Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Gidan Uncle 62


Bacci wahala tayi saboda jininta da yayi mugun hawa Hajiya ce zaune a gurinta rungume da yaron bayan anyi masa wanka ta qura masa ido tana hawaye tana tausayawa yartata ita kuma qaddararta kenan duk haihuwarta a gda to waima wanne laifi tayiwa Hameed mai girma haka harya yanke shawarar rabuwa da ita rabuwa ta har abada yanzu da bata kirata ba kenan saidai ta mutu ita kadai babu mataimaki ya dirka Mata cikin haihuwa tazo ya tsallake ya barta harda tukuicin saki har biyu yanzu shikenan babu aure tsakaninsu shikenan ta haramta gareshi shikenan tayi asara suruka irin Umaimah yarinya mai hqr ladabi biyayya da kuma bawa soyayya haqqinta yarinyar data sadaukar da duk wani farin cikinsa dominsa? Kaicon Hameed yayi kuskure me girma a rayuwarsa kuskuren da zai mutu yana nadamarsa saboda dama daya ALLAH yake baiwa mutum to shikam yayi wasa da damarsa Umaimah tayi masa nisa.

 

Da wannan tunanin taga ta fara motsawa ta matsa kusa da ita da sauri ta zuba mata ido kalma daya ce tak a bakinta “Bloody” abinda ta fara furtawa kenan kafin ta fara qifqifta ido abubuwa suna dawo mata ta bude idonta ta saukesu akan Hajiya tace “menayi masa Hajiya meyasa ya yanke shawarar rabuwa dani rabuwa ta har abada Hajiya ki tambayeshi qila ke ya fada miki wlh Hajiya bansan me nayiwa mijina ba Hajiya meyasa da mutuwa ta tashi bata hada dani ta daukaba ta dauki iyakar iyayena Hajiya ki roqamin Allah ya yafemin laifin da nayi masa Hajiya na jarabtu da yawa wlh Hajiya nafison mutuwata fiye da rayuwata Hajiya mesaya bakusa likita yayimin allura na mutu ba Allah na roqeka kada ka bani ikon tashi nayi rayuwar zawarci Allah ka kasheni na huta wayyoh Allah na rayuwata na kasa samun farin ciki Hajiya Ina ake siyar da farin ciki na siyeshi….”

 

Ba Hajiya dake tsaye ba hatta Daddy dake shigowa saida ya zubar mata da hawaye ya dagota ya rungumeta a jikinsa ya matseta sosai yana kuka mecin zuciya yace “kiyi hqr uwata qaddararku ce haka Allah shi kadai yasan dalilin da yasa yayi hakan uwata dama inada wani dan bayan Hameed wlh da ayau zan daura muku aure kowa ya huta” cikin kuka tace “Daddy bazan iya rayuwa da wani namiji ba Bloody ba shi na sani shi na saba dashi dashi na taso Daddy iyakar rayuwata tun daga quruciya ta har kawo yanzu bansan wani namiji ba bayanshi Allah na roqeka ka Kasheni qila idan na mutu na samu farin ciki Daddy haka zan qare rayuwata duk haihuwa ta a gdanku zanke yinta meyasa Hameed yayiwa soyayyata wannan tukuicin Daddy me nayi masa?”

 

Janye jikinsa yayi daga nata ya miqe saboda kalamanta mugun dagargaza masa lakar jiki sukeyi dole wannan karon ya samawa yarinyar nan farin ciki ya gaji da rayuwar quncin da takeyi yasani tanason Hameed amma ba dadin zama dashi takeji ba kuma yasani shima yanasonta to amma me tayi masa haka da ya yanke wannan danyen hukuncin akanta? Fita yayi ya kira likita ya dubata ya rubuta Mata wasu magungunan ya bawa Daddy tare da shawarwari masu tsauri saboda jininta ya hau sosai Dr Saleem yana mamakin abinda yakesa jinin yarinya qarama irin Umaimah me shekara ashirin yake hawa haka.

 

 

Shikuwa Hameed bai samu kansa ba saida aka fara kiran sallar asuba ya fara dawowa hayyacinsa ya soma janyewa a hankali na zare jikinsa gaba daya daga nata yanda ya zare zuruf din ne ya bashi mamaki yayi miqa yace “ahhh Bloody yau kin bude da yawa kodai haihuwar tazone hanya babyna yake nema” yana mgnr yana kai hanunsa saman makunnin fitilar ya kunnan ya juyo da murmushin sa wani abu yaji ya daki zuciyarsa ya zaro idanunsa waje a kidime yace “wayy… wayyoh me…meye hakan kama penis dinsa yayi da sauri ya duba yaga yanda tayi kaca² da jini ya qwallah wata qara yace “Salma… Ni nine na kusanci qazamar matar nan garin yaya ina Umaimah dama baa dakin Umaimah na kwanta ba kayy acan ne to meye ya kawoni nan?” Zabura yayi a matuqar gigice ya damqi wuyan Salma yana cewa.

