Breaking News

Duk Karfin Izzata Book 2 Page 26

ook 2

Page 26

Bugu É—aya Aunty farida ta É—aga chike da damuwa hiyana ta fara bata lbr abun da ya faru dariya Aunty farida tayi bayan ta gama jin bayanan hiyana chikin nitsuwa ta fara


magana “oh su Safras manya to an faÉ—a masa mata wasa ne wato har da wani che miki ki tsaya a matsayin ki na sister ko? Lallai zai gane shayi ruwane kinsan yanzu me abun yi? “Aa Aunty farida ban sani ba sai kin faÉ—a” ta faÉ—i maganar tana girgiza kai “na shan yau ba zai dawo da wuri ba ki tsara wanka ki shakwalliya ki shirya masa duk wani abun da kika san zai bukata kafin ya dawo,yanzu idan mun gama waya ki kirashi ki masa ya isa wajen Aiki lfy idan kuma kika kira bai É—auka ba to ki masa massage sanna idan ya kusa dawowa nan ma ki sake kiran sa idan bai É—auka ba ki masa massage ki tambaye sa ya Aiki sai ki kara masa da ya sawo miki chocolate a hanya idan har ya sawo miki chocolate É—in to ba shakka ya fara son ki idan kuma bai sawo ba to fa muna da sauran aiki a gaban mu sanna idan ya dawo bayan kin gama chire masa ta kalma kin masa duk abun da ya dace idan yayi wanka ya shirya ya zauna yana hutawa sai ki tawo ki zauna a kan chinyar sa tun da yanzu ba zai bugeki ba kina da daman zama a jikin sa ba yadda zai yi da ke idan yace ki tashi karki ta shi ki kwanta a kirjin sa chikin shagwaÉ“a kice yayi hakuri idan ya fara yi miki tsawa ki sa masa kukan shagwaÉ“a tare da sanya hannun ki a wani shashe na jikin sa kina wasa da shi ko ki sanya hannun ki chikin gashin kansa kina shafawa kina masa kukan shagwaÉ“a,wlh dole ya sauko idan kika masa haka saura kuma kije ki masa akasin hakan kin san idan kika kure sa ya zuchiya wlh mantawa zanyi da umarnin Ammi ya miki É—an ban zan duka kina jina ko? Tun da Aunty farida ta fara wanna bayani hiyana ta sunkuyar da kai kasa kamar a gaban Aunty farida dan take “hiyana ba dake nake magana bane nace kina jina!? Kasa kasa chikin jin kunya tace “eh Aunty farida ina jin ki kuma Nagode” “good yanzu dai ki tashi ki fara aikin abubuwan da na faÉ—a miki idan da dama ki shiga kitchen ki masa girkin gargajiya da kanki dan na san ya gaji da chin abincin turawan nan tukunnan ma kin iya girkin ne? kar kije ki masa shirme ko da yake Auta na nan zata nuna miki duk abun da ya dace kiyi tuwon shinkafa da miyar egusi zaki masa dan yana matikar son tuwon shinkafa da miyar egusi kinji? “Eh Aunty farida naji kuma In Sha Allah zanyi yadda kikace “yauwa nama fasa Auta tayi maki ni zan koya miki yadda ake komai ina system É—in yayan naki? “Ya tafi da shi” “ok to tun da ya tafi da shi idan lokacin yin girkin yayi sai muyi video call na nuna miki yadda zaki yi komai yanzu dai ki tashi ki fara yin abubuwan da na faÉ—a miki kuma saura ki sa hijabi idan ya dawo kaya zaki sanya waÉ—an da dasu da babu duk É—aya ne kina ji na?” chikin sauri tace “eh Aunty farida naji” “good to tashi kije ki fara duk abun da ya dace” “to” hiyana tace tare da chiro wayar daga kunnen ta ta katse kiran

