Breaking News

Mijin Malama Book 1 Page 18


MIJIN MALAMA
Paid book ne
Book 1 and 2 (1k)
08119237616
Nimcyluv19
Lokacin data koma gida ta same su duk suna breakfast Mami ta ce “Majeederh danÆ™i baya cin Æ™osai shi ya sa ban kira shi ba” Majeederh ta san babu abin da Little baya ci kawai dai bata taÉ“a gwada bashi Æ™osai bane balle ta ce. A hankali ta jinjina kanta kawai alamar “Eh” kana ta nufi cikin bedroom É—inta. Ta samu Little a tsakiyar gado ya yi É—ai-É—ai tare da langwaÉ“e kai kamar mara lafiya ta yi murmushi tana É—auke kai ya ce “Mami yunwa ina ji” a taushashe cikin sanyin murya ta ce “Na sani, bani 10 minutes”
Ya É—aga mata ta fita wajan 15 minutes ta dawo hannunta É—auke da plate É—in Indomie gefe kuma ta soya masa Æ™wai sai Æ™amshi suke. Yana ganinta ya miÆ™e tsaye yana kyakkyawan murmushi tare da tsalle ya ce “Idan na yi kuÉ—i zan baki kuÉ—i da yawa”
“Aikin me za ka yi” ya É—aga kai sama alamar tunani kafin ya watsa hannu baya ya ce “Zan samu kuÉ—i, naiwa duk wanda ya saki kuka duka” “Allah ya shirya ka ya yi maka albarka”
Ya yi murmushi da kyawawan haÆ™oran shi ta shiga bashi Indomie a baki yana zaune akan cinyarta. Bashi abincin kawai take amma a zahiri tunanin yana wani wajan daban ita kanta ba zata iya lissafa inda tunanin nata ya je ba,idan ta tafi wazai kula mata da Little? Wazai jure rigamar shi da É—akko mata magana da yake? Tana wannan tunanin ta ji yatsun shi biyar a cikin bakinta ya tura mata wainar Æ™wan data soya masa, ta zare idanu cike da maÉ—aukakin mamaki ta kasa magana sbd ya yi mata yawa a baki Little ya dinga tun tsire dry. Ta É—aga hannu kamar zata dake shi ya yi saurin rungumeta yana cewa “Sorry Mami” hugging nasa back ta yi tana shafa kansa tana gama bashi ta miÆ™ar da shi tsaye akan gadon ta kama hannunsa ta marairaice fuska ta ce “Little” “Mamina”
“Za mu gidan Uncle Isma’il yanzu” nan da nan ya haÉ—e fuska kamar bai taÉ“a dry ba zuciyarsa ta motsa ya yi Æ™asa da kansa. Ta yi murmushi domin ta san za a rina an saci zanin mahaukaciya.
Ta leÆ™a fuskarshi ya yi saurin rufe Idanu ta ce “Ba zaka ba?” Ya É—aga kai da sauri ta ce “To ni zani, ka zauna a gida”
Ya maÆ™ale ka faÉ—a ya ce “Mami mu zauna a gida” “Dole za mu, ai Uncle Isma’il É—in baya nan ka ji kuma a bayana zaka goyaka zan” ya yi saurin cewa “Baki da KuÉ—i?”
