Breaking News

Mijin Malama Book 1 Page 11


1kne 0811923761612
Jiri ta ji yana É—ibanta, kanta na juyawa zuciyarta tayi mata nauyi, wani abu ya tsaya mata a Æ™ahon zuciya, al’amarin daya kusan haifar mata da É—aukewar numfashi na wasu daÆ™iÆ™o. Ta tsaya cak ta zama kamar wata statue, kallon Uncle Isma’il kawai take tana Æ™ara son jin gaskiyar abinda yake faruwa. Ganin kamar bata hayyacinta ya sanya Uncle Bello dake tsaye gabanta ya sanya hannu ya kama nata cikin nutsuwa da tattausan harshe ya ce “Shiga ciki, domin igiyar aure ke zagaye da ke yanzu” Abraham was spaceless kalma É—aya ya iya ganewa shi ne “Aure”
Wannan dalilin ya sanya gurbataccen tunaninsa da rashin cikakkiyar sanin zallar Hausa ya sa tunaninsa ya yi ƙaura daga fahimtar abinda Uncle Bello yake faɗa.
“Uncle?” Ya furta cikin wata murya wacce zai wahala ka fahimci me ya sauya masa murya. Uncle Bello bai iya kallon Abraham ba ya juya yana faÉ—in. “Alhaji Isma’il talk to him” Uncle Isma’il ya ce “In sha Allah”
Yana faÉ—in haka ya ja hannun Malama Majeederh zuwa cikin gidan Uncle Isma’il, Abraham yana tsaye yana bin kowa da jirkitattun idanunsa wanda azabar abinda zuciyarsa ke ciki ne ya haifar da sauyawar launin su, ya Æ™ara rungume kyakkyawan ÆŠan shi Ibrahimul-khalil wanda ya yi luff a Æ™irjinsa yana barci kamar ya samu bayan Majeederh.
Ganin Uncle Bello ya shiga ciki da Malama Majeederh ya sa Abraham ya bi bayan su In his footsteps, like a full-fledged Muslim. Irin tafiyar nan ta cikakkun musulmai.
Bayan tafiyar su, cikin kamala da nuna isa irin na Uba da nuna bar martabar Æ´ar shi g dangin miji Uncle Isma’il.
“Allahamdulillah, da farko zan fara da yiwa His Excellency addu’a Allah ya bashi lafiya ya kuma tashi kafaÉ—onsa albarkacin Ubangiji” suka amsa da “Amin”
“Na biyu, ina son ku fahimta muna so da Æ™aunar Æ´armu kuma zamu amsheta da hannu bibbiyu a duk sa’ilin da Æ™addara ta faÉ—a mata, abin nufi bi ma’ana bamu baku auren Hawwa’u a sbd ta rasa mijin aure ba, duk da Æ™addara ta kifta tare da yin kutse a cikin nagartacciyyr rayuwarta ba hana masu neman aurenta zuwa garemu da buÆ™atar su ta yin hakan ba, duba da shekarun baya duk yadda take a kame a nutse amma babu wanda ya taÉ“a furta kalmar “so” a gareta balle maganar aure ya shiga, kana taga Allah yana nasa, tayi imani hakan Æ™addara ne mu duka mun yi, sai gashi a yanzu daya kamata ta rasa mijin aure sai kuma maneman suke Æ™oÆ™arin yi mata yawa, kaga babu mai yin haka banda Al-hakkamu sarki kowa da komai, mai juya Æ™addara zuwa abu mai kyau, mai jarabtar bawansa da jarraba mai wahala” Uncle Isma’il ya da kata kana ya kalli Shugaban Jam’iyya wanda yake tamkar Uba ga His Excellency Abu-turab. Ya ce
“Ina fatan wannan dalilin ba zai zama hujjar da za a gorantawa Majeederh ba, ba zai zama tubalin da za a gina shi a gidan aurenta har a hanata sakewa ba, Shi ne ya ganta ya kuma amince zai aureta a hakan nan, wanda har yake Æ™oÆ™arin jefa rayuwar shi cikin garari, ina da tabbacin ba za a taÉ“a samun matsala daga Hawwa’u ba, haÆ™urin ta ya shige yadda kuke tunani, tana da zurfin ciki” Dattijon ya numfasa ya ce “Haka Uba na gari ya kamata ya kasance, kuma mun amshi amana zamu riÆ™e babu abinda zai sameta domin da É—a da dukiya na Allah ne, Æ™addara kuma kamar riga ce zata iya faÉ—awa kan kowa, kada ka damu zanwa His Excellency magana da zarar jikinsa ya samu”
“To, madallah madallah dai” cewar Uncle Isma’il.
