Breaking News

Garkuwa 22

ByTa É—an buga table É—in, tare da cewa.
“Malam ka tashi kaje ka taimakawa yan uwanka musulmai! in kuma baka da lfy ne ka nemi bokaye irinka su duba lfyarka”.
Zuwa yanzu gaba É—aya jikinshi tsuma yakeyi ta ciki. Kanshi ne yakeji yana jujjuya mishi sabida yadda ta konkotsa glass table É—in da kanshi ke kife a kai. Ga kuma sautin muryarta da yake jinshi har tsakiyar kanshi.
Da sauri ya É—ago kanshi tare da ware


matsakaita kyawawan idanunshi na zaiba.
Cikin sauri Haroon ya matsoshi ganin idanunshi sun cika tab da ƙwalla sai sheƙi sukeyi alamun suna iya zubda ƙollan a ko wanne lokacin.
Cikin harÉ—ewar murya ta larabci yacewa Haroon.
“Please ka fitar da ita a nan, ta matsa kaina zata fasa min dodon kunne”.

Ita kuwa Shatu cikin tarin mamaki da al’ajabi ta zaro manyan idanunta tare da cewa.
“Laaah!”. Sai kuma ta fara É—an ja da baya tare da cewa.
“Afwan baka da lfy ne!?.” Wani irin fitinenne murmushi Haroon yayi tare da cewa.
“Eh baya jin daÉ—i ne, É—an fita zamu kira wasu bokayen suzo su dubashi”.
Cikin sauri tace.
“Subahanallahi bokaye kuma?”.
Kai ya gyaÉ—a mata tare da cewa.
“Yesss ba haka kikace ba, ya nemi bokaye Æ´an uwanshi su dubashi”.
Kanta ta É—an dafe tare da cewa.
“No kada ka munana min zato, ina nufin likita bokan turai ka gane ko?”.
Da sauri taja da baya ganin Jabeer ya miƙa tsaye da ƙarfi.
Shi kuwa Sheykh Jabeer tsayuwanta kusa dashi barazana ce ga zuciyarshi tabbas zata iya faso ƙirjinshi ta fito.
Ganin yadda ya haÉ—e fuska ya nuna mata hanyar fitane, yasa ta juya ta fita.

Shi kuwa Jabeer komawa yayi ya zauna tare da sauƙe wasu tagwayen ajiyan zuciya a jere a jere.
A hankali yake jin bugun zuciyarshin na É—an dai-dai-ta kamar dai yadda yaji kafin ta shigo.

Sai kuma ya fara jin zuciyarshi na tsinkewa ras-ras kamar dai tana tsoron kada wani abu yayi nesa da itane.
“Ya ilahi ya mujibadda’awati ya hayyu ya Æ™ayyum”.
Sune kalaman da Jabeer yaketa maimatawa a saman lips É—inshi.

Haroon kuwa wani irin kallo yakeyi ma Jabeer mai cike da nazari.

Jalal ma kallonshin yake cike da tarin mamaki duk da sun san baya son akeyin mgn da ƙarfi a kanshi, to amman idonshi bai taɓa ciko da hawaye ba, sai yau.

Ita kuwa Shatu, ido ta zubawa Rafi’a da ta tsareta da ido, cikin yin Æ™asa da murya tace.
“Rafi’a dama, wannan shugaban tuzuran Æ™asar nan, yana aiki anan asibitin gwamnatin jihar nema?”.
Kamo hannunta Rafi’a tayi tajata sukayi gaba.
Haroon kuwa dariya yayi sabida, duk da rage muryarta da tayi sunji abinda tace, sabida wurin da suke É—in yanada amsa kuwar amo.