“A’a kawai tafiyar Æ™afa akwai daÉ—i” Ta tallafo fuskarsa ta ce “Don Allah banda faÉ—a ka zama nice har mu taho yau É—in zan zan maka siyayya harda motar da ka ce”
“Har bindiga?” Ta kame fuska tana É—auka shi zuwa toilet ta ce “A’a, ko soja zaka zama?” Ya yi mata shiru. Ruwan wanka ta haÉ—a kana ta É—aura masa towel ta cire masa kayan tayi masa wankan tana mamakin baÆ™ar fatarshi kamar Æ™ara mata baki ake amma baÆ™in irin mai kyau É—in nan da É—aukan Idanu. A wajan saka kaya ma faÉ—a sosai shi baya son manyan kaya dole ta saka masa wata brown É—in t.shirt mai photon tiger a jiki sai wando 3gauter kayan su kayi masa wani irin sahihin kyau tare da amsar fatar shi. Tana gyara masa sumar kai ta ce “Ka tsaya na shirya ko ka fita parlour” ya ce “to”
Tana shiga wanka ta ya fita parlour ya leÆ™a yaga Aaliyyah ta ce “Big boy yau sai ina?” Ya lumshe idanu ya buÉ—e ya ce “Da Jee zamu” Aaliyyah ta ce “To daman ka isa ka fita kai É—aya? Zo na yi maka photo” ta tsayar da shi a gabanta ta shiga yi masa photo suna tsaye Raihana ta fito ta ce “A’a É—an baÆ™i na Anti Jeederh, kaga yaro mai uwar rana” bai kalleta ba daman jininsa bai zo É—aya da ita ba. Little yana da wanne irin hali ga shegen wayon masifa kamar wassafa masa wasu abubuwan ake. Duk wanda suke takura rayuwar Majeederh ya haddace su tar kuma baya kula su. Raihana har ranÆ™washin kansa tayi ta ce “Miskilin banza, daga gani uwarka fama tayi dakai kafin ya É“ata” “Mamin?” Ta ce “Uwarka na ce, ko an faÉ—a maka MAJEEDERH ita ce Uwarka?” Ya yi shiru kawai domin baya fahimta gabaÉ—aya. Suna nan yana yiwa Aaliyyah surutu yana itama zai siya mota bayan ya siyawa Maminsa Æ™atuwa “Wato dole sai ka nunawa kafi son Maminka, to ai Mamin taka tafi so na” ya maÆ™ale murya ya ce “A’a” Aaliyah ta yi masa gwalo ta ce “Ohho, wooo Mami ta fi so na akan ka” nan da nan ya haÉ—e fuska duk da yaro ne amma ya tsani ace Mami bata son shi. Aaliyyah za ta yi magana ya ji an sakar mata ranÆ™washi akanta. Ta kwaÉ“e fuska ta ce
“Kai Anti Jeederh akan Little zaki dakeni” Little ya yi tsalle sosai ya ce “Mamina” Majeederh dake tsaye sanye cikin shigarta as usual abaya ce mai kyau da É—aukan hankali ta yi rolling kana ta É—ora liÆ™ab. Cikin wani sabon yanayi data samu kanta ta ce “Ki kiyayeni Aaliyyerh” Aaliyyah ta tura baki ta ce “To Anti Jeederh ai da gaske kin fi so na” Little ya kalli Majeederh yana jiran ya ji me zata ce. Sai bata ce komai ba ta kama hannunsa zuwa bedroom É—in Mami ta sameta zaune ana ta buga waya ana faÉ—awa Æ´an-uwa an kawo kuÉ—in Rumana Dubu É—ari biyu cif. A sanyaye ta ce “Mami na ta fi” Mami ta ce “Zuwa ina?” “Gidan Uncle Isma’il, Yaya Bilkisu na kirana” Mami ta ce
“To to na ji, yanzu Ruhuma zata wajan Widad maganar ankon biki Imrana ne zai kaita na ji ma ta ce yana hanya ki bari ku ta fi tare, kici arziÆ™in Æ´ar-uwarki ko?”
Bata son musu sai kawai ta ce “To” tana fitowa ta ja hannun Little su ka yi waje. A bakin Æ™ofa taci karo da Latifa cikin shigarta riga da skirt na atamfa ta yafa mayafi ta kalleta sosai sai bata ce komai ba. Latifa ta yi dry ta ce “A’a fa yadda kike takura kanki da zafi cikin duguwar riga da liÆ™ab ni ba zan iya ba, shi imani a zuciya yake” Majeederh ta ce “Wane ya yi maganar imani?” Latifa ta É—aga kafaÉ—a ta ce “yanzu zaki fara faÉ—ar na bayyana tsaraici ki shiga kawo fatawa kala-kala, ke dai ka san ko a malamai tsaurin ra’ayi zaki” Ita dai Majeederh bata ce komai ba Latifa ta sake cewa “Sai ina?”
