Breaking News

Hariji Book 3 Page 89-90

89&90
*Alheri writers asso.*

Giransa daya Na sama ya d’age mata “Sorry babbar yarinya,baki wasa dani amma kina wasa da zuciyata,beside tell me,yaushe kika kwaye mun haka,as I can see,na hango wasu abubuwa masu kamanceceniya da juna a qwarar idonki,all for me Zinariyata??”


Gabanta ne ya bada sautin Dammam!!! “Wayyo quliya Na,ina sonka bazan ci amanarka ba!” Ta fadi magana a sarari,kallon ta yayi ,da sauri ya cafki baby hibba da take yinkurin faduwa “don’t be exhausted durling” “You kindly stop plz” tayi maganar jikinta Na kyarma ,tana miqa masa hannu “Ban yarinyata ”
“Yarinyata Na wane dady ya bani amanarta plz be matured durling ,Ina maki makantacciyar qauna wuce so”
Idonta taf qwalla ta kallesa “Adnan ka rantse kana sona ,ba tausayina kakeyi ba,ka rantse kana sona ba yaran nan kake sona don suba ,ka Kula dasu ,Adnan nice fa antynka matar dadynka,wani ido kake dashi da zaka kalleni da sunan so ,Ina wasa dakai ne?!”
Murmushi yayi “Naji komai my anty a da,my baby love a yanzu,Amma kinsan me?banjin zan daina nace maki ba,bcuz Na fara sonki ,a duniya ta tun ban ta6a ganin ki ba a duniya? I felt undeniable,lokacin da naganki matsayin matar dady,amma yanzu dady has gone ,this is our destiny I love dady ,but your love is much highly special don’t trash my will ,my ambitious plz”
Dafe Kai ummi tayi kurum ta janye qafarta da sauri ta bar wajen ,da sauri ta shiga motarta ta kullo ,waigawa tayi ta kalli nannyn su twins “Aisha Ina habu ?” (Tana nufin driver dinta) “yaje sallah,wai kafin ku fito a can masallacin menene anty?”
“Aisha jeki kiramun hajjo a ciki tayi sauri mu tafi”
“Ina hibba anty?”
“Ki fita nace!” Tayi mata magana cikin tsauri da daka tsawa abunda ummi bata ta6a yi mata ba kenan.

Dafe kanta tayi tana tunanin Adnan ,har jiri take gani kanta Na Sara mata da qarfin tsiya “Ina sonka Adnan , son da ya makantar dani ganin aibunka ,Adnan banso in bayyana maka son da Nike maka saboda son da Nike maka yafi gaban a rubuta ko a fadi da baki,dont allow me explore,a and fully vomit it out , coz idan hakan ta kasance ban sameka ba,i may go into insanity…I will be original insane out of hrt uncontrollable…” Dukan seat Din driver takeyi ta baya ,tana magana da qarfin gaske.

Adnan da tun fitar Aisha ya shigo zura mata Ido yayi ,sosai yike tausaya ma Kansu duka ,saida yaga kamar bata hayyacinta sannan yayi magana da sauri “Stop Ummulkulthoom inasonki enough ,plz,No challenge nothing and no more complain ”

Waigowa tayi a kasalance ,why Na tona sirrin zuciyata har yaji ? Y?

“Ummu Ina rokonki ki soni don su Hibban ”

“Bazan iya ba Adnan,zan Zama accused ,and bazan iya juran accusation ba any more”
“Koda Abba,umma ,anty ,dady na sun amince ? Koda quliya mijinki ya barmun ke?” Zuru tayi masa da Ido ,tana kallon sa ba ko qyaftawa ,a take yaji yina qara nutsuwa a sonta ,da sauri ya janyo ta jikinsa ya rungumeta “Munason junan mu ,mun dace da juna,plz ki Bari mu qarisa da juna ki bani Kula in baki kulan da ya dace ,nasan damuwarki,bazance ki manta da dady ba ,amma zan tattalinki fiyen fiyen yanda dady ya baki a dan qaramin lokacinsa,I will give you huge out of my time ,kinji ? Plz accept as I promised” fincike jikinta tayi a jikinsa “Banson iskancin layi ” ta Galla masa harara
Dariya ya saki yina shafa cikakken gashin gemunsa kamar Na sheqau
“I like your style baby ”
Lumshe ido tayi ,batace komai ba.
“Kina sona ummi ko? Dubeni dan kyakyawa dani kamar ke,Na fa iya soyayya ,kawai ki shigo rayuwa ta ,don’t hesitate zan jiyar dake dad’in da ma’aurata ke jiyar da junansu tun daga Daren…”
“Shishhh ya isheni rashin kunya”
“Naji to fada mun kina sona ? Zaki aureni ?”
Noqe kafadan ta tayi “Sai ka ce mun Anty”
“San girmanki ya shahara kulthoom ,I can’t”
“Shikenan qaryan jin Kai gareka ,fitarmun a mota ”

