Breaking News

Kawali Ne 1

*KAWALINE*

*Zahra Surbajo*

 

*Bissimillahirrahmanirrahim*


*wannan littafi nawa na kuÉ—ine 500,yazo da salo na musamman acikinsa dagajin sunan kuma kun san zeyi maana,sannan na É—auko wani ciwo dake damun mu ahalin yanzu na kawalci,so duk meso ya turo kuÉ—insa 500,in siya zakiyi kifitarmin karku siya,Sannan suk wanda yasayi wannan littafin AJEE DOWN kyauta zekarantashi*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*

*1*

 

*Abuja Nigeria*

 

A hankali motar ƙirar lexus 2023 fara rufe da baƙin glass,ke gangarowa harabar gun da aka tanada domin adana motoci,watakan parking space.
Ta jima da tsayawa kamin abuɗe ƙofar motar afito da ƙafa ɗaya waje wanda haka yabani tabbacin namijine acikinta duba da takalmin Gucci dake ƙafarsa daya laƙume milyoyin kuɗi.

Fitowa yayi,subuhanallah,Tsarki ya tabbata ga sarkin daya kyautata surarsa,dan Allah yayi halitta agurin.

Farine sosai,me murÉ—aÉ—É—en jiki,fuskarsa nada É—an faÉ—i ba sosaiba É—auke da saje me kyan tsari,gashin kansa nada yawa,sannan yaÉ—an mummurÉ—e,

Tracksuit ne ajikinsa farare na kamfanin Gucci,rigar armless ce hakanne yaba damatsan hannunsa damar fitowa.

Idanunsa masu kama da mejin bacci yana yawan lumshesu,kai takoina fa ya haÉ—u.

A hankali yataka zuwa bakin get É—in daya baro,ga mamakina yana isa gun tsohon dake gadin gidan durÆ™usawa yayi har Æ™asa ya cire glass É—in fuskarsa yace a tausashe cikin muryarsa me daÉ—i”baba barka da warhaka,mun sameku lafiya?”

Faraace ta bayyana afuskar tsohon dake nuna jin daÉ—insa yace”lafiya lau raihan,ya hanya kadawo lafiya?”

“Lafiya lau baba”ya faÉ—i yana murmushi.

“Allah yay maka albarka raihan ya baka mace tagari”cewar baba megadi.

Murmushi yayi ya miƙe cike dajin kunya ya nufi cikin gidan nasu.

Baba megadi bin bayanshi yayi da kallo,yana yaba kyawawan halayen Raihan É—in,duk da kasancewarshi megadin gidansu amma yana mutuntashi,tamkar mahaifinsa.

Da sallamarsa ya tura ƙofar falon ya shiga,fuska ɗaure tamau bame cewa shine yagama yiwa megadi murmushi yanzu.

Mutane uku yasamu afalon,Mahaifiyarsa,ƙanwarta,se kuma ƙanwarsa,sanaya.

Can kusa da mahaifiyarsa yaje ya zauna a ƙasa kusa da ƙafarta,yaɗan rusuna yagaishesu.

“babana idonka kenan ko,tun yaushe nacema kazo hajiya rabi tazo dan ku gaisa amma kaÆ™i zuwa seyau”cewar mahaifiyarsa fuskarta É—auke da faraa.

ÆŠan gyara zama yayi yace”mummy ayyukane sukai yawa,in na saki na taho ban kammalaba É“aci zasuyi shiyasa kikaga banzoba wancan satin”

“To agogo,nidama zuwa nayi inji ina aka kwana kan zancan auranka da nabeela,inyana nan ayi inbabu kar atakura kowa cikinku”cewar hajiya rabi Æ™anwar mahaifiyarshi tana murmushi.

Ƙasa yayi dakai alamun kunya,yace yana sosa Æ™eya”mummy Ni wlh ba yanzu zanyu aureba kawai abata damar auran wanda takeso”

Duka takai masa na wasa tana dariya tace”shaÆ™iyyi ay dama nasan zaa rina shiyasa kadena shigowa kano dan karma ku haÉ—u ko”?

“Aa mummy aykinane be bi tacan ba”ya faÉ—i yana murmushi dan yanzu yasaki fuskar dan zatonshi tilastashi auran nabeelar zaayi

Sun jima suna ɗan hirar sama sama kamin ya miƙe ya nufi ɗakinshi yana amsa waya.

Yana shiga ya kulle Æ™ofar É—akin sannan ya wuce cikin bedroom ya zauna gefen gado yana faÉ—in”jabeer da gaske kakemin Farhana ta diro nigeria?”

Dagacan É“angaren jabeer yace”wallahi raihan gatanan na É—aukota daga airport zamu masauki.”

“Look jabeer farhana kadarace me tsada dan Allah karka taÉ“a kabari indawo,sabida asan sashin da za’a turata ta jawo kaya pls”

Dariya jabeer yayi irin ta Æ´an bariki yace”banyi alÆ™awariba malam dan wallahi wannan kadarar daga kallo ma kawai baa hau gadoba zaa yi releasing”

Wata Æ™ara raihan yayi yace”dankutumar ubanka ganinan zan biyo jirgi yanzu wallahi tunda baka da amana”

Dariya jabeer yake masa kamar cikinsa zeyi ciwo,ya kashe wayar.

MiÆ™ewa Raihan yayi da sauri ya fice yana duba agogo,afalo yasami su mummy suna ganin yadda yake sauri sunsan ba lau ba,tun kan suyi magana yarigasu da cewa”mummy container kayanmune tazo yanzu kuma costom na Æ™oÆ™arin Æ™waceta shine zanyi sauri inje ayi clearance É—inta”

“To Allah yatsare raihan ka dinga kulawa sosai don Allah”cewar hajiya rabi.

Mahaifiyarsa ma fatan alkhairi taimasa yafice daga gidan,baba megadi namasa fatan isa lafiya.

Koda yaje airport be jimaba jirgin tafiya lagoa yazama ready dan haka ya bada ajiyar motarsa a inda aka tanada domin hakan,ya hau jirgi zuwa lagos wanda yake ganin sam vaya sauri,ya ƙosa ya dira kamin jabeer ya masa illa.

*500 kacal zaku biya kusha karatu karku bari abaku labari*

Surbajo for life.

No comments