Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Duk Karfin Izzata Book 2 Page 22

Book 2

Page 22

Uk 1am

Tana kwance saman katafaren gadon sa ta kasa barci duk bayan minti ɗaya sai ta duba time shiru shiru Bgs bai dawo ba tun abun baya damun ta har ta fara shiga damuwa miƙewa tayi zaune saman gadon tana


tunanin ina ya tafi Allah dai ya sa lfy tun da sukazo gidan nan bai taÉ“a wuce 12:10am a waje ba shin me ya daÉ—ar da shi yau, gajiya tayi da zama ta miÆ™e tsaye ta fara kai kawo tunawa tayi É—azun ta kalli waya a saman table É—in da yake ajiye ta kardu da system nashi da sauri ta nufa wajen tana addu’ar Allah ya sa akoi sim a chikin wayar,hannun ta har karma yake wajen É—aukar wayar ta kunna haske screen É—in,wani Cool murmushi ta saki lokacin da ta ga akoi sim a chiki already ta haddace number sa a kai chikin sauri ta shigar da number É—in sa chikin wayar burinta kawai ta kira shi batayi tunanin me zai je ya dawo ba, sau biyu tana kiran wayar sa bai É—aga ba sai a na uku ya É—aga tattara nitsuwar ta tayi gaba É—aya chikin sanyin murya tace “ina wuni yaya Prince” shiru yayi na É—an lokacin kafin yace “me menene!? “Babu komai daman naga baka dawo bane har yanzu shine nace…. Bata kai karshen maganar ba ya daga tar da ita ta hanyar chewa “kawomin black tea É—akin bincike” “yaya Prince ban san É—akin ba ai”guntun tsaki yaja kafin yace “ki fito palo awajen da ake ajiye remote ki duba zakiga farin remote ki É—auka ki sai ta sama ki dan na open stair case zai sauko sai ki haura ina wajen” yana gama faÉ—in hakan ya katse kiran, murmushi ta saki kafin ta ajiye wayar ta fice daga É—akin

Kitchen ta nufa ta haɗa masa black tea kamar yadda ya buƙa ta ta dawo palo kamar yadda ya sanar da ita haka tayi, tasha ruwan mamaki lokacin da ta ga wani ɗan siririn stair case na saukowa bayan ta danna remote,mutun ba zai taɓa zaton akoi wani abu a saman nan ba wai shi stair case tsoro hawa taji dan kar ta hau ta makale amma da ta tuna yaya Prince ɗin ta na wajen sai ta samu kwarin guiwa,
Chikin zafin nama ta haye saman stair tana hawa stair case É—in ya naÉ—e kansa da kansa

wani katafaren É—aki ne awajen mai chike da computers da na urori da ban daban gaba É—aya É—akin gauraye yake da hasken computers, yana tsaye gaban wata makekiyar desktop ya sanya wata na’ura a idon sa kamar glass sai aiki yake tika,tsayuwa tayi tana bin É—akin da kallon kafin ta mai da kallon ta kansa sanye yake da yar gakeren wando wadda ta É—ame sa sosai babu riga a jikin sa da alama wandon ma dolece ta sanya ya sa dan kallo É—aya zaka masa ka gane haka asalin kyakkyawar suran jikin sa ta bayyana gaba É—aya hannayen sa da chinyoyin sa baki lallausan gashi ne a kwance awajen sai sheki yake kai kallon ta tayi saman É—amtsen hannun sa daÆ™e murÉ—e dama dama wani mugun farinciki take a duk lokacin da ta kalli kyakkyawar bakin gashin dake kwance a saman faffaÉ—ar kirjin, Cool murmushi ta saki lokacin da idon ta ya sauka a kan haÉ—aÉ—en bakin gashin kansa wadda ke baje har bayan sa kasan chewar bai É—aure gashin ba ya sake ta har baya
duk da sanyin Ac dake É—akin hakan bai hana shi zufa ba saboda Aikin da yake tika kusa da shi tazo ta tsaya tace “sannu da Aiki yaya Prince” bai an sa ba kuma bai juyo ba aikin sa yake sosai da alama aiki ne mai muhimmanci