“Oh Allah !,anty! Anty!! Anty!!!…Na fada ce kina sona !”

Dariya ta fashe dashi ,da ta Dade rabon da tayi “ya Isa zan ce amma sai ranar da na yaye su Hibban”
“Kina nufin sai kin yaye su Hibban zamuyi aure”
“Yes of course”
“Hmmm ummi zaki kasheni ,Allah zan iya yi maki aika aika , Right from now,inada desires akan ki dannewa nikeyi ,ki yarda ai auran mu hade da na hajjo tarewa Randa kikaso zan baki wannna damar ” zata sake yi mata gardama hajjo tazo tayi knocking glass

“Hajjo kun gama ?”
“Eh ta bude boot ma’aikatan wajen suka zuba masu kayan da suka siya ”

Fita a motar adnan yayi ,ya kewaya ,yayiwa hajjo magana a sirrance “Hajjo ki taimakeni ummi ta shiga motar Na ,ku ku taho a nata ”

***
Adnan ya rigada ya zamewa ummi maqale mata ,har wani fadawa tayi saboda zullumin Kar wasu su fahimci halin da suke ciki ga soyayyar su kullum qara qarfi yikeyi , though ita har yanzu tana nuna denying
Abbah ya samu da maganar ya ringa rarrashin sa ,ya toshe masa baki da kudi amma ba da sigar bribing ba,a’ah saboda ya Zama fan dinsa
Aikuwa ya Zama ,don haka ya haukata gidan alankatafir ummi saita auri adnan tarewa daga baya ,ummi zuwa tayi ta samu umma “Umma wallahi wannan set up din adnan ne ,ya siye abbah ,kunsan shi akan kudi zai yi komai” barshi ni kuma Ina partynki indai baki so ba me matsa maki,eheee”
Adnan kam tunda abbah ya bashi assurance ,zuwa yayi ya fara cinikin gida amma a Abj don yace bazai iya rayuwa a matsatsin kano ba sunada zafi,gida kuwa ya siya Unguwa guda ,ya sa aka qawatashi daidai da tsarinsa wane Na quliya ,Ana sauran kwana uku bikin su hajjo Dangin quliya suka sauka don ya shaida masa maganar daurin auransa da ummi tarewa sai tayi yaye ,wai kawai yinason ya Kula da qannensa ne sosai
Sunji dad’in wannan al’amarin sannan sukayi ta shi masa Albarka
Duk wannan bidirin ummi batasan da ita za’a daura aure ba , gabadaya abbnsu ya Zama dan bala’i bala’i haka

***
Uwale yau ta daukesa a ranar da zata baza kalar rashin mutuncinta don a haqe take da uwargidan ta
Tun sanda take jera abinci a inda suke cin abinci take Lura da ita ,tana ganin ta kusa gamawa ,taje tayi wanka tayi masa gayun kansa tamkar ita keda mijin
Saida maiwada ya shigo sannan ta fito ,sanye da bomshort da wata crazyn riga ,yayi bala’in kar6anta hips da albarkatun qirjinta sunyi cifcif ,Zama tayi ta fara zuba abincin mijin ba tareda ta Kira uwale ba
“wai ina baby?”
“Au dama kanada qaramin yarone a gidan Bansaniba da kake Kira baby?”
“A’ah jamcy Nike nufi ”
“Ai wai ,uwale? Tana dakinta mana”
A hankali ta shigo qafarta sanye da takalmi indoor

“oyoyo mijina ,Alfaharina,mai martaba ,sadaukin birnin zuciyata ,ka dawo lafiya ,ya office ya mutan …”

“Ke dayalla gaja,daga dawowa naji kin hau zuba sai kace bishiyar kurna, ni banson haqa caaa caaa caaa ,ko hadiyar miyau BAKIYI…”

“Hmm hmm hmm ,My love kace ta kiyayeni ,daga kawai nayi kewarka ,sai kanaji tana zagina baza kayi mata magana ba,haka fa take hantara ta in baka nan ,Sai dai in qunshe a daki ban iya fitowa ,anyi gaskiya anmun adalci dan Allah?”

