Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Mijin Malama Book 1 Page 19


Paid book
MIJIN MALAMA
0811923761621
Sosai Majeederh ke kuka kamar ranta zai fita har da shassheÆ™a Mami dake tsaye ta riÆ™e haÉ“a ta dubi Majeederh ta ce “Yanzu ke kina Ina yaron ya zare sakata ya yi nasa waje” Ta kasa cewa komai sai kuka gabaÉ—aya hankalinta ya ta shi ta zama kamar Æ™aramar yarinya. Mami ta Æ™ara tafa hannu ta ce “Yaro ne mai shegen karambanin tsiya, ko gidan uwar wa ya sani wanne hannu zai faÉ—a ohho, ga yadda Æ´an mafiya da Æ´an kidnaping su ka yi yawa a gari” Majeederh ta Æ™ara rushewa da kuka ta ce “Little ba zai taÉ“a buÉ—e Æ™ofa ya fita ba, ina yaga tsayin?” Aaliyyah ta ce
“Kuma ko ya iya buÉ—e Ƙofar É—akin ki Anti Jeederh ai ba zai iya buÉ—e Æ™ofar waje ba” Abbu wanda ya fito da shirin fita Masallaci ya gyara muryar kowa ya shiga hankalinsa kamar sun ga mala’ika ya dube su É—aya bayan É—aya kafin ya ce “Lafiya?” Ruma ce ta ce “Abbu wai Little ne ba a gani ba” Ya yi jim alamar tunani kana ya kalli Majeederh dake fuskarta ta yi jajur a cikin wutar lantarkin dake gidan. “Hawwa’u garin ya ya?” Jikinta na rawa ta ce “Abbu wallahi ban sani ba, tare muka kwanta sai da ya yi bacci na yi, yanzu na farka nayi raka’atul fjr na ga babu shi” Ta goge hawayen fuskarta wasu na sake zubuwa ta ce “Na rufe Æ™ofa, amma na ganta a buÉ—e” Ya dubeta sosai yana nufar waje ya ce “Allah ya bayyana shi, akwai ban mmki? Wani ya shigo? Wani ya buÉ—e masa Æ™ofar? Ko fita ya yi da kansa?” Ruma ta É—aga kafaÉ—a tare da shigewa É—akin da suke kwana su uku, ita, Raihana, Aaliyyah. “Abbu zan je duba shi?” Da sauri ya ce
“Ina?” Kanta a Æ™asa tana shassheÆ™a ta ce “Waje, maybe yana waje ko police please Abbu”
“…. Bada yawona ba”
Cewar Abbu. Ta marairaice fuska ta ce “Ka tausaya mini, bashi da kowa” Cikin tsawa ya ce “Ki fita daga idanuna Hawwa’u, ke bakya tausayin kan ki sai yaron da baki san waye ba? Kin san wanne kallo ake miki a unguwa? Wasu tunaninsu É—anki ne kawai kike É“oyewa, to wahainiyarki ta kiyaye ramata, nan da waje kika fita dalilin neman yaron nan ban yafe ba, ina akan shi kika Æ™i zuwa karÉ“o form wato kin girma kin manta wahalar dana sha akan ki, har ki ka yi growing zuwa yanzu? Idan kika je Misira yanzu kin san irin matsayin da zaki taka? Ni za Hawwa’u ni mahaifinki?” Ya Æ™are maganar yana nuna kansa da yardarshi. Majeederh ta zube gaban Abbu akan gwiwoyinta hawayenta ya tsaya zuciyarta ta yi mata nauyi sosai ta kasa tantance wanne kalar yanayi take ciki. Ta riÆ™e Æ™afafuwan Abbu ta ce”Na tuba Abbu, na tuba na bi Allah na bika Mahaifina ka yafe mini zan zama yadda ka ke so, zan yi karatu zan je matakin da kake buÆ™ata ka yafe mini Abbu don Allah?” Aaliyyah kukan tausayin yayarta Majeederh ya kamata ta durÆ™oshe a wajan tana kuka sosai. Abbu ya É—an sassauta murya ya ce “Ki je anjima zan kira ki, amma ki cire maganar yaron nan a ranki” A karon farko a iyakacin rayuwarta da za ta yi wa Abbu magiya ta ce “Abbu please… Little.,”
“This is noises!”
