Breaking News

Kurkukun Kaddara Book 2 Page 6

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

 

_The Prisoners E6_

*Daga alƙalamin Boss Bature*


~Middle step~

 

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty._

 

 

*JUSTICE DEMOCRATIC PARTY*

(JDP HQ)

Manyan mutanene dattawa da matasa zazzaune a babban É—akin taro na jam’iyyar Justice democratic party É—aya daga cikin jam’iyun da su ka shara a Æ™asar Nigeria, zungureran table ne wanda ke kewaye da kujeru, daga saman teburin akwai microphones na kowani member da zai yi magana, An tanadi kayan sha jere saman table, É—akin taron yai tsit babu mai magana a cikin su, fitinannan Æ™amshin turaren jikinsu ya gauraya da sanyin A.c na comference room É—in da su ke a ciki.

Tsabar 6acin rai ne da fusata akan fuskokin su ga dukkan alamu suna fuskantar tashin hankali a jam’iyarsu, musamman party leader É—in su Alhaji bukar mai guduma fuskarshi a murtuke ta ke babu annuri, baÆ™in shi ya nunku har shining ya ke yi, Ya dunÆ™ule tafin hannayensa da ya É—aura su saman table din, Kowannan su ya É—auki wankar tsadaddiya shadda daga gani naira ta zauna masu, kuma gogaggun Æ´an siyasa ne waÉ—anda su ka jima a harkar suna gwagwarmaya, tsawon mintuna goma shabiyar, kafin shugaban jam’iyar mai guduma ya sassauta fusatar fuskarshi idanuwanshi jawur ya É—ago yana kallon mambobin su, tun daga jerin waÉ—anda ke a 6angaren damansa, Alhaji ubaid wadata Alhaji musa wadata former president, Alhaji badamasi da sauran Æ´a’Æ´an jam’iya, A hankali ya É—auke idanuwan shi daga ta 6angaren dama ya mayar dasu kan mambobin dake zaune 6angaren hagunsa, Jinjina kansa ya É—anyi yayin da ya ke fitar da huci ya soma magana tamkar mayunwacin zaki”Me ke shirin faruwane da jam’iyar mu? Zamu zauna ne mu zuba ido kamar mazurai muna kallon su? Mun É—aura shugaban Æ™asa dudu 4 yrs ya faÉ—i aza6e, mun kuma tsayar da sabon É—an takararmu ubaid wadata an kayar dashi aza6e, Ga dukkan alamu durÆ™ushewar jam’iyarmu ce tazo, tayaya jam’iyar da bata fi shekara biyar da kafuwa ba zata nemi ruguza tarihin tamu party din? A zafafe ya kai Æ™arshen maganar yana kallon kowan nan su, babu wanda yai yunÆ™urin tanka mashi saboda sunsan halin shi idan ranshi ya 6aci, wani irin bauÉ—aÉ—É—an mutunne,

Jinjina kan shi yai yayin da ya ke fitar da huci duk irin sanyin A.c da ke shawagi a É—akin hakan bai hanashi fitar da gumi ba.

“Babu irin tarihin da jam’iyar mu bata kafa fa, Ina ce shi kanshi dattijon arziÆ™in rainon jamiyar jdp ce, daga baya ne ya sauya ra’ayin shi akan wata manufa tashi ta daban wadda ba mu da masaniya akanta ya kafa tashi jam’iyar mai taken Progressive action party (PAP) Yan zu ga shi cikin Æ™anÆ™anin lokaci sun Æ™wace Æ™arfin ikon da mu ke da shi a Æ™asar nan, tsabar haÉ—ama gaba É—aya Æ´a’Æ´an shi ke juya Æ™asar nan idan har bamu ta6uka wani abu ba zamu tashi a tutar babu ne”! Ya Æ™arasa maganar tare da kai hannu Ya daki table din gaban shi, kowa yasha jinin jikin shi, damuwace Æ™arara akan fuskokin su.

Gyaran murya Alhaji Ubaid wadata yai kafin atsanake ya soma magana cikin dattako

“Allah ya huci zuciyar mai girma jagoran mu, Ni anawa ganin yakamata mu fito da dabarun da za mu bi don ganin mun dawo da Æ™arfin ikon da mu ke da shi ada, idan ma ta kama mu bi tsarin da su ka É—auko wanda yasa jama’a suke rububin tasu jam’iyar, Idan har muna so mu farfaÉ—o da tamu jam’iyar” bayan Alhaji ubaid yai magana sauran Ƴan jam’iyar kowa Yana tofa albarkacin bakinsa, Idan ka cire mutun É—aya wanda tun da ya zauna meeting É—in idanuwanshi su ke a lumshe daga gani yana da jiji da kai da izza, É—akin taron ya rikice da zafafan zantuttukan su kowa yana faÉ—in ta cikinsa, rai amatuÆ™ar amace Ya sanya hannu ya daki table É—in gabanshi wanda silar hakan ya janyo hankulansu ga dubanshi, Ƙaraminsu babbansu slowly ya buÉ—e idanuwanshi akan faces É—in su, sun kasa kunne suna jiran jin me zaice hatta shugaban jam’iyar tasu ya natsu yana jiran jin bayani daga gare shi.

