Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Kanwar Maza 5

P5

Sak suka yi gaba ɗayansu, lomar da Yaya umar ya haɗiya ya ji taƙi wucewa tana kai komo a wuyansa kamar zata dawo. Amma ya basar kamar bai san me suke faɗa ba.

Huzaifa kuwa tsam ya miÆ™e yana faÉ—in “Ai sai da na ce kar ki saurareta ki ka Æ™i, sai ku san abin da zaku gaya mata” yana maganar ya bar tsakar gidan.
Mama ta rasa mai zata cewa Ruma da hankalinta zai É—auka, sam yarinyar bata tunani dai-dai da shekarunta.

“Wai ya na ji kin yi shiru? Me kuma nayi?” Ta yi maganar cikin taÉ“ara.

Cikin Æ™arfin hali mama ta ce “Ke a ina ki ka ji wannan kalmomin da ki ka tambayeni?”

“Mama ya kuma ki ke tambayata bayan nima tambayarki nayi”

“Ki amsa mini dan ubanki” mama tayi maganar a hasale.

Ta É—an cuna baki sannan ta ce “Ba wani ne ya gaya mini ba, kece ki ke jin radiyo ranar, na ji ana cewa ayi wankan janaba idan aka yi ko me? Oho na manta shi ne nake son na san meye janaban, kuma meye wankan. Shi kuma fayÉ—e idan aka faÉ—a a radiyo sai na ga hankalinki ya tashi kina girgiza kai kina Allah ya tsare zuriyar musulmi baki É—aya, shine nake son na san menene?”

“TirÆ™ashi, aiki ga mai Æ™areka mama Allah ya bamu alkhairi ” Yaya Aliyu ya faÉ—a yana Æ™oÆ™arin shigewa É—aki.

Yaya Usman ya ce “Kuma duk abin da ake faÉ—a a radion babu wanda ki ka riÆ™e sai wannan?”

Ruma ta ce “To ai akwai wasu ma, mantawa nake yi ne sai yanzu na tuna”

Mama tayi ajiyar zuciya ta ce “Kina jina ko Ruma?”

“Eh ina jinki”

“Yauwwa, zan gaya miki zan miki bayani, amma ba yanzu ba sai an kwana biyu, yanzu ko na yi miki bayani ba zaki gane ba, kuma nan gaba ko ba a gaya miki ba ma, zaki gane da kan ki”.

Cike da yarinta ta ce “Nan da kwana biyu ranar asabar kenan, in Allah ya yarda zan tuna miki ki gaya mini”

“Ba wanna kwana biyun nake nufi ba hansai, sai kin Æ™ara girma da hankali”

Cikin mamaki Ruma ta ce “Yaushe kuma zan Æ™ara girman da hankali, wancan karon ma fa na taÉ“a tambayarki menene MATA MAZA, ki ka ce mini sai na girma, na tambayeki menene haila ki ka ce mini ba yanzu ba, amma da zan yi wani abun sai ki ce ina girma amma bana hankali wane irin girma ki ke son nayi to?”

“Ke tashi ki wuce ki kwanta dan uwarki, kawai kin saka mutane a gaba da tambayoyinki na shirme, ko a gidan uban wa ki ke jiyo wannan manyan maganganun oho miki, wuce kan na karya ki biyu, ba zaki tambayi abu daidai da hankalinki ba sai wanda ya fi Æ™arfin kanki” sai da ta kalli in da Yake zaune yana bata umarni, bayan da fari yayi kamar bai san me suke yi ba.

A hankali ta tashi ta nufi É—aki, tana tunanin menene aibun tambayarta?.

Tafiya ta yi ɗaki, ta gyara shimfiɗarta ta kwanta, tana tunanin meyasa kullum tayi tambaya sai ace mata ba yanzu ba sai an kwana biyu, ko ace wai tana tambayoyin da suka fi ƙarfin ƙwaƙwalwarta me hakan yake nufi kenan?. Da wannan tunane-tunanen bacci yayi awon gaba da ita.