Cikin yin Æ™asa da murya sosai Rafi’a tace.
“Garkuwa ki nitsufa ki rufa mana asiri, kin ko san waye wannan?!”.
Shiru sukayi dukansu lokacin da suka juyo wata kekyawar mata tana bawa wasu ƴan mata Nurses a ƙalla sun kai goma lbri.
Ido Rafi’a da Shatu suka zubama wannan matar cewa.
“Shi wannan Dr Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero JoÉ—a, ba kamar sauran mutane bane, shi mutunne da Allah yayi masa wasu baiwa da nasabobi masu tarin yawa”.
Wata Æ´ar kekyawar cikinsu ne ta É—an lumshe ido tare da cewa.
“Allah ya sani Aunty ina sonshi, ina son wa’azin shi, muryarshi kawai in naji yana zuba larabci sai inji bani da sauran damuwa a duniya, sai dai shi kuma yana nan kamar dutse!”.
Da sauri Matar nan tace.
“Ai bazai yiwuba, wlh bazai taÉ“a kulakiba, duk nacinki da korkosarki, shiyasa wasu ke raÉ—e-raÉ—in shi waliyi ne!”.
Numfashin ta sauƙe tare da ci gaba da cewa.
“Duk matsayinki, kyanki, mulki, sarauta, gata, ilimi!. ko da meye kike taÆ™ama dashi a duniya ya fiki abin”.
Kusan a tare suka haÉ—a baki wurin cewa.
“Kawai dan shi jikan sarkine sai yafi mu komi?”.
Kanta ta jinjina tare da gyara zaman ta cikin sanyi tace.
“Ba haka bane. Bari kuji kaÉ—an daga cikin nasabarsa.
Kunga forko dai shi mutum ne wanda ubangijin yayi mishi baiwar ilimin addini dana zamani.
Yana É—aya daga cikin manyan malam da Afirka gaba É—aya take ji dashi.
Sabida a ƙiyasin malamai babu yaro matashi mai jini a jiki da tarin ilimin addini kamarshi.
Tun yanada shekaru takwas a duniya ya haddaci al’Æ™ur’ani mai girma.
Sannan ya fara karatun littafai shine matashin da yakeda haddar hadisai zunzurutunsu a kanshi sama da dubu ashirin.
Kunji wannan darajeta da tasa ko manyan mutane suke girmama shi.
Sannan shi jinin Masarautar JoÉ—a ne ta wurin mahaifinshi.
Ta wurin mahaifiyarshi kuwa shi jinin sarki Jalaluddin ne, masarautar sarkin Musulmai.
Kana ta wurin kakarshi data haifi mamanshi. Asalin balarabiyar saudiya ce, wacce zuriyarta ne limamen Harami.
Kunga nasaba kan nasaba kenan.
In kyau ne na halitta, babu irin kyan da bai ganiba,
In kuwa kuɗine, ku leka ƙasan gidan saman nan zakuga ayarin motocin da sukayi mishi rakiya, to ko kakan nashi Lamiɗo motar da yake hawa bata kai ta Jabeer ba.
Uwa uba shi mutun ne da ya Æ™oshi da sunna, baya son bidi’a.
Shi mutun ne wanda ya samu kekyawan zato a wurin mutanen duniya ake mishi shaidar salihi, mumini, mai tausayi.”
Da sauri suka ƙatseta da cewa.
“To Aunty meya hanashi yin aure har yanzu?”.
Cikin maida numfashi tace.
“Allahu alamu, sai dai ance kamar shi bana miji bane!”.
Cikin sauri wata tace.
“Kai mgnar. Duniya dan Allah kiji zancen Æ´an shashi faÉ—i. Bita da Æ™ulli har an samo sharrin da aka liÆ™a mishi bawan Allah.”
Rafi’a kuwa kai ta jinjinawa Shatu alamun kinji ko, ita kuwa Shatu zuru tayi kamar makahon daya tsinka garaya”.
Cikin sauri wacce tace tana sonshin tace.
“Wlh ni dai ko shi bana miji bane zan iya zama dashi a hakan in da zai yarda muyi aure”.
A hankali Shatu ta gyara riƙon da tayiwa wayarta tana ɗaukar su video.

A hankali matar nan ta nisa tare da cewa.
“Uhum Nafeesat kenan ai kuwa da wuya ya aureki duk abinda zakiyi.
Sabida kin ga Dr sugzana yar India ce ƙabilar buramin bautar wuta takeyi.
Tace tana sonshin, tace in dai zai aureta zata musulunta, amman yaÆ™i”.
Da sauri É—aya dake cinsu tace.
“Sabida me yaÆ™i duk da tayinta na shiga addinin Allah?”.
Cikin sanyi matar tace.
“Yayi bayani kuma manyan malamai sun gamsu da hujjarsa, inda yace, tace dole sai in zai aureta zata musulunta, kenan badon Allah zata musulunta ba sai dan sonshi.
Ta kuma ce in sunyi aure duk yaransu rabasu zasuyi rabi suyi addininshi rabi suyi addininta bi ma’ana wasu suyi bautar wuta wa iyazubillah.
Yace wannan dalilin yasa bazai aureta ba, kuma shi baya sonta, ya kuma gargaÉ—i mata su dena cewa suna sonshi.
Dan shi yanzu al’majiri ne sai ya girma zaiyi aure”.
Dariya sukayi baki É—ayansu.
Jin hakane yasa Rafi’a yana Shatu suka ci gaba da tafi.

Su kuma waÉ—ancan sukaci gaba da hirarsu.

Tafiya kaÉ—an sukayi suka samu wasu yan mata da samari suna hira É—aya daga cikinsu na cewa
“Ni tsarin Sheykh Jabeer yana masifar burgeni a rayuwata.
Shifa tunda yake a duniya babu wani mahaluƙin da zaice yaga koda singalalin hannunshi ne a waje.
Mutum ne da Allah yayi mishi sutura, yake kuma suturce kanshi.”
Cikin dariya wani yace.
“Kai nima yana burgeni sai dai tsarinshi na wai mata su dena yafa gyale, su rinÆ™a yin shigar zurmuÆ™a-zurmuÆ™an hija baine bai minba, to mu matasa taya zamuyi ta kallonsu munajin daÉ—i.
Ni wlh wani lokacin a kallonma nake biyan buÆ™atar damuwata sai dai inje inyi wonka”.
Cikin tashin hankali É—aya daga cikinsu yace.
“Ouzubilla, ka nemi gafar Allah wlh zina kakeyi”.
Cikin zaro ido yace.
“Kai malam dakata ni banyi zinaba”.
Cikin sanyi babban nasu yace.
“Wlh kayi sabida ita zina ai kashi-kashi ce akwai ta ido akwai ta kunne haka kuma akwai ta zahiriya, fisabilillahi ka kalli yar mutane na tafiya har kaji ka biya buÆ™atar ka?”.
Kai ya gyaÉ—a musu cikin sanyin jiki.
Nan sukayi ta mishi nasi daya kame idanunshi