Ya juya zuwa ga P.a Hammad “Hammad kai abokin Abu-turab ne na Æ™warai, kasan halayyar shi mai kyau da akasin haka, ba ina doubting akan shi ba ne, ina son sanin mene halinsa wanda ya dace ace ko wane Uba ya sani a matsayin wanda zai bada aure?”
Hammad ya yi shiru kai a kai a Æ™asa. “Ka ji tsoran Allah, a maganar aure ba wasa ba batun kuÉ—i da mulki babu wanda bashi da zuciyar da zata iya kai shi zuwa wani bigirin na sauyin hali, faÉ—a mini gaskiya” Ya É—ago kai tare da zubawa Uncle Isma’il idanu kafin ya ce.
“No!, actually no, he’s innocent bashi da matsala” Uncle Isma’il ya yi murmushi ya ce “Allhamdulillah” shugaban Jam’iyya da Dattijon su kayi godiya sosai, tare da nuna farin ciki na auren Malama Majeederh Abdul’aziz Khan, da Governor Abu-turab AlÆ™asim. Sai Hammad motoci suka shiga kai tsaye kuma Government house sukai.
Tsaye Ya samu matar shi Hajiya Luba sai masifa take,ya ja ya tsaya tare da yin shiru yana son jin wannan masifar ta mece. “Fisabilillahi duk kin cika kunnen jama’a? Hala ke da Sona ne?”
“A’a, ni da Uban Sona da Jawaad ne, yanzu abinda ku ka aikata ya yi daidai kenan? Kamar kuna neman kai da Majeederh sai a É—aura mata aure sama taka without her permission? Meke damunka tana da iko na zaÉ“awa kanta wanda take so take Æ™auna kuma ai a bari ko yaye yaron tayi?” Uncle Isma’il ya ce “Tab É—in, wannan masifar taki bata da gurbi yanzu, zuciyar fulani ta motsa kyaci kanki to” ta yi saurin tarar shi da
“Muci kan mu tare dai, naga alama shi His Excellency É—in ka kewa baÆ™in cikin gyaran Fulanin Gombe, yadda ka susu ce a kaina ka ke takaicin ya ji haka?” Ya hangame baki tare da riÆ™e haÉ“a ya ce “Haba ko da na ji, cewa zaki Soyayyar da nake miki ba banza ba, to maza maza karya asirin da ki kaiwa zuciyata ina buÆ™atar Æ™arin aure” ta maka masa harara irin ta wasan miji da mata sam bata ji daÉ—in hawan Æ™awarar da su ka yi wa rayuwar Majeederh ba. Tana buÆ™atar hutu da nutsuwa tana buÆ™atar sanin waye zai so ta, so na gaskiya waye ba zai gorantawa Æ™addararta ba. Uncle Isma’il bai tsaya da maganar ba ya ce “Ki ji tsoron Allah Hajiya Luba, ashe shi ya sa kullum ki ke zaune daram a zuciyata, shi ya sa kullum nake ganinki tamkar alawa mai tsinke a leda, Oh! Ni Alhaji Isma’il Khan, Allah na tuba ka yafe mini ina da arziÆ™in yin mata huÉ—u amma sharrin matan fulanin Gombe ya hana”
Duk yadda Hajiya Luba ta haÉ—e rai bai hanata yin murmushi ba ta ce “Stop kidding me, ban ji daÉ—i ba, ban ji daÉ—i ba kuma still ban ji daÉ—i ba, yarinyata nada gata a bari ayi mata auren gata mana? Kuma batun ta tare yau babu shi” Uncle Isma’il dariya yake sosai he’s so friendly
“To me Æ´a, ai sai dai ayi haÆ™uri aikin gama ya gama kada ki manta daman ita ba mai son bidi’a ba ce, ki yi haÆ™uri ko wacce mace darajarta É—akin mijinta, a yanzu babu abinda Hawwa’u take buÆ™ata irin aure ta zama cikakkiyar matar aure, damar data rasa a baya ita ta samu yanzu, ki dubi Allah ki yafe mini amma ki janye batun cewa sai tayi yaye ai daman ba shayar da shi take ba” Hajiya Luba ta ce “Idan daÉ—in baki ne ba daga nan ba”
“Da shi na siye zuciyar Æ´ar mutan Gombe” su kai dariya ya bata side hug ta zaro ido waje irin ya haka?. A tsaye ya samu Abraham wanda ya kasa zama har yanzu yana riÆ™e da Ibrahimul-khalil, haka kawai zuciyarsa ke faÉ—a masa something bad was gonna happen to him, babban damuwar shi yadda a karo na biyu daya hango tashin hankali akan fuskar Maluma Jee. GabaÉ—aya Uncle Isma’il ya mance da Abraham gabansa ya faÉ—i, musamman daya tuna shi Abraham bai san Æ™addara ba balle ya yarda ya kuma yi Imani da ita, cikakken mabiyin addinin Yesu ne na Injila. Ga Grandpa É—in shi cikakken Pasto ne, zuciyar su a gurÉ“ace take. Ya nisa tun kafin ya yi magana ya ji saukar muryar Abraham ya ce