“Gidan Uncle Isma’il” “mu je na rakaki” tafiya suka fara a hankali Latifa ke surutu ita É—aya domin Majeederh idan ka ji maganarta Little ne ya ce wani abu ko da Aaliyyah da suke Uwa É—aya Uba É—aya bata fiya hira da ita ba, sai dai faÉ—a idan ta yi kuskure akan abu. Tun da ya karyo kan motar shi idanunsa ya sauka akanta, wani irin maganaÉ—isun abu ya shiga fisgarsa zuwa gare ta. Ya tsorawa yatsun hannunta idanu wanda suke É—auke da Little dake kafaÉ—arta a hankali yake lura da juyawar Idanunta tana bubbuga bayan yaron tafiyar a hankali mai cike da É—aukan hankali wani abu ya ratsa zuciyarsa irin abun nan da ake kira da soyayyar fari, har suka zo daidai motarshi bai kula ba sai da suka gilma kaÉ—an ya sauke numfashi tare da buÉ—e motar shi ne ya fito. Kyakkyawan matashin saurayi mai fama da rufin asiri daka gani yanzu yake ji da samartakar shi. Fari ne kyakkyawa mai matsakaicin jiki nutsuwa da ilhama a tare da shi, yana sanye cikin kyakkyawar shigar dake nuna kamalar shi. Amy green É—in shadda ce a jikinsa ya murza hula saman kansa zai Æ™amshin turaren (Thierry mugler). Ƙamshin dake narkar da dukkan wata zuciyar Æ´a mace. Ya Æ™arawa tafiyarsa sauri harya tarar da su tunda ba wani sauri suke musamman tafiyar Majeederh wacce take kamar an zare mata laka. “Assalamu alaikum” Cak suka tsaya tunda sun san darajar sallama babu cancantar suna tafiya kuma wani na binsu. Ƙamshin Thierry mugler bai firgita Majeederh ba, deep down na zuciyarta addu’a take Rabbil izzati ya sanya wa’adin zamanta a gidan Abbu ne ya zo Æ™arshe, addu’ata take Allah ya sa mai rusa zuwanta karatu ne ya bayyana, Al-hakkamu sarki kowa da kowa ya Æ™addarta masa ikonsa a yanzu nan, Allah ya da mai yaye mata damuwar dake sanyata azumi ne ya zo. Ta rufe Idanunta tana jiran Æ´ar manuniyyarsa ta tsaya akanta. “Wassalam” cewar Latifa tana duban matashin wanda ya amsa komai na kamalar mutum. Ya dinga kallon Majeederh ba zai ce ga kalar kyan fuskarta ba, amma yatsunta sun bayyana wace ita abubuwa da yake ji game da ita sai ya ji sun ninku ainun kamar zubar ruwan sama ya yi da hadari ya Æ™ara kankame. Cikin wani irin al’amara da gilamar wasu sabbin Æ™addarori masu wahalar fasaltasu ba tare da sanin abin da yake faÉ—a ba ya juya gabaÉ—aya kan Latifa ya ce “Amincin Allah ya tabbata ga ma’abociyar kyau da kwarjini, fatan san samu number wayarki ganin akan hanya kuke” a baÉ—ini kalamar direct domin Malama Majeederh Abdul’aziz Khan! Ya zayyana su amma a zahiri tubalin ginin maganarsa da yadda ya zayyana su ya nuna mai fahimta da ganin komai cewa da Latifa Omar yake. Latifa ta yi jim ta ce “Ni, ko ita?” Ya É—an tafe baki kaÉ—an ba tare sanin ainahin abin da yake ba ya ce “No, dake nake kyakkyaw” Dam! An koma. Zuciyar Majeederh ta bada sauti ta Æ™ara rufe Idanunta Allah ya sa zalamarta bata fiyi ba balle ta kunyatar da ita. Majeederh ta Æ™ara lamuncewa zuwa karatun nan nata na daga cikin Æ™addarorinta masu girma. Latifa ta ce “Amma sauri muke” “Kuyi mini alfarma ba don na isa a yi mini ba, sai dai ta yaku kare mutumci ku shiga na Æ™arasar daku” ya faÉ—a yana haÉ—e hannu bibbiyu. Latifa ta juya ta kalli Majeederh ta ce