Da sauri suka wuce su.
Ita kuwa Rafi’a cikin murmushi tace.
“To bari in baki amsar tambayar ki.
Yana zuwa nan asibitin sau É—aya cikin ko wanne sati. In yazo kuma ranan duk wanda ya duba magani kyautane, in kuma aikine kyautane.
Kinga Hospital É—in school É—inmu shi kuma a wata yake zuwa sau É—aya,
Nanam da kyar ya yarda, yanada asibitinshi mai zaman kanshi can yafi maida hankali”.
Ajiyan zuciya Shatu tayi tare da cewa.
“Uhum can yake tara kuÉ—in bayin Allah ya Æ™wamushewa dai”.
Kai Rafi’a ta jujjuya tare da cewa.
“No ba haka bane, duk abinda zan ce miki bazaki gamsuba in sha Allah sai Next month in ciwon mararki ya tashi, zan kaiki can zakiga zahiri.
Amman dai daga sunan asibitin zaki iya fahimtar manufarsa”.
Kallonta ta É—anyi tare da cewa.
“Menene sunan asibitin?”.
Ƙara saurin tafiyarsu sukayi tare da cewa.
“Ballitai Hospital”. Kanta ta gyaÉ—a alamun gamsuwa da sunan asibitin kana taja hannun Rafi’a suka tafi can maraba da baÆ™i.

Abin mamaki suna isa suka samu.
Kusan rabin DOCTOR’S din asibitin duk suna wurin.
Duk DOCTOR’S É—in da Shatu tayiwa mgna sunzo nan sunata basu taimakon gaggawa.
Kana ga Nurses tako Ina, sunata tura marasa lfyan ana basu gadaje.
Cikin abinda bai gaza awa É—aya da rabi ba.
Komai yayi dai-dai hatta waÉ—anda za’ayiwa aikin anyi musu.

Bisa umarnin Lamiɗo kana ya rinƙa bin gadajensu yana ajiye musu kuɗi dubu biyar-biyar.

Sosai wannan abun yayi masifar yiwa Shatu daÉ—i, tana kallon dattijon tamkar wani nata,
Godiya sosai sukayi musu da zasu tafi, suna fita nan sukayi kiciɓis da Jabeer da yanzu ya fito ɗakin tiyata.

Ita kuwa Shatu Junaidun Junainah ta kalla lokacin da aka dawo dashi daga É—akin tiyata,
Inda aka É—inke mishi inda aka sareshi.
Cikin murmushin yace. “Adda Shatu zamu kwana ko?”.
Murmushin jin daÉ—i tayi tare da cewa.
“A a Junaidun yanzuma zan tafi, kasan Ummey ba lfy, amman jibi ma zanzo gobe su ya Salmanu zasu zo, yanzu dai hankalinmu ya konta tunda kun samu kulawar likitocin yanzu sai matsalar abinci”.
Cikin sanyi Sumaye matar marigayi Sarkin bakansu, tace.
“La abinci kam bamu da matsalarshi, tako ina zakiga musulmai na dafo abinci suna kawo mana sadaka, harda kayan zaÆ™i da kuÉ—i wasu ke bamu”.
Ajiyan zuciya ta sauƙe tare da cewa.
“Alhamdulillah yau kam mutanen Rugar Bani zasuji lbri mai daÉ—i”.
Cikin kula tace.
“Toni yanzu zan tafi in Sha Allah gobe akwai masu zuwa, Allah ya baku lfy”.
Ta faÉ—i tana kallon sauran mutanen nasu.
Haka Rafi’a ma tayi musu fatan lfy kana suka fita tare.
Adaidaita suka shiga, saida ya kai Shatu tasha kafin.
Ya wuce da Rafi’a school É—in su.

A can wurinsu LamiÉ—o kuwa ganin lokacin sallan la’asar yayine yasa Jabeer cewa, suyi salla a masallacin asibitin kafin su tafi.
Haka kuwa akayi, sai gashi masallaci ya cika maƙil da bani adam,
saida suka idarne kana suka kama hanyar tafiya garin Rugar Bani.

A cikin motocin kuwa kowa da abinda yakeyi.
Shi kuwa Sheykh Jabeer tsuratul Khaf yake karantawa a hankali.
Hakama LamiÉ—o.

Su Jalal kuwa kowa na ruggume da waya.
Haroon ma waya yakeyi da Umaymah tana tambayarshi sun isane.
Nan yake gaya mata inda suke da abinda sukayi.

A cikin Rugar Bani kuwa, kamar ko wacce ranar jumma’a yauma hakane.
Tunda aka taso sallan jumma’a suka dawo tsakar garinsu suka zauna suna Æ™ara jadda mitin É—in su na É—aukar fansa.
Zuwa yanzu garin yana amsar baƙoncin Fulanin da suka gaiyata tako wani sashi na Afirka. Sunata shirye-shiryen su.

Suna cikin masallaci suna sallan la’asar ne suka rinÆ™a jiyo, shigowar motoci cikin Rugarsu kamar bazasu Æ™are ba.

Cikin nitsuwa sukaci gaba da sallan su.