Tana tsaye shi kuma yana ta aikin sa almost 10mins da zuwan ta sanna ya chire na’uran dake fuskar sa ya juyo kallon É—aya ya mata ya É—auke kai kayan barcine riga da wando a jikin ta fari tas masu laushi sai É—an karamin hijabin da bai wuce kirjin ta ba ta sanya a kanta baki

ansan cup É—in hannun ta yayi ya É—ora saman wasu takar du dake wajen chikin sanyi murya yace “wayace ki É—auki waya har ki kirani? Banche duk wanda zaki kira sai kin sanar da ni ba!? Baya baya ta farayi tana girgiza kai tana addu’a a zuchiyar ta Allah ya sa kar ya bugeta,takowa ya farayi a hankali yana bin ta tana baya baya, “ba dake nake mana bane? Kasa magana tayi ta chigaba da yin baya tana girgiza yana bin ta kai har suka kure bango,runfa ya mata da faffaÉ—ar kirjin sa chikin tsawa yace “bazaki bani amsa ba sai na É“allaki”slowly ta É—ago kanta tana kallon saitin wuyar sa ta fara magana “daman naga baka dawo bane shi ya sa na kiraka amma kayi hakuri ba zan sake ba” har chikin ran sa yaji daÉ—in amsar ta dan duk yan uwan sa ba wanda ya taÉ“a damuwa ko ya kirasa awaya idan ya wuce lokacin dawowarsa É—an garama Aryan daman shi duk abun da suke a tare suke duk kuma in da zasuje tare suke zuwa for the first time yau sister sa ta damu da bai dawo ba har ta kirasa awaya wow wanan abu yayi,afili kuwa É—aure fuska yayi sosai chike izza yace “idan kika saÆ™e É—aukan waya kika kira sai na hukun taki!” ÆŠago kai tayi sosai dan ya fita tsawo sosai idan suna tsaye tana son kallon face na shi sai ta É—aga kai sosai kwata kwata tsawon ta bazata wuche kirjin sa ba da kanta da komai

Kallon face na shi tayi kafin tace “In Sha Allah ba zan sake ba amma dan Allah idan ba zaka dawo da wuri ba ka faÉ—amin kafin ka fita” abu guda É—aya ne ke burgesa da yarinyar nan koda batayi laifi ba idan ka mata faÉ—a tana ansan laifin tace kayi hakuri bata damuwa wajen dole dole sai ta sanar da kai ba tayi laifi ba da tayi da bayayi ba zatache kayi hakuri bazata sake ba kuma tana kokarin taga ta kiyaye abun da kayi magana a kai, yana sane ba ita take faÉ—awa Ammi yana mata mugun taba amma da yace idan tasake faÉ—a sai ya bugeta duk da ba ita É—in che ta faÉ—an ba bata nuna ba ita É—in bace hasalima hakuri ta bashi ta ansa laifin da ba tayi ba

Shiru suka tsaya yana kallon face nata, sunkuyar da kanta kasa tayi tana jiran taji me zai che da ita gaba
saukar hannun sa taji saman kanta zame mata É—an karamin hijabin jikin ta yayi a jefar kasa shafa gashin kanta ya shigayi tare da jawota jikin sa, jin abun tamkar mafarki Hiyana take, sun daÉ—e a haka yana shafa gashin kanta kafin ya zame hannun sa daga kan nata ya É—ago habar ta suna kallon juna matso da face nashi yayi dai dai nata chikin sauri ta runtse ido kirjin ta na dukan uku uku kasa kasa yace “ki shirya gobe zan sanya a kira muku masu gyaran gashi” yana kai karshen maganar ya sake ta tare da juyawa ya koma wajen aikin sa ya É—aukk tea É—in da ta kawo masa ya koma saman sofa dake a É—akin ya zauna,ya fara sha chikin nitsuwa