Cikin harshen turanshi Ya soma magana da kakkausar murya”Let’s take a step back and focus on what we need to do right now. We need to come up with a strategy for the next election, We need to come up with a plan to fight back. We need to show the people that we are the party that can make a difference in their lives. We need to show them that we are the party that cares about their needs. We need to show them that we are the party that will fight for them, And We need to let them know that we are the party that is on their side.” tun da Alhaji musa wadata ya soma magana Æ´a’Æ´an jam’iyar su ke jinjina kansu ga dukkan alamu ya É—auko magana mai ma’ana a Æ™arshe ya daki table din gabanshi ya furta”Sharafudden obinna ba zai haura 4 years a mulki ba! AlÆ™awarine na É—aukar wa kaina, duk yadda za’ae sai mun kayar dashi a za6e na gaba, dole jam’iyar mu ce asama babu wani mahaluÆ™i da ya isa ya durÆ™usar da jam’iyar mu, abokan hammaya ba za su ta6a cin galaba akan mu ba,” yana kai Æ™arshen maganar azafafe ya yunÆ™ura ya miÆ™e yana gyara malunmalun É—in jikin shi, Ko sallama baiyi masu ba, Ya haura Æ™afa yabar cikin É—akin taron, yayin da su ke bin bayanshi da ido, har saida ya 6ace ma ganinsu tukunna suka dawo da dubansu kan maiguduma. tattaunarwar tasu ta É—auki tsawon awa É—aya kafin suka rufe taron da addu’a da kuma fatan nasara ga jam’iyarsu, ÆŠaya bayan É—aya suke fitowa harabar headquater inda jerin danÆ™ara danÆ™aran motocinsu suke a killace. Bayan sun Æ™ara gaisawa da juna kowa Ya nufi motarshi, Musa wadata Yana kishingiÉ—e a back seat na danÆ™areriyar motarshi tsadaddar gaske, Ya lumshe idanuwanshi sanyin A.c ta ko’ina, gefen shi P.A dinsa ne, security É—in da ke jigilar tuÆ™a su yana zaune a driver seat yana jiran jin umarninsa.

ƘwanÆ™wasa glass É—in motar da akayi ne yasa shi ware manyan idanuwanshi, muryar Alhaji ubaid ce ta ratsa kunnuwanshi”Ina son magana da kai” Iya abunda ya furta mashi kenan, Muryarshi da izza ya amsa mashi da toh, daga haka yaba drivern nashi iznin ya tada motar su nufi gida” A jere motocin su su ka nufi gate É—in fita daga cikin headquater É—in su…

*JOS CITY*

Zaune ya ke saman darduma cikin shigar larabawa farare ƙal, kyakkyawan balarabe daga ganin fuskarshi ba ƙaramin mutun bane ya ɗan fara manyanta, Arab turban ɗin da ke nannaɗe akanshi, ya ƙara mashi kyau ga wani kwantaccen saje baƙi wulik mai matuƙar jan hankali, lallausar sumar kanshi ta sauko har saman wuyanshi dark black.

DaddaÉ—an Æ™amshin turararen jikin shi mai matuÆ™ar sanyaya zuciyar mai shaÆ™ar shi, idanuwan shi suna a lumshe yayin da ya ke yin qira’ar Alqur’ani mai girma, Yatsun hannunshi na dama na a asargafe da cazbaha, Qur’anin da ya ke karantawa yana agabanshi saman wooden qur’anic stand dogayen eye lashes É—insa a jiÆ™e su ke sharkaf da hawaye ga dukkan alamu ayar da ya ke karantawa ce ta sanya shi tsuma.

Sam bai ji takun tafiyar mutun acikin É—akin shi ba, tafi Æ™arfin mintuna talatin da shigowa, idanuwanta akanshi ganin bai da niyar tsagaita karatun Æ™ur’anin nashi ne yasa ta ambaci sunan shi

*”DR SHUREIM*”Nasan kana jin takun tafiyata don haka idan ka kai Æ™arshen Aya ina son magana da kai”! tamkar ta yi magana da bango ko kallo bata ishe shi ba, sai ma Æ™ara sautin muryashi da ya yi” dogon tsoki taja tare da zuwa gaban dardumar ta shi ta kai hannu ta rufe qur’anin da ya ke karantawa, a tsiyace ta Æ™wace cazbagar dake nannaÉ—e a hannun shi ta É—aura ta saman qur’anin, don ta fahinci da gayya ya ke yin karatun duk don kada ya saurari maganarta.