Su LamiÉ—o kuwa suna shiga garin ganin tsit kuma alamun ana salla, sai yace su tsagaita gudun.

Jabeer kuwa zuwa yanzu tuni zuciyarshi ta fara luguden dukan ƙirjinshi ya rasa wannan abu na menene?
Yanzu wannan karo na huÉ—u kenan yana jin wannan abun a rayuwarsa, ya kuma gwada kanshi yaga bashi da BP dan sani BP nayin hakane ya sashi godawa.

A jere a jere sukayi parking motocinsu cikin nitsuwa,
Dogarai da fadawa suka fito suka zagaya motocin.

Bayan sun idar da salla sunyi addu’o’insu ne kana suka fito.
Gani fadawa da dogarai ma kaÉ—ai ya ganar dasu waye yazo.
Dan haka cikin karrama da mutun-tawa ArÉ—o Bani ya nufi inda suke.
Sosai dogarai sukayi mamakin yadda wannan karon kuma yakeyi kamar ya haɗiyesu dan farin cikin zuwansu saɓanin wancan karon da yayi ta aunawa Lamiɗo boma-boman baƙaƙen maganganu.
Jiki na rawa ya juyo ya kalli matasan tare da cewa.
“Maza ku shiga cikin gidan ku fito da dardumai da kilisai kuzo ki shimfiÉ—a.
Ina sarkin kiÉ—a maza a fito da gangaguna a fara sanarwa.
Mabusa ku fito.”

Ai kuwa cikin abinda bai gaza 25 minutes ba aka gama shirya komai.
Tuni mutane sun cika sunyi maƙil ko ina ya cika da bani adam.
KiÉ—e-kiÉ—en da bushe-bushen sarewa da al’gaita kuwa tuni ya cika illahirin garin tako ina mutane ke shigowa.

Ba’ana da tun jiya yake cikin É—akin dodon tsafinsu Bonon.
Jin al’gaita ShaÉ—i ne, ya sashi fitowa bayan ya gama shafe magunguna.
Dama yayi zaton wannan hegen mai jajayen kunnuwan zaizo shiyasa tun jiya ya shiga É—akin sirri dan a dafashi da kyau.

Jinsu ne yasa ya fito dashi da tawagarsa suka nufi Rugar Bani.

Lamiɗo kuwa da tawagarsa a hankali cikin ƙasaita da kwarjini suke taku har i zuwa cikin rumfar karan da aka malale musu kujeru da kilisai.

Bayan sun zaunane duk dattawan wurin sukazo suka gaida LamiÉ—o da tawagarsa.
Jabeer kuwa ji yake tamkar ya kira Sojoji su zo su zazzane mishi mutanen garin gaba É—ayansu ko zaiji ya huce da abinda sukayi mishi.
Sam baya son ganin fuskokinsu, ga toshe mishi kunne da sukayi da wannan bushe-bushen sarewa.
Ga bugun zuciyarshin dake neman zautar dashi.
Allah ya sani baya son ganin ko ƙasar garinne.

Cikin kula da nitsuwa da kamala Bappa ya kalli Jabeer É—in tare da cewa.
“Yaro ya Æ™arfin jikin naka”.
Ba tare daya É—ago kanshiba ya amsa, sabida jin muryar tanada kamala.
A hankali yace.
“Alhamdulillah”.
Gaba ɗayansu suna farin cikin ganin Jabeer yazo cikin ƙoshin lfy.
Sunyi masifar mamaki ganinshi garau ya worke cikin mako É—aya tak.
Wannane ya ƙara sawa Ya Salmanu wani farin ciki na ban mamaki.

A hankali Bappa yace.
“Masha Allah, Allah ya Æ™ara sauÆ™i”.
Idonshi ya É—an É—ago ya kalleshi, haka nan yaji dottijon ya cika mishi ido a hankali yace.
“Amin ya Allah”.
Bukar ne ya É—an kalleshi tare da cewa.
“Yanzu yaron nan kaine? Ka sake zuwa garin nan lallai baka son ranka”.
A daƙile Jabeer yace.
“Inuwa tace”.
Galadima ne ya É—an kalleshi tare da mishi alamun kada yayi mgna.
Kwaffa yayi tare da murtuke fuska.

A hankali su ArÉ—o bani suka koma wurin zamansu.
Kana Barmuji ya fara sanarwan ana son ganin Ba’ana a tsakiyar fili.

Wannan abu shine na forko a tarihin shi a nemeshi yazo tsakiyar fili dan a rama gasar da yayi.
Haka yasa cikin karsashi da buɗa ƙwanji yayi wani irin tsalle ya faɗo tsakiyar taron.
Juyi ya farayi da ihu da É—aga hannunshi sama, saida yayi kusan sau goma kafin yacewa Barmuji.
“Ka gayawa yan kallo in dai an cini gasa zan tafi in bar Æ™asar nan, zan koma Æ™asar Cameroon nida Æ™asar nan sai dai ziyara,
Dan ba’a yin jarumai biyu a gari É—aya kamar yadda ba’a sarakuna biyu a gari É—aya.”
Wani irin ihu da shewa gaba É—aya mutanen suka ruÉ—e dashi lokacin da Barmuji ya sanar da ikirarin Ba’ana.