Juyawa tayi zata fita sai ta tuna da massage ɗin yaya Khalid in da yake chewa idan ya saura kamar kwana biyu alluran ya sake sa kirin ƙa yawan zama kusa da shi kina yawan yimasa magana ko da ba zai amsa ba domin awan nan lokacin duk karfin alluran ya ragu yana gab da karewa ne gaba ɗaya alokacin zai ɗan fara jin feeling kaɗan kaɗan,tuna hakan ya sanya ta koma wajen sofan da yake zaune ta na kokarin tsugunnawa kasa ya nuna mata gefen sa da hannu ba tare da yayi magana ba, nauyayyar ajiyar zuchiya ta sauƙe kafin ta zauna kusa da shi tana satar kallon sa ta kasan ido, kaɗan ya sha tea ɗin ya ajiye ya miƙe ya koma bakin aikin da yake yana miƙewa ta kwanta a wajen dan daman ta fara jin barci tana kwanchiya ba jimawa barci yayi awon gaba da ita

2am ya kammala aikin da yake gaba É—aya ya kashe duk wani kayan wuta dake É—akin nan take duhu ya gauraye É—akin haske wayar sa ya kunna kasa kasa yace “tashi muje” shiru bata amsa shi ba tsaki yaja kafin ya nufi wajen da take kwance hannu É—aya ya sanya ya É—auke ta chak ya saÉ“ata a kafaÉ—a ya nufi hanyar fita da ita sai da ya kai tsakiyar É—akin ya danna remote stair case É—in tayi kasa ya sauka yana sauka stair ta koma kai tsaye bedroom ya wuce,saman katafaren gadon sa ya shin fiÉ—e ta ya wuche ya nufi toilet wanka yayi chikin sauri yayi shirin barci dan dare yayi sosai, saman gado ya dawo ya haye tana kwance yadda ya kwantar da ita gefe ya kwanta ya karanto addu’oe in barci ya shafa sannan ya lunshe ido

Kamar jira take yana lumshe ido yana lumshe wa ta mirgino ta faÉ—o jikin sa slowly ya waro green eyes na shin karaf sai saman face nata, zuba mata ido yayi yana kallon ta barcin ta take chikin kwanchiyar hankali yauche rana ta farko da ya karewa face nata kallon, shafa nashi face É—in yayi kafin yace “haka ne fa kamannin mu É—aya da yarinyar nan” dawo da kallon sa yayi saman É—an karamin bakin ta ya zuba mata ido zuchiyar sa na ingizashi akan ya sunbacheta É—ayan É“angaren na zuchiyar sa yace “idan ka sunbace ta ka sunbaci wa keman?” da sauri É—ayan É“angaren yace “ka sunbaci sister ka kuma zaka iyayin komai da ita a matsayin ta na sister ka, kawai ka É—auke ta a matsayin abun rage kewar ka,shiru yayi sai tunaninnuka daban daban yake a zuchiyar sa amma ya rasa wanne É—aya sai kama ji yayi ba zai iya jure kallon lallausan lips nata ba batare da ya sumbata ba

slowly ya kai bakin sa saman nata da niyar ya sumbace ta amma sai ya zarce ya fara kissing nata ba tare da ya sani ba, sosai yake kissing nata tare da kara jawota jikin sa sosai duk abun da yake mata tana jin sa dan daman batayi barci ba da gangan ta faɗo jikin sa yaya Khalid ne ya rubuta mata a massage kar ta yarda ta rinƙa barci ba a jikin sa ba tarinƙa nuna masa kamar barci take ta mirgino jikin sa ta nuna kamar bata san ta faɗo jikin na shi ba,kara matse ta yayi sosai a jikin sa yana bata hot kiss tula tulan breast nata dake sokin sa a kirjin sane ya fara damun sa ɗan sassauta rungumar da ya mata yayi dan ya samu su ɗan raba jiki, kaɗan kaɗan yake jin feeling akan ta sai da yayi kissing nata mai isar sa sanna ya zame bakin sa daga nata tare da raba jikin su ya ɗan juya ya lumshe ido shi duk a tunanin sa tana barci bata ji me ya mata ba ita kuwa mutuwar kwanche tayi dan gaba ɗaya ya gama kashe mata jiki ya ruɗar da ita dannewa kawai take tunani ta shigayi anya zata iya biyewa shawarar yaya Khalid da yaya Aryan kuwa? Gaskiya wanna aiki ne mai wahala ba zata iya ba gaskiya sai dai su kawo wani shawarar da wanan tunani barci yayi awon gaba da ita, kusan tare barci ya ɗauke su