Tana huci ta É—ago tana kallon shi still bai buÉ—e idanuwanshi ba, kuma bai dakata da yin karatun Æ™ur’anin ba domin kuwa haddace akanshi

“Ka da ka bari raina ya 6aci wlh zan yi maka abunda baka tsammani, na rasa uban me na yi ma ka daka É—aura mun karan tsana sai ka ce ba uwarka ba! Ko kana da wadda tafi ni ne a duniyar nan”? Ta jefa mashi tambayar, Shiru bai ce uffan ba, gyaÉ—a kai tayi”ilmin addinin na ka ya tashi abanza tunda ba ka san ka girmama iyayen ka ba, tsawon shekara da shekaru kana nuna wariya tsakanina da mahaifinka laifin me namaka Shureim”? Cikin jin Æ™unar rai ta yi maganar, A hankali ya buÉ—e idanuwanshi farare Æ™yal da su ya É—aura su akan fuskar Mahaifiyar tashi, ba kowa ba ce fa ce Layla mahaifiyar Benazir, Doctor shureim shine babban É—ansu, Ya ya ne awurin Benazir mahaifiyar Angel.

DaddaÉ—ar muryar shi ce ta ratsa kunnuwanta”ba ki min laifin komai ba, har yanzu kina nan a matsayinki na mahaifiyata, kawai bana buÆ™atar kusancin ki da ni” Zagayawa ta yi zuwa gefen gadon shi ta zauna suna fuskantar Juna”Nasan dalilin dayasa ka ke yin fushi dani, haba shureim tsawon shekaru nawa why za ka ruÆ™e abu aranka yai ta damun ka? Yakamata mu manta da abunda ya wuce, kuskure ne an riga da an ta6ka, kuma in sha Allahu hakan bazata Æ™ara faru wa ba” fuskarshi a É—aure ta ke babu walwala” tayi tsammanin zai tanka mata sai ji ta yi ya yi shiru bai Æ™ara magana ba.

Ƙululun baÆ™in ciki ne ya tokare mata maÆ™oshinta, zuciyarta na Æ™una tace”na lura sam faÉ—uwar mahaifinka bata dame ka ba, An ya kuwa shureim kana Æ™aunar mu a matsayin mu na iyayenka? Cos na fahimci baka son cigaban mu” murmushin takaici dr shureim ya saki, da ido tabi shi da kallo ganin yana dariya har fararen haÆ™oran sa su ka bayyana masu kyau da tsari.

“Mahaukaciya ka mai da ni? ina magana kana dariya” fuskarta a É—aure tayi maganar, YunÆ™urawa yai tare da mikewa Ya fuskance ta kafin ya soma magana”Saboda ku ba iyaye bane daya kamata a nuna damuwa akan ku! Daga ke har shi bakusan ciwon kan ku ba, Gaba É—aya hankalin ku na akan son abun duniya damuwar ku akan cigaban ku ne ba akan mu ba! Ta ya ya zan damu don mahaifina ya faÉ—i a za6e? Aini abun farin cikine agare ni, don na fahimci siyasarshi tafi komai mahimmanci awurinku! Saboda rashin sanin ciwon Æ´a’Æ´a Yau tsawon shekara goma sha shidda Benazir bata a tare da ku, hankalin ku a kwance ba ku iya ta6u ka komai ba, duniya kawai kuka sa agaba, Wlh na jima ina danasanin kasancewar ku Iyayen mu! Na yi fatan ace mutun yana iya canza iyaye da tuni na yi hakan, Nifa ba ku da amfani acikin rayuwata! Kun riga da kun yi min abunda har abada zuciyata bazata ta6a mantawa da shi ba, kune silar duk wata masifa dana tsinci kaina aciki…….” daÆ™yar ya Æ™arasa maganar cikin jin Æ™unar rai, a bun ka ga farin mutun tuni fuskarshi ta canza launi zuwa ja, numfashi yaja muryarshi adisashe yace”kun manta cewa Æ´a Æ´a amana ne agare ku? Ranar gobe Æ™iyama Allah zai tambaye ku game da amanar da ya ba ku, Rashin nasara yanzu ku ka fara gani, in sha Allah ba zaku ta6a samun abunda ku ke so ba, har tsayuwar dare zanyi maku akan kada Allah ya cika maku burinku na mallakar kujerar…..” bai Æ™arasa maganar ba sakamakon zazzafan marin da Layla ta sakar mashi, da sauri ya dafe kuncinsa da tafin hannun shi na dama, Idanuwanshi sun rune zuwa ja.

