Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

In Bani 47


47….

 

_masu fitarmin da novel waje suda Allah_

_Zaki tura 300 access fee ta 3107021073 first bank aisha Muhammad in kinason this book, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting_

_you can also send MTN card na 300 for those da basu da account number ta watsapp number na 07012181461_

_karki karanta in baki biyaba, in kika karanta ina binki bashi pay anan or pay achan_

 

“Mamiii” ya kwalama Mami kira da karfi sosai yana wani irin kuka yana kokarin fizge hanunshi daga na Abie, fitowa Mami tayi daga part dinsu adan rude tana waige waige batare datama lura da inda yay parking motar ba, cikin kuka sosai ya kwalama Mami kira. “Mamii” juyowa Mami tayi ta gansu , ganin Abie da rabonda tasashi a ido yau kwana uku kenan najan Aadil da babu kaya ajikinshi saidan gajeren boxer yana kokarin turashi a mota da karfi da yaji yasa da gudu tayo wajen tana salati. “innalillahi wa innailaihi raji’un, Abie lafiya, me Aadil yamaka? Ina zaka da shi ahaka, menene?” tun kafin takaraso wajen take jero uban tambayoyin nan, tana karasowa wajen Aadil ya daddage cikin kuka sosai ya fizge hanunshi tareda tura Abie yakoma bayan Mami da gudu ya rungumeta ya kulle hanunshi akan cikinta yana kuka sosai, yanda Mami taji kirjinshi na bugawa yana kuka yama kasa magana yasa ta dago kai ta kalli Abie dayake ma daga Mami har Aadil din mugun kallo, cikeda tashin hankali Mami tace “Abie mai Aadil yama haka kaji yanda kirjinshi ke bugawa kuwa ai wanan saiya iya fadi ya mutu, menene Abie ina zaku ina zaka kaishi ahaka babu kaya ajikinshi?” cikin kumfar baki sosai Abie ya nuna bangaren Aadil din yace “zan rabashi da shegiyar yar iskan yarinyar dakuka auramai ne, ni dama tun farko bantaba son auren nan ba aka nunamin iko da isa nida dan cikina amma aka nunamin banda ta cewa akan rayuwanshi, kamasu nayi fa yanzun nan tana koyama Aadil dinmu lalata ke kinga abubuwan datake mai kuwa saisa zan tafi da Aadil din kafin ta kaimu tabaro tana koyamai irin wayan nan abubuwan ai duk macen dayagani danneta zai dingayi yana duramata ciki kindaisan condition din danki kindaisan ba hankalin kirki gareshi ba, bazan zauna raye ba idanunna biyu, da karfina da lafiyata inga wata mace nakoyama d’ana lalata ba in kyale, dis innocent boy yaushe ya girma dazai fara irin wanan rayuwan” cikin kuka sosai Aadil dahar lokacin bai dawo daidaiba yace “he beat my Hamida Mami, he strangled her she almost faint” kallon Abie Mami tayi da idanunta dasuka kada tace “Abie da girmanka zaka fada dakin danka da matarshi at this hour of the night?” tai maganan ahankali saikuma cikin harsh tone tace “kace lalata? Wani irin lalata kuma da auren su, auren sunna da dumbanim jama’a sun shaida ne zakace haka? And inda ace Aadil yanada halin danne mata ai daba tun yau yafara ba dan naga batun yau yabalaga bako, shekaran Aadil talatin aduniya, uku da sifili Abie ba uku kadai ba dakake neman maidashi yaro dan shekara uku, daka fito dashi ahaka da daddaren nan karabashi da matarshi ina zaka kaishi? Wai anya lafiyan ka