya so yake ya ɗan kure Bgs,dogon tsaki Bgs yaja tare da wurga ma sa harara ta chikin wayar “zaka bata wayane ko ko” harara wasa shima Aryan ya wurga masa kafin yace “2dys ba muyi bane shi ya sanya yau nake maka tsiyar” ya kai karshen maganar tare da komawa kusa da diyana dake kwance saman gado tana barchin wahala,mikawa hiyana wayar Bgs yayi hannun ta har kerma yake ta ansa tamkar diyana na jin ta haka tafara surutai

“diyana ina kika shiga kinsan tashin hankali da na shiga bayan tafiyar ki kuwa? dan Allah ki tashi daga barchin nan ko zan samu naji daɗi a rayuwata alhadulillah Allah mai kyauta mai kari ko iya ganin ki kawai danayi ya kawarmin da duk wani tashin hankali da damuwa dana ke chiki, dan Allah diyana ki tashi kimin magana kinji buɗɗon bappa kin tuna sunan ko” tana magana tana kuka hawaye sharɓa sharɓa, shi kanshi Aryan kawar da fuskar sa yayi daga gaban Cameran dan idon sa sun cika da kwalla lokacin guda Bgs yaji mugun tausayin yaran ya kama shi ashe ba shi kaɗai yake son yan uwan sa kaman ran saba Allah sarki marayun Allah first time a rayuwar sa da yaji zai iya tsayawa mace zai iya share mata hawaye.

Slowly ya kai hannun sa saman face nata abun da bai taɓayi ba a rayuwar sa, chikin nitsuwa ya fara share mata hawaye yana sharewa wasu na zubowa, kamar pampo, shiru yayi yana tunanin ta yaya ake rarrashin mutun ya daina kuka ita kuwa sai surutai take tana hawaye bata ma san Bgs na goge mata hawaye ba idon ta na kan diyana dake kwance ko motsi ba tayi “dan Allah yaya Aryan ka tashe ta ka tashe ta tayi mun magana ko zanji daɗi wlh ji nake kamar in ganni gani gata wayyo Allah” ba karamin tausayin su Aryan ya jiba chike da zullumin abun da zai biyo baya idan ya tashi diyana ya sanya hannu yana ɗan shafa fuskarta yana faɗin “my jidda my jidda” zubur diyana ta mike zaune tana yan waige waige,da karfi hiyana tace “diyana diyana kimin magana kinji? sai lokacin diyana ta kai kallon ta kan wayar da ke hannun Aryan, zubawa hiyana ido tayi tana kallon ta kamar bata taɓa ganin taɓa ita kuwa hiyana sai kuka take tana faɗin “diyana kiyi magana ki faɗamin kina lfy ki chemin in da kikaje ba a chutar da ke ba dan Allah diyana kiyi magana” chikin sanyin murya diyana tace “kamar na san ki kamar sunan ki hiyana ko? a razane Aryan ya ɗago yana kallon ta domin bai taɓa tunanin diyana zata gane hiyana na ba, dafe kai diyana tayi da hannu bibbiyu tana jujjuya kanta da ɗan karfi karfi, chikin sauri Aryan ya rikota yana faɗin “my jidda menene? Shiru diyana batayi magana ba sai juyi take tana kankame da gashin kanta da karfi tana kokarin ta tunano wasu abubuwan, kawar da kai Bgs yayi daga kallon su ya juya gefe chak hiyana ta da katar da kukan da take chikin zafin nama kamar zata chafko diyana ta chikin wayar tace “diyana lfy me kuma ya sameki ko dai baki da lfy ne? Diyana kiyi magana mana” kokari diyana take ta tunano wasu abubuwa na rayuwar ta, tabbas ta tuna wacece hiyana sannan tana jin kamar bayan hiyana akoi wasu da ya dace ta sani, wani marayan kuka hiyana ta kuma saki wadda ya sanya Bgs juyowa yana kallon ta tsabar kukan da ta sha har Voice nata ya dai na fitar da sauti sosai, da sauri ya ansa wayar sa daga hannun ta ya katse kiran ya ajiye wayar a gefen sa dan kukan da hiyana take yayi yawa