Tana hu ci ta nuna shi da yatsa”don uban ka ka tattara kayan ka kabar gidan nan tunkafin ranka ya 6aci, shashasha kawai wanda baisan ciwon kanshi ba,” Cikin sanyin murya yace”zan tafi koda ace baki kore ni ba Mommy, dama ita gaskiya É—aci gare ta, kuma in sha Allah zanje na nemo Æ´ar uwata benazir aduk inda take, idan ku bakusan ciwon kanta ba ni na sani….” tunkan ya kai Æ™arshen maganar layla ta nufi Æ™ofar fita É—aki kamar zata tashi sama tsabar 6acin rai.

Zuƙunnawa yai saman gwiwowinsa idanuwansa jawur hawaye na cigaba da gangarowa saman kuncinsa, haƙiƙa mahaifiyarshi ta fama mashi mikin dake acikin zuciyarshi, matsawa yai gaban gadon shi ya miƙa hannu ya ɗauki wayarshi yana duban hoton da ke a kan wallpaper na wayarshi, lumshe idanuwanshi ya ɗanyi kafin ya ware su sosai akan hoton da yake kallo, baya gajiya da kallon fuskarta A hankali ya furta

_ke ce silar tarwatsewar farin cikina kuma kece silar shiriyata! Ki yafe min nayi kuskuren da bazan ta6a gyara shi ba, ina son ki sosai ina jin ki har cikin raina, nasan haƙƙin ki ne ya ke bibiyar rayuwata_

kifa kansa yai saman mattress sosai ya fashe da matsanancin kuka kamar ƙaramin yaro.

Bayan fitar Layla kaitsaye ta nufi falon gidan, ranta ya 6aci sosai, kalaman Dr shureim sun sosa mata zuciyarta, yau kusan shekara uku da dawowarsu Nigeria tun bayan barin su Dubai, Layla taji takaicin faÉ—uwar Alhaji ubaid saboda tafi kowa Æ™wallafa rai akan hawan shi mulkin shugaban Æ™asa don ta ji daÉ—in yin sharholiyarta a matsayin first lady, sai dai Allah bai basu nasara ba, bugu É—aya aka Æ™undumo shi Æ™asa, tun farko sai da ya ji fargabar tsayawa takarar jin wanda za su kara da shi, don kuwa yasan muddin Sharafudden Ya nemi takarar shugaban Æ™asa zaiyi wuya ya iya kada shi, sanin farin jinin da Allah ya yi mashi, Mutun ne na jama’a mai kyautatawa al’umma.

“Hajiya..”muryar mai aikin gidan su ce a dabarbarce ta ambaci sunanta ganin yadda ta bi ta da matsiyacin kallo”lafiya”?

Cikin harshen larabci ta ce “Mun yi baÆ™i ko da ya ke sun wuce baÆ™i”

“Saboda Æ™annan uwata ne”? Ta jefa mata tambayar, Sunnar da kai Æ™asa zainab ta É—an yi”Hajiya Aisha ce matar governor tare da….” bata kai ga Æ™arasa maganar ba, layla ta dakatar da ita ta hanyar É—aga mata hannu”ni ban gayyaci uban kowa ba a gidana, Matsiyatan banza gulmace ta kawo su wato an zo aga yadda na Æ™are to ta Allah ba ta su ba Æ´an kutmar uba, jajen ne har yanzu bai Æ™ara ba abu an kusa rabin shekara da faruwarshi saboda baÆ™in hali sunÆ™i su manta..” tun da ta fara sambatu zainab ta yi kasaÆ™e tana kallon fuskarta ba ki asake, ta fahimci zallar baÆ™in ciki ne Azuciyar uwar gidan ta ta, rashin nasarar su ya tsaya mata a zuciya nema ta ke ta zauce, dama ya lafiyar gwiwa mutun mai Æ™arancin imani.

Tsawa layla ta daka mata, firgigit! zainab ta É—an zabura”Ki je ki sanar da su cewa bana nan” muryarta na É—an rawa tace”Ae an riga an faÉ—a masu cewa kina a cikin gidan, yanzu haka anyi masu iso suna acikin main palour…” daÆ™yar zainab ta Æ™arasa maganar tana mai haÉ—iyar yawu ganin irin kallon da layla ta ke jefa mata tamkar Æ™wayar idonta zata faÉ—o Æ™asa, guntun tsoki taja”masu aikin gidana sun fara raina ni saboda rashin nasarar mu dole na yi wani abu akai, su kuma waÉ—ancan taron magulmatan zanje gare su, bari na fara zuwa É—aki in zuba gwalagwalai na don kar su raina ni” acikin zuciyarta ta yi maganar tare da juyawa ta nufi sashen da É—akinta Ya ke.