Kana dattawan garin kuma kowa da abinda ke cikin ransa Arɗo Bani dasu Bappa kamar su haɗiye haƙorinsu dan daɗi.

Arɗo Bani ne ya ronƙofo kusa da Lamiɗo cikin nitsuwar datattaku yace.
“Allah rene, bisimilla GARKUWA ya fito fage shi ake jira.”
Kai ya gyaÉ—a mushi kana ya juyo ya kalli gefen damanshi inda Jabeer ke zaune cikin shigarsa ta al’farma, yayi masifar kyau, yana zaune cikin kamala sai lips É—inshi ke É—an motsawa a hankali alamun tasbihi yakeyi.
Cikin yanayi girma da bada umarni da tsare fuska LamiÉ—o yace.
“Jabeer kai ake jira tashi kaje muyi abinda ya kawomu.”
Fuskarshi ya tsuke tare da lumshe idonshi, muryar Galadima da yajune yasashi buÉ—e idonshi.
Shi kuwa Galadima hannu ya miƙa ya kamo hannun Jabeer, tare da fara ja alamun zai miƙar dashi tsaye.
Cikin mamaki Jabeer ya zubawa tsohon ido wanda yake Bappa ne ga Lamiɗo, in banda ƙarfin hali inashi ina iya ɗaga Jabeer.
Muryar LamiÉ—o yaji yana kuma cewa.
“Jabeer DAN ALLAH KA TASHI”.
Tsaki ya ɗan ja kana ya yunƙura ya miƙa a hankali.
Cikin jin daÉ—i Galadima ya kama hannunshi yaja suka fara taku, zuwa cikin taron.
A hankali yake bin bayan Galadima kana fadawa na biye dasu.
Al’kyabbar shi ya É—an gyara mahaÉ—inta.

Suna isa tsakiyar taron. Mabusa da makaÉ—a duk suka kaceme wurin da bushe-bushen sarewa da al’gaita kana da kaÉ—e-kaÉ—en.

Barmuji ne ya matso bayanshi da alamun zai cire mishi Al’kyabbar shi.
Da sauri Barmuji ya dakata sabida ganin wani irin lallo da Jabeer ya watsa mishi cikin tabbatarwa yace.
“Kada ka sake gangancin ciremin suturar da Allah yayi min har abadan. In kuwa ka gwada tabbas zakaji yadda raÉ—aÉ—in marin tafin hannuna yake, in kunnenka ya kuramce ansan kuramtane yasa bazakaji gargaÉ—i da kashedi na ba!”.
Ya ƙarishe mgnar da tafasar zuciya,
cikin tsuma Barmuji ya rusuna tare da cewa.
“Duk da dokar gasa ce, anyi maka wannan lamunin tunda kaine mai duka ba kai za’a dakaba”.
Ba’ana kuwa wani murmushi jin daÉ—i yayi sabida yasan yin duka da Æ™atuwar riga haka, zai takurashi bazai samu damar zage Æ™arfin shi ya zabga mishi bulaliyar ba.
(Allah sarki Ba’ana bai san zafin hannun Sheykh bane.
Sarkin Shaɗi ne, ya miƙe tsaye tare da tanɗun shantun da a ciki suka zuro bulalin nasu.
Ya nufi wurinsu Jabeer yana zuwa.
Yasa hannunshi ya zaro bulala ɗaya daga cikin bulalin ya miƙa mishi.
Hannun yasa ya amshi bulalar.
Kana ya gyara al’kyabbar jikinshi.
Shi kuwa ba’ana gabanshi ya matso ya tsaya ya buÉ—a sawunshi, kana, yasa hannunshi duka biyu ya riÆ™e Æ™ugunshi, ya buÉ—a Æ™wanjinshi da kyau.

Sheykh kuwa ƙasar garin ya zubawa ido, yana tuno irin zafi da ƙunar sashi cire kayanshi da sukayi satin daya gabata, yana tuna raɗaɗin da zuciyarsa ta masa a wannan lokacin.
Busar sarewa da akayi azaban ƙarfi ne, tabbacin an bada dama a farane.
Yasa Jabeer gyara riƙon da yayiwa bulalar, yana maiji cikin ransa da jikinsa zai rama dukan azaba da wannan ya mishi.
Yanajin zai ramane kuma dan tsorotar dashi kan sake dukan wani.
Yasani in sha Allah daga kanshi baza’a sake wannan gasar daba adadin bane, yayi niyar yin ramuwar ne dan tare wannan É“arakar zai ramane ko zai samu ya huce tsanar da yayi mutanen garin, sabida kasan cewarsu Musulmai Æ´an uwansa baya son yayi musu irin wannan tsabar lokacin É—aya fushinsa na ranar ya dawo.
Shiyasa ya murza yatsunshi da kyau tare da matsawa gefe kaÉ—an, Rumtse bubalar yayi a tafin hannunsa da kyau, kana É—agata tare kuma da cewa Bismillah, ya fara da sunan Allah kana ya É—aura da fara karanto ayatul shifa sannan ya zabgawa Ba’ana ita a tsakiyar bayanshi.

Gaba É—aya hankali da idon kowa bisa fuskar ba’ana yake.
Shi kuwa ba’ana wani irin murmushi yayi tare da kallon gefe da gefenshi kana, yayi fito alamun babu wani abu da yaji dai yaji tsikar jikinshi yana tashi yar-yar.

