Breaking News

Jarabta 13


13…

Juyowa kakkyawar matar tayi tace “Islam yaushe kika tashi Farida tacemin kanki na ciwo sannu ko, kinsha magani?” Gyada mata kai tayi sanan takara matsowa kusa da Mum tai wani kini kini da fuska kaman zatai kuka da murya chan kasa dan tasan Allah yama Anty Hindu baiwar kunne tace “Mum wai mesa tazone, yanzu dukzata damu mutane da masifa” murmushi kawai Mum tayi ta girgiza kai tana arranging abincin a babban tray mai kyau tace “yayar mahaifin nakine kike cewa haka akanta ko yaran zamani, matsamin kiga na wuce jekiyi salla” fita Mum tayi ta barta a kitchen din, fitowa tayi takoma sama tana shiga daki Farida ta fashe da dariya tace “our Baba sister don land again” tsaki Islam tayi tana balle boturan abayan datasa Farida tace “wlh ko yau datazo jinayi kaman inyi kuka shikenan yanzu mun shiga uku” abayan Islam ta wurga akan gado tai hanyar bathroom Farida tace “Islam wai dan Allah mesa Anty Hindu batason muna kiranta dawani suna kaman irin su Mama, Inna ko Goggo tunda dai yayar daddyn muce amma saidai muce Anty Hindu” hararan ta Islam tayi tace “go and ask her” tabude bathroom tashiga batare data karabin takan taba, daga murya Farida tayi tace “okay nikikema iskanci ko next time bazan rufamiki asiri ba wlh” daga bayi tadaga murya tace “eh karkiyi din” dariya Farida tayi dan tasan abinda zatayi. wanka tayi tareda dauro alwala tazo tai sallan magrib sanan ta kalli Farida dake daddana waya tace “Daddy is back zomuje muyi dinner” sakkowa Farida tayi suka sauka kasa, afalo aka zazzauna yara mazane manya guda uku biyu manya sai karami da bazai wuce 5 years ba akan cinyar Daddy duk ana zaune anacin abinci, gaishe da Daddy sukayi ya amsa musu sanan suka zauna kusa da Mumy, rice ta zuba a plate da pepper soup na goat meat, spoon tasa a abincin tanata wasa dashi takasaci tunanin abinda yafaru yau kawai take, tunda ta sakko Daddy ke lura da ita, dan gyara murya yayi yace “Islam” da sauri ta dago kai ta kalli Dad ahankali tace “Na’am Daddy” “meke damunki?” murmushi tayi da sauri ta girgiza kai tace “bakomi Daddy kaina ke ciwo har yanzu” Yayan ta Abdallah dake gefenta mai kimanin 25 years ne ya kalleta yace “kinsha magani?” gyadamai kai tayi, murmushi yamata yace “eat to ko kadanne” rice din tadebo takai baki tafaraci.
A massallaci suka fara tsayawa sukai magrib sanan suka wuto gida. Part dinsu suka wuce, direct bayi ya shiga yay wanka yafito sanye da bathrobe white ajikinshi ganin Yusuf baya dakin hakan yasa ya zauna akan kujera lumshe ido yay nayan sakkanni da sauri ya bude tareda fuzar da iska tashi yayi yaje gaban wardope ya canza zuwa milk color jallabiya, tsayawa yayi agaban madubi yadau turare a fesa, wayar shi yagani dake jikin madubi hakanan yaji yanaso yakira Ammin shi, daukar wayar yayi yakoma kan kujera ya zauna yay dailing number Ammi ba karamin mamaki Ammi tayiba dataga kiranshi na shigowa ba, ringing biyu ta dauka cike da murna tace “Son” har cikin ranshi yaji wani irin natsuwa, ahankali yace “Ammina I missed you” share hawayen daya zuboma Ammi tayi da sauri azuciyar tako godiya takema Allah, Allah na godema daka amsa addu’a ta, ya Allah kadawo mai da farin ciki da walwalan shi back, ka bashi mace tagari wacce zata maye gurbin Aisha. “Ammina are you there” da sauri yace “yes Son, ya kake hope kanacin abinci sosai ko” Ahankali yace “eh” murmushi sosai tayi tace “are you okay” shiru yayi baice komiba cikin wani irin muryan lallashin yaro tace “how about tomorrow kayi your two fevorite thing, read your Quran, and kaje ka buga kwallo ko kaje stadium ka kalli kallo anyone dakayi is okay” murmushi mai kara yay tunawa da dafa Ammin ce ke masifa duk idan yaje kwallo, murmushi yasake yi yace “okay Ammi bari naje nai salla” katse wayar yayi yatashi yafita dan zuwa massallaci.
Washegari da safe yadade yana karatun AL qur’ani da muryar shi mai dadi, sai wajen 9 yarufe ya ijiye haka nan yaji kaman ancire mai wani nauyi dake damunshi arai, yajuya ya kalli Yusuf dake bacci abinshi, bathroom ya shiga yay wanka yafito ya shirya cikin brown shirt, short sleeve ne hanun rigar ya kama muscle dinshi hakan yakara bayana girman muscles din, dogon black jeans yasa dayamai kyau sosai ya dauko turaren shi ya fesa, ya zira takalmin shi Prada, agogon da Eesha ta bashi ya dauka daga gaban mirror, shafa agogon yayi yay shiru yana kallonshi, ahankali ya daura ahannun shi sanan yadau car key dinshi da waya yay hanyar fita daga dakin, da Goggo yacikaro tana dauke da tray hakan yasa ya karba tace “ina zaka haka?” komawa dakin yay da tray din tana biye dashi abaya yace “inaso nai aski ne” washe hakora tayi danba karamin dadi tajiba tace “toai saikayi break ko, kaga dakaina fa a hadama, ina Yusufa” muryan Yusuf sukaji daga bedroom cikin bacci yace “tsohuwar nan kidena batama mutum suna, niba Yusufa aka yanka rago aka samin ba” hanyar bedroom din Goggo tayi tace “uwar kace tsohuwa, katambayi Sama’ilan koni saida na yanka maka rago da aka haifeka” da sauri Yusuf yaja bargo ya rufe kanshi jin ta shigo bedroom din, duddu Goggo ta zubamai Abaya tace “dan kan uba” ihu sosai Yusuf yayi abin yabama Khaleel dariya, cup din shayin ya ijiye yadau one slice bread ya shafa cheese spread dake dakinsu yaci, da tissue ya share baki yay murmushi jin Goggo da Yusuf nata daru yadau wallet dinshi yasa a aljihun bayan wandon shi yafita daga dakin.
Wani babban barbing saloon yaje aka mai aski da gyaran fuska ba karamin kyau yayiba sanan yabiya kudin yabar shagon, ganin he is running out of fuel gashi baida enough cash atare dashi yasa yay parking agaban wani ATM ganin akwai 2 people infront of him yasa ya tsaya ya jingina da motar shi yana kallon titi, ihu yaji hakan yasa ya juya da sauri, wata yarinya yagani ta fashe da kuka tana nuna wani guy dake gudu ga jakar ta a hanunshi tana cewa barawo ya kwacemin jakana.
[6/11, 9:19 AM] Maman Jedda: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

No comments