Binta da ido zainab ta yi haÉ—i da É—an girgiza kanta”Allah ya shirye ki layla” har zata Juya idon ta ya sauka akan Dr shureim da ke shirin fitowa daga É—akin shi hannun shi ruÆ™e da key É—in motarshi, tsananin tausayin shi ne ya kamata ganin yadda ya canza, ta lura da damuwar da ke akan fuskarshi, a hankali yake tafiya yana tunkaro inda take ga dukkan alamu bai lura da ita ba har sai da É—an yi mashi gyaran murya, tukunna ya É—aura fararen idanuwanshi akanta, Sam babu walwala akan fuskarshi, darajar da ta ke da shi a idon shi yasa shi nufarta, ya É—auki zainab taimkar auntynsa, Babbar macace mai hankali da natsuwa.

Yana ƙarasa gabanta ya duƙar da idon shi ƙasa ba tare da ya gaishe da ita ba

“Ko ba ka faÉ—amin ba dr shureim naga damuwa akan fuskarka, na É—auke ka tamkar É—an ciki na, dan Allah shureim ka da ka bari damuwa ta canza ka, inaso ka sani komai ya faru muÆ™addari ne daga Allah, rubutacciyar Æ™addara ce wadda ba wanda ya isa ya canza ta” cikin kwantar da murya ta ke lallashinsa, sai faman karkaÉ—a car key É—in hannunsa yake yi, tun da ta fara yi mashi nasiha bai tanka mata ba sai da ta kai aya tukunna ya soma magana a tsanake “Aunty zainab na aikata babban zunubin da har abada ni nasan Allah ba zai ta6a yafe min ba, Ni kaina nayi danasin mara amfani….” duk yadda yaso ya jure ya kasa kamar Æ™aramin yaro cikin muryar kuka yaci gaba da cewa”Ina sonta aunty zainab sune silar komai, bazan ta6a yafe masu ba na tsane su, Mu kuma tamu jarabtar ta iyaye ce, basu damu da mu ba, buÆ™atar su itace agabansu, Yan zu haka da nake maki magana Mommy ce ta kore ni saboda na faÉ—a mata gaskiya, ki yi haÆ™uri Aunty zainab kada ki ce za ki dakatar dani Æ™wara na tafi, zama atare dasu bai da amfani, zanje na nemo Æ´ar uwata Benazir In ruÆ™e ta a hannuna waÉ—annan mutanan ina zargin sune silar tarwatsewar rayuwarta kamar yadda su ka yi silar tarwatsewar tawa rayuwar……” yana magana hawaye na cigaba da wanke fuskarsa, ita kanta zainab É—in tuni idanuwanta sun cicciko tab da Æ™walla, ruÆ™o hannunshi tai a cikin nata, da sauri ya É—aura kanshi saman kafaÉ—arta”Shureim Allah ba azzalumin bawansa bane, duk wanda ya cuci wani Allah zai saka mashi, ko a tsakanin Æ´a’Æ´a da iyayen su akwai hisabi, Na yi maka alÆ™awarin zan taimaka maka akan komai, ashirye ni ke dana zama uwa agareka, Ae É—a na kowa ne idan su basu so to ni inaso, dama ban ta6a haihuwa ba” jin abinda tace ne yasa shi É—ago da fuskarshi yana kallon ta, murmushi ya Æ™aÆ™aro akan fuskarshi, haÆ™iÆ™a kalamanta sun sanyaya masa zuciyar shi.

“Aunty zaina are u serious zaki taimaka min”? Jinjina mashi kai tayi alamar eh, farin cikine ya bayyana akan fuskarshi’Aunty zainab akwai wani aiki da nake so mu yi atare bana so kowa Ya sani….” bai kai Æ™arshen maganar ba, Takun tafiyar Mahaifiyarshi Ya dakatar dashi, muryar zainab na rawa tace mashi

“Ka tafi kawai zan kira ka awaya anjima sai mu yi magana” amsa mata yai da toh, Da sauri Ya fuce ita kuma ta nufi hanyar kitchen.

Cikin takun izza ta ke tafiya, har ta canza kayan jikinta zuwa tsadadden leshi wuyanta da hannyenta Zinari ne, ta buga uban ɗaurin kallabin nan ture kaga tsiya, Takalman ƙafarta high hills ne, ta wanke jikinta da turare, tana tafiya tana hura hanci

Tana dab da zata shiga palourn gidan muryoyin manyan matan da suka kawo mata ziyara ta karaÉ—e kunnuwanta, da sauri ta la6e tana sauraron abunda su ke tattaunawa

“Ae ban ta6a ganin mutum mai haÉ—amar tsiya irin Alhaji ubaid ba, nifa tun lokacin da ya sauka mulki yana fama da ciwon Æ™afa raina ya bani cewar wani munafuncin suka Æ™ulla ashe kujerar shugaban Æ™asa yake so, yanzu gashi ba wan ba Æ™anin duka sun rasa” 6a66akewa su ka yi da dariya