“Ka yi haÆ™uri” Jikinta duk rawa yake kamar ba babbar Æ´ar daya haifa ba ta yi cikin É—akinta. Sosai Raihana ta ji tausayin Anti Jeederh amma babu yadda ta iya, ta ja bakinta ta yi shiru. Mami ma É—akinta ta yi tana É—aukan hijabi domin daman da alwala a tare da ita. Aaliyah ta miÆ™e bayan ta ci kuka ta Æ™oshi sosai ta nifi É—akin Majeederh. A zaune ta sameta bakin gado ta sanya hannunta a tsakanin cinyoyinta tana kaÉ—awa a hankali kanta sunkuye. Jiki ba Æ™wari cikin muryar kuka sosai Aaliyyah ta ce “Anti Jeederh mene haka? Me yake shirin faruwa? Me ya sa sai ke kawai?Anya Abbu shi ne Ubanmu? Wannan abun it’s too much, this is not fair zuciyata ta fara raya mini bashi ne Ubanmu ba ko Uncle…..,” Kau! Majeederh ta É—auke Aaliyyah da wani kyakkyawan mari har sai da ta yi baya daga tsugunen take. Ta fashe da kuka sosai ta ce “Anti Jeederh ki dakeni son ranki, beat me amma ba zai iya sauya tunanin da zuciyata ta fara wanzar mini da shi ba, na buÉ—e idanu da soyayyar da kike mini Anti Jeederh, na fahimci kece madadin uwa a gareni ko da baki shaida mini Mami ba ita ta haifemu ba, Innati ta faÉ—a mini komai, amma kullum kina nuna mini hanzar tsira hanzar da zan kare kai na a matsayina na É—iya mace, na tashi naga yadda Abbu ke son ki ya fifita ki da kowa, komai Hawwa’u musamman É“angaren karatu, Anti Jeederh baki da lokacin kan ki kullum karatu kullum karatu, mene nufin Abbu? Imran ya zo neman aurenki ya ce ba aure zai miki yanzu ba, ya yi masa korar kare, yanzu kuma ya amshi kuÉ—in auren Ruma bayan kece babba kece ya kamata ki fara yin aure kafin ita…” Kuka ya ci Æ™arfin Aaliyyah ta ce “Soyayyar kenan? Za a ci karatu ne? Idan bai barki kin yi aure ba yanzu sai yaushe, Anti Jeederh tun kina jss 3 na ji kina faÉ—awa Yaya Latifa aure kike so, idan ya tilasta miki yin karatu ya hanaki aure shin ya miki adalci? Mufa Æ´a Æ´a ajjiye ce, amana ce a wajan iyayenmu za a tambaye su yadda suka kula damu, Malaminmu ya faÉ—a mini duk É—iya macen da ta ce ayi mata aure bata son karatu mafi alheri shi ne a aurar da ita, domin ita tasan me take ji,mene ya sanya ta ce tana son auren, idan ba a aurar da ita ba komai yana iya faruwa da ita kuma….” Majeederh ta yi saurin toshe bakin Aaliyyah tare da rungume yarinyar a jikinta ta ce “Enough, enough is a enough, ok”
Kukan zuci take wanda ya fi komai cin rai da sanya damuwa da ciwo a zuciya, bata son hawayenta ya zuba gudun Æ™arawa Aaliyyah nata kukan da damuwa. Sun jima a haka tana jin Aaliyyah na kuka tana bubbuga bayanta a hankali har ta fara sauke ajjiyar zuciya kafin ta É—agota tana riÆ™e fuskarta murmushin dole bayyane a fuskarta ta ce “Stop crying my dear, hannunka baya taÉ“a ruÉ“ewa ka yanke ka yar, Abbu yana so na, soyayya ce ta sanya ya yi haka, kuma yana da iko kaina, yana ganin kuma karatu ya dace dani ba aure ba, shi ne mahaifinmu our own father, biological father ok ba a taÉ“a sauya tuwo suna, kuma idan na yi karatu zan samu aiki Abbu zai ji daÉ—i i most be proud, zai alfahari da ni, zan gyara mana gida, na siya masa mota, na kaisa Makka na buÉ—e masa wajan aiki ya fita daga halin talaucin da yake ciki” Da sauri Aaliyyah ta ce “Aure fa?”