ArÉ—o Bani da sauran dattawan kuwa har ji sukeyi tamkar su kamo hannun Jabeer suyi ta zabgar Ba’ana babu Æ™aƙƙautawa.

Shi kuwa Jabeer wani bulalan ya kuma shimfiÉ—a mishi a tsakiyar bayanshi tare da sunan Allah.
Still murmushi yayi sai dai wani irin masifeffen bugawa da zuciyarsa tayi ya tsinke ras.
A karo na uku ya tabka mishi bulalar a tsakiyan kafaɗunshi wannan karon baiyi murmushi ba, ƙebta idonsa yayi, tare da gyara tsayuwa sai kace dutse ake tabkawa bulalin.
Fargabane ya fara dukan Æ™irazan dattawan Fulani, yayinda Æ™abilar É“achama kuwa, suketa ihu da tsalle da fito da kiran ba’ana suna Æ™ara mishi Æ™arsashi.
Bulala ta biyar Jabeer ya kuma tsula mishi, still babu sauyi.
Cikin sauri ArÉ—o Bani ya juyo ya kalli LamiÉ—o dake zaune.
Ko ajikinshi dashi da tawagarsa, Sarkin ShaÉ—i kuwa murmushi ma yakeyi.

Cikin fargaba, ArÉ—o Bani yace.
“Allah rene LamiÉ—o wannan yaron bai iya duka da Æ™arfi bane? Ko dai ba bulalin masarautarku bace!?”.
Wani irin kallo mai cike da mamaki da kuma tuhuma LamiÉ—o yayi mishi.
Sai kuma dai ya kauda kanshi.
ÆŠanzagi ne yace.
“Hattara dai ArÉ—o , Masarauta JoÉ—a sun wuce aro, zuba ido kaga ikon Allah”.
Bulala ta bakwai ne, Jabeer ya É—ago ya tsulala mishi ita a gadon bayanshi.
Da sauri Ba’ana ya rufe Æ™wayar idanunshi sabida wani irin tashi da yaji tsikar jikinshi yayi.
Tsikar jikinshi bai gama konciya ba, yakuma jin Jabeer ya rausa mushi wata bulaliyar, da sauri ya buÉ—e idonshi sabida.
Wani irin Yar-yar da yaji tsikar jikinshi tana zubawa duk gashin jikinshi ya miƙe tsaye.
Bai gama dawowa nazarin meyasa yakejin hakaba ya kuma jin wata bulaliyar.
A hankali yaji zufa ya fara keto mishi duk ta inda hudan gashin jiki yake a fatarsa.
Murmushi yakeyi har yanzu sabida bawai zafi yakeji ba, sai dai fargaba ta rufeshi, sabida jin alamun sihirurrukan jikinshine ke fecewa.
A haka Jabeer yayi ta tsula mishi bulala har zuwa bulala ta goma sha É—aya.
Ata goma sha biyu ne, da ya tsula mishi yayi wani irin gantsarewa sabida wani irin azabebben ƙaiƙayi da yaji wurin yanayi mishi.
Da sauri yasa hannunshin a bayanshi alamun zai sosa.
Ife-ife da sowan da matasa suka farayi ne da Muryar Barmuji na cewa.
“Dokar gasa banda susa”.
Da sauri ya dawo da hannunshin tare da cewa.
“To ya dane karatun da yakeyi, bana so, ya dena kira min sunan Allah”.
Wata bulalar Sheykh ya zabgawa shege tare da cewa.
“Sunan uwarka zan kira maka in ban kira sunan Allah ba?”.
Arɗo Bani kuwa wani irin ajiyan zuciya mai ƙarfi yaja.
Shi kuwa Ba’ana wani irin masifeffen Æ™aiÆ™ayi ne yakeji a duk inda Jabeer ya zuba mushi bulala, a bulala ta goma sha biyar ne, da aka zuba mushi.
Yayi wani irin gantsarewan da yafi na É—azu.
Wani irin azabebben zafi da raÉ—adine yakeji yana tsarga mishi jiki da zuciya.
Zuface ta ketomishi tako wanne sashi na jikinshi.
Cikin sauri Jabeer ya juya bulalar ya amshi ta biyu ya haÉ—a data forkon.
Ya damƙesu a hannun hagunshi.
Wanda dama shi badamene kuma bahagone duk abinda hannun damanshi kan iya yi to na hagun yana fi iyawa.
Sai dai kasamcewarshi mutun mai ilimi da sanin addini shiyasa yake amfani da hadinsin nan da Manzon Allah ke cewa.
A cikin dukkan abinda zamuyi mu wakilta dama a forko, har dai sai in shiga bayan gidane aka ware shiga da ƙafar hagu.
To juya hannun yayi da hannun hagunshi, kana ya riÆ™e mahaÉ—in al’kyabbar jikinshi da hannun damanshi.
Gyara tsayuwarshi yayi kana ya É—aga bulalar da Æ™arfi ya zubawa Ba’ana a tsakiyar bayanshi.