“Ni dama tun da naji Sharafudeen Ya tsaya takarar shugaban Æ™asa raina ya bani cewar shi zaiyi nasara, sai gashi ta tabbata, wa zai Iya ja dasu? Ganganci ne ya kai Alhaji ubaid, Ko da ya ke matar shi ce mai haÉ—amar a yadda na fahimta” hajiyar da ta yi maganar ta Æ™arasa tana dariya, wata ta É—aura da cewa”ai ko sharafudeen bai tsaya takara ba kinsan Allah ba wanda zai za6i ubaid, Mutanan da basu son darajar Æ´a’Æ´an su ba taya zasu Iya ruÆ™e Æ™asa irin nigeria mai cike da taron Talakawa? Ƴar ta fa benazir tana Æ™asar ture, ayadda naji labari karuwanci take yi kuma ana zargin uwarce ta turata, Allah na tuba zato zunubi, duk da ni dai daga majiya mai Æ™arfi naji …”Hankalin layla idan yai duba toh ya tashi, tseguminta da suke yi yayi matuÆ™ar gigitata, bata ta6a tunanin mutane zasu sanya masu ido game da rayuwarsu ba, haÆ™iÆ™a ranta ya 6aci, Ta yi niyar ta shiga tayi masu korar kare amma saita lallashi zuciyarta, Ta daidaita natsuwarta tare da yi masu sallama ta kutsa kai cikin katafaren palourn jin motsin shigowar ta ne yasa su ka yi saurin dakatawa da yin firar, É—aya bayan É—aya ta ke binsu da kallo, mata kenan abin a Jininsu ya ke…….

*UNCLE ABDALLAH*

A ƙalla yau wata ɗaya da dawowarsu Nigeria, sun fara sauka a adamawa state wurin dangin hajiya adama kafin dawowarsu gidansu da ke anan Jihar jos, zaune ta ke saman sofa mai mazaunin mutun uku, Jikinta na sanye da riga bubu ta material ta yafa mayafi akanta, Yayin da idonta ke asanye da farin glass, hutu yazauna mata ta ƙara ƙiba abunta.

Ta natsu tana kallon portrait artist ɗin dake zuƙunne agaban Drawing board Yana gudanar da aikinsa, daga ƙasa gefenshi Kayan zananshi ne, Hada hoton Angel da hajiya adama ta miƙa mashi don Ya zana mata Ita, tana son ganin yadda zata koma a shekarunta na yanzu don su samu sauƙin gane ta

“Ranki shi daÉ—e, Yarinyar zata kai shekara nawa Ayanzu”? Me zanan ne yai mata tambayar.

“I think 15 to 16 years,” amsa mata yai da okey, Kafin yaci gaba da aikin zanan shi,

“Mijina ya faÉ—a min cewa kai Æ™wararre ne a 6angaren zana mutane, so please don’t disappoint me” murmushi mutumin ya saki ba tare daya juyo ya kalle ta ba ya furta mata”In sha Allah”

“Assalamu Alaikum”! Muryar Uncle abdallace ta janyo hankulansu ga dubanshi, Shigowarshi kenan Jikinshi na a sanye da shadda launin maroon, idan ka kalli fuskarshi Sak Uzair hatta duhun fatarsu iri É—ayane.

Cikin girmama mai zanan ya gaishe da uncle abdallah, Bayan ya amsa mashi da fara’a ya É—ago ya kalli Hajiya adama”mu shiga ciki ina son magana da ke” amsa mashi tai da toh, Yai gaba ta miÆ™e tabi bayanshi, A cikin bedroom É—insu su ka tsaya suna fuskantar Juna

“Tun É—azu nake jiran shigowarka, Inataso muyi maganar zuwan mu abuja, almost one month da dawowarmu Nigeria banje naga jikana ba duk irin yadda na Æ™wallafa raina akan son ganinshi, ”

“Duk yadda kika kaiga Æ™agara da son ganinshi ba ki kaini ba,”

“Ni banga alamun hakan ba, pls idan munje mu tafo dashi, tunda ka ga bamu da wani É—a da zamu dinga kallo muna jin daÉ—i” fuskarta amarairaice tayi mashi maganar, girgiza mata kai Uncle Abdallah yai”idan mukayi hakan bamuyiwa Mahaifiyarshi adalci ba, ta rasa mijinta yanzu kuma sai mu tada zancen zamu kar6i yaro daga gurinta”? ÆŠaure fuska Hajiya adama tayi, ranta ya 6aci”Abdallah baka son farin cikina, Ni zan koma palour wurin mai zanan can” Ta ambaci hakan tare da juyawa a fusace zata tafi, Har takusa kaiwa bakin Æ™ofa muryarshi ta katse mata hanzarinta”ba zan ta6a manta irin wahalar da nasha kafin na mallake ki a matsayin matata, ta ya ya kike tunanin bana son farin cikin ki”? shiru bata Juyo ta kalle shi ba, idonshi na akan bayanta

“A yanzu haka da ni ke yi ma ki magana, na yi mana cuku cukun komawa can da zama, na samu aiki a babban companyn sharafudeen saboda ba zan Iya raba uwa da É—anta ba, haka zalika bazan Iya raba kaka da jikanta ba, shiyasa na yanke shawarar komawarmu can, Nasan hankalin ki zaifi kwanciya idan kina ganin shi akai akai” idanuwanta ne suka cuko tab da Æ™wallar farin ciki.