Da safe tana kwance tana baccinta, duk samarin gidan sun gama komai, har abin karyawa, Kasancewar Asabar ce Ruma tana ta baccin asara, ba aikin fari balle na baƙi, har ƙasan ranta tana matuƙar jin daɗin rashin zuwa makarantar allo da ba ta yi, saboda tana samun isasshen lokacin bacci.
Ji take ina ma ace bokon ma ta daina zuwa, idan tayi baccinta ta Æ™oshi da yamma ta kfa suyar wainar fulawa a Æ™ofar gida ta tara ‘yan kuÉ—aÉ—enta.
Baccin yayi mata daɗi, tayi nisa sosai a duniyar mafarkai kala-kala, ta ji kamar daga sama ana taka mata ƙafa.
Buɗe ido tayi a hankali, amma taƙi motsawa, tana son ta tabbatar da a zahiri ne ko duk cikin mafarkin ne.
Ji tayi an kuma zungurarta da Æ™afa, ba tare da ta waiwayo ba ta ce “Wallahi Huzaifa zan maka rashin mutuncin da baka taÉ“a tunani ba, kar ka sake takani”
Bai ji kashedin ba, ya sake haurinta da Æ™afa, “Allah ya isa wallahi, kuma ba zan tashi ba” tayi maganar tana sake dunÆ™ulewa a wuri guda.

Ƙashin bayanta ya kuma daka da ƙafarsa, ta yinƙuro a matuƙar zafafe, da nufin ta kafa masa haƙora ko a ina ne, amma me tayi tozali da Umar a tsaye a kanta.
Jikinta ne ya hau tsuma, ta ma rasa me za ta yi, ko ta ce.
Shiru yayi yana nazartarta, daga bisani ya ce “Ki tashi ki je ki ki yi wanka ki karya ina jiranki, kuma idan ki ka É“ata mini lokaci kin san sauran”

Saroro tayi tana kallonsa, da ba ta gama fahimtar me yake nufi ba.

“Za ki tashi ko sai na yi ball dake?” Cikin hanzari ta tashi, ta É—auke katifarta ta nufi banÉ—aki tana mamakin to ina zasu je, kar dai boarding É—in zai kaita kamar yadda ya ce. Gabanta ne ya faÉ—i ta fara tunanin ko ta gudu.
Kai tsaye ta nufi banɗaki, tana shiga ta tarrar da an haɗa ruwan wanka, ba tayi tunanin ko ruwan waye ba, ta rufe ƙofa ta hau wanka da shi.

Yasir ne ya nufo banɗakin da sauri, wuyansa ɗauke da soson wankansa, zai shiga banɗaki saboda ya kai ruwan wankansa, amma yana zuwa ya ga ƙofar a rufe.
Iya Æ™arfinsa ya hau dukan Æ™ofar yana faÉ—in “wani É—an rainin hankalin ne ya shiga bayan na kai ruwa?”

Gyran murya tayi masa, tsaki ya ja ya ce “Ki hanzarta zan yi wanka na fita na kusa makara.
Tun yana saka ran zata fito har ya tashi ya fara zaginta yana bugun ƙofar.
Ba ta da tabbacin wankan da tayi ta fita, ta buɗe ƙofar banɗakin, zagi ya dinga surfa mata, bai kai ga rufe baki ba, idonsa ya sauke a kan bokitin da ya haɗa ruwa, Ruma ta zubar da komai.

A hasale ya zura hannu ya janyota tsakar gida ya ce “Wallahi yau mai Æ™watarki sai Allah, na zuba ruwa na kai zan fita makaranta kina can kina bacci, amma ki zubar mini”.
Babu alamar nadama ta tsuke fuska ta ce “To ba Yaya Umar ne ya ce nayi wanka ba”

Wani ranƙwashi ya yi mata a tsakiyar ka, da azabar zafinsa ya sanya ta durƙusa a kan gwiwoyinta, tana sakin wani irin kuka mai sauti.

Yaya Umar ya É—aga labulen taga ya leÆ™o ya ce “Ƙyaleta tun da ka daketa” ba Æ™aramin É“aci ran Yasir yayi ba, dan niyyarsa sai ya yiwa Ruma dukan da duk taurin kanta sai ta bashi haÆ™uri.