 

“Ke dan kutumar ubanki tashi wlh saikin fadamin ubanme kikayi min na kusanceki” dagata yayi yayi wani wurgi da ita kanta ya hadu da bango bai damu da jinin daya balle mata a kanta ba ya dauki rigarsa yasa a firgice ya nufi qofa ya bude da gudun tsiya wanda shi kansa baisan ya iyashi ba ya nufi bangaren Umaimah a bude yaga qofar hakan ya bashi mamaki amma bashi da lkcn wannan sama ya haura da gudu yana kiran “bloody kada ki zargeni don Allah tsaya kiji wlh bansan ya akayi naje dakin shegiy….” Mgnr ce ta maqale masa ganin dakin nata a bude ya danna kai ga mamakinsa babu kowa a ciki ya bude bandakin nan ma babu kowa fitowa yayi ya shiga dakinsa yanata doka mata kira fadi yake “Ummuh Shurafah kada kimin haka fito kiji banason irin wannan wasan wlh bada niyya nayi ba basan ya akai naje dakin ba kai anya ma kuwa nine?” Tsayawa yayi cak bayan ya gama karade gdan lungu da saqo bai ganta ba yana kiranta yana kiran sunan Shurafah yana cewa “na shiga ukuna Umaimah bake kadai bace kada kisawa kanki damuwa wlh yau zan saketa na tsaneta Umaimah kada ki wahalar da kanki da cikin jikinki”

 

 

Waje ya sake fita ya nufi gurin megadi yana fadin “Mal Ibrahim Ibrahim Ina Ummuh Shurafah take Ina kaga ta tafi?” Cikin in…Ina yace “ranka ya dade jiya misalin 12:30am Hajiya da Daddy sukazo suka dauketa da alamun batada lfy….” “What? Sukazo suka dauketa ina ina ni meyasa bata fadamin batada lfy ba Mal Ibrahim meye yake faruwa ne?” Juyawa yayi da sauri ya koma part din Umaiman ya fada wanka ya tsarkake jikinsa a gurguje yayi sallah ya dauki key din motarsa lkcn bakwai na safe ya fita a guje zuciyarsa tana bugawa da qarfi yama rasa tunanin da zaiyi yana zuwa gdan megadi yace masa yanzu suka shigo gda ya shiga yayi parking ko kashe motar baiyi ba ya shiga gdan a guje sukayi karo Daddy yana qoqarin fitowa daga dakin Hajiya da jariri a hanunsa matsawa yayi da sauri yace.

 

“Yawwa Daddy ina take ta haihu ne?” Kallonsa yayi batare da ya nuna masa wata damuwa ba yace “Eh Allah ya sauketa lfy Hameed bata mutu ba Allah bai cika maka burinka na kasheta da kayi niyyar yi ba banda abinka Hameed ai ko baka batta cikin halin ciwo ba takardar sakin daka batama shaida ce ta baka buqatar zama da ita to yau dai qurunqus dan kan barya Hameed aure babu tsakaninka da Umaimah kuma aure indai irin nakane to Umaimah ta barshi har abada wlh indai irin zaman da tayi a gdanka ne gara nasata a gaba nayita kallonta” duk cikin kalaman na Daddy babu abinda ya fahimta ya dago zaiyi mgn Hajiya dake fitowa ta daki bakinsa har saida ya fashe tace “sannu da zuwa tatacce dan’uwan koko ubanme kazo fada mana kazo ka jaddada mana ka saki Umaimah saki biyu ne ka cike mata ya zama uku?” Murmushi tayi me ciwo tace.

 

“Ai dama kayi zamanka gurin matarka abar qaunarka basai kazo ba saboda zuwan naka bashida wani amfani” dagowa yayi cikin tashin hankali da kidima yace “na roqeku badon halina ba ku taimakeni ku warwaremin qullin nan wlh fahimci me kukeso kuce ba” kallonsa Daddy yayi kallon tsaf yace “waye Abdulhameed Adam Hameed Shuwa ne?” Dagowa yayi yace “nine Daddy” ya kuma cewa “wace Umaimah ne?” Sake dagowa yayi yace “qanwata ce kuma matata ce Umaimah” murmushi Daddy yayi me ciwo yace “to tunda hakane karanta wannan takardar rubutun waye a jiki?” Miqa hanunsa yayi jikinsa na rawa ya karbi takardar daya rubuta da manyan kalmomi _“NI ABDULHAMEED ADAM HAMEED SHUWA NA SAKI MATATA UMAIMAH SAKI BIYU BATARE DA WANI DALILI BA_

 

Tashin hankali wanda baasa masa rana wata uwar zabura da yayi yayi cilli da takardar yana ja da baya yana girgiza kai yanason bude bakinsa amma ya kasa wani mugun jiri yakejin yana fuzgarsa kuma ya kasa tsayawa da tafiyar da yakeyi da baya da baya Daddy ne ya miqawa Hajiya Shuraif dake hanunsa ya tafi da gudu ya ruqoshi yana dafe da kansa dake sara masa yace “rur.. rubuta nane Daddy amma yaushe na saki matata ni da kaina na saketa Daddy aa wlh bani bane”……..

 

 

_Kuyi hqr da wannan banida charge kuma inason muyi fira_

 

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍*
[1/31, 8:55 AM] UMMUH HAIRAN CE…✍: *GU*

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Post a Comment for "Gidan Uncle 62"