Breaking News

Kurkukun Kaddara Book 2 Page 13

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

 

_The Prisoners E13_


*Daga alƙalamin Boss Bature*

~Middle step~

 

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty._

 

Juyawa yai da sauri ya nufi kitchen maimakon É—akin shi, Yana shiga ya ci karo da zainab tana goge tiles da floor wiper sam bata lura dashi ba, har saida yai mata sallama tukunna ta É—ago suka haÉ—a ido
Fara’a ta sakar mashi”shuraim tun jiya na ke son yin magana da kai, fargaban Iyayenka ta hanani tunkarar ka” Æ™arasa shiga kitchem É—in yai

“Aunty zainab Ya zamuyi? Uncle musa ya matsa min akan saina bishi abuja, Æ™arfe sha biyu zamu bar jos, ” dafe kai ta yi da hannu É—aya

“Naji takaicin jin haka shureim, Duk plan É—in da muka shirya ya tashi abanza kenan”

Girgiza mata kai yai”in sha Allah komai zai tafi dai dai aunty zainab, ko da ace bana nan that will not change anything”

Damuwa ce cunkushe akan fuskarta

“How ka ke tunanin komai zai tafi dai dai bayan bamu a wuri É—aya”?

murmushin gefen fuska ya sakar mata har dimples É—insa suka lotsa.

“Kin manta da waya? Ina da ita kina da ita, zamu dinga yin communicating da junanmu, hakan ma zai fi ba tare da wani ya zarge mu ba” Æ™ayataccen murmushi zainab ta saki

“Allah ya yi maka albarka shureim ni sam na manta da waya, amma fa zan yi missing É—inka sosai mutumina

Murmushin fuskarshi bai washe ba yace”Ni kaina zanyi missing É—in auntyna mai share min hawayena, amma in sha Allah zamu dinga yin waya akai akai, Inaso komai da ke faruwa a gidan nan kidinga sanya min ido, da zarar an samu update ki kirani awaya ki sanar dani, amma fa sai kinyi takatsantsan kinsan Iyayen nawa ba Æ™ananun mutane bane”

jinjina kai Zainab ta yi don ta gamsu da bayanin shi

“In sha Allah zan kiyaye shureim, kaima ka kula min da kanka, ” idanuwansu duk sun ciko da Æ™walla, don ba Æ™aramin Æ™aunar juna su ke yi ba, tana jinshi tamkar ÆŠanta, shima Yana jinta tamkar mahaifiyarsa, sun jima a kitchen É—in sunayin magana kafin daga bisani yai mata sallah.

Ba tare da 6ata lokaci ba, Dr shureim Ya fara shirye shiryen tafiya abuja, bai canza komai na suturar jikinsa ba, Iya turarurrukansa kaÉ—ai ya feshe jikinsa, sannan ya warware ÆŠaurin larabawan dake akanshi, Ya sharce lallausar sumar kanshi Ya gyarata tsaf yabi da mayukansa ya shafe ta, Kafin barinsa É—akin saida yai Nafila Ya roÆ™i Allah da ya tsare shi ya kare shi daga sharrin mutun sharrin zuciya da duk wani abun cutarwa, ya kuma roÆ™i Allah da ya sa silar komawarshi gidan uncle din shi abuja rayuwar shi ta canza ya dawo kamar yadda yake ada, addu’o’i sosai shureim yayiwa kanshi, Bayan ya kammala ya zaro memory É—inshi da ya 6oye a cikin rigar pillow ya zaura shi awayarsa, Hankalin sa Ya É—an kwanta zai samu natsuwar cigaba da kallon hotunan Abar Æ™aunarsa awayarsa.

A gefen gadon shi ya zauna yana daddana wayar shi, Lokaci ya ke jira ya cika.