Ganin yaya Prince ya anshe wayar sa ne ya sanya ta tattaro sauran sautin Voice nata ta fasa kuka mai sauti ta fika kanta saman guiwowinta tana faɗin “wayyo diyana ni che yau baki gane ba? to meya same ki? me aka miki? waya sa kika manta da ni? shiru yayi yana kallon ta, yana son ya sanya ta tayi shiru amma kwata kwata bai san ma ta yadda ake rarrashin mutun ba wani ɓangare na zuchiyar sa na faɗa masa ya rungumota yace tayi shiru zatayi haka ko akayi chikin sauri da zafin nama ya jawota jikin sa, ya rungume ta sosai da sexy Voice na shi kasa kasa a sai tin kunnen ta yace
“kiyi shiru ya isa kukan” ko jin sa hiyana ba tayi ba sai ma kara sautin kukan nata da tayi dan ji take tamkar zuchiyar ta zai fashe ya fito waje, idan ta tuna ba ta san menene ke damun diyana ba sai ta sake kara sautin kukan nata, Bgs ya rasa yadda zai yi da ita shi gashi bai san fita ya barta a hankalin da take chikin nan dan ba karamin tausayi suka bashi ba gashi bai iya rarrashin mutun ba, iya tsawa da umarni kawai ya iya bawa mutane karo na farko a rayuwar sa da ya sanya ƙwaƙwalwa sa tuna ta yadda ake rarrashin mutun, almost 10 mins suna zaune haka sai kuka hiyana ke karawa taki yin shiru

ko me ya tuna sai yayi saurin ɗago habar ta chikin zafin nama ya haɗe bakin su waje guda, lokaci guda hiyana tayi tsit ta daina kukan waro idon ta ta sukayi jaa suka kunbura saboda kuka tayi waje tana kallon sa yayin da shima ita yake kallo tunani ta shigayi an ya yanzu ma ba mafarki bane kuwa anya da gaskene, tayi nisa chikin tunanin da take sai jin tayi ya sanya ɗayan hannun sa ya rufe mata ido tare da zame bakin sa daga nata kasa kasa yace “kiyi barchi” yana kai karshen maganar ya kwanta da ita a kirjin sa, ita dai hiyana har yanzu ganin abun take tamkar mafarki ne irin na ɗazun,shiru ɗakin yayi almost 30mins suna kwanche haka

ɗago kai Bgs yayi yana kallon face nata idon ta a lumshe tayi barchi, ajiyar zuchiya ya sauƙe chikin dabara ya juyar da ita yanason ya kwantar da ita amma me sai jin yayi ta kankame sa sosai da hannayen ta dukka biyu, guntun tsaki ya ɗan ja tare da komawa ya kwanta da ita a haka tana jikin sa har barchi yayi awon gaba da shi

Chikin barchi yaji zafi ya damesa da kyar ya iya buɗe idon sa, lokaci hiyana ta ɗan sake sa, a hankali ya kwantar da ita a gefen sa ya ɗauki AC remote ya kunna yana kokarin lumshe ido, idan sa ya sauka saman face nata dake ta faman zufa saboda hijabin dake jikin ta,tsaki yaja tare da mirginawa ya matso kusa da ita ya sanya hannu ya ɗan ɗagota kaɗan ya chire mata hijabin

gaba ɗaya tula tulan breast nata a wajen sakamon mutsu mutsun da ta rinkayi a jikin sa ɗazun daman rigan ba ta da hannu shiyasa rigar ta gangaro ta koma chikin ta, zubawa breast nata ido yayi yana kallon na yan mintoci kafin ya mai da kallon sa kan face nata tasha kuka ta koshi hawaye a bushe a kumatun ta, komawa yayi ya kwanta tare da sauke ajiyar zuchiya, ya lumshe ido ya chi gaba da barchin sa

