Breaking News

Gidan Uncle 75

Yanda Hajiya taga ta shigo gdanne yasata zuba mata ido sannu kawai tace mata ta bude qofar ta shiga daidai lkcn dashi kuma ya shigo gdan shima baiyiwa Hajiyan mgn ba ya shige dakinsa ya kwanta ya lura wahala zaisha sosai da Umaimah tunda ya fahimci babu digon tausayinsa a qwayar idonta amma duk da haka zai jure zai gwada tasa baiwar har ya cimma gaci.


 

Wayarsa ya dauka yayi short write ya tura mata tana zaune a bakin gado tana feeling din yayanta tana kallonsu saqon nasa ya shigo ta dauka ta bude
_Tunda na rasaki Umaimah mace ta fita a raina ki daina jin tsorona wlh ba Hameed din da bane nasamu lfy ki bani dama bloody banason komawa California batare dake ba banajin dadin rayuwa ni kadai bloody inason mu rayu tare yaranmu su rayu a cikin kulawar mu inason twins dina amana tace babansu ya bani su tun kafin a dora masa ajalinsa yayimin kyautarsu tun kafin suzo duniya ki aminci su rayu qarqashin kulawata_

 

Jikinta ba qaramin sanyi yayi da kalamansa ba wata kalma daya da D.S yayi mata ranar data haifi twince ta fado mata _“nayi farin ciki da haihuwar nan Sweet duk da inaji a jikina bazan rayu dasu ba amma banajin komai saboda Hameed yana raye_”

To dama kalamansa abinda suke nufi kenan ajiyar numfashi tayi cikin sanyin jiki da sallamawa rayuwa farin ciki wata kalmar da yake yawan maimata mata ta dawo mata.

 

_“Umaimatu ina kishinki bana fatan ko Nazir qanina ya riqe hanunki mutum daya tak nake burin bayan bana numfashi ya zama replacing dina Sweet Hameed nake nufi da ace zan iya dana halatta masa ke ina raye amma bazan iyaba course_ _inasonki sonda idan na rayu babuke zan galabaita sweet zansha wahala fiye da wadda Hameed yakeyi saboda ke dalili ni qaramar zuciya ce dani bantaba shiga tashin hankali makamancin wannan ba kiyi hqr kada ki qullaceshi wlh ba laifinsa bane sharrin qaddara ce yanzun wacce ta zama sanadin rabakun tana ina? Tana asibitin mahaukata idan ba saaba ita da hankali har abada itama ki yafe mata duk da nasani Hameed bazai yafe mata ba saboda ta cutar dashi ita duniya qaramin gurine da zaka zo ka taka rawarka ka kauce wani ya taka Umaimah ki yarda da hakan_ _watarana _muma zamu kauce mu rabu rabuwa ta har abada rabuwar da bazaki sake ganina ba”_

 

Wannan kalamai suna dukan zuciyarta dole tayi biyayya ga kalamansa wannan kamar wasiyya ce adali aqili managarcin mijinta ya bata miqewa tayi a sanyaye ta zaunar da yaran ta nufi bathroom taci kukanta me zuciya ta jima kafin ta daure ta miqe ta fito a zaune ta tarar dashi yana yiwa twince wasa ya dauki madara yana basu yana mitar anbar masa yara da yunwa bata kulashi ba ta fice daga dakin ta shiga kitchen ta zubo abinci ta zauna a dinning din tana juya cokalin Hajiya tana ankare dasu amma batace musu qalaba tanajin lkcn da Hameed din ya shiga dakin taso yi masa mgn amma ta lura duk a zauce yake wani abun ma baisan yanayi ba tarasa wanne irin so yakewa Umaimah kamar wanda tabawa ruwan nono yasha indai yana ganinta baya iya control mind dinsa har tausayinsa takeyi musamman wannan karon data lura kwata² baya gaban Umaimah.

 

Zama Hajiya tayi a parlourn tana zaune yazo ya wucceta hankalinsa nakan Umaimah yaje ya zauna a kujerar kusa da ita ya ajiye twince suka tafi harkarsu yasa hannunsa ya dago fuskarta yaga yanda hawaye kebin kuncinta gabansa ya fadi sosai ya sanya hanunsa ya fara share mata hawayen yana girgiza mata kai idanunsa nakanta yace “don Allah kiyi hqr wlh ban turo miki text din da nufin bata ranki ba bloody bani na dorawa kaina sonki ba Allah ne ya jarabceni da qaunarki tun bakisan kanki ba wlh bazan iya rayuwa da wata mace ba da zan iya kema shaida ce a yanda nake da tuni nayi aure amma na hqr na zabi na rinqa azumi akan na hadaki da wata Umaimah ke dayace matata bazan qara hadaki da wata mace ba….”