**DAULAR OBIE ESTATE**

A Hankali Jigunannun Motocinsu su ke kunno kai saman shantalelen titin obie estete, gaba da baya Sojoji ne ke tafiya akan Æ™afafuwansu, Hannayensu ruÆ™e da bindigu, Motar farko mallakin Sir mubarak ce, motar dake a biye da ita zungureriya Æ™irar Navigator limousine wadda cikinta tamkar bedroom ya ke saboda tsabar haÉ—uwarta, Dattijon arziÆ™i ne hakimce acikin motar tare da Jikokinsu tagawaye zain da zaid sai Dr Jazz shalelensa, Motar da ke abiye da tasu DanÆ™areriyar gaske mai numfashi mallakin Senate president Lateef Obinna ce, Yayin da motar Æ™arshe Ta pravin Obinna ce, gayu mutanan Allah su kansu motocin da dattaku ake yin driving É—insu a tsanake cikin Æ™warewa, sautin karatun kur’ani mai girma ne ya karaÉ—e ko’ina, Ƙirar Ahmad suleiman mai matuÆ™ar ratsa sassan jiki, daga motar dattijon arziÆ™i Æ™irar ke fitowa, Æ™a’ida ne a lokacin da suka fito zasu tafi masallaci sai yasa an kunna masa Æ™irar Ahmed suleima haka zalika idan zasu dawo daga masallaci sai an kunna masu karatun wani sa’in Idan Æ™irar takai mashi karo har bi yake yi yana lumshe ido, A yanzu haka dawowarsu kenan daga masallacin Juma’a.

Sannu A hankali su ke tunkarar Moto park É—insu, kusan atare motocin suka Yi parking at same time, Da azama sojoji su ke bubbuÉ—e masu mota, A hankali Obie Ya sauko Æ™afarshi dake sanye cikin takalma kalar na sarakuna, Jikinsa Jallabiya ce daga sama Ya É—aura alkebba haÉ—aÉ—É—ar gaske sai Æ™yalli ta ke Yi, É—aya bayan É—aya su ke fito daga Cikin motocin, gaba É—ayansu haÉ—aÉ—É—un Jallabiyoyi ne a jikin su daga Iyayen Har Æ´a’Æ´an.

“Mu shiga ciki ko”? Obie ne Yai masu maganar, Zaid da zayn Sai faman sunnar dakai Æ™asa suke yi kamar marasa gaskiya, mamakin hakan yasa Mahaifinsu pravin tanka masu

“Lafiya”? Kafin su yi yunÆ™urin bashi amsa Sir Mubarak ya tari numfashin su

“Zaku ci Æ™aniyarku ne, Æ™ananun Ƴan iska masu kwana da wando, har ni zaku dinga kakkaucema wa? Kun raina ni ko”? Fuskar shi a É—aure ya ke yi masu magana, sir mubarak mutunne mai fusatacciyar zuciya abu kaÉ—an ke hasala shi sai da ta wani 6angaren yana da sauÆ™in kai.

Dr jazz Yana ruƙe da hannun Obie dariya ce ƙumshe abakinsa, ya ƙi bari ta kubce masa gudun kada Ya ji saukar mari daga Sir mubarak, Twins kuwa Duk sun sha jinin jikinsu sai faman noƙe kai suke yi haɗi da sosa ƙeyarsu.

A fusace Ya daka masu tsawa har saida suka É—an razana atare su ka É—ago da fararen idanuwansu akan fuskarshi” Ina magana kuna kallona? Saboda tsabar fitsara”? Da sauri suka sunnar da kawunansu Æ™asa, Alkunyace ta hana Pravin sanya baki, Gyaran murya senate Lateef Ya yi ma É—an uwan nashi, Ya juya yana duban shi, cikin muryan Manyantaka Ya soma magana
“Aymasu afwa, Yarane su har yanzu, basu mallaki hankalin su ba, Sai ana haÆ™uri da su”

girgiza kai Sir mubarak yai”Pls ka daina wannan maganar, Yara sun balaga kana faÉ—in basu mallaki hankalinsu ba”? Juyawa yai tare da kallon su twins muryarshi a kausashe yace”Dagaske baku mallaki hankulan ku ba”? Har suna haÉ—a baki wurin furta”wlh mun mallaki hankalinmu, pls Ka yi haÆ™uri Uncle mun gane kuskurenmu zamu gyara in sha Allah, Dan Allah daddy ka bashi haÆ™uri wlh ba zamu Æ™ara ba” A marairaice suke kallon Mahaifin nasu pravin, Shi dai Obie bai tanka masu ba, murmushi ne É—auke akan fuskarshi.