“Zan yi, idan da rabo” Ganin zata sake magana Majeederh ta haÉ—e fuska sosai ta ce “Je sallah, kiyiwa Fulani addu’ar samun rahama a kabarinta, kiyiwa Abbu addu’a da su Ruma da Mami” Ta ce “Anti Jeederh ke ma zan miki addu’ar Allah ya kawo miki mijin aure ko gobe ne” Majeederh bata ce komai ba, a ranta tana jin cewa karatu zata aura shine zai zame mata miji da zuri’a. Bayan fitar Aaliyyah kuka taci ta Æ™oshi son ranta, kukan ya dace da ita Æ™ilan hakan zai sanyaya mata zuciyarta daga yadda take ji, idan ta tuna babu Little bata san kuma inda zata same shi ba, bata san wanne hannu zai faÉ—a ba zai samu kula ko ba zai samu ba sai zuciyarta ta karaya damuwarta ta Æ™aro fiye da ko yaushe. Ga Abbu ya yi mata katangar Æ™arfe tsakaninta da nemo Little É—inta. Tunaninta ya tsaya ta rasa me za ta yi, rashin Little tamkar rasa wani gefe ne na rayuwarta. Ganin lokaci na tafiya ya sa ta miÆ™e tare da shiga banÉ—aki yau ko wankan da take da asuba domin kiyaye jikinta daga mafarkan da take yi bata samu zarafin yi ba, ta É—aura alwala tare da shimfiÉ—a ladduma ta yi sallah raka’a biyu. Ta jima tana addu’a akan Allah ya dawo mata da Little É—inta abin sonta, abin wasanta, abin hirarta, me É—auke mata kewa. Ta yi shiru na rashin abin yi har Æ™arfe 7 tana zaune kanta Æ™asa sai wajan 7:48 bacci É“araho ya É—auketa.
Misalin 11 na safe Hajia dake zaune cikin haÉ—aÉ—É—en parlourn gidanta ta yi ado cikin atamfa mai kyau da É—aukan Idanu (Valisco) fara ce kamar buzayen Niger. Ta dubi agogo dake parlourn ganin lokacin na tafiya ya sanya ta É—auki wayarta tana Æ™oÆ™arin kiran Aliyu taga Almustapha ya fito, ta ajjiye wayar idanunta akansa tare da duban bayansa har ya iso ya zauna dab da ita ya ce “Good mrng Hajia” Ta dube shi kafin ta ce “Mrng, Zaki fa?” Ya É—aga kafaÉ—a ya ce “Tun sallar Subhi rabona da shi” Ta yi shiru “Bai fito bane?” Almustapha ya faÉ—a yana miÆ™ewa, Hajia ta ce
“Jeka kawo mini Yarona”
“Ya zama dole ai” Tsakanin part É—in Musty dana zaki ba nisa suna opposite da juna ko wanne ha haÉ—u kasancewar su masu rufin asiri sosai. Komai na part É—in zaki light blue ne, looking so Masha Allah. Furniture’s É—in Æ´an Turkiyya sbd yadda suke É—aukan Idanu. Ganin Æ™ofar shiga cikin bedroom É—in a buÉ—e bayan ta parlournsa dake buÉ—e ya tura kai ciki, Æ™amshin room air-freshener, a hankali Musty ya shiga hannunsa É—aya yana gyara hular kansa yana faÉ—in “Autan Hajia bacci har yanzu? U have to wake up” Jin shiru ya sa Musty Æ™arasawa har bakin bed É—in da Zaki ke kwance ya lulluÉ“e jikinsa bakiÉ—aya idanunsa rufe numfashinsa na sauka a hankali. Da mamaki Musty ya ce “Zufa?”
Ya duba yaga A.cn É—akin na working domin har yawa taso yi, ya É—an bubbuga pillown da kansa yake kai. Slowly a hankali Aliyu-haydar ya shiga buÉ—e idanunsa wanda su ka yi masa nauyi, ganin sauyin idanun Zakin Hajia musamman da yake cikakken Baushi Nigerian, ya bawa Musty tsoro. Suka kalli juna ya ce “Lafiya kake?”
“In capital letters, FINE”
Aliyu-haydar ya faÉ—a yana janye jikinsa daga bed É—in kansa ya yi masa nauyi sbd rashin bacci na kwana biyu, hakan ma jiya ta kasance masa sai daya dawo daga masallaci bacci ya É—auke shi. Musty ya bisa da kallo musamman yadda yake tafiya kamar bai so sai kawai ya girgiza kansa ya shiga danna waya. Yana zaune har Aliyu ya fito É—aure da towel cikin sauri ya shirya cikin wani carton É—in Yadi mai kyau da taushi wando da half É—in riga sai hannun rigar half dark blue ya haska farar fatarshi. Bai saka hula ba sai sunglasses daya saka ko gyara sumar shi bai ba. Ya nufi waje kai tsaye, Musty ya miÆ™e yana mita “Ji wulaÆ™anci na gama gadinka har ka shirya shi ne zaka fita?”