Kasa karyawa tayi saboda kuka, tana tsaye tana duru-durunta, Umar ya shigo hannunsa riÆ™e da leda ya miÆ™a mata ya ce “Maza ki shirya ki wuce mu tafi”

KarÉ“ar ledar tayi tana duddubawa, uniform ne na islamiyyar su Huzaifa, makarantar da ta ce ko aljanna ake rabawa a cikinta ba zata yi ta ba, saboda azabar tsaurinsu, asabar da lahadi tun tara sai biyar ake tashi, ba a fashi balle makara, ga haddar Alqur’ani ake yi da gaske ba wasa ba.
Saroro tayi tana kallon Yaya Umar, cike da rashin fahimta amma ta kasa yi masa Magana.

Wata uwar harara da ya yi mata ne, ya sanya ta shiga É—akin Mama, ta saka uniform É—in jikinta sai tsuma yake yi, ita ta san har ga Allah ba zata iya zaman makarantar nan ba.
Mama dai ba ta ce musu kanzil ba, ya tasa ta a gaba suka tafi.

A zuciyarta tana ta addur Allah ya sa makarantar suce ba zasu karɓeta ba, bata tunanin ko su Huzaifa sun san za a sakata a makarantar su, dan da sun sani cewa zasu yi basu yadda ba.

Tun da suka shiga makarantar, tashin karatun Alqur’ani kawai ka ke ji, daga kowacce kusurwa, kuma da alama É—aliban makarantar a nutse suke.
A ofishin shugaban makarantar aka titsiye Ruma ana yi mata interview, amma ba abin da ta iya, izifi biyun da aka yi mata tambayoyi da ƙyar ta kai.

Umar ya shiga tunanin tsawon lokacin da Ruma ta shafe tana zuwa makarantar allon nan, me take yi da ta kasa izifi biyu.

Ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, ya hau ta da faɗa a gaban mutane.

Cikin kuka ta ce “Wallahi yaya na iya karatu”

“To uwar me ki ka iya, kin kasa izifi biyu”

Ta É—an yi shiru sannan ta ce “Eh na iya, amma ba a allona na rubuta na iya ba, na allon wani almajirin malam babba ne, idan aka Æ™ara masa nake iyawa, ni kuma sai na kasa nawa”
Murmushi malamin yayi ya ce to biya mu ji “Tiryan-tiryan da Æ™ira’ar warsh, take karanta suratul Yusuf, ko tuntuÉ“e babu”

Shugaban makarantar yayi mata kabbara ya ce “Ahh gaskiya ‘yar baiwa ce, zamu san a in da yakamata mu sanyata, daga islamiyyar har tahfiz É—in, zaku ga sauyi in sha Allah zata yi karatu”

Yaya Umar ya ce “To masha Allah, haka muke so” aka saka wani malami ya kai Rumaisa aji.
Tare suka fito da Yaya Umar, ya dubi Ruma ya ce “Ga makaranta nan na kawo ki, idan kin ga dama kiyi karatu, idan baki ga dama ba nan ma ki yi musu halin naki, kiga abin da zai biyo baya” ta sunkuyar da kai kamar ta Allah, yayi faÉ—ansa ya gama ya tafi.

Gaba É—aya ba tayi murna da zuwa makarantar nan ba, haka aka kai ta aji ta nemi wuri ta zauna.
Gaba É—aya É—aliban sun mayar da hankali, suna ta zuba karatu, Ruma kuwa sanyin fanka ne ke nema ya sanyata bacci.

“Ke ya ba kya karatun?” Cewar malamin da yake kula da karatun nasu.

Kallonsa ruma tayi, shima uniform ne a jikinsa na É—alibai, amma ya tsaya zai yi mata iyayi.

“Sabuwar zuwa ce ni, ban iya wurin ba” ta bashi amsa kanta tsaye.
Bai kuma saurararta ba, ya cigaba da tilawar tare da sauran É—aliban.

Ta dubi wata É—aliba ta ce “Ke, dan Allah nan aji nawa ne?”
ÆŠalibar ta kalli Ruma sannan ta ce “Aji É—aya ne”

“Kutmar, ban gane aji É—aya ba, kina nufin aji É—aya aka kawo ni?”

“Eh mana” yarinyar ta bata amsa.

Ruma ta jinjina kai ta ce “Lallai ma an raina mini hankali, wallahi ba zan zauna a aji É—aya ba”.