“Malama Majeederh ke ce me matsala Kinga Little har ya yi bacci ki zo mu je” Bawai fuskarta suke gani ba,amma ta Æ™ara kame kanta bata da wani kuzarin yin magana. Ya juya a hankali da É—an sauri kuma ya buÉ—ewa Majeederh Æ™ofa ta shiga a nutse da addu’a bakinta. Ya buÉ—ewa Latifa Omar gaban motar ta shiga. Tafiya suke a nutse ya gyara zama ya ce “Sunana Barrister Aliyu Sufyan Alhassan” “Nice” Aliyu ya shafa gemu ya ce “A gida more especially Hajia suna ce mini Zaki, am the second born of my parents, ina da babba yaya Almustapha, mahaifina sunan shi Sufyan Alhassan yana nan tare damu, ya su nayi aikin jarida na Æ™i, to ya na iya abincina yana ga Shari’a, sai mahaifiyata we call her Hajiya, I love my mother more than anything dake duniyar nan tamu, na yi karatu mai yawa akan Shari’a now an working with Shari’a court of appeal ban jima da fara aiki ba” Tunda ya fara magana Latifa ta rufe Idanu sosai har cikin zuciyarta Aliyu ya kwanta mata irin mijin da take so daka gani zai yi haÆ™uri sosai. Har suka isa gidan Uncle Isma’il Majeederh ko tari ba tayi ba ta rungume Little kamar zata mayar da shi ciki, lokaci zuwa lokaci Aliyu ya dinga kallon Majeederh ta madubi, duk sanda ya kalleta sai ya sauke numfashi a É“oye. Suna tsayawa ta buÉ—e Æ™ofa ta fita ta shige ciki, da sauri kamar wacce wani abu ya biyota. Innati dake maÆ™ale a bayan labule ta buga tsalle tana faÉ—in “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un, wahala haula wala Æ™uuwata, uban waye a wannan wajan?” Majeederh ta shiga tana sauke numfashi Innati ta ce “Amma dai Allah ya isa Kululu, Allah ya isa saura kaÉ—an na saki gudawa É—aukan hakÆ™in nan har ina? Ashe Æ™atuwar jahila muke zaune da ita kinsan alhakin da kika É—auka? To wallahi ba wani yafewa nayi Æ´ar banza da fuska kamar karas” Majeederh ta tura baki tare da kwaÉ“e fuska ta ce “Ki barni” Innati ta riÆ™e haÉ“a ta ce “Na barki ba? Idan na barki a duniyar nan Kululu na kama ubanwa? Wa kike da shi daga duniya har lahira wanda ya shige ni?” Majeederh dai ba tayi magana ba ta É—aga liÆ™ab É—in fuskarta Innati ta zabga sallati ganin yadda fuskar Majeed ta yi jajur kamar jini ya kwanta. Innati ta kwasa a guje zani na faÉ—uwa ta shiga faÉ—in “Muhammadur Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama, Isma’ila masifa ta faÉ—o mana uban kowa ya yi ta kansa Aljana mai kama da Kululu a É—akina….

*A yi karatu a nutse, a fahimta a ilmance, a nishaɗantu. Muna nutsawa a labari zaku kasa bacci da sukuni. Soyayya ce mai wahalar gogewa, ƙaddara ce mai wahalar fahimta. Babu batun sadaukarwa faɗa ne akan Soyayya!*

Allah ya nuna mana Monday Lafiya, a yi weekend cikin farin ciki…. 08119237616

Nimcyluv20
“Masifa da bala’i, Kamarni har wata Aljana ta isa ta firgita? Ina Isma’ila ya zo ya yi mini iyaka da wannan Aljanar tun kafin raina ya É“aci” Innati ta faÉ—i hakan jikinta gabaÉ—aya rawa yake na fargaba da tsoro, tuni ta yi wurgi da zanin jikinta sai É—an tofin daya rage mata banda haka tsirara za ta yi.
Uncle Isma’il daya fito a hargitse sbd jin kiran shi da Innati ke yi ya sa yana zuwa ya ce “Innati lafiya dai? Mene ya faru?”