“Za ku Yi bayanine, muddin Owais ya dawo Æ™asar nan zan sanya shi Ya ba ku horon isod, Ni dama can ban Goyi bayan aikin Company da ku ke zuwa yi ba, saboda ba ku iya komai ba” Zaro ido waje su ka yi jin abunda yace Hankalinsu ya tashi matuÆ™a, saboda suna mugun tsoron training É—in Isod har Æ™wara abasu horon aikin Soja, tuni sun raina kansu, Muryoyinsu tamkar zasu fashe da kuka su ke kallon Kakansu obinna don ya sa baki akan maganar
Pravin na murmushi yace”dama kun daina wahalar da kan ku, kunsan wanene Kawun na ku mubarak, Idan ya yanke hukunci babu wanda Ya isa ya dakatar dashi, Ni ma kuma na goyi bayan hukuncin da ya yanke”

Ransu ya 6aci jin abunda daddyn su Yace, juyawa su ka yi afusace suka nufi gidan.

Girgiza Kai Sir mubarak yai”kun ga irinta ko? Ana magana sun juya sun tafi saboda rashin ganin girman nagaba da su, duk izzar Owais ba ka ta6a yi mashi magana Ya juya maka Æ™eya duk mun rashin daÉ—inta, natsuwa ya ke yi ya saurareta, Ai duk laifinka ne Pravin da kai da Saratun Kun sangartasu duk cikin Ƴa’Æ´anmu babu sangartattu irin twins, Zanyi maganinsu ne” Maganar Sir mubarak ta ta6a zuciyar Pravin, yana É—aya daga Cikin abunda ya tsana, ya ji an kushe Æ´a’Æ´an shi an yabi na wasu, Musamman owais, gani yake kamar don saboda Shi ba Jinin family É—in bane Shiyasa suke nuna ma Æ´a’Æ´an shi wariya.

Tuni yanayin fuskarsa ya canza sam babu annuri, Ba tare da ya kalli fuskokinsu ba Ya furta”Ni zan Shiga ciki Sai kun Æ™araso” Yana faÉ—in hakan Ya zura hannayenshi cikin aljihun jallabiyar shi ya nufi gidan.

Gaba É—aya sun fahimci canzawar da yai, Senate Lateef ya girgiza kai Yana bin bayan pravin da kallo

“Narasa gane kan mutumin can, Æ™aranci Hankali nadamun shi, meye aciki don Anyi maganar Æ´a’Æ´an shi sangartattune? Ƙarya aka yi ne”? ran sir mubarak Yafi na kowa 6aci”Ka barni dashi, zan koya mashi hankaline, Maganar horon Isod da za’a ba Æ´a’Æ´an shi ba fashi ko da zuciyarshi zata buga ne É—an rainin wayau”

gyaran murya Obie Yai masu hakan Ya janyo hankulansu ga kallon shi, ya É—an jingina bayan shi jikin motarshi su kaÉ—ai suka rage a harabar ajiye motocin, tun bayan isowar su gidan sojojin da ke take masu baya suka watse zuwa 6angaren da suke kula da shi na gidan.

“Sai kuna Yi mashi uziri, Pravin yana da raunin zuciya, ga shi dai a ido kamar Namiji sai dai a zuciya baida mararraba da mace, shima auta ne kamar saratun, mijin auta ai auta ne shima inda kara”

ƙumshe dariya Dr jazz yai jin sharrin da Obinna ke yiwa Pravin

Fuskar senate Lateef É—auke da murmushi yace”A’a, baba ai ko saratun dakakkiyar zuciyace da ita, kaima ka sani gaba É—ayanmu Jinin ka muka Biyo, babu ragwantaka atare damu, shi dai ne macen Mijin tace, ita kanta saratun Juya shi take yi son ranta, Ina ji ran nan mun shigo gidan tana yi mashi masifa akan Ya zari kuÉ—i a account É—inta ba tare da ya nemi iznin ta ba, sai lalla6ata ya ke yi kamar zai yi mata sujjada”

Gaba É—aya suka tuntsire da dariya, daga obinna har shi Sir mubarak É—in.

Dr Jazz ya saki baki yana tiÆ™ar dariya kamar wani babba ya shige cikinsu, sai da suka kammala Yin dariyar, Sir mubarak Ya lura dashi, sam ya manta da dr Jazz a cikinsu, ÆŠaure fuska Yai”kai! Me ka ke wa dariya? Akwai tsaranka ne acikin mu”? Da sauri Dr jazz Ya shanye dariyarshi, Hada la6ewa bayan Obinna.