“What’s going on? Uncle?” “Nothing”
“Malumana, she’s crying” “She most” Abraham ya ware idanu yana Æ™ara rungume babyn a Æ™irjinsa yana jin tamkar ya tsaga jikinsa ya mayar da shi sbd tsananin son da yake masa. Ganin kallon tuhumar da yake masa ya sa Uncle Isma’il ya haÉ—e rai, ya ce “Ba zamu shirya da kai ba, kuma ita Maminka ba dole tayi kuka ba acikin jama’a akan idanun manyan mutane dana mahaifinta ka sanya hannunka ka É—auke ta? Sbd kai baka jin nauyin aikata abin kunya daman ka saba, ka ji ma da sanin bakwai jituwa da mahaifinta yadda ka mayar masa gida kamar wani muzuru duk sanda kayi niyya sai dai ka haura, to a hir É—inka ba zan zuba idanun hakan ba, ko da wasa na sake ganinka inda Majeederh take sai na saÉ“a maka, banda abin kunya ba taci kashi da fitsarinka ta goyaka a bayanta ta yi maka wanka amma sbd….,”
“….. She’s not my mother” Unclu ya ce “Ba shakka” Abraham ya zube gaban Uncle kansa a durÆ™oshe ya ce cikin turanci “Na maka al’Æ™awari sauya, zan zama yadda addininku yake son ya zama”
“It is too late to cry, Abraham” Abraham ya É—aga gajiyayyun idanunsa kamar wanda ya sha ya yi tatul da basara ya ce “You’re kidding me, right?” Uncle ya yi shiru Abraham ya Æ™anÆ™ame Ibrahimul-khalil yana jin tamkar shi ya rage masa a rayuwa, daman tuntuni ya haÆ™ura da mahaifina. Tausayinsa ya kama Uncle Isma’il ya ce “Kawo a kai mata É—an?”
“…. No! Uncle help me kayi saving rayuwata, I love Mulumana, and am ready to convert to Islam ba zan Æ™ara taÉ“a Jeena ba sai ta zama halak a gareni” ya faÉ—a cikin turanci. GabaÉ—aya ya rasa me zai ce.
“Ok, I’ll think about that” zan yi tunani akan hakan. Ya Æ™ara da “Kai mata babyn, ask her forgiveness sai ka je ka fara tunani idan kana son musulunta da gaske”
Ya miÆ™e cikin takunsa na isa kai ka ce cikakken Muslim ne yadda yake tafiya, yana tafiya arms É—insa na motsawa yana yin jikinsa har Mmk yake bawa Uncle Isma’il, ya yi kusan ukun Abuturab baÆ™ar fatar jikinsa irin wacce ake so É—in nan, so romantic and classic. Abraham is always stronger when he has Majeederh by his side, knocking ya yi ya daÉ—e kafin ya sanya hannu ya tura cikin kamo kalman da suka rage masa na Hausa ya ce “Salamu… Alayk” tana zaune saman kujera cikin abayar dake cikinta tun safe ta zura hannunta a tsakanin cinyoyinta sai girgiza Æ™afa take slowly slowly, fuskarta tayi jajir kamar wacce ta ji ciwo haka ke tabbatar da ranta. ” I can’t believe this” Abraham said quietly. Da sauri ya ajjiye Ibrahimul-khalil ya zube gabanta tayi saurin É—auke kai, girman Abraham tsoro yake bata, musamman idan ta tuna sanda yake yaro yana binta yana Mamina, gashi da son jiki da taurin kai baya jin magana bashi da tsoro. Ya jima da sanin rauninta ya san me sanyata magana ya san abinda zai sanya ta ji sanyi a ranta, but she hate him yana ganin Æ™iyayyarsa a Æ™wayar Idanunta. Ya rasa ta ina zai fara sbd sometimes bai wani iya rarrashi ba, One thing daya iya idan zai rarrashi mutum shi ne ya rungume shi, he just give a tight hug É—in nan. Gently ya miÆ™e daga tsugunen da ya ke tare da fara zagaya É—akin yana nutsa hannunsa cikin hargitsatsiyyar sumar kan shi. Da sauri ya yi kamar zai fita sai kuma ya sanya Æ™afa da Æ™arfi ya rufe Æ™ofar bedroom É—in Majeederh tare da zura key É—in cikin wandon shi….

 

No comments