Ta girgiza kai ta ce “Lafiyar kenan, maza maza a haÉ—a mini kayana yau sai gidan Bello, ba zan zauna matarka da kasheni ba, ina sane ita take tura mini Aljanu” Uncle Isma’il ya kusan tuntsirewa da dariya amma babu hali duk abin da ya kuro É“era da ga wuta, ya fi wutar zafi. “Majeederh ta Æ™arasu?” Ta zare idanu ta ce “Wata abace haka? Ka je dai kaga turan da akai mini da wata Bafullatanar Aljana” Uncle Isma’il ya bar Innati a tsaye, tare da nufar É—akinta. Yana shiga ya samu Majeederh durÆ™oshe a saman gwiwoyinta ta dafe kanta da hannu bibbiyu wanda yake bazaranar rabe mata gida biyu sbd tsananin ciwon da yake mata, ta rufe idanu sosai sbd komai bibbiyu take ganinsa a cikin idanun nata. Uncle Isma’il ya zuba mata ido cike da tausayinta yasan duk abin da zai sanya Majeederh cikin wannan yanayin ba abu ne mai sauÆ™i ba. Ya dubi Little dake tsaye ya É—ora kansa a bayanta ya saÆ™alo wuyanta tare da yin lamo, yanayin Mamin tasa ya taÉ“a kuzarin yaron. Ya nemi waje ya zauna saman kujerar dake É—akin na Innati, cikin kulawa ya ce
“Hawwa’u!” Ta yi sauri ta É—ago kanta tare da Æ™aÆ™aro murmushi ta É—orawa fuskarta matsayin dole. Cikin sanyin murya kamar kullum ta ce “Ina yini Uncle?” Ya ce
“Lafiya” ya yi jim kafin ya É—ora da “Ke kika firgita mini uwata ko?” Ta Æ™ara yin murmushi kamar ba za ta yi magana ba ta ce
“Da Aljana take haÉ—ani fa” Ya yi murmushi ya ce “Dole ta haÉ—aki da Aljanu, ni kai na mamakin kyan da Ubangiji ya yi wa Æ´ata nake, sai yanzu nake Æ™ara ganin cancantar suturta fuskar da kike”
“To ALLAH ya isa, Allah ya isa shi kaÉ—ai zai isar mini idan ka yafe Allah ya tsine” Innati dake bakin Æ™ofa tana leÆ™owa ta furta hakan lokacin data tabbatar Jikarta ce Majeederh Abdul’aziz Khan! “Ki yi haÆ™uri Innati”
Innati ta fashe da kuka sosai tana face hanci ta ce “Wallahi ba dani kike ba, ba kuma ni ki kaiwa ba, Ubanki mai faÉ—in ran nan da manyan Idanu Audil azizu shi kika tsoratar” Majeederh dai bata kulata ba, domin tunaninta baya wajan gabaÉ—aya zuciyarta tana wani birgire wanda kullum take ganin kanta acan, a cikin mafarkanta na kullum.
“Majeederh wa kika bari a waje? Na ga mota” Uncle Isma’il ya faÉ—i hakan cike da zumuÉ—in jin Majeederh ta ce wani ne ya kawota, addu’a yake Allah ya sa nata rabon auren ne ya zo.
“Latifa Omar ce”
“Ayya to, Allah ya amfana” Ya gyara zama sosai ya ce “Hawwa’u ki faÉ—a mini gaskiya, mene hujjarki na barwa Rumana saurayin dake son ki yake son aurenki a lokacin baya, sai yanzu kwatsam! Reshe zai juye da mujiya wai kin fasa auren shi ya auri Æ™anwarki Rumana anya akwai Æ™amshin gaskiya? Domin na lura da rashin nutsuwarki, A can gidan” Ta yi shiru domin bata da amsar tambayar Uncle É—in nata, ita yanzu a yadda take ji ko sa’an mahaifinta Abbu aka bata matsayin miji da gudu zata amsa, koda ha za ta yi farin ciki ba da zama da shi muddin zai É—auke buÆ™atar ta, wacce ke damunta take sanyata rama da ibadar dole.
“Ina jinki, kin fi ganewa ki zauna duka Æ´an-wanki su yi aure ke kina gida? Kin fi ganewa ki gansu da mazajansu gwanin sha’awa suna yin soyayya da rayuwar aure mai tsafta? Su haifi Æ´aÆ´a wanda ko wanne mai rai yake muradi, inma namiji inma mace? Zuciyarki ta yi rayuwarki adalci? Anya Hawwa’u-Jidderh?”