KANO NIGERIA

Auty Amarya na kokarin fita bedroom nata dan lokacin chin abinci yayi tasan yanzu gaba É—aya su Abba sun haÉ—u a palo dai dai zata fita wayar ta dake bedside drawer tafara rigging kamar bazata je ta É—auka ba sai kuma ta fasa ta koma taje ta É—auki wayar sunan hajj sadiya che ta bayyana saman screen É—in wayar zama tayi a bakin gado kafin tayi picking call É—in tare da manna wayar a kunnen ta

Daga É—ayan É“angaren hajj sadiya tace “Hello hajj ya hajara Ykk”dogon numfashi Aunty Amarya taja kafin tace “lfy Ykk” “Alhadulillah daman nakira na sanar da ke ne yanzu gagarabadau ya mutu sai dai na kaiwa malamina dake bayalsa ya yi mana aikin Farida da Aisha” miÆ™ewa tsaye Aunty Amarya tayi tare da dafe kirji chike da raza na tace “yaushe ya mutu!? “Yanzun nan gani nan ma a kofar gidan sa yanzu baafi minti É—aya ba”komawa Aunty Amarya tayi ta zauna gaba É—aya jikin ta ya mutu tama rasa me zata che wa haj sadiya “haj ya hajara ina zulaihat ne? Tun shekaran jiya bata kirani awaya ba itama malamin mu na Niger ya kusa kammala aikin ta tsakanin ta da Safras”tsaki Aunty Amarya ta ja kafin tace “zulaihat bata koma wajen ki ba ai ni tun shekaran jiya da na ganta da safe ban sake ganin taba na yi tunanin ta gaji da zama da nine ta koma wajen ki ai” “aa zulaihat bata dawo waje naba kai amma wanna yarinyar yanzu a gidan naki ma sai data fita yanzu tana chan kila wani saurayin nata tabi yarinya kwata kwata bata jin magana ni Allah yasa malamin nan ma ya gama aikin nan da wuri mu sa mu ayi auren nan kila idan ta shiga gidan Safras É—in ta rage yawon banzan nan,barima na kira layin ta dan uban ta koma ina take ta wuce ta dawo” guntun tsaki Aunty Amarya taja dan ita gaba É—aya yanzu haushi ma suke bata daga zulaihat É—in har Haj sadiyar “haj sadiya sai munyi waya yanzu zanje palo muyi breakfast ne kowa ya hallara saura ni zamuyi waya anjima” tana gama faÉ—in hakan ta katse kiran ba tare da ta jira amsar haj sadiya ba mayar da wayar tayi saman drawer gefen gadon ta miÆ™e ta fice daga É—akin tana mai bakin ciki mutuwar gagarabadau

Da sallam É—auke a bakin ta ta shiga palon Abba gaba É—aya wayan da suka rage a gidan suna zaune saman table diyana na zaune kusa da Aryan É—in ta tayi shiru ta kasa chin abinci zama Aunty Amarya tazo tayi a kujerar kusa da Abba tana harara Aryan da diyana