kalau kuwa Abie am worried about you fa, rabon dana saka a ido yau kwana uku daga shigowan ka kuma sai wanan, kaga nan tsakar gidane akwai yan aiki a part dinsu, kaga Baba ba ishashen lafiya gareshi ba karyaga muna hayaniya hawan jinin shi yatashi, Aadil wuce mutafi na rakaka part dinku” tai maganan tana zare hanun Aadil din daga kan cikinta ta rikeshi tana juyawa da zumar su tafi, wani irin unexpected fizgowa Abie yama Aadil da Mami tarike yace “na rantse miki da ubangiji yagama rayuwa da Hamida idan ke kwakwalwarki batasan miye lalata ba ni nasani because am a Man, and i can not risk karuwan yarinyar dakuka auromai tabatamin d’ana ba” yay maganan yana yin hanyar mota dashi Aadil na turjewa yana mikama Mami hannu, da sauri Mami tabisu tarike bayan rigan Abie tace “wai wat is wrong with you Abie? This is not you fa, bahaka kake ba, inma lalatan sukayi ba a dadin ka bane, at least zamusa ran watarana zamuga jikokin Aadil dinmu ko, to meme amfanin auren damuka mai mawai? Badan yasami natsuwa ajikin matarshi bane sanan su hayayyafa ko, so let go off this boy you know clearly Aadil can not live without me gakuma Hamida dayake so kasan idan karabashi damu u are just killing him ne completely” juyowa Abie yayi yana rike da Aadil din yama Mami wani mugun kallo cikin fushi da daga murya yace “sakeni, sakeni nace kodan kinga ina cikin gidan ubanki ne yasa kike feeling you have d right to grab my shirt like this” wani irin kallonshi Mami tayi dan as far as she knows Abie baita regarding Baffa as ubanta ba saida ubansu, mahaifinsu, baban su, amma yau jibi abinda kefitowa daga bakinshi, cikin wani irin mugun tsawa Abie yace “sakenmini raga kafin namiki abinda bantaba mikiba tsawon aurenmu shekara talatin da daya yanzu” rawa muryan Mami yafara ita tsoron Abie ma take hakan yasa takara rike rigan nashi da kyau tace “not until kasaken mini d’ana nima sanan zan sakeka” sakin Aadil Abie yayi cikin fushi daidai lokacin Baffa nafitowa daga shashinshi sabida hayaniya dakuma kukan Aadil daya cika ko ina na gidan, wani irin wawan Mari Abie ya dauke Mami dashi ya fizge hanunta daga riganshi ya murde hanun da karfi yana mata mugun kallo, wani irin kara Mami tayi cikin azaba Baffa yay salati yana karasowa wajen da sauri. “assha, assha, subhanallahi, Abdullahi me haka? A tsakar gida kuke irin abinnan” ture Mami yayi cikin tsananin tsana tai baya tafadi akasa ya finciki Aadil dake mugun kuka yana dukanshi abaya sabida murdema Mami hannu dayayi yawani irin turashi abayan mota da karfi da yaji ya rufe motar yabude gaba ya shiga yay locking motar ya danna wani jarababben horn mai gadi daketa kallon drama tun dazu ta window dakinshi yafito danya bude gate, Baffa yakaraso wajen yana dogara sanda ya tsaya ta wajen window yana kiranshi. “Abdullahi, Abdullahi, Abdullahi bakaji nane, ina zaka da daddaren nan?” cikin fushi yaja glass din motar sama yay reverse batareda ya kalli Baffa ba yafita daga gidan Aadil na dukan glass din motar sosai yana kallon Mami da Baffa da Hamida daya hangota a labe chan gaban shashinsu tana wani irin kuka mai cin rai.