Wani irin azabebben ihu mai Æ™arfin amo da karaji Ba’ana ya kurma tare da fara karkarwa kar-kar tamkar mai farfaÉ—iya.
Ihun da ya kurmane yayi masifar tada hankalin dukkan kafurai magoya mayanshi.
ArÉ—o Bani kuwa a gabansu LamiÉ—o ya tashi tsaye ya juya ya fuskanci al’Æ™ibila yayi sujjada.
Bappa ma da kanshi wani irin murmushin jin daÉ—i yakeyi.

Hakama duk sauran dottawan.
Shi kuwa Ba’ana wani irin azabebben kuma masifeffen zafi yakeji a dukkan sashin jikinshi.
Wani irin tsalle ya buga da ƙarfi lokacin da aka kumayi mishi bulala ta ashirin.
Wani irin tsuma da karkarwa jikinshi keyi hatta Ba’anansa miÆ™ewa tayi tana karkarwa, wata tafasashiyar zuface ta sinÆ™o mishi, zafi yakeji har cikin Æ™oÆ™on kanshi da zuciyarshi.
Bulala ta ashirin da biyu akayi mishine yasashi fashewa da wani irin kuka mai azaban ƙarfi wani irin masifeffen fitinenne fitsarin azaba ya fara kwaranyo mishi, ihu mai cike da azaba yayi.
Wanda gaba É—aya rugar saida kowa ya jiyoshi.
Ƙabilar ɓachama kuwa gaba ɗaya suma kuka suka saka.
Shi kuwa Ba’ana da Æ™arfi ya faÉ—i Æ™asa yana burbuwa, tamkar wanda yayi al’janu.
faÉ—uwanshi Æ™asane yasa Jabeer rusunowa ya rinÆ™a tabka mishi bulalar, ihu da burbuwa da rarrafe alamun guduwa Ba’ana yakeyi cikin azaba da karaÉ—i da kuka yake cewa.
“Wayyo! Wayyo!! Wayyo Bonon!!! Ka ceceni zan mutu zai kasheni.
Wayyo Bononnnnnn! Yau bakayi min ranaba, ga bulalin karin sihirina sun iso gareni wayyoooooooo Bonon meyasa baka gaya minba na hudu tun kan wannan malamin ya kasheni ya karya min komai na jikina da sunan Allah.”
Ya ƙarishe mgnar da ƙarfi tare da miƙewa tsaye ya fuskanci kudu. Ya ɗiba a guje ya ari ta kare ya nausa a guje.
Wani irin taku Jabeer yayi tare da biyoshi baya da sassarfa abunka da dogon mutun sai gashi ya isoshi a gigice ya fara kai mishi bulalin hagu da dama,
Jin azabar ta zarce azabar da yake zatone, yasa Ba’ana kurma ihu da kururuwan da yasa kab mutane suka nufosu.
Gudu yakeyi Jabeer na binshi yana zaneshi har ya fiddashi cikin taron gaba É—aya.
Barmuji ne ya riƙe hannun Jabeer tare da cewa.
“A dokar gasa ShaÉ—i in dai ya gudu ka bishi ka korashi cikin farfajiyar shike nan ya faÉ—i a gasa kaci.
Kuma bazai sake samun damar shiga gasarba bazai kuma sake zama a garinba.”
Wani irin busar sarewa da al’gaita kana da kiÉ—e-kiÉ—en tsantsar farin ciki, al’ummar Rugar Bani suka farayi.
Sunayi suna zagaye Jabeer. Haroon kuwa da Arɗo Bani da Galadima miƙewa sukayi cikin farin ciki suka ruggumeshi.
Jamil, Jalal, Imran, Hashim, Sulaiman. Suma kab farin cikine ya cika musu zuƙata.
Laminu kuwa ji yakeyi tamkar ya shaÆ™o Jabeer ya karshi sai dai tabbas dama ya zaci aha dan shi mari É—aya nema Sheykh ya masa ya kusan suma, shiyasa ya tausayawa Ba’ana.
LamiÉ—o kuwa jinjina kai yakeyi yana tattausan murmushi.

Koda su Galadima suka ruggumeshi, ArÉ—o Bani kuwa kama hannunshi yayi ya É—aga sama alamun yaci gasar ShaÉ—in.

A haka suka iso gaban LamiÉ—o hannunshi yasa ya dafa kan Jabeer tare da sanya mushi al’barka.

Mutane kuwa duk an kacame da farin ciki.
Ya Salmanu kuwa kusan suma yayi tsabar masifar jin daÉ—i.
Alhamdulillah yau dai burinshi ya cika ya samu konciyar hankalin duniya an É—auka musu fansa, shida masoyan Shatu na baya, harma da yayanshi.

Jan gefe makaÉ—an suka sabi, da sauran zugar jamar gari.

Jabeer kuwa mamaki yakeyi yadda yaga.
Fulani nata shigowa garin tako ina wasu bisa dawakai wasuma ƙan raƙuma.
LamiÉ—o kuwa waya yakeyi da amalun a sirrance yake mgnar sabida ko Jabeer É—in dake kusa dashi baya jinshi.

Bisa umarnin Arɗo Bani ne aka rinƙa fito da ƙwaran nono da fura da dambu da ƙwaran zuma,
Ana kawowa su LamiÉ—o.

Wanda fadawa da dogarai ne sukasha.