“my diyana kici abinci mana” chewar Abba yayi maganar yana kallon diyana,sai lokacin Aryan ya É—ago kai tare da ajiye wayar sa a gefe saman table É—in ya jawo plate na abincin nata ya É—auki spoon É—in ya É—ibo chips É—in ya kai mata bakin ta, shiru tayi bata buÉ—e baki ba kuma bata É—ago ba tana kallon kasa, mai da spoon É—in yayi chikin plate É—in ya É—an rungumota da hannu É—aya yana faÉ—in “my jidda menene kuma….bai karshen maganar ba yaji ta sake masa jikin ta gaba É—aya a jikin sa kokarin faÉ—uwa take dan bai riÆ™e ta da kyau ba chikin zafin nama ya rikota da kyau yana faÉ—in “my jidda lfy me ya faru” miÆ™ewa Abba yayi yana faÉ—in “suma fa tayi Aryan” tun Abba bai gama rufe baki ba Haidar ya miÆ™e da sauri ya nufi fridge ya É—auko ruwa, É—aukan ta Aryan yayi chak suka koma tsakiyar palo ya shinfiÉ—e ta saman karpet Haidar ya miÆ™o masa ruwa, chikin sauri ya balle bakin robar ruwan ya tarbo a hannu ya fara shafa mata a face nata gaba É—aya su Ammi sun kewaye su suna jiran farfaÉ—o war ta zama saman sofa Abba da Aunty Amarya su kayi Ammi da Ummi kam sun kasa zama suna tsaye Omar Haidar suma suna tsaye,sai kwaÉ“e fuska Aunty Amarya take

Sau uku Aryan na zuba mata ruwa amma shiru bata farfaÉ—o ba sai a na huÉ—un ne taja dogon numfashi tare da sauke ajiyar zuchiya tun bata buÉ—e ido ba ta fara sambatu “Aunty farida yaushe ne jirgin mu zan tashi wlh na kosa na ga su hiyana ina kewar yaya Aryan kin san me Aunty farida ina zuwa gida Ammi zan fara runguma sai yaya Aryan sai kuma hiyana da Aunty Zahra aa na manta Ammi ce first sai Abba tukun nan yaya Aryan” shiru palon yayi suna sauraron sambatun diyana Allah sarki wato shine maganar ta na karshe tana cikin hayyacin ta lokacin guda Abba yaji idon sa ya chiwo da kwalla ba karamin tausayi diyana ta basu ba,mutun ya zauna chikin fitar hayyaci ba karamin abu bane, amma Alhadulillah dan da alama ta dawo hayyacin ta tun da har tana iya sambatu da sunayen yan gidan

Ji Aryan yayi ba zai iya chi gaba da jin sambatun nan nata ba tana tayar masa da hankali hannu ya sanya ya shafa fuskar ta tare da matsowa kusa da ita ya riÆ™e hannun ta É—aya chike da kaunar ta ya fara magana “my jidda buÉ—e idon ki kallemu ai tun É—azun jirgin naku ya iso gida” jin muryan Aryan ya sanya ta waro blue eyes nata da sauri tare da miÆ™awa zaune tana binsu da kallo É—aya bayan É—aya miÆ™ewa tayi da sauri ta rungumi Ammi tana murmushin tana faÉ—in “Ammi nayi kewar ki daman na faÉ—awa Aunty farida muna isa ke zan fara runguma” sosai Ammi ta rungume itama tana faÉ—in “my diyana nima nayi kewar ki sosai amma yanzu dai duk bamu ya kamata ki fara runguma ba mijin ki ya kamata ki fara nunawa farimcikin ki dan ya fimu bukatar ganin hakan” turun diyana ta tsaya chike da mamaki tace “Ammi miji kuma yaushe na samu miji” Abba ne ya ansa zanchen da chewa “Eh my daughter mijin ki” sakin Ammi tayi ta kariso wajen Abba tana faÉ—in “Abba wanene kuma mijin nawa? Da hannu Abba ya Nuna mata Aryan dake tsugunne ya kasa mikewa dan gani yake kamar har yanzu bata dawo dai dai ba a wani bangare na zuchiyar sa kuwa farincike yake yana godewa Allah da dawowar matar sa hayyacin ta

