Gidan Uncle 66
Haka kwanaki sukayita tafiya rayuwa taqiwa masoyan dadi duk yanda Umaimah takeso ta watsar da lamarin Hameed ta kasa jinsa takeyi a cikin jininta ciwon da yakeyi yafi komai daga mata hankali musamman a yan kwanakin nan da abin nasa yaci tura ranar daya rage saura sati daya bikin Umaimah
dangin Sulaiman suka kawo lefenta ya zuba mata kaya sosai babu harkar qaranta komai na budurwa yakeyi Mata rawar kafa yake sosai akan auran amma abu daya da yake sanyaya masa jiki yanda amaryar tasa bata nuna masa farin cikin.
A wannan ranar kuma Hameed jikinsa yayi tsanani sosai Daddy ne ya matsa masa sukaje asibitin aka bashi gado hankalin Umaimah kwata² baya jikinta dauriya kawai takeyi bisa tursasawar Hajiya da take qarfin halin itama ake hidimar bikin itadai Umaimah ko lalle batayi ba saboda duk dakiyarta lkcn da suka fita domin zuwa gdan kwalliya ranar dinner ta roqi Saudat da Sa’ud akan su taimaka su rakata ta dubo jikin bloody dinta da farko qi sukayi Saida sukaga yanda hankalinta ya tashi sannan suka yarda sunayin parking ta bude murfin ta nufi dakin da yake da sauri cikin saa kuwa babu kowa ta tsaya ta zuba masa ido yanda duk aka daure masa qirjinsa da na’urori shine yafi komai daga mata hankali gashi kwance kamar gawa sai idanunsa da suke motsi kawai yana ganinta ya fara qoqarin miqewa tayi saurin matsawa jikinsa ta dora kanta a saitin fuskarsa ta qanqameshi ta saki kuka a haka su Sa’ud suka shigo suka tarar dasu tana kuka shi kuwa bama zai iya kukan ba sai zafin zuciya kawai daqyar ya motsa bakinsa yace.
“Shi..shikenan na rasaki Umaimah na roqeki kada ki manta dani a addu’ar ki idan bazan taba yafewa duk wanda ya rabani dakeba Umaimah nasani kema saboda babu yanda zakiyi ne zaki auri wani amma ki riqe kuma kisa a ranki watarana zaki dawo gareni Umaimah don Allah idan kinje kada ki bari ya tabamin ke idan na tuna abinnan zuciyata neman tarwatsewa take bansan meyasa naqi mutuwa ba….”
Rufe masa baki tayi tana girgiza masa kai tace “bazaka mutu ba Hameed zaka miqe kaci gaba da rayuwa kayi hqr haka Allah ya tsara mana…” ji tayi an janyeta tana juyowa taga Sulaiman ne suka shigo da mahaifinsa da Daddy kuka ta saka me sauti ta fada jikinsa ta qanqameshi tana kuka tace “kayi hqr dani a yanda nake D.S wlh inason sabawa zuciyata dakai amma na kas…” Rufe mata baki yayi yayi murmushi me ciwo yace “kiyi hqr ki daina kukannan banaso inasonki zanyi hqr dake a duk yanda kika zomin kuma zan riqeki amana da zuciya daya nayi alqawarin saina goge miki duk wani namiji dake zuciyarki nazama nikadai ne nake mulkinta”
Yana fadin haka yaja hanunta suka fice ya sata a motarsa Saudat Alfah da Sa’ud suka biyosu ya zage sai goge mata hawaye yakeyi duk da yanda yakejin kishinta a ransa amma ya kasa nuna Mata saboda yasan nunawar qarin shigarta damuwa ne Sa’ud ce ta leqo tace “ango kabamu aron amaryar taka yamma tayi kwalliya zamu” kallonta yayi yace “kuyi gaba zamu biyoku” hakan kuwa akayi shine yakaita har gurin kwalliyar Saida ya shigar da ita har ciki ya sumbaci hanunta yace “ki kulamin da kanki iya yau na baki amanar kanki daga gobene”
Qasa tayi da kanta tana murmushi yayi murmushi yace “yanzu hankalina ya kwanta matata tayimin murmushinta me tsada” juyawa yayi ya fita yana daga Mata hannu ta bishi da kallo tana masa murmushi shima yanayi mata kiss ya jefo mata ta kumayin dariya har haqoranta suka bayyana.
Hakanan akayi musu kwalliyar suka fito suka tafi gda suna zuwa gda motocin daukar amare sukazo 6:30pm suka isa gurin dinner ba tare suka taho ba amma tare suka shiga anatayi musu tafi da ihu suka isa gurin da aka tanada dominsu suka zauna daqyar yasata ta tashi suka shiga filin rawar lkcn da M.C din ya kirasu suka dan taka kadan kai ranar Umaimah taga rashin kunya a gure D.S ko kunyar mahaifiyarsa bayaji da Hajiya da suke gurin kamota yakeyi tako ina suna hotuna itadai hawaye kawai takeyi da ta rasa na meye farin ciki ko baqin ciki basu tashi ba sai sha biyu suna zuwa gda wanka kawai tayi ta kwanta tana kwanciya D.S ya kirata yana fada mata wai yau bazai iya bacci ba duk ta tayar masa da hankali ji yake kamar ya janyo gobe itadai murmushi kawai tayi masa sukaci gaba da hirarsu waishi ya matsu yaji abinda akeji.
Washe gari qarfe goma daidai na safe aka daura auran Dr Sulaiman kabir Yola da Umaimah Ahmad Hameed Shuwa farin ciki gurin Sulaiman baa cewa komai ita kuwa da aka sanar da ita an daura auran kamar yanda Hameed ya suma haka itama ta yanke jiki ta fadi hankalin gdan biki ba qaramin tashi yayi ba shidai Daddy baa gama bikin dashi ba ya dauki dansa suka wucce India ita kuwa amarya Umaimah lbr yana zuwarwa Sulaiman babu kunya ya shigo cikin gdan har dakinta ya shiga ya kuwa yi saa babu kowa ya mayar da qofar ya kulle ta bude idonta a hankali da suka kumbura saboda kuka zama yayi a kusa da ita ya dagota jikinsa yace “ni bantaba ganin aure irin namu ba sweet Ina cikin farin ciki ke kina baqin ciki yakamata ki yarda da qaddara ba duka abinda zuciya takeso take samu ba ki qaddara dama Hameed ba shine mijin da zaki qarasa rayuwa dashi ba wlh Umaimah inasonki kuma zanyi miki komai donki yarda da hakan babu saki a tsarin aurena dake aurene na mutu ka raba”
*UMMUH HAIRAN CE…* ✍
[2/1, 1:44 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍: *_GU_*
Post a Comment for "Gidan Uncle 66"