KANO NIGERIA

rungume diyana Aryan yayi sosai a jikin sa yana faɗin “my jidda me ya faru ne? shiru diyana batayi magana ba hannun sa ya sanya ya chire mata hannun da ta kama kanta da shi ya ɗauke ta chak ya wuche da ita toilet tsai data yayi a tsakiyar toilet ɗin ya kunna ruwan zafi sai data ruwan ta kusa tsakiyar baff ɗin wankan sai ya kashe ya kunna na sanyi sai da ruwan ya surku dai dai wanka, sannan ya juyo ya kalle ta tana tsaye tayi shiru kamar mai tunani a hankali ya kira sunan ta “my jidda” ɗago ido tayi tana kallon sa,alama ya mata da hannu akan tazo,ba musu taje riƙe ta yayi da kansa ya chire mata kaya jikin ta tana tsaye bata hana shi ba ɗaukan ta yayi a tare suka faɗa chikin baff ɗin shiru tayi sai kallon sa take kamar mai son tuna wani abun bai bi ta kan ta ba ya mata wanka ya fito ya ɗaura towel sanan ya fito da ita ya ɗaura mata towel ya ɗauke ta chak suka koma chikin ɗakin duk in da yayi binsa take da ido, kwata kwata baya son kallon ta a yadda taken nan dan zata iya jefashi chikin wani hali

zama saman gadon yayi ya zaunar da ita, ya shiga dressing room nashi chikin yan mintuna ya fito sanye chikin jallabiya fara hannun sa na ruke da wata farar jallabiyar, wajen ta ya dawo tana zaune kamar yadda ya barta zura mata jallabiyar yayi tare da zama kusa da ita hannun ta ya riko yana kallon cikin idon ta a nitse ya fara magana “my jidda kiyi magana mana why kika zauna shiru” shiru tayi bata yi magana ba sai kallon sa da take “in kawo miki coffee? Jin sunan coffee ya sanya taja dogon numfashi ta rumtse idon ta da karfi ta furta “yaya Aryan” chikin sauri Aryan ya miƙe yana kallon ta itama miƙewa tayi tsaye tana kallon sa saisai ta Voice nata tayi tace “yaya Aryan ko? Da sauri yace mata “eh my jidda kina nufin kin tuna dani kenan? Shiru tayi bata sake magana ba, shima shiru yayi yana tunani wato a hankali hankali zata dawo dai dai kenan? in dai hakane no need mu bata wani kwaya ko wani abun ai, rungumota yayi a jikin sa a kunne ta ya fara bata lbr abubuwan da suka wuce dan ya lura idan tana kallo ko tana jin abubun da suka wuce tana iya gane wasu abubuwan daukan ta yayi chak suka koma saman gado ya zauna ya ɗaura ta a jikin sa ya chi gaba da bata lbr kwanciya tayi saman kirjin sa tayi shiru tana sauraron sa.