Kallon sa diyana tayi kafin ta É—ago ta kalli sauran jamaar palon chikin nitsuwa tace “Abba ni yaya Aiman nake so ba yaya Aryan ba da yaya Aiman mukayi alkawarin Aure ba yaya Aryan ba” tirkashi gaba É—aya zuba mata ido jama’ar palon sukayi Aryan jin kalaman nata yake tamkar ana zuba masa garwashi a zuciya ashe Aiman yayi gaskiya shi diyana ke so chije lips nashi yayi lokaci guda idon sa ya sauya jijiyoyin kansa suka miÆ™e huci ya fara yi kamar wani zaki diyana ta haÉ—a masa zafi biyu lokaci guda na farko ta tuna masa da Aiman na biyu tace ba shi take so ba zuciyar sa zafi yake masa jiyake tamkar zata fasa kirjin sa ta fito waje,chikin zafin nama ya miÆ™e yana kokarin barin palon da sauri Abba ya dakatar da shi ta hayyar riko hannun sa yana faÉ—in “koma ka zauna” ba musu ya koma saman sofa ya zauna tare da dukar da kai kasa umarni Abba yayiwa su Ammi akan su zauna zama sukayi gaba É—ayan su, saman sofas

“Kai Omar kaje É—akin Aryan zakaga wata jaka baka mai É—an girma ka kawomin” chewar Abba da sauri Omar ya juya ya fice daga palon
Dawo da kallon sa Abba yayi kan diyana dake zaune kusa da Ammi ya fara magana “my daughter kiyi hakuri da Auren da na miki ba tare da na tambayeki ba, abu na gaba Allah ya yiwa Aiman rasuwa inason ki anshi Aryan a matsayin miji domin da Aryan da Aiman duk abu É—aya ne kuma Aryan ya riga Aiman fara son ki kema kuma Aryan ki ka fara so ba Aiman ba nasan kinche Aiman kike so ne ba dan komai ba sai dan alkawarin da kika masa akan zaku yi Aure nasan da kin san Aiman ya rasu ba zaki che hakan ba,ina jinjina miki da kokarin chika alkawari da ki kayiwa Aiman duk da ba shi kike so ba” shiru palo yayi ba abun da kakeji sai kukan diyana kuka take sosai kukan da take ne ya sanya Aryan É—agowa baya san kukan ta ko kaÉ—an idan tana kuka zuciyar sa zafi yake masa

Chikin kuka tace “Abba dan Allah ka chemin wasa kake yaya Aiman bai rasu ba wlh na yarda yaya Aryan nake so ba yaya Aiman ba pls kucemin wasa ne yaya Aiman na É—akin sa” kuka take sosai kakar ranta zai fita kasa jurewa kukan nata Aryan yayi ya miÆ™e ya dawo kujerar kusa da tasu ya zauna chikin kulawa ya fara magana “my jidda ya isa kukan nan kiyi shiru” “yaya Aryan kai ma ka yarda yaya Aiman ya rasu kenan? “My jidda dole na yarda dan ba’a wasa da mutuwa yanzu dai ki dai na yin maganar kinji idan ba haka ba zaki sanya zuciya ta ta fashe” rage sautin kukan nata tayi dai dai lokacin Omar ya shigo hannun sa É—auke da jakar da Aryan ya bawa diyana tsaraba lokacin da ya dawo makka