A hankali Jabeer ya kalli LamiÉ—o cikin gajiya yace.
“To ai sai ku tashi mu tafi ko!”.
Shiru LamiÉ—o yayi mishi, ganin hakane, ya gyara hiramin kanshi kana ya kuma cewa.
“Mu tafi ko”.
Galadima ne yace.
“Ai bamu gamaba”.
Cikin sauri Haroon yace.
“To meya rage kuma?”.
Galadima ya buÉ—e bakin zai bashi amsa kenan. Sai kuma duk suka juyo suna kallon wasu tsala-tsalan motocine masu masifar kyau da tsada, suna shigowa Rugar Bani a jere-a jere. Cikin fidda numfashi Haroon ya É—an kalli motocine da mamaki yace.
“Ha Jabeer kalli wannan kamar tawagar motocin Uncle Abdulkarim da Abudulfata kalli kamarfa harda Jadda”. (Sarki Jalaluddin suke cewa Jadda)
Sai kuwa ya juyo ya kalli LamiÉ—o cikin nitsuwa yace.
“LamiÉ—o lfy kuwa?”.
Kanshi ya gyaÉ—a mishi alamar eh Lfy kau.
Shi kuwa Sheykh Jabeer cikin nitsuwa yake kallon ayarin motocin a fakaice tabbas.
Su Jalaluddin ne da yaranshi. Kana ga kuma Baban Haroon, ga kuma su Dr Aliyu da Barrister Kamal da su Baba Basiru Baba Nasiru dama duk sauran manyan masarautarsu.
Da sauri ya juyo ya kalli LamiÉ—o da nufin yin tambaya sai kuma yayi shiru ganin LamiÉ—o na mgna da Galadima da kuma wani amintaccen bafadanshi.
Tsaki ya É—an ja tare da cewa.
“To wannan Æ™us-Æ™us du na menene, ku duk abinda babu kyau kuna jin daÉ—in yinshi.”
Shiru yayi ganin motoci sama da talatin ne suka shigo Rugar.
Kana duk manyan mutanene kuma sun fito cikin motocin sun nufo inda suke zazzaune.
Wanda tuni ArÉ—o Bani yasa an kuma firfito da taburman cikin masallacin su.
Kana yasa an fito da sauran dardumai da kilisai anzo an shimfiÉ—a.

Suna isowa sarki Jalaluddin da Abba suka dafa kafaÉ—un Jabeer tare da sanya mushi al’barka kana suka zauna gefenshi ya zama sun sakashi a tsakiya.
Kusa dashi Abbanshi ya zauna,
Kana Jalaluddin ya zauna kusa da Abban.
LamiÉ—o kuwa na kusa dashi shida Galadima.

Da sauri Haroon dasu Jamil kan sukabi bayan fadawan da suka nufi motocin da sukazo yanzu da ido.

Shi kuwa Sheykh Jabeer ido kawai ya zubawa wayarshi.
Yana wasu aiyukanshi a ciki.

A hankali ya ɗago kanshi ya kalli Haroon dake taɓashi.
Da yatsa Haroon ya nuna mishi gabanshi.
A hankali ya juya kanshi ya kalli inda Haroon ke nuna mishi.
Fadawane da hadimansu keta jido katon-katon É—in sweet ga kuma fufun goro shima sunata jidowa suna ajiyewa a gabansu ArÉ—o Bani.

Cikin mamaki ya kalli LamiÉ—o tare da cewa.
“Me za’ayi da wannan kuma? Kamar wanda suka zo É—aurin aure!”.
Da sauri Galadima yace.
“Eh ashe ka gane ai É—aurkin auren ne”.
Cikin mamaki Haroon yace.
“Aure kuma? To auren waye?”.
LamiÉ—o ne ya kalleshi cikin isa yace.
“Auren Muhammad Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero JoÉ—a!”.
Wani irin yunƙura Jabeer yayi zai miƙe, cikin tsananin haɗe fuskarnan tamkar zatayi aman jini ya kalli Lamiɗo tare da yunƙurin miƙewa yace.
“Zancen banza kenan a wurin banza, ai wlh baka isaba, wlh LamiÉ—o kafa kiyayeni kanafa shigemin rayuwa, ka fita hanyata ka fice min a ido kar in rintsa da kai fa kadafa ka bari in juyo kanka”.
Ya ƙarishe mgnar da miƙewa tsaye. Sai kuma ya juyo jin an kamo hannunshi an medashi zaune, a fusace ya kalli inda yaji anja hannun nashi ganin Sarki Jalaluddin ne ya riƙo hannunshi ya sashi kuma tsuke fuskarsa cikin faɗa yace.
“Jadda sakarmin hannu bana so! Bana son abinda kuke min da rayuwata, wlh gwarama kun tashi mun tafi, dan babu ruwana dan Ni bazanyi aure ba”.
Da sauri ya juyo jin muryar Abbanshi yana cewa.
“…!

Littafin GARKUWA na kuÉ—ine turo katin mtn na É—ari uku kacal ta wannan number 09097853276, sai in saki cikin Normal group wanda a kwana talatin za’a gama littafin. Ko kuma kiyi min TRANSFER É—in dubu É—aya ta asusuna na Jaiz 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number dai 09097853276. Sai in saki a Special Group inda cikin mako biyu kacal za’a gama Part 1 da izinin ubangiji.

 

 

 

No comments