Layin Bgs ta fata kira bayan ta kammala waya da Aunty farida sau uku tana kiran layin amma shiru bai É—aga ba, massage ta tubuta masa kamar haka “yaya Prince ya Aiki fatan ka isa lfy? Ni dai ba zan gaji da ce maka kayi hakuri ba” Tana gama turawa ta ajiye wayar ta buga tagumi tana tunani kamar daga sama taji karar wayar alamar shigowar sako chikin sauri ta duba sakon zubur ta miÆ™e ganin sakon yaya Prince ne “I’m good” shine abun sa ya rubuta a sakon murmushi ta fara yi tare da rungume wayar a kirjin ta tana faÉ—in “kai yaya Prince shine kana ganin kirana kaki ka É—aga ko to zaka dawo ka same ni ne Allah yau na san me zan maka
Bgs dake zaune chikin katafaren Office na shi yana kallon ta ta chikin system É—in dake gaban sa ya waro ido waje jin abun da tace kasa kasa yayi magana wadda ina da tabbacin ko shi bai ji me yace ba lokaci guda kuma ya ja tsaki tare da kawar da system É—in daga gaban sa ya jawo cup É—in tea ya fara sha a hankali

Ita kuwa sai surutun ta take tana juyi a tsakiyar É—akin tayi nisa chikin abun da take wayar ta ya fara kara tana dubawa sai taga number yaya Aryan chikin sauri ta É—aga kira tare da manna wayar a kunnen ta chikin nitsuwa ta fara magana “yaya Aryan ina kwana? Daga É—ayan É“angaren diyana ta kwashe da dariya tana faÉ—in “Kamar wata mutuniyar kirki har da kashe murya wani wai yaya Aryan ina kwana to ba yaya Aryan bane Aunty diyana ce” dafe kai Hiyana tayi kafin ta saki cool murmushi ta fara magana “amma diyana baki da kirki wai har yanzu baki hankali ba” tsaki diyana taja kafin tace “ni ba wanan ne ya sanya na kiraki ba kin san me ni so nake ki che wanan mugu mai kama da ke É—in maza ya sake ki ki dawo gida idan ba haka ba wlh shaiÉ—anun yara mugaye zaki haifa” lokacin guda hiyana ta É—aure fuska chike da jin haushi zagin Bgs da diyana tayi ta fara magana “ke diyana kina da hankali kuwa kin san wanene yaya Prince awajena? miji nane fa ina mutuwar son shi ina kaunar sa fiye da rayuwa ta ina son farincikin sa fiye da nawa bani da buri a duniya da ta wuche yau na ganni gani ga shi mun zauna muna hira idan har ba zaki tayani son abun da nake so ba to bai ka mata ki zageshi a gaba na ba ni ina son kaya na a haka ke in ta kai ce miki komai yaya Prince yayi burgeni yake komai nashi kyau yake min komai idan yayi kyau take masa kamar dan shi akayi abun Kum…. Bata karisa ba diyana tace “ya isa haka hajiya soyayya sai yanzu na gane chewa nayi kuskure yanzu dai ba abun da zanche sai dai in che ki chi gaba dan son yaya Prince Allah ya sanya ya soki shima ko dan maraicin mu da wahalar da kika sha a kan mu Allah ya miki zaÉ“i mafi alkhari” ajihar zuciya hiyana ta sauke kafin ta chi gaba da magana “amin diyana ki rinÆ™a tayani da addu’a Allah ya sa yaya Prince ya so ni ko da kwatan son da nake masa ne amma na sha wahala sosai a kan sa” “in Sha Allah zai so ki hiyana zai so ki sosai ma in dai yana da tausayi da imani to tabbas zai so ki in dai yana da ido kuma idan sa na gani da kyau to dole ya soki in dai yana da ilimin addini kuma yana amfani da ita to dole ya soki zan tayaki da addu’a”

taÉ“e baki Bgs yayi yana kallon su ta system nashi yana jin me suke faÉ—e abun ma har mamaki yake bashi “wai yanzu yar yarinyar nan ta san me so tab gaskiya Abba ya chucheni ya haÉ—a ni da wahala” dogon tsaki ya kuma ja tare da miÆ™ewa ya fice daga office É—in

AÉ“angaren hiyana kuwa sosai ta bawa diyana lbr tun zuwar su Uk har yau sosai suka sha hira diyana ta jajan tawa hiyana akan wahalar da ta sha, ji suke kamar su haÉ—iye juna saboda so da kauna har sun yi sallama hiyana ta kuma chewa “diyana karfa ki faÉ—awa kowa hiran da mukayi” “ba zan faÉ—a ba hiyana na” godiya Hiyana ta mata sanna sukayi sallama ta ajiye wayar ta É—auki hijabi ta sanya ta fito ta nufo part É—in su Zahra