“Ka yi haÆ™uri Uncle, Idan da rabo zan yi auren”
Maganarta ta narkar da zuciyar Uncle Isma’il, kalamanta sun nuna karaya zahirin fuskarta kuma ta amshi Æ™addarar tare da godewa Allah bisa tarin Ni’imar da ya yi mata, tasan yana sane da ita bawai barinta ya yi ba. “Shikenan, ALLAH ya yi miki Albarka ki je wajan Luba” caraf Innati ta ce “Wacce masifar ce Luba? Ka fita daka idanuna Isma’ila matar taka da ban gama sanin zuciyarta ba ita zaka turawa Kululu? Ƴar Gombe? Wato ta tsaface ta bayan kasan yadda Fulanin Gombe suke?”
“Allah ya baki haÆ™uri Innati, zan shige taron da ake yau babu mamaki na samu dacewa da aiki mai kyau” “A to! Ya dai fi maka, kamar tsiya akan Æ´aÆ´ana ta kare kowa fama yake da kansa da azababben talauci, In sha Allah tsalelen miji Kululu zata aura na tarkata na koma gidanta” Murmushi kawai Uncle Isma’il ya yi tare da shafa kan Little ya ce “Yau ba magana?”
“Mami kakewa faÉ—a”
“To É—an Maminta Allah ya baku haÆ™uri kai da Mamin” Yana fita Innati ta yi Æ™asa da murya ta ce
“Munafuki, ai duk tsinewa matarsa da nake to ta shi nake, daga shi har Ubanki Audil azizu sai na kai su hisba uban kowa ya huta, turmin atamfar ankon wannan yarinyar Wifat fa na ce ya siya mini wai bashi da shi?” Ta Æ™ara girgiza kai ta ce “Hoo! Ƙasa Ubangiji ya baki miji mai kuÉ—i wanda zai so ki”
Majeederh ta marairaice fuska sosai ta ce “Innati bar maganar auren nan”
Innati ta riƙe haɓa ta ce
“To ba zan bari ba, Annamimiyya ina nan watarana idan ban mutu ba sai mijinki ya sunkuya ya miki doki-doki dake da yaran da zaki haifa, wallahi ko bana raye sai kin tuna wannan maganar tawa, zaki haifi zuri’a mai yawa zuri’ar da babu Uban wanda ya taÉ“a haifarta a cikin Æ´an-uwanki da iyayen naki” Majeederh ta lumshe idanunta a zuciyarta tana tona tsayin shekarun da zata É—auka kafin tabbatuwar hakan! Innati ta fashe da kuka ta ce “Allah ba zai barki haka ba, wallahi halin Uwarki Fulani kika É—auka, har tsinannen kyan da kike da shi duk nata ne, ki rubuta ki ajjiye watarana sai labari ni dai ki sani ina son ki ba zan baki gurguwar shawara ba, amma dai Allah ya yi É—aiÉ—ai da zuciyar Rumana” Surutun Innati ya hau wa Little ka, daman ba daÉ—i yake ji ba ta shagwaÉ“e fuska tare da fashewa da kuka ya faÉ—a jikin Majeederh ya Æ™anÆ™ameta “Mami gida”
Majeederh ta yi saurin rungume shi tana shafa kansa yau É—in gabaÉ—aya ta rasa meke damunsa ga kanshi zafi kamar mai zazzaÉ“i. “Innati kin firgita mini yaro” Innati ta riÆ™e baki ta kasa cewa komai sai can ta ce “Ba zan ce komai akan yaron nan ba, amma dai a guji gobensa akwai abubuwan Al’ajabi cikinta” Majeederh ta É—auke É—an ta tare da rungume shi sosai a Æ™irjinta tana ji yana sauke numfashi ya Æ™anÆ™ameta.