Senate lateef yace”Ni zan wuce gida Baba, In sha Allah zan samu lokaci in shigo ciki mu Æ™ara gaisawa” obie yace”kada ka ta kura kanka, Ai kuna Æ™oÆ™ari ma, Ko awaya ne munyi magana, Idan ka shiga gidan ka gaishe min da hajiyar taka, Ina nan ina jiranta ta zo ta same ni agida mu gaisa”

Amsa mashi yai da toh, kafin Ya kalli É—an uwan nashi”Ni zan wuce Mubarak agaishe min da Turai,” amsa mashi yai da toh”Nima a isar min da saÆ™on gaisuwa zuwa ga madam É—in taka” A mutunce sukayiwa junansu sallama,

“Baba nima zan shiga ciki, amma kafin nan zan raba ka da wannan mata mazan” yai maganar yana Æ™oÆ™arin damÆ™o hannun Dr jazz, ƘanÆ™ame obie yai, Sir mubarak yace” So ka ke ka karyamana Uban namu, Fito nan, Ni ba wani abu zanyi maka ba, Inaso ne mu shiga ciki, ka gaida mahaifiyar taka, nasan saboda ni ya sa ka daina leÆ™owa wurinta, tsakaninka da sai kira awaya sai kuma idan ta shigo gaida baba”

Jin abunda yace ne yasa shi sauke ajiyar zuciya, don ba ƙaramin jin shakkar Uncle mubarak ya ke yi ba, ruƙo hannun shi mubarak Yai

“Zaka rabani da sanyin idaniyata” acewar dattijon arziÆ™i.

Dr jazz yace”kada ka damu kakana, Ba zan jima ba, zan shigo gidan, pls Ka kwanta ka huta,” lumshe ido obie yai idonshi akansu har saida suka 6ace ma ganinshi, tukunna Ya ruÆ™e sandarshi Ya nufi cikin gidan.

Hajiya saratu ce zaune gefen gadonta cikin shiga ta bubu gown anyi mata kaftan style, kanta babu mayafi, Ta natsu tana kallon screen ɗin laptop ɗinta dake ajiye a gabanta saman round table, fuskarta ɗauke da murmushi, Video call ta ke Yi da ƴar autarta Faryat dake zaune gidan Yayanta Hateem na ƙasar canada

Matashiyar budurwace launin fatarta kalar na mahafiyarta ne, tana a zaune saman wasu haÉ—aÉ—É—un kujeru dake a kewaye da table, agaban tafkeken swimming pool, gefen laptop É—inta Cup É—in coffee ne ajiye, ta É—auki wankan short gown ajikinta launin pink tabi shape É—in jikinta.

“Yaushe zaki dawo gida ne? Na yi missing É—in ki daughter”
Fuskar Faryat ta cika screen ɗin laptop ɗinta, faɗaɗa murmushin fuskar ta tayi da zazzaƙar muryarta ta furta

“I’ll come home as soon as we have a school break because I can’t wait to see you, my first love.”

“Canada ta kar6e ki daughter, kinyi haske kinyi kyau abunki, faÉ—amin dame dame ki ke yi a lokacin da ba ki yin komai”?

Farfari Faryat tayi mata da ido kafin ta soma jera mata

“Going to the movies, beach, club, playing games… ”

tunkan ta Æ™arasa maganar Hajiya saratu ta dakatar da ita, Fuskarta a É—aure tace”Faryat! Kina zuwa club? Da beach..? waro ido Faryat tayi batasan tayi su6ul da baka ba, da sauri ta toshe bakinta da tafin hannuwanta

“Mom, I was just joking. You know Uncle Hateem would never let me go to those places. Also Yazrin and Nazli keep an eye on me, even when there’s no school, they keep me company. I’m too busy to waste time.”
Hankalin saratu har ya É—an kwanta

“Dama nasan Æ™arya kike yi min, Na yadda da yayana Hateem nasan duk wani shige da fucen ki Yana a tafin hannun shi, duk da yana busy hakan bazai hana shi sanya jami’an da zasu dinga kula da motsinki ba, shiyasa tun farko na tura ki can don su gyaramin natsuwarki, kuma Alhamdulillah naga canji” Dariya Faryat ta saki jin abunda mommyn nata tace, Tsawon mintuna talatin sunayin wayar kafin daga bisani sukayi sallama da juna.

Layin Landline na kitchen Hajiya sarah ta kira Safa ce ta É—aga kiran.