Ansar jakar Abba yayi ya buÉ—e ya fido da abubuwan dake chiki wayan nan Box guda biyu da Aryan ya É“uye bai nunawa diyana ba Abba ya É—auko É—an babban ya fara buÉ—e wa, wani dangareren sarkan gold ne wanda ya ansa sunan shi gold ne awajen,mai matukar kyau da tsada sai É—aukan ido yake É—ago kai Abba yayi ya kallin diyana da ta kwantar da kanta jikin Ammi tana kuka kasa kasa “my daughter ga sadakin ki 100m shine kuÉ—in sadakin ki daga mijin ki” hannu Ammi ta sanya ta ansa ta sanyawa diyana a tafin hannun ta tana faÉ—in “an sa ki gani my diyana” kuka kawai take taki kallon sarkan buÉ—e É—ayan kwalin Abba yayi ya miÆ™awa Aryan ansa Aryan yayi ya fito da wasu kananan Fararen box masu bala’i kyau daga chiki buÉ—e É—ayan yayi dan kareran diamond ring ne wadda ya amsa sunan sa diamond sai kyalli yake yana É—aukan ido ring É—in É—auke yake da harafin A ajikin sa ta tsakiya ajiyewa yayi a gefe ya É—auko É—ayar box É—in ma ya buÉ—e shima ring ne irin É—aya da wan da ya buÉ—e da farko komai nasu É—aya sai dai wanan É—auke yake da harafin D a jikin sa É—ago kai yayi ya kalli diyana dake ta faman kuka kasa kasa yace “my jidda tashi ki zo”tashi tayi tazo gaban sa ta tsaya dan saman sofa mai zaman mutun É—aya yake zaune hannu ya sanya ya nuna mata saman chinyar sa akan ta zauna satar kallon su Abba tayi kasa kasa yana kallon chikin idon ta miÆ™ewa Abba yayi yana faÉ—in “zama chikin turawa ya É“atamin Æ´aÆ´a basa kunya ta yanzu kwata kwata” ya kai karshen maganar tare da fice palo chikin sauri su Ammi suka bi bayan sa taÉ“e baki Haidar yayi ya fice shi da Omar suna mamakin yaya Aryan

Aryan Kamar jira yake su Abba su fita ya jawota jikin sa yana faÉ—in “my jidda ya isa kukan nan haka kwantar da kanta tayi saman kirjin sa kasa kasa tace “yaya Aryan kukan ne ai yaki tsayawa” hannu ya É—aura saman face nata yana goge mata hawaye yana faÉ—in “to ya isa karki bari hawayen ya sake fitowa kinji? GyaÉ—a masa kai kawai tayi ta kara lafewa a kirjin sa hannun ta ya riÆ™o ya sanya mata diamond ring mai tambarin harafin A sanan ya miÆ™a mata mai tambarin harafin D yace ta sanya masa ansa tayi ta sanya masa a ya tsan sa na kusa da karamin ba karamin kyau ring É—in ya musu ba kamar dan su akayi shi
Kasa kasa da murya kamar mai raÉ—a yace “my jidda tashi muje na baki abinci” maÆ™e kafaÉ—a tayi chikin shagwaÉ“a tace “aa na koshi yaya Aryan” jan karan hanchin ta yayi chikin wasa yana faÉ—in “idan baki chiba zan miki Allura” chikin sauri tace zanci to amma kaÉ—an” ba tare da ya sake magana ba ya miÆ™e ya saÉ“ata a kafaÉ—ar sa tana faÉ—in “yaya Aryan dan Allah ka sauke ni zan tafi da kafana” bai tan ka taba ya wuche ya É—auki Box na sarkan sadakin ta da sauran kayan ya fice daga palon kai tsaye part na shi ya wuce

Masu karatu mu damalmale da ku a soyayyar Habibi da jiddan sa gobe idan mai dukka ya kai mu su habibi yau abun nema ya samu 

Ina muku fatan alkhari masoyana masoyan Duk Karfin Izzata fatan Allah ya chika muku burin ku na alkhari

Ina miko gaisuwa da jijjina gare ku

Aunty Asma’u
Aunty Hauwa’u
Maman Twins
My mum
Dr Aisha
Aisha
Hauwa’u yar adamawa jinin yola
Sister Halima
Sister Deeja
Aunty Amira
Nana farida
Deenat Ahmad
Maman Amir
Hafsat Rabi’u Abubakar

Da duk sauran wayan da ban samu daman kiran sunan su ba ina godiya ina ganin comments na ku ya sanyani farimciki da nishaɗi yana rage min kishin hiyana da nake ki dan na lura hiyana ta fara shisshigewa masoyina 沈

Pls a bani hot comments

Duk Karfin Izzata 

 

The Talent Troupe Writer’s 

Story And Written
⬇️
*Star lady*

Maman Shureim gaba ɗaya wanan page ɗin na kine more love 殺

Post a Comment for "Duk Karfin Izzata Book 2 Page 22"