Kano Nigeria

Gaba É—aya iyalan Abba suna zaune a palo suna cin abincin rana sai hira suke tsakanin su ban da Aryan da Aunty Amarya da suke zaune shiru Aryan na latsa waya Aunty Amarya na chin abincin ta
“Aryan gobe fa zamu wuce hope ka kammala abubuwan da zakayi” chewar Abba sai lokacin Aryan ya É—ago kai “Eh Abba akoi in da zanje yau idan na dawo zan zo muyi wata magana” Abba yana kokarin yin magana diyana ta rigashi da chewa Abba eyya ina son muje kauye ina son inje in kalli su yaya bello da innar sa” satar kallon Aryan Abba yayi dan yasan halin Æ´aÆ´an na shi chike da zolaya yace “to my diyana an jima zakuje da mijin ki” a sukwane Aryan ya É—ago ido yana kallon Abba kashe masa ido É—aya Abba yayi É—aure fuska sosai Aryan yayi ya dubi diyana ya fara magana “ke idan kika sake yi mana Maganar wanchan ban… HaÉ—a ido da Ammi ya sanya ya mata kara bai karisa maganar ba ya miÆ™e chike da É“achin rai zai bar palon Abba yayi saurin chewa “aa ba sai ka É“ata rai ba ai ba yadda za ayi na yanke wa diyana abun da zatayi yanzu dole sai da izinin ka zatayi komai” zama yayi saman sofa mai zaman mutun 2 a palon yana latsawa da alama wani sakon yake turawa “Abba yanzu ke nan duk abun da yaya Aryan yace na yi shi zan rinÆ™a yi? Chewar diyana tayi maganar tana kallon Ammi dan ta lura da Ammi tun É—azu kamar tana son yi mata magana “eh my daughter yanzu duk wani abun da zakiyi sai kin nemi iznin sa idan bai yarda ba sai ki hakura” “to amma Abba in tambaye ka? GyaÉ—a mata kai Abba yayi alamar Eh “Abba menene fyaÉ—e na tambayi yaya Aryan yaki faÉ—a min” a sukwane Aryan ya juyo yana kallon ta ita ko batama san yana yi ba hankalin na kan Abba “my daughter ai na ki kajiyo wanna kalmar? “Abba wata yarinya che tace zatayiwa yaya Aryan fyaÉ—e kuma tun da na kalli yarinyar batayi kalan mutanen masu hankali ba shi yasa nake son sanin manar maganar da ta faÉ—a” gaba É—aya su Abba suka juyo suna kallon Aryan É—auke kan sa yayi kamar bai san suna yi ba “my daughter ai na kuka haÉ—u da yarinyar? “Abba jiyane muna tafiya da yaya Aryan a mota shine wasu mutane suka kama mu suka kaimu wani waje wai zasu kashe mu shine wanchan mai kama da hiyana ya turo sojojin sa suka kashe su” tsaki Ammi taja kafin tace “wanna É—an baki akoi magana wlh ke dai diyana ina ganin manne bakin nan naki zamu rinÆ™a yi” chikin sauri diyana tace “wai ni me baki na ya muku ne kowa sai ya rinÆ™a zagin baki na haka ma yaya Aryan yace sai ya shanye min É—an baki na É—in nan na dai na magana” kasa kasa Haidar ya sachi kallon Omar suna murmushi kasa kasa,

diyana na kokarin chi gaba da magana Abba yayi saurin chan za mata topic É—in hiran da chewa “baki faÉ—a min ya akayi kuka kuÉ“uta daga hannun mutane da suka kamaku ba” dafe kai Aryan yayi Abba zai kara kwaÉ“e masa abubuwa yanzu idan diyana ta bada lbr abun ya faru tsakanin su da zulaihat ai ta rusa musu shiri gashi ita mutunce da bata karya bata iya É“uye abu ba iya gaskiyan abun da ya faru take faÉ—e yanzu tana basu lbr ma Aunty Amarya zata tasa shi a gaba sai ya faÉ—a mata me ya faru,har Abban ma ba barinsa za suyi ba sai sun dame sa akan me ya faru kuma su waye mutane yanzu idan yace zai kira diyana su tafi É—aki dole Aunty Amarya zata zargi wani abu zata tasa shi agaba sosai Aryan ya shiga damuwa akan surutan diyana gashi ya rasa mafita abun haushin ma shine biye mata da Abba ke yi wlh Abba ya chika shagwaÉ“a yara wlh yayi nisa chikin tunanin,diyana kuwa sai bawa su Abba lbr abun da ya faru take har da yi musu kwatan chen zulaihat

