Gidan Uncle 41
PAGE FOURTY ONE*
Kwanaki bakwai tsakani Umaimah tayi shar da ita baby Shurafah tayi wayonta tayi qiba kalar fatarta kalar fatar iyayenta kamarta da mahaifinta ta fito sosai Daddy ya gama musu komai na tafiya qasar Saudia duk tsayin lkcn nan Umaimah bata taba zuwa ta duba Hameed ba kuma ko a baki bata taba tambayar ya jikinsa ba.
Kwana biyu tsakani jirginsu ya daga qasar Saudi tun ranar da Daddy yace Hameed ya tafi da Shurafah rabon da ta sanyashi a idonta sai yau data hangeshi a zaune saman welchair kansa yayi gefe sai gyara masa kan yakeyi gefe ta koma ta zauna har lkcn tashinsu yayi suka shiga jirgin suka daga zuwa qasa me tsarki itadai bata cewa kowa komai game da Hameed din ba kowa yana jajanta jikin nasa amma banda ita da tayi qasa da kanta ta zubawa yarinyar ido wasu hawaye masu zafi sunabin kuncinta.
Koda suka sauka a filin jirgin saman Saudi Arabia motar asibitin da akayima Hameed boorking ce tazo Daddy da Yusuf suka shiga Umaimah da Hajiya da Aunty Jameelah suka shiga ta masaukinsu suka tafi.
Wani babban hotel ne kusa da harami anan suka sauka Hajiya dakinta daban Umaimah da Aunty Jameelah suna shiga dakin ta kwantar da Shurafah ta shige bathroom ta fara kukan da taketa qoqarin hadiyewa tunda suka taho koda wasa bata taba tunanin jikin Hameed din yayi zafi haka ba tausayinsa ya kara darsuwa a zuciyarta mutum lafiyayye me tashe quruciya da qarfi da mazantaka wai yau shine a kwance haka kamar gawa saidai a kwantar dashi a tayar.
Lallai Allah ya cika me ikon yin komai a lkcn da yaso a hankali cikin kuka ta zube ta dora goshinta saman tiles din toilet din tace “Allah kaji qaina kabawa dan’uwana lfy Allah ka yafe masa zunubansa Allah kada ka kashe Uncle ka mayar min da Shurafah marainiya kamar ni Allah ka tausayawa bawanka me qoqarin tsayawa akan dokokin ka Allah na sani qaddara ce da sharrin shaidan tasa Hameed watsi da umarninka wannan jarabta tayi masa yawa da wanne zaiji”
Ta jima a bathroom din sannan ta fito ta zauna kusa da Shurafah ta daukota ta sanya mata nono ta kuma fashewa da kuka Aunty Jameelah ta dubeta da sauri tace “mene kuma na kuka Baby?”
Dagowa tayi tace “Aunty kinga Hameed fah yanda ya koma aunty anya Hameed zai koma normal kamar da?” Harara ta zabga mata tace “to meye damuwarki da komawarsa kamar da Umaimah na dauka ko babu komai tsakaninki da Hameed yafi qarfin wannan wulaqancin daga gareki Umaimah me Hameed yayi miki da zafi haka da zaki kwana ki tashi ki kasa tambayar iyayensa jikinsa kina ganin hakan daidaine a gurinki Umaimah kina tunanin Daddy da Hajiya basajin zafi da ciwon ko in kula din da kike nunawa dansu gudan jininsu akan laifin daba tursasa ki yayi ba kece kikaba da qofar da hakan ta faru Umaimah ko kina tunanin Daddy da Hajiya zasu soki fiye da son da sukewa dansu na cikinsu? Amsar itace aa Umaimah qaramin misali yanzu ki duba ki gani shekara nawa kikayi kina wahala da Nihal da Maliha kwana nawa kikayi da haihuwar Shurafah amma soyayyar Shurafah ta disashe hasken soyayyar da kika dauki shekaru kina nunawa Nihal da Maliha saboda itadin jininki ce da wani bangare na jikinki aka halicceta balle su da suka dauki shekara sama da talatin da biyar da dansu wacce soyayya zasu nuna miki data dara ta dansu? Ki fadamin ita Umaimah”
Ta qarashe mgnr tana matsawa kusa da yar uwar tata ta kamo hanunta tace “amma saboda tsabar rashin kunya da tsageranci da cin fuska kika iya duban tsabar idonsu kika iya furta musu bazaki qara zaman aure da dansu ba kuma kin tsaneshi hmn yarinya kiyi gaggawar sake tunaninki wlh mutanen nan basu cancanci wannan sakayyar daga gareki ba Umaimah kinsani Hameed yana sonki bazai iya rayuwa babu keba kamar yanda yasha fadamin, ko kinsan yasha zuwa ya fadamin irin wulaqancin da kikeyi masa da tsanar da kike nuna masa Umaimah Hameed yasha zuwa har Damaturu yasani a gaba ya rinqa yimin kuka yana fadamin zuciyarsa zafi take masa a duk lkcn da yaso ganinki ko yaso jin muryarki yazo gdan kikaqi yarda ku hadu ko ya kiraki a waya kikaqi amsawa Umaimah ko kinsan Hameed yasha fadamin sonki shine zai kasheshi ko kinsan a ranar da abin ya faru yana fitowa daga gdan Daddy ya daga waya ya kirani yake fadamin zuciyarsa fashewa zatayi Ina bashi hqr naji ya saki wata qara tare da kiran sunanki shikenan har yau tsayin sati biyu da kwanaki uku baisan kansa ba”….
Ajiyar zuciya ta kumayi kana ta dora da cewa “bakiyi kuka ba Umaimah sai ranar da kika daura aure da wani ba Hameed ba aka kaiki gdansa dare yayi ya shigo yayi mu’amalar aure dake minti biyu ya sauka ya bingire ya fara bacci bai farka ya sake nemanki ba saida safe ki nemeshi yace kin cika karuwanci da takura shi ya gaji to a sannan ne zaki fara kukan nadamar gujewa namiji daya tamkar da dubu namijin da mace da yawa take burin mallakar irinsa kuma namijin da bazaki qara samun irinsa ba a duniya ke bari nayi miki kalmar qarshe Umaimah wallahi tallahi billahillazi La’ilaha illah huwa bazaki iya zama da kowanne namiji ba sai Hameed shine ya fara saninki dashi kika saba kuma shine daidai dake saboda danshi kadai aka halicceki kamar yanda yasha fadamin”……
_Kuyi manege da wannan_
*UMMUH HAIRAN CE…✍*
[1/22, 8:35 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍: *GIDAN UNCLE*
Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:
Post a Comment for "Gidan Uncle 41"