To masu karatu mukoma Uk muga tom and Jerry chan me suke ai katawa

Chikin barci gaba ɗayan su sukaji a takure suke basa numfashi sosai kusan a tare suka waro idon su a kan fuskar juna,chikin razana hiyana ta yunkura tana kokarin miƙewa amma ina gaba ɗayanta tana tsakiyar faffaɗar kirjin sa ya baybaye ta ta ko ina ba halin ta tashi,jikin sa a mace saboda barci ko motsin kirki ya kasa calmly ya fara magana
“me ya kawo ki jikina” yayi magana dai dai lokacin da green eyes nashi ya sauka saman tula tulan breast ɗin ta dake saitin kirjin sa,kara wato idon sa waje yayi yana kallon su,chikin sauri ta sauke idon ta tana bin in da yake kallo da kallo,ganin breast nata a wajen rigan ya gangara ya koma saman chikin tane ya sanya ta kara rungumesa da kyau ta shige chikin kirjin sa tana ɓoye fuska, wani yarrr yaji a jikin sa lokacin da abubuwan nata suka fara sokin sa a kirjin sa, lokacin guda ya shiga chikin wani yanayi hannu ya sanya da karfi yana kokarin turera kara shigewa jikin sa tayi sosai ta riƙesa chikin tsawa yace “sake ni!” Ba shiri ta sake sa tare da sakin kuka kasa kasa, kokarin jan rigar ta take ya hauro sama amma rigar yaki saboda tana kwanche ne ta danne rigar, da sauri ta miƙe ta nufi toilet, dogon tsaki yaja tare da miƙewa shima ya shiga toilet ɗin ta na tsaye ta chire rigar jikin ta daga ita sai pant ta chikin mirrow ta ga shigowar sa ihu ta fasa ta juya ta nufi kofar fita da gudu tsawa ya daka mata “ina zaki je a haka” chak ta tsaya ba tare da ta juyo ba jikin ta sai ɓari yake, ko kallon in da take bai sake yi ba ya wuce ya ɗauro alwalal sallar la asar ya zo ya raɓa gefen ta ya wuce ya fita daga toilet ɗin tana tsaye ta kasa motsawa har sai da ya fice sanan ya koma ta chigaba da abun da take gaba ɗaya kunya ya ishe ta yaya Prince ya gama kalle ta.

Washe gari 11:30am

Tana zaune a palo tana latse latse a wayar ta, sanye take chiki farin wandon jeans da top pink color, ba karamin kyau kayan suka mata ba kasan chewar tasan dukka su yaya Prince basa nan suna wajen aiki ya sanya tayi zaman ta a palon babu hijabi,ta ɗaure gashin kanta da ribon ta zuba jelar har tsakiyan bayan ta ɗan karamin bakin nan nata kamar an sanya pink jan baki tayi kyau sosai kamar ita tayi kanta, tayi nisa chikin game da take bugawa ba zato ba tsammani taji shigowar mutane palon chikin sauri ta ɗago kai tana binsu da kallon yaya Prince ne da wasu turawa su biyu suna sanye chikin wandon sojoji da t-shirt na su kallon ɗaya zaka musu ka gane manyan generals na sojoji ne, kasa miƙewa tayi dan kunyar kayan jikin ta take

saman sofa suka zauna yaya Prince ya chiro waya ya kira jourfree akan ya yawo musu abun sha, chikin sauri ɗayan baturen ya fara magana chikin harshen turanci “aa Bgs kabari wanan sister nan ta ka ta kawomin dan ni saboda ita nazo gidan nan tun ranar dana kuka sauka a Airport ido na ya sauka akan kyakkyawar face nata naji duk duniya idan ban same ta ba zan iya mutuwa shiyasa na takura maka akan muzo gidan nan tun da ko mun tambaye ka awajen aiki baka bamu amsa shi ya sanya nazo da kai na na ganta baki da baki na furta mata abun da ke rai na” da sauri ɗayan ya miƙe yana faɗin kai dest karya kake na rigaka ni barima ka gani” ya kai karshen maganar tare da nufar in da hiyana ke zaune

ita dai tayi mutuwar zaune tana kallo ikon Allah, kusa da ita yaje ya zauna yana faɗin “hii baby” shiru ta yi bata amsa ba sai ma takure jikin ta da tayi tana kallon gefe, hannu ya kai yana kokarin kamo face nata ya juyo da ita bai kai ga taɓa fuskar nata ba yaji an yiwa hannun sa wani wawan damka

da sauri ya juyo, zaro ido yayi waje ganin yadda face ɗin Bgs ta sauya lokacin guda idon sa ya sauya yayi jaa

Da karfi Bgs ya murɗe hannun ya mai da ta baya ji kake kas kas kashin ya karye ihun azaba baturen sojan ya saki, da gudu ɗayan ya miƙe ya bar palon dan ya san halin Bgs, bugun mutuwa Bgs yayi wa baturen har sai da ya suma, a guje hiyana ta bar palo ta shige betroom jikin ta sai rawa yake,tsoro ya hana ta hawa gadon tsayuwa tayi a tsakiyar ɗakin, tana tunanin irin hukuncin da zai mata