“Assalamu alaikum” Sarah ce tai sallama, Hajiya sarah bata tsaya amsa sallamarma ta ce”Jira ake sai nace akawo min abinci? Ko so ake in taÆ™o da Æ™afafuwana in zo kitchen É—in in É—iba”? Muryar safa adabarbace ta furta”Ba haka bane Hajiya, duk laifin abla ne, itace take da aiki apart dinki, amma in sha Allah yanzu zata Æ™araso” yatsina fuska Hajiya saratu tayi fuskar ta babu annuri ko misÆ™ala zarratin

“Okey, ina buÆ™atar dambun nama, A haÉ—o mun da fresh fruit, kada amanta da farfesu…” a Æ™alla ta lissafa kusan abu takwas da za’a kawota don tayi breakfast….tunkafin Ta yi rejecting kiran muryar Pravin ta ratsa kunnata

Ranshi a6ace ya shigo yana zazzaga masifa”wannan wani irin wulakanci da cin fusk ne, Nifa nagaji da aibata Æ´a’Æ´ana da ake Yi” yana huci ya Æ™arasa maganar tare da goya hannayensa saman Æ™irjinsa, idon saratu akanshi bayan ta katse kiran ta É—aura wayar saman nightstand
A tsanake ta soma yin magana”wanene ya ta6a min romeo É—in nawa”? ko sallama babu ka shigo kana ta zazzaga masifa? Tell me meya faru”? AÆ™agare tayi maganar, tare da yunÆ™urawa ta miÆ™e tana fuskantar shi
Zuciyarshi A harzuÆ™e ya furta”Yayyanki mana, Akan me zasu dinga kushe Æ´a’Æ´ana suna yabon nasu? sai yaushe ne zasu daina nuna min wariyar launin fata? Saboda kawai ni bani da alaÆ™a daku shine zasu dinga kushe min Æ´a’Æ´ana”? Idan da kara Æ´a’Æ´ana ai nasu ne’ Tsabar fusata yana magana facial muscles É—insa na kerma.
Matsawa tayi kusa dashi, fuskarta a É—aure ta furta”what? Wanenen acikinsu yai maganar”? Da alama ranta ya 6aci hakan ba Æ™aramin daÉ—i yayi mashi ba

“Lateef ne da Mubarak, Agaban obie da sangartaccen Yaron nan dr jazz suke kushe Twins, har faÉ—i sukeyi wai sangartattune basu Iya komai ba irin na maza, zaifi kyau su ajiye aikin da sukeyi na company su koma É—aura zani” Baki asake saratu ke kallon shi hada ruÆ™e qugu, muryarta akausashe tace”Pravin dagaske sune suka furta hakan? Kuma agaban Baba shine bai tsawatar masu ba”? Kwa6e fuska pravin yai”ae abunda zai baki haushi, baisanya baki amaganar ba, saima murmushi da yake saki, hada wannan munafukin Yaron, Shi da ba É—an kowa ba agidan face É—an mai aikin, wama ya sani ko shege ne, dani da uwarshi duk É—aya muke ai, yadda bani da alaÆ™a da ku, itama haka har Æ™warani mun samu Æ™aruwa ta Æ´a’Æ´a har uku”

Ran Hajiya saratu ya 6aci matuÆ™a, sai faman jinjina kai take yi tana fadin”bari naje wurin baban, yanzu har takai ga Æ´a’Æ´ana aka kushewa agaban sakaran yaron nan jazz? suma waÉ—anda suka yi maganar zasu fuskanci 6acin raina wlh, zasu san dani suke magana” takai Æ™arshen maganar tare da juyawa tana neman mayafin da zata yafa, Pravin hada saurin rigata Æ™arasawa gaban closet É—in kayansu Ya buÉ—e ya É—auko mata mayafi da kanshi ya É—aura mata shi asaman kanta, A fujajen ta fuce daga cikin É—akin, fitarta keda wuya pravin ya soma sakin shu’umin murmushi, ba tun yau ba ya saba haÉ—ata faÉ—a da Æ´an uwanta, mugun munafuki ne na bugawa a jarida, A zubin halitta idan ka kalle shi tamkar Namiji.

Bayan fitar Hajiya saratu da Æ´an mintuna, ya sauke ajiyar zuciya yana Æ™oÆ™arin zame jallabiyar jikin shi da niyar canza kaya, Sallamar Abla ta ratsa kunnuwanshi, Jimm ya É—anyi kamar bazai amsa mata ba, daÆ™yar Ya iya buÉ—e baki Ya furta”shigo daga Ciki” a hankali ta turo Æ™ofar, Hannunta biyu ruÆ™e da faffaÉ—an tray na Kayan breakfast É—in Hajiya saratu.