Kurum saita fashe da kukan kissa
Murmushi yayi ,sarai yasan uwale case ce ,yasan tafi uwargidan sa masifa ,inama za a hada da baiwar Allah ,yina murmushi yakai cup din plain ruwa bakin sa ya kur6a
“ke kuwa duk jarumtarki watannan abar zata gasaki haka? To kiyi haquri,ke kuma karki sake”
Jinjina kai tayi ,ta zuba masa abinci a plate ta tura masa gabansa ta 6alle bakin exotics ta fara tsiyaya masa a glass cup
Wani tuquqin kishine ya isheta “Magana fa nikeyi?”
“Ohhooho ,wallahi Na gaji uwale plz,ki bari yaci abinci ai anjima kafin mu kwanta zai shigo yayi maki saida safe”
“ke me bakin ja6a,naci kaza kazanki,da mijina nikeyi ba ke ba ,jikan baba me wanki ,tsoho yayi gado a wajansa tsohuwa Na sukolon mata da yara sai anyi za aci abinci …”

A take fada ya sarqe sai dambe ,takuwa hada duk warmers din da lemu kan ta hakadesu suka sheqe da gangar ,a sukwane ya miqe da qyar ya rabasu
A zuciye yaje wajen fridge ya dauki wani raguwar exotics rabi ya kafa Kai ya qwalqwale ,yayi hanyar dakinsa yina sababi “Banson gani kowa duk ku tafi kowa ta kwana a dakinta ”

Gwalo tayi mata “woo kece da asara”
Dakinsa ta shiga itakuma tayi zaune a falo ,a karce ta fito ya jefota da takalmi ,aikuwa uwale ta bushe da dariya

Shaf shaf taje tayi masa soyayyen Irish da plantain da qwai ,ta hado masa da qaramin mug Na coffee yasha maganin qara sha’awa saida ta ninninka doses din yanda zai masa saurin aiki.

A tray ta jera da Goran ruwa ta shiga ,daure fuska yayi “jamila ki fita yau kin qona mun rai ,tunda kema bakiso a zauna lfy”

“Wallahi nayi nadama mijina shiyasa nayi gaggawar yi maka sassauqar abinci ,kayi zaman ci kafin in hado maka lafiyayyen dishes ” tsaki yayi ya hau hura hanci ,bata damu ba taje ta ajiye masa

“In bazaka Sha ba ,ga coffee kasha,ko me kake so in dafa maka? Iyanba kaga shalele ,tauraro mai haskawa ,Allah dai ya taimake ka.. bari in Nemo maka wani abincin to,amma don Allah dai kayi mana afuwa kaji mijina ”
Bai tankata ba amma ya sauka don zawon bakin uwale kata’ine,

“Wannan abun da kika yi munne zan kuma neman abinci ? Ya isheni ,Allah ya kaimu safe Kar ku sake ,ki bi eruwarki

Jinjina tayi masa kamar wacce take gaban sarki ,ta dunkula hannu “Allah ya taimake ka”
“Ki zauna to kin min tsaye”
“Godiya Nike ” ta fada tana fadada fara’arta
A nutse ya dauki fork ya soma ci ,a hankali ya fara sakkowa kowa dai yasan mayunwaci dama mafadaci ne , yinajin cikinsa ya dauka ya fara janta da fira ,tas ya shanya cofeen ,minti kadan kuwa ya fara bin jininsa

Rolling eyes dinsa ya fara yi ,daga gayya take juyi ,sosai ya fara Zama wani kamar dan maye ba shiri ya miqe ya fara cire kayansa ,tana kuwa ganin hakan ta fara hada kayan zata fita

Da sauri ya janyo ta yina shinshinan ta “ina zaki jamcy”
“Barci ka manta ,ba ni ke dakai ba ?”
“Amma ai dai gindina naki ne ko?”

No comments