ÆŠaliban suna ta tilawarsu, yayin da malamin yake jin haddar wasu, amma Ruma hankalinta na kan yadda zata fita daga ajin, dan zaman ajin ya isheta.
Daga bisani ta koma gefe ta hau gyangyaÉ—i.
Lokacin da aka fita break, yunwa ta saka Ruma a gaba, dan ba ta karya ba Yaya Umar ya taso ta a gaba.
ÆŠalibai ne masu yawa sosai a makarantar, dan makarantar sananniya ce sosai a unguwar, dan kusan babu ta biyunta. Daga yanayin mayar da hankalin su Huzaifa da yadda suke bayar da labarin tsananin makarantar ya sanya ta ji ba ta son makarantar sam.
Tun da aka fita break da salla, wuri É—aya ta samu tayi zamanta tana bin ko ina da kallo, sai da ta gaji ta tashi ta fara dubawa ko zata ga Yasir ko Huzaifa amma babu wanda ta gani a cikinsu. Haka aka koma aji ba tare da ta samu komai ta saka a cikinta ba.

Aka dawo aji aka É—ora da karatu babu Æ™aƙƙautawa, gaba É—aya Ruma ta gaji da zaman makarantar. Malamin ajinsu ya fara yi musu Æ™ari, ta buÉ—e Alqur’anin ta ajiye, ta cigaba da gyangyaÉ—inta.

Tun da Ruma ta shigo ajin É—azu yake kallonta, sam ya lura babu alamar son karatun a tare da Ruma, daga hamma sai bacci take yi.
Ƙarshe ta haɗa jakarta ta cewa malamin fitsari take ji, ya ce taje tayi, ta ɗau jakarta ta bar ajin.
Zagayawa take tana lelleƙa azuzuwa ko Allah zai sa taga mutum ɗaya a tsakanin yayyenta, dan har wani irin jiri take ji, dan a duniya ba ta wuce ƙarfe ɗaya ba ta ci abincin rana ba, yau sai ga ta har azahar babu ko karin kumallo.

Ajinsu yayi tsit, sun tattara hankalinsu a kan Æ™arin karatun da ake yi musu, kamar daga sama ya jiyo muryarta “Huzaifa, dama nan ne ajinki tun É—azu nake neman ku” gaba É—aya ajin aka waiwaya don ganin waye yake wannan wautar.

Kallon da ake yi mata bai sanya ta nutsu ta daina maganar ba “ka ganni a makarantar ku ko? Hmm É—an zo ka ji wata magana mana”.

“Ke wacece haka, baki ga karatu muke yi ba?” Malamin yayi maganar yana kallon tagar da Ruma ke tsaye.

“Yunwa nake ji, shiyasa nake nemansa” ta faÉ—a tana sake leÆ™o cikin ajin.

Shi Huzaifa mamaki ne ya cika shi, yaushe aka saka Ruma a makarantar nan bai sani ba?.
Ganin babu komai a kan Ruma sai wauta ya sanya malamin ya kalli Huzaifa ya ce “Je ka ka sallameta”

Cike da jin kunya ya tashi ya fita, yana fitowa ta tare shi da murmushi, shi kuma ya haÉ—e rai ya ce “Uban waye ya kawo ki makarantar mu?”

Kallonsa tayi ta kalli harabar da suke ta ce “Sai ka ce wata makarantar arziki, nima ban ce a kawoni ba, wayewar garin Allah kawai mai sunan Baba ya bani uniform ya kawoni, ni wallahi gara na koma na bawa malam babba haÆ™uri, in koma makarantar allon mu ba zan iya wannan jidalin ba”.

“Ke dalla rufewa mutane baki, daga zuwanki kin fara nuna hali, kawai ki zo ta window kina kirana saboda hauka, maimakon ki yi sallama ki tambayi malamin, ke Allah sai kin bar makarantar nan, dan ba zaki zubar mana da mutunci ba”.

“Saboda gani annoba ko?” Tayi maganar tana hararasa.

“To ba gara annoba ba, idan aka samo maganin ta shikenan ba, ke kuma maganinki sai Allah, yanzu uban me zan miki?”

Ta yatsuna fuska ta ce “Ni yunwa nake ji, kuma wallahi sonake na tafi gida”
Huzaifa ya ce “Lallai baki da hankali, to ke da gida sai Æ™arfe biyar, wuce muje ajin su Yasir gara mu raba abin, da ki dinga yi mini ni kaÉ—ai”tura baki tayi, ta rungume jakarta, Huzaifa ya sanyata a gaba yana mita suka nufi ajinsu Yasir.
Ita kuma sai mita take, a kan daga yau ba zata sake zuwa wannan makarantar ba da ake uzzurawa mutane.