kamar daga sama Aryan yaji wayar sa na ringing picking call É—in yayi tare da manna wayar a kunnen yana faÉ—in “hello my blood” daga É—an É“angaren Bgs yace “bata wayar” ba musu Aryan yace “my jidda zo ki anshi waya yaya ki na son magana da ke” make kafaÉ—a ta tana faÉ—in “wanchan mai kama da hiyana? Idan dai shine bana son magana da shi tun da yana azabtar min da yar uwa hiyana ta faÉ—a min duk abun da yake mata kuma wlh sai Allah ya saka mata tun da ba abun da ta masa wlh ni ban gama me yasa hiyana zata che tana son shi kamar ta mutu ba ita ma yar banza wlh rashin duka ke damun ta Allah ya sama ya mata dukan mutuwa ta yadda zata dai na son sa shike nan tana dai na son sa dole ya sake ta ta huta da ukubar sa mugu wlh da ina chan ba zan taÉ“a barinsa ya rinka bugun taba abun haushi ma har da wani chemin wai karna faÉ—awa kowa abun da ta faÉ—a min to me abun rufa masa asiri ni wlh na kusa barin gidan nan dan ba naso……bata kai karshen maganar ba Aryan ya daka mata gigitatchiyar tsawa “kimin shiru!!! wadda ya sata miÆ™ewa tsaye ta rungumi Abba tana faÉ—in “kai ma yaya Aryan zaka dawo irin sa kenan? Mamaki ne ya kama Abba ita dai diyana ko zaa kashe ta bakin ta ba zai yi shiru ba ta wani gefen kuma albarka yake sa mata yau bakin ta yayi rana tun da sunji halin da hiyana ke chiki lallai ya zama dole a kai na a matsayina na uba na É—au mataki chikin fushi Aryan ya tako ya kariso wajen da hannu É—aya ya damko hannun ta ya jata suka nufi hanyar fita ko ajikin ta sai ma kallon sa da take tana faÉ—in “yaya Aryan ya naga da ka É“ata rai kafi kyau ne? Ba karamin dariya ta bawa su Abba ba wato ita batama damu da É“acin ran nasa ba dogon numfashi Omar yaja kafin yace “tab wani abu sai soyayya idan ban da soyayya yadda yaya Aryan ya bata rai É—in nan ai da yanzu ya tashi gidan nan da bom lallai yarinyar nan ta chiri tuta tun da har yaya Prince yace zai yi magana da ita awaya tab lallai samun irin ta akoi wahala” Haidar ne ya chaÉ“i zanchen da chewa “kai dai Omar bari ai wlh da da ne yaya Aryan ranshi ya É“achi haka ai da gaba É—aya gidan nan munji a jikin mu Sister fa tayi winning akan zafin zuchiyar yaya Aryan” “kai dalla ku mana shiru” chewar Ummi “miÆ™ewa Abba yayi chike da É“achin rai ya nufi bedroom nashi mikewa Ammi tayi chikin sauri ta bi bayan sa dan ita ma maganganu diyana sun É—aga mata hankali duk tunanin ta yanzu Hiyana ta samu peace of mind a gidan Bgs amma ba komai za suyi maganin sa