 

Daga masa hanu tayi tace “ya isheni haka Hameed ka matsamin wlh banason ganinka banason tuna baya shiyasa bana fatan sake rayuwa dakai Hameed me zaka fadamin na qara yarda dakai wacce kalma ta rage maka da zaka fadamin tayi tasiri a zuciyata ina cikin halin mutuwa ko rayuwa ina tsananin buqatarka da buqatar taimakonka lkcn da kowacce mace take samun soyayyar mijinta da tausayinsa lkcn da ya kamata kaji qaina ka tausaya min lkcn ne ka yanke shawarar rabuwa dani rabuwa ta qasqanci da wulaqanci Hameed saki biyu a lkcn da nake naquda ba lallai ne na tashi naci gaba da rayuwa ba ma nayi maka Hameed me kake tunanin zakayimin na manta da wannan abun a rayuwata Hameed wannan abun bazan taba mantawa dashi ba a rayuwata Hameed banyi rayuwar farin ciki ta shekara guda dakai ba tunda na fara rayuwa dakai cikin damuwa nake daga wannan matsalar sai wannan amma qoqarin dannewa nakeyi saboda so da tausayinka daka cusawa zuciyata Hameed bansan dadin aure a gdanka ba sai a gdan D.S wlh Hameed abubuwa da yawa idan na tuna badan arzikin zumunci ba dako gaisawa bazamu keyi dakai ba Hameed na tsani zaman aure dakai bana fatan sake shi idan ma kuma qaddara tasa na amince da sake rayuwa dakai to kasa a ranka Umaimatun daka sani da me sadaukar da farin cikinta akan na wani me qoqarin tursasa zucciyarta tayi biyayya ko bataso Umaimah shashasha da batasan ciwon kanta ba bata da choice a rayuwa sai naka Hmn Hameed wlh babu kaffara a kaina yanzu bada ita kake zaune ba na shaqi iskar yanci wata qaddarar gata ce rabuwata da qaddarren aurenka ta sanya idona budewar da bazan taba zabar farin cikin wani fiye da nawa ba”

 

Tana gama fadin haka ta miqe ta kwasa da gudu ta fada dakinta a guje ya bita yana qwala mata kira amma Ina ta datse qofar ya durqushe a gaban qofar cikin rawar murya idonsa na zubar da hawaye yace “wal…wlh duk yanda kike tunanina ba haka nakeba bloody ki bude kiji abinda zan fada miki ni kaina shaidane kin canza daga yanda na sanki bakya tausayina amma koma ya kika zama inasonki sonki ya rufemin idona banaji bana ganin kowa sai ke zan rayu dake a haka Umaimah so dangin mutuwane baya duba rarrashi so gubane kamarsu daya da madara wlh ko zaki rinqa tsinkar gashin jikina ina mutuwa Ina dawowa kece zabina sonki yariga ya illatani bana iyayin komai sai Ina tare da tunaninki Umaimah baki taba soba shiyasa baki gane so ya yakeba wlh Hameed nakine ki yarda dani bloody….”

 

Shassheqar kukan Hajiya ne yasashi waiwayawa ya miqe da sauri yana dafe da qirjinsa ya fadi a gabanta yace “haj… Hajiya ki tayani bata hqr kinsani baa cikin hankalina na saki Umaimah ba wlh duk duniya bata da masoyin da yafini Hajiya ku auramin Umaimah idan ba haka ba komai zai iya faruwa dani wlh duk ma abinda take tunanin nayi mata a baya don zalinci nasani banyi don cutar da itaba Hajiya bayin kaina bane ciwone da ubangiji ya jarabceni dashi kuma na samu lfy wlh duk yanda takeso haka zamu rayu idanma tace batason na riqe ko yatsanta ne na amince nidai naji a raina itadin tawace matata ce yafimin komai dadi Hajiya kice wani abu mana”……….

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍*
[2/4, 6:58 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍: *_GU_*

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

No comments