Yasir kansa salati ya dinga yi da salallami “Dan girman Allah meyasa mai sunan Baba zai yi mana haka, ya saka yarinyar nan a makarantar nan ba a shawarce mu ba, wallahi mun kaÉ—e”

“Oho muku, ku kwantar da hankalin ku, ni ba kuma zuwa zan yi ba, kawai ku bani Abinci”
Yasir ya dungure mata kai ya ce “Shegen ci kamar kazar hausa” suka sakata a tsakiya suna tafe suna zaginta, suka saya mata awara da ruwa ta cinye tsaf, sannan suka korata aji.

Ko da ta isa aji, tuni an gama karatun Alqur’ani, ana jiran wani malamin ya shigo.

“Ya aka yi daga zuwa fitsari ki ka daÉ—e, gashi an gama Æ™arin Alqur’ani, sati mai zuwa idan Allah ya kaimu zamu bayar da hadda” cewar yarinyar dake kusa da Ruma.
Ruma ta kalleta ta ce “Ina aka biya É—in?”.
Yarinyar ta buÉ—e Alqur’anin tana nunawa Ruma ta ce “Rabin shafi aka Æ™ara, gobe in Allah ya kaimu ma za a Æ™ara rabi, feji É—aya kenan sati mai zuwa idan Allah ya kaimu sai ki kawo haddar”.

Cikin ko in kula Ruma ta kawar da kanta gefe, alamar zancen yarinyar ma bai shigeta ba.

“Ya na ji kin yi shiru ne? Ki buÉ—e sai na koya miki, idan fa baki iya ba babu ruwan ya sayyadi da sabuwar zuwa ce ke, zaneki zai yi”.

Rumaisa da shishshigin yarinyar ya fara Æ™ular da ita ta ce “To a kasheni mana kar a barni da rai, ba cewa aka yi nan aji É—aya bane ba, kuma sai a Æ™ara mini rabin shafi, kuma wai na haddace yo ta ina zan iya ni, nifa a makarantar da na baro sai nayi wata ina nanata aya biyu nake iyawa, wannan karatun ma na san ba zan iya ba sai dai ayi kwaÉ—ona da mai da yaji a cinye” galala yarinyar ta bi Ruma da kallo ta jinjina kai ba ta sake cewa komai ba.

Bayan an kaÉ—a Æ™ararrawar tashi, malamin da ya yi mata interview ya kirata ya gaya mata cewar za’a fara karÉ“ar haddarta daga tushe, sannan za ta dinga yi tana haÉ—awa da wanda ake yi musu a aji.
Da yake ma bata fahimci bayanin da yayi mata ba, hankalinta na kan ta tafi gida, dan ta san ba iyawa za ta yi ba, kuma ta gama yanke shawarar daga ranar ba zata sake zuwa ba sai dai Yaya Umar yayi mata abin da ya ga dama.

Ko su Huzaifa ba ta nema ba, ta nufi gida.
ÆŠa da uwa sai Allah, wuni gudan da mama tayi babu Ruma a kusa da ita duk sai ta damu, ta ji gidan babu daÉ—i, gashi tana ta tunanin ko abinci Ruma bata tafi da shi ba, balle ta samu ta ci haka mama ta wuni sukuku.
Tana tsaka da tunanin Ruman ne, ta É—aga kai taga Ruman a tsakar gida.

“Meye haka, babu sallama ki shigo ki tsaya?”

Ruma bata amsawa mama ba, sai kumbura baki da take yi, ta cire hijjabinta da jakar makarantar ta dungurar a wurin ta tafi kitchen tana dube-dube.

Ba ta saurari mama ba sai da ta ci ta Æ™oshi, Sannan ta dubi mama ta ce “Ni fa mama gaskiya ba zan sake zuwa makarantar nan ba”.

“To ai ba ni zaki gayawa ba, wanda ya saka ki a makarantar zaki gayawa”.