“Waya kake dannawa fa Yaya?” Suna fitowa a jere Hajia ta miÆ™e tsaye a daidai lokacin Papa ya fito cikin shirin fita office. Ya dubi samarin yaran nashi a tare suka ce
“Mrng Papa”
“Babana, Almustapha, kun makara yau” Almustapha ya ce “Yanzu zan fita” Papa ya juya ga Aliyu-haydar ya ce “Kai fa?” Ya É“ata fuska ya ce “Ina gida” Da mamaki Papa ya ce “Gida? Daga fara aikin?” Nan da nan Aliyu ya nuna Autansa a fili ya marairaice fuska tare da langwaÉ“ewa, Papa murmushi kawai ya yi ya ce “Hajia bari na fita” Hajia ganin yadda idanun yaran nata ya sauka akanta suna jiran su ji me zata ce, ta girgiza Æ™afa kawai ta ce “Allah ya tsare ya kiyaye” Papa ya yi jim kamar na jiran wani abu sai kuma ya ce “Amin” A tare suka fice shi da Almustapha kowa ya shiga mota, Almustapha na driving kansa, Papa kuma yana baya Busy reading news paper driver na jansa a haka suka fice. Hajia ta dubi Aliyu ta ce “Auta sai yanzu?” Ya rufe idanu ya ce “Just woke up Hajia”
“Ka yi breakfast?” Ya girgiza kai kawai tare da miÆ™ewa tsaye ya ce “Ki mini addu’a zan fita yanzu zan dawo” Tana lura da yadda yake yawan lumshe idanunsa yana riÆ™e kai ta ce “Allah ya tsare” Hannunsa É—aya zube cikin Aljihu É—aya riÆ™e da key ya nufi harabar gidan, motarshi ya shiga yana yi mata key while yana kiran number Latifa Omar. Majeederh na zaune idanunta ya yi zururu sun faÉ—a fuskar nan jajur karan hancinta ya yi jaa sosai sbd damuwa. Da Æ™yar ta cira kai ta kalli Latifa Omar ta ce “To ya zan yi? Mahaifina ne, na haÆ™ura da Little” Latifa Omar ta ce “haka zaki zauna Takaicin Uba na cin zuciyar ki?” Kallon da Majeederh ta yiwa Latifa Omar ya sa ta fahimci bata ji daÉ—in maganar ba ta ce “Ki yi haÆ™uri, yanzu kina nufin bakya nan zan yi aure?” Kamar ba za ta yi magana ba ta ce “Aure zaki?” Latifa ta yi dry tana gyara zama ta ce “Aure zan yi In sha Allah, ina wannan wanda ya kaimu gidan Uncle Isma’il da Yaya Bilkisu? To shi ne ya ce yana so na, na ji tsoro ganin shi ne wani ne masu arziÆ™i kuma ni gani Æ´ar gidan Malam Shehu, amma ya ce babu komai iyayensa basu da matsala yana da kyawawan hali” Ba zata iya gane yanayin reaction na Majeederh ba kanta a Æ™asa yake. “Majeederh kina ji na?” Ta ce “Allah ya sanya albarka” Kafin Latifa Omar ta yi magana wayarta ta fara Æ™ara ganin wanda yake kira yasa tafiya murmushi hannunta na rawa ta É—auka ta ce “Hello”
“Is not allowing, Assalamu alaiki” Majeederh ta miÆ™e zuwa É—akin Abbu cikin Æ™aton hijabi har Æ™asa kana kallonta kasan a hargitse take. Ta yi sallama yana zaune hannunsa riÆ™e da wani file na takardun Majeederh ya ce “Hawwa’u kin fito? Yanzu zan office É—in zaki?” Ta É—aga masa kai ya ce “To ya za ayi? Bani da kuÉ—in mota” A sanyaye ta ce “Ina da shi” Ya miÆ™a mata file É—in yana murmushi na nuna jin daÉ—i ya ce “Allah ya yi miki Albarka, Kinga kina zuwa Misira Shekaru takwas kin gama karatunki, idan da hali kawai ki yi zamanki a can ki fara aiki ance albashinsu akwai auki sosai” Ba zata iya tantance halin da maganar Abbu ya sanya zuciyarta a yanzu ba, kuma ta yi alÆ™awarin ba zata sake masa Æ™orafi ba. Ta miÆ™e taiwa masa sai ta dawo taiwa Mami ma, Aaliyyah da su Ruma na makaranta. A hankali ta nufi waje kanta a Æ™asa ga yunwa domin kafin ta farka har an cinye abinci abincin safen, jiri na É—aukarta a haka ta yi waje ganin mota a Æ™ofar gidansu ya sanya ta É—aga kanta cikin rashin sa a Idanunta ya faÉ—a cikin nasa suka kafe juna da wani irin kallo….

 

Post a Comment for "Mijin Malama Book 1 Page 19"