Ganin Pravin shi kaÉ—ai a É—akin Yasa ta É—anji faÉ—uwar gaba, miryarta na rawa ta furta”umm..amm dama Kayan breakfast ne na kawoma Aunty saratu” lumshe idon shi Ya É—anyi, tare da tunkarota Ya ruÆ™e tray din hannuta”bari na Æ™arasa shigar maki da shi ciki,” kar6a yai tare da juyawa ya É—aura tray É—in saman table, kafin Ya juya ta yi saurin kai hannu zata tura Æ™ofar É—akin saboda sanin halin shi, sai dai kafin ta kaiga Æ™arasawa ga Æ™ofar yai saurin damÆ™ota ya janyota zuwa jikinshi, Hankalin abla Ba Æ™aramin tashi yai ba tsananin tsorone da fargaba duk ya cikata, Æ™amshin turarensa ya addabi hancinsa, cikin shessheÆ™ar murya take faÉ—in”pls ka sake ni dan Allah, na roÆ™e ka kada kaja min bala’e,” kwantar da kanshi yai saman kafaÉ—arta dogon hancin shi na gogar fatar wuyanta, yayin da hannayensa ke asaman Æ™irjinta ahankali yake matsasu, kamar zatayi hauka Æ™oÆ™arin kwace kanta take yi saida ya hanata yin haka saboda Æ™arfine dashi kamar doki, fashewa tayi da matsanancin kuka tana yakushin hannunshi da akaifun hannunta kamar zatayi hauka.
“Nashiga uku, Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, Ya Allah ka kawo min É—auki,” hankalin shi kwance yake cigaba da Æ™oÆ™arin tura hannayenshi cikin rigarta

“Daddy!” muryar Zayn ce tasa shi saurin sakin Abla, É—aure mata fuska yai

“Don’t you dare tell anyone what happened. Wipe ur tears off your face right now.” Jinjina mashi kai tayi da sauri ta sanya Æ™asan rigarta ta share hawayenta, shu’umin murmushi pravin ya saki’Good zaki Iya tafiya sai mun haÉ—u wani lokacin” wani irin É—aci taji acikin zuciyarta, Tana buÉ—e Æ™ofar É—akin taci karo da twins, ko kallonsu batayi ba da sauri tabi ta gefensu ta wuce, awata Æ´ar corner ta la6e ita kaÉ—ai ta zuÆ™unna tana cigaba da yin kuka haÆ™ika pravin ba Æ™aramin cin zarafinsu yake yi ba, shiyasa suke gudun zuwa su tarar da shi a É—akin Hajiya saratu musamman idan bata nan, Romancing É—insu yake yi tamkar zai kashesu, halinshi ne bunsuranci, har Æ™wara Ƴa’Æ´an shi twins duk iskancinsu babu ruwansu da masu aikin gidan, amma shi uban nasu baya iya kauda idonshi akansu, Ya maidasu kayan biyan buÆ™atar shi, Kuma ba su isa su ce zasu hana shi ba, saboda barazanar da yake yi masu, hakan yasa suke mugun jin shakkar fallasa shi awurin masu gidan, kuma hada Æ™arin basu son yayi masu silar barinsu aiki gidan, ba don kudin da ake biyansu da dollar ba, sai don sabon da sukayi da mutanan gidan sannan da yawansu Iyayensu masu Æ™aramin hali ne, wasu ma babu Iyayen neman na kansu suke yi don su rufawa kansu asiri.

Ex-prisoners Meya hwaru Bayan jirginsu Ya É—aga daga Cikin Dajin Evil forest shin sun sauka lafiya ko kuwa akasin hakan”?

*SAN ANTONIO-TEXAS*

*UNITED STATES OF AMERICA*

San antonio texas babban birni ne da ke a cikin jihar Texas ta america Yana É—aya daga cikin jigunannun manyan biranan America Masu matuÆ™ar Æ™ayatarwa Manya manyan gine gine na tarihi dana zamani, abubuwan more rayuwa masu ban sha’awa na musamman da kuma wadatar arziki, Hadaddiyar daula ce a U.s tsayawa suffanta kyawun birnin 6ata baki ne, balle ni da nake da abunyi.