“Mama kin ga uban dukan da ake yi a makarantar nan kamar an samu bayi, kuma dan rainin hankali wai aka kai ni aji É—aya ni za a kai aji É—aya saboda raini, to wallahi makarantar malam babba zan koma ba zan iya ba”

Mama ta girgiza kai kawai, ta cigaba da aikin da take yi, Ruma ta saki baki ta dinga zuba tana cin alwashin ba zata sake zuwa ba.
Huzaifa ne suka yi sallama shi da Yasir, mama ta amsa musu. Basu kai ga zama ba suka hau mita.

“Mama dan Allah meyasa aka saka yarinyar nan a makarantar nan ba tare da shawarar mu ba? Kin san halin yarinyar nan tun a yau ta fara nuna halinta”.

Ruma ta ce “Sha kuruminka ni ba komawa zan ba, daga yau ko za ayi Æ™uli-Æ™ulina ba zan koma ba, wai saboda tsabar abu wai Æ™ari shafi guda, kuma wani satin ka kawo hadda, ni aya biyu nake iyawa waye zai yi wannan karatun taÉ“ ga uban duka wallahi ba zan sake zuwa ba

Yasir ya ce “Ai makarantar mu ba ta daÆ™iÆ™ai ba ce ba, ki koma inda ki ka fito ba zaki zubar mana da mutunci a makarantar nan ba”.

Ba tare da sun san Umar yana gidan ba, yana É—aki a kwance suke ta wannan zubar.

Tsuru-tsuru suka yi, musamman ruma da ta fi zaƙewa, sai ganinsa suka yi ya fito tsakar gida.

“To dan ubanki ki daina zuwan kin ji ko, daga yau kar ki sake zuwa ki ga yadda zan yi da ke, kuma na gaya musu ba kya jin magana, idan har ba ki yi karatu ba su kama ki su zane ki”

Ruma a ranta ta ce “Ai wallahi sai na yi abin da za a koreni waye zai zauna ana jibgarsa kamar jaki”

Ya kalli su Yasir ya ce “Ku kuma, kune zaku dinga tsayawa a kan karatunta, ku zaku dinga koya mata dan daÆ™iÆ™iya ce, duk daÉ—ewar da ta yi tana zuwa makarantar allo ta kasa kawo izu biyu, sai karatun wani ta je tana iyawa, daÆ™iÆ™iya ki yi musu shirme na bayar da damar a zaneki”

Kawar da kai Ruma tayi gefe, Umar ya gama bala’insa ya bar gidan.

Yana ficewa daga gidan, Ruma ta dasa wa mama kuka, a kan lallai sai ta saka Yaya Umar ya cireta daga makarantar, mama ta ce babu ruwanta.

Ko da wasa Ruma ba ta sanya a ranta za ta yi wannan karatu ba, dan idan za a kasheta ba ta ma san in da aka ƙara musu ɗin ba, ta cigaba da sabgoginta.

Da sati ya zagayo zata koma makaranta, sai da a ka kai ruwa rana, tana kuka su Huzaifa suka sanyata a gaba zuwa makaranta, suna tafe suna zaginta suna mita an haɗasu da alaƙaƙai.

Yau mama ta bata kuɗin makaranta, dan haka ta tsaya ta sayi goriba a ƙofar shiga makarantar.
Duk da babu malami a ajinsu, amma kowane É—alibi ya nutsu sun haÉ—a baki suna ta tilawa.

Taɓe baki tayi, ta samu lungu ta zauna, ta kashingiɗa tana cin goribar ta a nutse.
Shigowar malamin bai hanata cigaba da hangale baki tana gwaigwayar goribarta ba.
Ba ƙaramin ƙulewa malamin yayi ba, tun a wancan satin ya lura ba ƙaramar gaɓuwa ce ba yarinyar.

Yayi mata alama da hannunsa ta je, ta tashi ta fito da jakarta da goribarta a hannu ta ce “gani”

Ya ce “Yauwwa, ta kan ki zan fara jin karatu yau, É—auko Alqur’anin ki ki karanta Æ™arin da na yi muku, sannan ki bani hadda” É—an waro masa idanuwanta tayi sannan ta ce “Gaskiya ban iya ba wallahi, karatun yayi yawa ina laifin aya É—aya ko biyu”

“Koma gefe ki tsaya” babu ban haÆ™uri babu komai ta koma gefe ta ja ta tsaya.