Fasa fita ta yi daga Cikin ɗakin, Jiki asanyaye ta nufe shi tare kwantar da kanta saman ƙirjinshi, Hannun shi Ya ɗaura saman bayanta yana cigaba da gayamata daɗaɗan kalamai masu kwantar mata da hankali, tsawon mintuna biyar kafin ta ɗago dakai Tana kallon shi

“Inaso zanyiwa Aneelerh kyautar zanan fuskar Angel da akayi min a south korea, Nasan za ta yi farin ciki saboda tana matuÆ™ar Æ™aunarta, kuma zatayi mamakin ganinta a shekarunta na yanzu don inada tabbacin idan har Allah yasa ta bayyana zamu iya ganinta da suffar da mai zanan ya zanata, kasan sun Æ™ware a iya zane” tana magana Hannunta ruÆ™e da gaban rigarshi kamar tana gyara mashi ma6allinta

“Idan ki ka bata zanan ke fa? Almost dala dubu É—ari akayi maki shi fa”

murmushi ta É—an saki”saboda haka yasa nace ka kiramin wani mai zanan ni sai na É—auke shi,” yace”mai zai hana ki bata sabon zanan da za’ayi ke sai ki ruÆ™e na koriyan? Girgiza kai ta yi alamar “a’a, Nafison nayi kyauta da abunda yafi kyau da tsada, Farin cikinta kawai nakeso,” yanayin fuskarshi ya nuna tamkar bayason taba Aneelerh zanan fuskar Angel da akayi mata aÆ™asar korea, ba ta kawo komai aranta ba saboda ta fahinci Son zanan ya ke yi ba don saboda tsadarshi ba.

“Hajiya an kammala” daga Cikin palour su ka jiyo sautin muryar me zanan, da sauri Hajiya adama ta nufi falon uncle abdallah yabi bayanta, tunkan su Æ™arasa shiga Ciki idanuwansu suka soma hango masu Kyakkyawar fuskar Angel jikin allon zanan nashi, Tsabar mamakin yadda suffarta ya fito ne yasa su sakin baki, Kamanninta sak dana tajudden Hasken fatarne kaÉ—ai na mahaifiyarta da kuma sumar kanta.

“Wow! Zanan sak kalar na south korewa nayi mamaki! Banbancin kawai tsadar kayan aikin da akayi amfani wurin yin wancan zanan amma wlh yayi kyau over” hajiya adamace take ta sambatun ganin zanan, Shi kanshi uncle abdallah Ya yi mamakin ganin zanan, Suffar Angel sak sai dai an Æ™ara mata girmanta, takai dai dai age É—inta na yanzu 15 to 16 years,

Mai zanan yana atsaye yana kallonsu, sai sakin murmushi yake yi jin yadda suke yabon aikinsa

“Ina fata Angel ta bayyana kamar yadda muka ganta a zananta, in har hakan ta faru nayi maka alÆ™awarin zan ninka maka kuÉ—inka” fuskarta É—auke da murmushi tayi maganar tana kallon mai zanan, washe baki yai yana faÉ—in”In sha Allah ranki ya daÉ—e Æ´ar ki zata bayyana kamar yadda na zana ta a hoton nan, kuma ina roÆ™on Allah yasa zanene ya zama silar ganinta” atare suka amsa mashi da ameen, Kafin tafiyar mai zanan saida suka haÉ—a mashi sha tara na arziÆ™i.

*EVIL FOREST*

*the Prisoners*

Kamar matattu haka su ka sha baccin su cikin kogon dutse, Allah kaɗai yasan awanni da su ka kwashe suna sharar bacci, Bawan Allah Danish A zaune ya ke bacci, Wutar da ya kunna masu tuni ta jima da mutuwa, Hasken rana ya kwalo daga sararin samaniya duhun dajin ya ɗan washe, A hankali ta soma mutsun mutsun buɗe idanuwanta a yayin da ta ke ambaton Sunan Allah, tsabar kumburan da idon nata yai daƙyar ta ke iya buɗe shi, ga uwar kwamtsa cunkushe da idon, kaɗan ta ke iya buɗe shi tana kallon Saman kogon dutsen, cikin rashin fahimtar ina ne? sam ta manta cewa sunbar kurkukun ƙaddara, wani irin tsorone ya kamata muryarta sam babu wadataccen sauti ahaka take ƙoƙarin ƙwalawa ƴan uwanta kira ɗaya bayan ɗaya, duk tabi ta furgice.