Latifa Omar ta yi murmushi mai kyau tare da kallon Aliyu ta ce
“Kana da abin dariya”
Aliyu Sufyan Alhassan ya ce “Uhm Latifa Ina son ki, bana son a É—auki lokaci ki bani dama”
“Daka ganin sarkin fawa sai miya ta yi zaÆ™i?” Ya yi murmushi kawai kana ya ce “Bani labari”
“Na me? Akan wa?” Latifa Omar ta tambaya. Ya ce “Your friend”
Ya nuna Æ™ofar gidan da Majeederh ta shiga. Latifa ta juya idanunta ta ce “Oh, Sunanta Majeederh Abdul’aziz Khan! Iyayenta suna yawan ce mata Hawwa’u, Æ™annenta musamman Aaliyyah tana ce mata Jeederh. Mun yi makarantar primary lokacin É—aya, amma ta fini Æ™oÆ™ari ne sa ba kusa ba, da yawan lokaci ina hana kai na bacci ganin na zama ita, sai na fahimci iliminta baiwa ce, daga Allah. Biye É—aya takewa ayar Alkur’ani ta hadda ce ta, tun muna primary ta rasa mahaifiyarta, she left her, at the same time ta yi saukar Alkur’ani, ni kuma na maimaita aji, a lokacin da ta zama hafiza a lokacin na yi sauka ta farko” Ta yi jim,tana rayuwa da step mother É—in ta, kishiyar babbar ta, ilimin Majeederh ya sa Manyan mutane na primary school É—in mu suka shige mata gaba wajan samun scholarship a matakin secondary school, ta samu makaranta mai kyau tun a lokacin Karatun ta a É“angaren Islamic yake, yanzu maganar da nake maka ranar Candy ranar ta zama Gwarzuwa a É“angaren musabaÆ™ar Alkur’ani, wannan shi ne kashi na wajan uku na dai manta Makarantarmu Ahlul Madar tana bada sunanta matsayin wacce zata jagoracemu, yanzu haka sunanta yaje ko’ina duk wata gasar karatun Alkur’ani indai Kano zamu shiga to ita za ta yi” Ta ja aya tana sauke numfashi. Tunda ta farar maganar idanun Aliyu a rufe yake ruf ta ce
“Lafiya?” A taushashe ya ce “Ina jinki”
“Majeederh ta zama malama a Ahlul Madar duk wata suna bata albashi, da albashin take kula da yaron daka gani a wajanta” Ya ware idanu da mmki ya ce
“Yaro? I heard you kin ce single take, not house wife” ta ce “Eh, Tsintar yaron ta yi, kuma tana son sosai banda kada na yi maka Æ™arya bayan iyayenta babu wanda take so kamar Little, tana iya haÆ™ura da cikinta ta bashi ya ci, kuÉ—in Makaranta, kayan sawa duk da albashinta take masa, kuma a ciki take taimakon Abbu da abincin gida, by the way yanzu tana shirin tafiya Æ™asar waje Africa, ta samu scholarship za ta É—ora University É—in ta a can É“angaren Islamic and Arabic studies”
Ta yi shiru ganin kamar Attention É—in Aliyu baya kanta ta ce “Ya dai?”
“Wacce Æ™asa?” Ya faÉ—a yana murmushinsa mai kyau da aji. “Misira”
“Ok Egypt, Allah ya taimaka” Latifa Omar ta ce “Amin”.
A can cikin gida Hajiya Luba ta kalli Majeederh ta ce “Yanzu karatun zaki?” Majeederh ta sauke ajjiyar zuciya a fili tare da jinjina kanta alamar “Eh, Mama”
“To Ubangiji ya sa rabokin ke kiranki, Allah ya baki ikon cinye Æ™addarorinki mutane ne kawai da basu son zama lafiya gabaÉ—aya nawa kike balle Æ´an-uwanki shekaru Ashirin bai ci har a fara gorantawa mutum bai aure ba”…
“…… Allah ya kyauta”
Ta ci-gaba da bata haƙuri da ban mamaki. Har Latifa Omar ta shigo suka ta fi gidan Yaya Bilkisu domin acan ake Sabgogin bikin Widad ɗin. Ko! Da ta je bata iya zama ba ƴan matan familyn Khan, suka shiga sauke magana. Kusan duk akan Idanunta aka haife su sbd rashin aure ya sa girmanta ya zube. Tana zaune kiran gaggawa ta sameta zuwa Orphanage for young children, kira ne daga kai tsaye daga Akeeth. Yaya Bilkisu ta bata kuɗin napep daman tuni ta ce Latifa Omar ta tafi kawai. Tana gab da zuwa ta sake kiranta.
“Assalamu alaika”
Majeederh ta furta cikin muryarta mai sanyi daÉ—i a kullum. Akeeth ya amsa ya ce “Am sorry Majeederh,na samu meeting na gaggawa idan na gama ko kiranki ne zan yi” Jikinta san yi Æ™alou ta kashe wayar ba tare data ko amsa masa ba.