 

Juyowa Baffa yayi ya kalli Mami dake zaune dabas akasa tana kallon hanunta dahar ya kumbura nan da nan yace “me haka kukeyi a tsakar gida Maryama? Tarbiyan da mahaifiyar ki tabaki kenan kafin tarasu chachan baki da mai gidan ki har kina rikemai riga iyye Maryama” share hawaye tayi tamike tsaye da kyar tace “bahaka bane Baba” nan takoromai abinda yafaru daga A to Z, salati Baffa yayi yadaga kai ya kalli bangaren su Aadil din, hango Hamidan tsaye ta rabe ajikin bango tana kuka sosai yasa yace “tashi Maryama yi shiru, je, jeki lallaso ta, dubo mana diyar mutane, bari naje nakira Sulemanu karki damu komi zai wuce kinji” ahankali tace “to Baba” ta tashi tana kakkabe jikinta tai hanyar shashin su Hamidan, tsayawa tayi agaban Hamidan da bama tasan da zuwanta ba, ahankali ta daura hanunta mai lafiya kanta, dago jajayen idanunta tayi ganin Mami ne yasa tafada jikin Mami tasaki kuka sosai jikinta na bari tace “am sorry Mami, am sorry” rungumeta Mami tayi back tanajinta kaman yarta mace tace “shiii ya isa” tai maganan tana dagota daga jikinta ta tallabo kanta tana kallon shatin hanun Abie akan fuskarta da wuyanta dayay jajir, ahankali tace “innalillahi wa innailaihi raji’un, am sorry Hamida, am sorry for everything kinji, ke amanar mu ce daga zuwanki gidan nan look at what happen to you, yi shiru muje dakina na gasa miki wajen na shafa miki rub” tai maganan tana share mata hawaye ta rufo musu kofar part dinsu sanan tarike mata hannu suka tafi part dinsu, bedroom dinta Mami ta shigar da ita ta zaunar da ita akan gadon tawuce ta shiga bathroom bata wani jima aciki ba tafito dauke da bowl da karamin towel aciki tana kallon fuskar Hamidan tanajin wani irin bakinciki, tsoro duk yakamata tana addu’a Allah karya kawo yan uwanta gidan nan kwanan nan inba hakaba mezata ce musu, meya sami yarsu, zama tayi a gefenta jikinta duk rawa yake ta matso towel din daga ruwan zafin tadaura wuyanta da hanun Abie yafito sosai tana cewa “sannu kinji daughter dan Allah kiyakuri” saida tagama sanan tamata na fuskan takawo rub ta shafa mata sanan ta gyara wurin ta dawo rike da paracetamol da ruwa tabata tasha tasake rungumeta feeling guilty sosai akan abinda Abie yama yar mutane ahankali tace “nakawo miki wani abu? Nahada miki smoothie?” girgiza kai tayi ahankali hakan yasa Mami ta kwantar da ita taja bargo ta lullubeta dashi tace “get some rest kinji, don’t worry Aadil zai dawo” gyadama Mami kai tayi tana hadiye kukan sabida Mami, Mami ta shafamata gaban goshi tana sauke ajiyan zuciya tana kallon yanda fuskarta da wuyanta sukai jajir har baccin dole yay gaba da Hamidan. Sai alokacin Mami tafarajin zugin hanun nata ta tashi ta shiga bayi tasaka hanun acikin ruwan zafi sanan tafito ta mitsike da rub tadau wayarta ta kashe wutan dakin tafita daga dakin ahankali ta wuce ta shiga dakin su Aadil ta zauna akan gadonsu tabuga uban tagumi.

 

She taught yanda suka aurama Aadil Hamidan nan dayake mugun so sunyi solving 90% of their problem sauran 10% din zai zama na yanda zasu nemamai magani ya warke ne, wanan problem din Abie daya kunno musu kai kumafa, yanzu ina yakai Aadil? Wai da gaske abinda yace suda Aadil har abada did he really mean it? Wat did he mean? Wat is Abie up to? Aadil bai isa yataba matarshi bane or wat? Ina yakai Aadil? Tasan yanzu ko ina Aadil yake kuka yakeyi bana wasaba yana kiranta, hakan yasa tafashe da kuka sosai bana wasaba takai kusan 20min tana kuka ganin kewan yaranta da tunanin Aadil din na neman mata illa danhar kirjinta yafara zafi yasa tadau wayarta ta kunna tai dailing number Aabid.

Post a Comment for "In Bani 47"