“Batool! Gabriel! Haris kuna ina ne? Duhu bana iya gani da kyau, Naufal wai Ba mai ji na ne”? Shiru taji babu motsin mutun a kusa da ita, Jikinta yai mata tsami, ko yatsanta ta gaza motsawa, ga dukkan alamu dannau ne ya danneta, kware muryar tayi da Æ™arfi ta furta Sunan Danish! Har cikin dodon kunnan shi ya ji sautin muryarta, slowly ya É—an ware kyawawan idanuwanshi akan fuskarta, bargon da ya lullu6a mata a iya Æ™irjinta ya tsaya hakan ya bashi damar kallon ta da kyau, duk da jinin da matsafa su ka yi mata wanka dashi ya koma mata tamkar fenti tayi muni sosai, cikin sanyin murya ya furta sunanta”My Angel” jin muryarshi yasa ta dakatawa da yin sambatun nata, Æ™oÆ™ari take wurin ganin ta motsa jikinta don ta samu damar zuwa gare shi, fahimtar hakan yasa shi matsawa dab da ita, kwanto da fuskarsa yai saitin fuskarta yai mata rumfa da faffaÉ—an Æ™irjinsa, numfashinsu har yana kokawa dana juna, kaÉ—an ta ke iya ganin fuskarshi, wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta, muryarta na É—an rawa ta furta sunanshi”Da..Nish” fatanta Allah yasa ba mafarki bane.

Dogayen yatsun hannun shi ya ɗaura a gefen fuskarta ya shafa a hankali da sauri ta ɗaura nata hannun saman nashi dake akan face ɗinta, Sai yanzu ta samu damar motsa jikinta, zafafan hawaye ne su ka soma wanke mata fuskarta, Ɗago da ita yai zuwa saman ƙirjinshi Ya kwantar da ita, duka yatsun hannayen shi na acikin sumar kanta, sosai ya ƙanƙameta, yanayin yadda su ka rungume junansu zai tabbatar maka da irin kewar juna da su ka yi, ba ka jin komai sai sautin nunfashinsu, da bugun zuciyarsu dake harbawa da sauri da sauri,

“I can’t explain how much I miss you. I’m sorry for what happened, it’s all my fault. I’m sorry, Angel.”

Cikin rauni na murya yai maganar, Cikin shessheÆ™ar kuka ta soma yi mashi magana”ba laifinka bane Danish, ka daina faÉ—in hakan, ni abunda yafi damuna rashin Æ´an uwan mu da suka rasu, na yi takaici Danish, ban cika masu alÆ™awarin da na É—aukar masu ba, Jemimah da Azeeza sunci burin fita daga kurkuku don suje gidan daddyna, haka parveen burinta ta ci abincin gidan daddyna, baiwar Allah deejah ga sauran Æ´an uwan mu da mu ka rasa” daÆ™yar ta Æ™arasa maganar, zafin jikin su duk ya É—umamasu, Yanayin weather É—in dajin San yi sosai, daga inda suke suna iya jiyo sautin kukan Namun dawa.

ÆŠaura tsinin hancinsa yai saman sumar kanta, shi kaÉ—ai yasan raÉ—aÉ—in da ya ke ji acikin zuciyarshi, Jin shiru bai tanka mata ba, yasa ta É—ago da kanta daga saman Æ™irjinshi ta É—aura eye balls É—inta akan fuskarshi, bacci ne bai ishe shi ba, sai faman lumshe idanuwanshi yake yi, a tsanake su ke Æ™arewa juna kallo tsawon mintuna goma sha biyar, ‘

“Bana so su Gabriel su farka su taras da gawawwakin su azeeza, abun zai Æ™ara ta6a zuciyarsu, ka taimaka min Danish mu binne su kafin farkawarsu,” shiru bai tanka mata ba sai kallon ta ya ke yi kamar yau ya fara ganinta

“Danish! Am talking to u, bana jin daÉ—in jikina, maganar ma daÆ™yar nake iya furtata” Still bai motsa la66ansa ba’ ta rasa meyasa ya ke kallonta yana lumshe ido Ya Æ™i tanka mata,” GyaÉ—a kai tai”shikenan tun da bazaka taimaka min ba, Ni zan je na rufe su” tana Æ™oÆ™arin miÆ™ewa sexy voice É—in shi ta ratsa kunnuwanta”Kin ta6a ganin an binne mutun da ranshi”!! ras taji gabanta ya faÉ—i a matuÆ™ar ruÉ—e ta zazzaro idanuwanta waje tana kallon shi……..

 

*Boss Bature✍️ Mu haÉ—u Monday Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun Æ™addara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuÉ—in*

 

First bank

 

3196407426,

 

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number É—ina 08103884440, Banda kira whatsapp kawai*

No comments