*San Antonio International Airport*

Katafaren Airport ne na tashi da safkar jirage dake a cikin birnin san antonio, Æ™ayataccen gaske, sanarwa ce ta soma fitowa daga muryar na’urar computer (PA announcement) Kunnuwan Ma’aitakan Airport É—in da fasinjojin dake zirga zirga a cikinsa gaba daya sun natsu suna sauraron sanarwar kwamfutar

“Attention, passengers. A UH-60 Black Hawk helicopter is scheduled to land at San Antonio International Airport in approximately 10 minutes. We appreciate your patience and understanding.” (“Amaida hankali, fasinjoji. Jirgin sama mai saukar ungulu na UH-60 Black Hawk yana shirin sauka a filin jirgin saman San Antonio a cikin kusan mintuna 10. Muna godiya da haÆ™uri da fahimtar ku.”)

Tunkafin Æ™arasowar Helicopter É—in nasu tuni Daga can headquater na sojoji an kira Emmergency Number ta Asibitin University Hospital Domin zuwa É—aukar Marasa lafiyan da Jami’an su suka É—auko, Da wata irin jiniya Jibga jibgan Ambulances din suke zuba uban gudu saman titin da dai sadaka da airpot din, jiniyarsu ta karaÉ—e ko’ina duk inda suka bi darewa akeyi abasu Hanya tunkafin su Æ™araso saboda sanin aikinsu na agaji, kowace ambulance tana É—auke da tambarin sunan asibitin UHS which means (University Health System) daga gefen rubutun Zanan white cross ne backround dinsa launin Ja,Kusan su uku ne Motocin suka jera, a Airport helipad ambulances É—in suka Yi parking, helipad yanki ne na musamman da aka tanada domin safka da tashin helicopter.

Mintuna goma na cika cuf cuf A gogon birnin San antonio ya buga ƙarfe 5 na safe, adai dai Wannan lokacin sautin Danƙareran Jirgin Da ke shawagi Saman iska Ya karaɗe kunnuwan kowa dake a yankin airport ɗin ga dukkan alamu Matafiya sun ƙaraso .

Sannu Ahankali Helicoptern Ya sauke tayoyin shi yayin da ya ke yin ƙasa ƙasa, Slowly yake tafiya har yakai ga inda zai dakata a filin helipad, Sojoji ne Kewaye da Jirgin waɗanɗa suka zo tarbarsu daga headquater, Motocinsu na ajere dana ɗaukar marasa lafiyan.
BuÉ—e Bayan Ambulances É—in akayi at same time, Ma’aikan Jinyane waÉ—anda ake kira EMTs (emergency medical technicians) suka soma diddirowa daga bayan motar, mata da maza turawa cikin shigar fararen kaya masu É—auke da tambarin Lafiya Hannayensu da Æ™afafuwansu duk safunane haka zalika Sun toshe rabin fuskokinsu da face mask.

Saukowa Sojojin helicopter É—in suka soma Yi daga cikin shi, Biyu daga cikinsu ruÆ™e da É—an ta’addan da su ka damÆ™o a evil forest, Kaitsaye suka nufi motar Æ´an uwansu sojoji da suka zo daga headquater, Abayan Kanta suka wurga shi tare da datse Æ™ofar,
Dawowa su ka yi wurin Æ´an uwansu, nan fa aka fara rungume juna, Æ´an uwan nasu nayi masu jinjina ta ban girma, akan Nasarar cafke É—an ta’addan da su ka yi.
Ba tare da 6ata lokaci ba, Emts suka Curo stretcher daga motarsu kusan guda Takwas, agaban Helicopter É—in suka Æ™arasa da shi É—auke a hannunsu, Da taimakon sojoji suka dinga Jigilar É—aukar su Angel suna miÆ™a su cikin motar, da aka zo kan Danish Sai dai sojojin suka kar6i stretcher É—in suka shigar dashi ambulance É—in, Bayan sun kammala kwasarsu, Motar sojoji gaba da baya a yayin da motocin Ambulances É—in ke a tsakiya, da wata irin Jiniya suka haura saman titi da gudun gaske, sauran sojojin dake acikin motar da É—an ta’addar yake tuni sun raba hanya sun nufi headquater É—insu da shi.

 

*Boss Bature✍️ Mu haÉ—u gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun Æ™addara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuÉ—in*

 

First bank

 

3196407426,

 

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number É—ina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

No comments