Zaune bankin gado ta samu Abba gefen sa ta zauna chikin sanyin murya tace “ranka ya daÉ—e menene abun yi yanzu dan ka san dai maganar diyana gaskiya ne bata faÉ—en magana idan ba gaskiya ba” É—ago kai Abba yayi yana kallon ta ya fara magana “ni ba wanna ne damuwa ta ba babban damuwa yadda diyana tayi maganar bakiji me take faÉ—e bane ta tsani Safras bata son sa kuma sai ta chusawa hiyana tsanar sa” “bai kamata ka É—auki zanchen diyana na chewa ta tsane sa da sauran su ba dan yarinya cen yanzu dai kamata yayi mu nemi mafita akan zaman hiyana da yaron nan” “no Aisha ni na san ya zaman su yake dan ba wani motsi na Æ´aÆ´a na da ban sani ba ni damuwa na kalaman da diyana ta faÉ—a ne kin san fa fulanin daji basu iya tsanar abuba idan sukace miki basu son abu tofa tabbas basu sone kuma zasu iya yin komai dan suga sun rabu da wanna abun yanzu damuwa ta a nan kar diyana ta juyawa hiyana tunani dan shi Safras ya fara sauya wa yanzu haka maganar da nake miki ina da tabbacin yana son hiyana sai dai shi bai fahimci hakan ba ina gab da shirya masa wani tarko da shi da kan sa zai furta yana son ta to amma kalaman diyana sun kashemin hiki” “to menene abun kashe maka jiki kuma diyana fa yarinya ce kuma idan ka auna ka gani hiyana tana da hankali bazata É—auki zanchen diyana ba” “aa Aisha ina raba ki kin san fa yaran nan suna matikar kaunar junan su to kinga É—aya zata iya sadaukar da abun da take so domin É—ayan ke baki bibiyar sune shiya sanya bazaki gane abun da nake gudu ba wlh tsab hiyana zata iya hakura da Safras saboda diyana” shiru Ammi ta É—an yi kafin tace “karka damu daga yau zan sanya Aryan ya dawo min da diyana domin na faro tarbiya daga farko diyana na bukatar abubuwa da yawa” shiru Abba yayi bai sake magana ba miÆ™ewa Ammi tayi ta fice daga É—akin Ammi na fita Abba ya gyara kwanciyar a saman gadon

A É“angaren Aryan kuwa yana fita tare da diyana part na shi ya nufa kai tsaye a tsakiyar palon kasa ya tsaya tare da sakin hannun ta chikin fushi ya fara yi mata faÉ—a sai magana Bgs yake masa ta chikin wayar amma Aryan baya ji kasan chewar ya chire wayar daga kunnen sa katse kiran Bgs yayi ya sake kiran sa kamar ba zai É—auki kiran ba dan É“achin rai amma sai ya danne ya É—aga kiran tare da manna wayar a kunnen sa “mika mata wayar” abun da Bgs ya faÉ—a kenan ba musu Aryan ya miÆ™a mata wayar ganin ransa ya É“aci sosai ne ya sanya ta ansa wayar a kule ta fara magana zuba mata ido Aryan yayi yana kallon yadda take matana a nitse kamar ba ita ba kome Bgs ya faÉ—a mata oho sai gashi ta kwashe da dariya har da dukawa kasa shi dai Aryan ya zubawa sarautan Allah ido almost 30mins suka kwashe tana hira da Bgs tantama Aryan ya shiga yi anya ba da hiyana take magana ba dan Bgs ba zai tsaya yayi hira mai tsawo da diyana haka ba mutumin da magana ma wahala take masa kai ina akoi dai wani abu sai da diyana ta kwashe 1h tana magana da Bgs sanna sukayi sallama sai mamaki Aryan yake tana katse kiran ta tsugunna kasa tace “yaya Aryan kayi hakuri namaka alkawarin ba zan sake faÉ—in abun da baa tambaye ni ba kuma ko da an tambaye ni ma ba zan faÉ—a ba har sai ka bani izinin” Aryan ya rasa bakin magana tunani yake to wa’azi Bgs tayiwa diyana yasa ta sauya kome dan dai ya san halin diyana idan kace zata mata tsawa wlh bazata taÉ“a yimaka abun da kake so ba sai dai ma ta kara yi maka abun da baka so É—in to me Bgs ya faÉ—a mata haka kai dole na san ya akayi irin wanna sauyi lokacin guda haka yau Bgs ya shafe 1h yana hira da mutun akoi alamar tambaya

ganin yayi shiru bai tan ka taba ya sanya ta miÆ™e ta rungume sa tana faÉ—in “yaya Aryan fushi kayi da ni” dawo da kallon sa yayi kan face nata ya rungumeta da kyau yana faÉ—in “aa my jidda akan me zan yi fushi da ke?” Hannun ta chusa chikin gashin kansa tace “to yaya Aryan muje yau ma na maka kitso” chikin sauri yace “aa kije wajen Ammi tana neman ki ni ma akoi in da zanje idan na dawo sai muje shan ice cream” murmushi tayi tare da sakin sa tana kokarin juyawa kara kankame ta yayi kasa kasa yace “my jidda tafiya zaki ba tare da kin bani hot kiss ba? Saukar da idon ta kasa tayi chike da jin kunya tace “yaya Aryan ni kam ban iya kiss ba” É—aukan ta yayi chak suka haura sama

Duk Karfin Izzata 

 

The Talent Troupe Writer’s 

Story And Written
⬇️
*Star lady*

No comments