Unguwar Darmanawa
Idanunsa rufe yake kallon selling É—in dake cikin bedroom É—insa, lokaci na farko a rayuwa da ya yi nauyin baki wajan furta abin da yake so. Ya juya kaÉ—an yana sake mirginawa hoton idanunta kawai suke gilmawa cikin nasa idon, ganin abin bazai goge ba sai ma Æ™aruwa da yake ya sa a hankali ya miÆ™e ya shiga bathroom tare da sakarwa kansa shower yana riÆ™e Æ™ugunsa bugun zuciyarsa na Æ™aruwa gabaÉ—aya Latifa Omar ba tsarin aurensa ba ce, me ya kai shi? “Density” Shi kansa bai adadin lokacin daya É—auka a bathroom É—in ba, sai da ya ji ana knocking Æ™ofar part É—in shi ya fito É—aure da towel a jikinsa.
“Meke damun É—an autan Hajia yau da bai yi dinner damu ba?” Aliyu ya shagwaÉ“e fuska sosai autar ta motsa daman rauninsa da wuri yake fallasa asirin zuciyarsa. Ya ja baya yana zama kan kujerar dake kusa da gadon shi, É—an Æ™asar Turkiya. “Hajia”
“Na’am Autan Hajia” Hajia ta amsa tana jiran ta ji dame yau kuma ya zo, domin shi Aliyu baya rabo da issues sbd tsabar taÉ“ara gashi kyakkyawan ajin farko sai ka É—auka Half-caste ne. Looking so classic. “Aure zan yi, na samu mata” Ya faÉ—i hakan domin a tunaninsa shi ne mafita ga abin da yake ji, wacce zai aura daban, wacce ta yi zuciyarsa kamo daban. Ko mene hakan hakan? Only God knows.
Sosai Abbu ya yi wa Majeederh faÉ—a don me bata Æ™arasa ta karÉ“o form É—in ba? Ita dai bata ce komai ba ita kaÉ—ai ta san abin da take ji. Yau É—in ma sai da ta yiwa Little wanka ta sanya masa kaya masu É—an sauÆ™i bata son ya kwana da zazzaÉ“i. Ta tsora masa idanu a hankali ta ce “Little zaka manta dani?” “Me?” Ta tambaya domin bai fahimta ba.
Ta ce “Idan na ta fi karatu, karka manta dani ka ji? Kada ka bawa wata matsayin uwa a zuciyarka idan ba Maminka ta gasky ba, ka da ka ci amana” Ita kaÉ—ai take magana ita kaÉ—ai kuma take fahimtar me take cewa. Ya shafa laÉ“É“anta da suke jajir ya ce “Mami ni ma irin naki”
Ta yi murmushi tana É—aukar shi tare ta É—ora a cinyarta ta ce “Until you grow up” Ya shiga buga Æ™afa da yarfe hannu shi a dole sai laÉ“É“ansa sun yi irin na Maminsa Jee ta tura masa baki ta ce
“Ok Shafi kaÉ—an, da safe sai koma red” Ya yi murmushi yana tsalle ya É—ora bakinsa a nata ya shiga goga sai ta gaji ta É—auke shi tana dungure masa kai, Æ™ara wayarta ta yi tana duba taga albashi akai mata sosai ta ti farin ciki gobe za ta yi masa siyayya. Tunanin yadda zata rabo da Little tsayin shekaru takwas shi ne ya bijiro mata, rabon da ta yi kuka ta manta sbd kansa cewar ta mace jaruma da zurfin ciki. Ta samu kanta da rungume Little ta fashe da kuka sosai, kukan da rabon da ta yi shi tun rasuwar Fulani. Wani irin kuka take da dukkan Æ™arfinta wanda yake tasowa tun daga Æ™asan zuciyarta. Ganin tana kuka ya sa Little fashewa da kuka sosai. Da Æ™yar ta rarrashe shi suka kwanta bacci. Kiran sallarsa farko ya farkar da Majeederh daga bacci a hankali ta shafa tana son taÉ“a jikinsa ta ji ko da zafi. Wayam! Ta buÉ—e idanu taga babu Little a kan gadon ta miÆ™e da sauri idanunta ya sauka akan Æ™ofar É—akinta dake buÉ—e bayan har rufewa ta yi. Da sauri ta ce “My Son, Little?….

No comments