Ya cigaba da sauraron tilawar ‘yan aji, Ruma kuma ta mayar da hankali a kan cin goribarta, ya É—aga kai ya kalli Ruma, wani irin takaici ya Æ™ule shi ko a jikinta abin da ya dameta kawai take yi, ya ce “Ke zo nan”

Ta ƙaraso ta tsaya, miƙewa yayi ya ɗaga bulala zai daketa.
Ta Æ™walalo ido ta ce “Kar ka dakeni ba a dukana” bai saurari ruma ba, ya zuba mata a Æ™afarta har sau biyu.

Wani uban ihu ta ƙwala, ta zube a kan ƙafarta tana jujjuya kai.
Gaba É—aya ‘yan ajin suka yi shiru suna kallonta, sai a lokacin da ya daketa ya huce sai kuma ya sha jinin jikinsa ganin uban kukan da take yi.

“Wallahi ni sikila ce ba a dukana, shikenan ba zan iya tafiya ba” gaban malamin ne ya faÉ—i, amma ya maze ya cewa ‘yan ajin su cigaba da karatu.
A ƙalla ruma ta shafe awa guda tana kuka babu ƙaƙƙautawa kuma taƙi tashi daga wurin, wai sikilarta ta tashi.

Abu kamar wasa magana har kunnen malamai, kasancewar malamin nasu, É—an ajin da suka yi sauka ne yake koyar da su, ba cikakken malami bane a makarantar.
Malamai suka taru a kan ruma, amma taƙi tashi wai sikila ce da ita, ba zata iya tashi tsaye ba.
Malamin nasu jikinsa sai rawa yake yana cewa “Wallahi bai san ba ta da lafiya ba”

Malamin da yayi mata interview ya ce “Kuma ni a form É—inta yayanta bai rubuta tana da wani ciwo ba, ina ne gidanku?”

“Ni ba zan gane hanyar gidan ba, akwai yayyena a makarantar nan ku kira mini su su kai ni gida in ga mama zan mutu”

“Su waye yayyen naki?” Nan gaya musu ajinsu Huzaifa.
Huzaifa yana can yana karatu aka kirashi, yana zuwa ajinsu ruma ya ganta zaman dirshan malamai sun kewayeta.
Nan suka yi masa bayani, turus yayi yana kallon ruma yana son gano ko makircinta ne, dan shi a iya saninsa ruma ba ga da wata sikila, ban da zazzaɓi ba ta ciwon uban komai, amma a ina ta samo wata sikila?.
Ya miÆ™a mata hannu ya ce “Taso in mayar da ke gida”

“Ni na kasa motss Æ™afata ciwo take mini” tayi maganar cikin kuka.

Huzaifa ya durÆ™usa ya ce “To hau bayana na mayar da ke” aikuwa ta ja jiki, ta hau bayansa ya É—au jakarta ya ce bari ya kai ta gida.

Sai da suka yi nisa sosai da makarantar sannan ya sauketa, aikuwa ta tsaya cak a kan ƙafafuwanta.

Ya kalleta ya ce “A gidan uban wa ki ke da sikila?”

“To gani nayi za a kasheni da duka, naga a makarantar bokonmu ba a dukan wata me sikila, da na ji zafin dukan sai na ji kamar nima ina da sikilar”.

Galala ya bi ruma da kallo, ‘yar mitsila da ita amma ta iya makirci haka.

“To mu je ki yiwa Yaya umar abin da ki ka aikata”

Marairaicewa tayi ta ce “Dan Allah kayi haÆ™uri”

“Wallahi ba zan goyo ki a banza ba, ko ni sai na miki shegen duka yau” yana gama maganar ya danÆ™eta ya saÉ“ata a kafaÉ—arsa dan zata iya Æ™wacewa ta gudu.

 

 

Ayshercool
08081012243
[22/06, 9:49 pm] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA
Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER’S ASSOCIATES

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ku yi subscribing  YouTube channel É—in
@Cool Hausa Novels, domin samun daÉ—aÉ—an litattafan hausa na sauraro.
Ku yi following É—ina a arewabooks a kan account É—ina na ayshercool7724
Ko watpad Ayshercool7724 kowanne a cikin manhajojin za ku iya samun litattaiafaina da na yi a baya, da wanda nake yi a yanzu na gode.

 

*AFUWAN BAN EDITING BA*

Post a Comment for "Kanwar Maza 5"