Bayan ya gama sumar da baturen ne ya chiro wayar sa ya kira jibga jibgan sojojin dake tsaron gidan su kazo suka ɗauki sumammen baturen sukayi waje da shi,chikin zafin nama ya juya ya nufi betroom ɗin tana jin shigowar sa ta kwasa a guje ta nufi wajen hutawar sa, taku biyu yayi ya damko kugun ta ta baya chikin tsawa yace “me ya kai ki palo da har kika zauna a chan!!? Runtse ido tayi ta kasa magana dan ji tayi gaba ɗaya hanyar maganar ta ya toshe harshen ta ba zai iya motsawa ba, jiran saukan duka kawai take tsawa ya sake daka mata tare da juyo da ita suna fuskantar juna “ba da ke nake magana bane!!! Ɓari kawai lips nata keyi hakoranta sai karaf karaf suke suna haɗe wa da juna, ganin tsoratachiyar face nata ya sanya ya ɗan ji zafin zuchiyar sa ta ragu, dan ya lura ta gama tsorata ko magana ba zata iya ba calmly yace “Open your eyes” kamar jira take ya sake magana ta saki wani kuka mai ban tausayi da ratsa zuchiyar mai sauraro, chije lips na shi na kasa yayi da karfi yana ɗan shafa kan sa da hannu ɗaya kasa kasa yace “kukan me kuma ki ke? Sai lokacin ta samu damar buɗe baki ta fara magana “dan Allah yaya Prince kayi hakuri ba zan sake ba idan ba ka so ko palon ma ba zan sake zuwa ba dan Allah kar ka bugeni”

Kara chije lips na shi yayi da karfi ya jawota ta faɗa saman faffaɗar kirjin sa ya rungume ta da hannu ɗaya ɗayan hannun nasa kuma ya chusa chikin gashin kanta yana shafawa da Cool Voice yace “it’s ok” shiru tayi ta kara lafewa a jikin sa kasa kasa yayi magana ɗago kai tayi dan bata ji me yace ba “yaya Prince banji me kace ba” shiru yayi yana kallon face nata sake mai mai ta maganar nata tayi nan ma shiru yayi bai yi magana ba slowly ya fatso da face nashi dai dai nata sunkuyar da kanta kasa tayi dan kunyar sa take ji,kwantar da kansa yayi saman wuyar ta yana shakan kamshin man tashin ta “wayace kimin amfashi da man gashi? Saxy Voice nashi ya daki dodon kunnen ta “kayi hakuri ni bani da shine kuma gashi na ya fara hardewa” shiru yayi bai sake magana ba chigaba yayi da yawo da face nashi samar wuyar ta kamar mai neman wani abun sosai yake shafa lallausan bakin gashin kanta da ɗayan hannun sa,ba karamin daɗin taɓawa lallausan fatar wuyar ta ya masa ba

Kokarin faɗuwa hiyana take dan gaba ɗaya ya kashe mata jiki kafofin ta ba zasu iya ɗaukan taɓa amma haka ta daure ta chigaba da tsayuwa dan tana tsoron yi masa magana, Almost 15mins suna tsaye sai shafa gashin kanta yake ya dawo da face na shi saman kanta yana shaƙar kamshin da kyau

Gangaro da kansa yayi kusa da kunnen ta yace “kije ki kawomin wayar ki” ya karisa maganar tare da sakin ta,da gudu ta wuce ta bar wajen ta koma palo

Masu karatu sai mun haɗe gobe idan mai dukka ya kaimu Nagode sosai da comments na ku kuma ina matikar jin daɗin comments ɗin Allah ya saka da alkhari

The Talent Troupe Writer’s 

 

Story And Written
⬇️
*Star lady*

Wanna page ɗin nakine Aisha baita jidda My mum ina godiya da comments naki ina matikar farinciki da jin daɗi Allah ya bar zumunci ya barmin ke

Post a Comment for "Duk Karfin Izzata Book 2 Page 20"