Breaking News

Mijin Malama Book 1 Page 40


MIJIN MALAMA na kuÉ—i ne pay before you read….. More information via WhatsApp number 08119237616″Na auri mijinki? Do you want me to marry your husband?” Da wani Expression na tashin hankali take faÉ—ar maganar tana kallon idanun Latifa Omar. Latifa ta watsa hannunta cikin rashin damuwa ta ce “To mene na tashin hankali a nan? Bayan iyayena dake, babu abinda nake a cikin duniyar nan irin mijina, amma wallahi na amince miki hundred patient da ki auri Aliyu, ki auri mijina mu zauna tare, ba zan taÉ“a yi miki kallon kishiyata ba, don Allah ki rufa mini asiri ki auri Aliyu” Latifa ta faÉ—a muryarta na rawa. MiÆ™ewa Majeederh ta yi tana É—aukan handbag É—inta da wayarta ta nufi hanyar fita daga cikin parlourn. Da sauri Latifa Omar ta miÆ™e tana shan gaban Majeederh ta ce “Ina zaki? Ki tsaya mu yi magana don Allah, this is the right time da zamu kawo karshen matsalarki Majeederh” Murmushin takaici Majeederh ta yi hawaye na sakko mata a a kumatu ta ce “Well-done Latifa Omar, sbd na tako Æ™afa da Æ™afa har cikin gidan ki na faÉ—a miki matsalata shi ne zaki dubi idanuna kika ce i should come and marry ur husband? Are you mad?” Magana take amma hawaye ne ke zuba daga cikin idanunta. Latifa ta girgiza kai itama hawaye ya shiga sauka daga cikin idanunta ta riÆ™e hannun Majeederh sosai cikin nata ta ce “Wallahi that’s not what i mean, tun kafin yanzu ayi miki maganar fitar da miji nake son faÉ—a miki ki auri mijina ina tsoran abinda zaki faÉ—a, Majeederh na san halinki nasan how hard you’re, You have a deep heart, even if the worry will kill you, you will never tell anyone, na kasa jure yanayin na kasa fahimtar cewa jarrabawa ce, maganganun mutane akan ki ya fara yawa, me ya sa ina da maganin damuwar ki a hannu zan zuba idanu kina cutuwa? Aliyu na da kyau, ilimi both boko da Arabic, yana da kuÉ—i ko kuÉ—in mahaifinsa bai damu da shi ba, Hajia Mahaifiyarsa na da kuÉ—i, Ubangiji ya hore masa arziÆ™in da zai zauna da mata har huÉ—u ba biyu ba, Zan iya mallaka miki komai na rayuwa daga ciki har mijina If that makes you happy,if that will make you look like any other woman in her husband’s house,Please marry my husband, Aliyu!” A hankali Majeederh ta zare hannunta daga cikin na Latifa Omar ta durÆ™oshe a wajan tana sakin wani irin raunataccen kuka, mai cin rai da ciwo a zuciya. Wani irin kuka take Wanda ta jima ba ta yi irinsa ba, ga Æ™oshi ga kwanan yunwa,ga maganin matsalarta amma ko duniya da abinda suke cikinta zasu haÉ—u ba zata taÉ“a auren mijin Latifa ba, bata taÉ“a kawo hakan ba ko da, da wasa. Zubewa Latifa ta yi itama ta rushe da wani irin kuka kamar an musu mutuwa ta ce
“Ashe ba zan iya rufa miki asiri ba? Ashe zumuncin banza muke? Ashe ban zama Æ™awar da zata É—auki damuwar Æ™awarta matsayin tata ba? I have been friends since we were children, we trust each other, we know each other’s behavior,Even if you marry my husband, there will be no worries between us, wlh ko Aliyu kika aura babu É“arakar da zata gilma tsakaninmu, babu wani yaÆ™unanne ko shegen kan lafiya da zai sako lalataccen bakinsa, zamu zama abu É—aya, zuri’a É—aya one single family mu zama Matan Aliyu, ki haifa masa yara tunda har yanzu Allah bai bani haihuwa ba” Majeederh kuka take sosai kamar ance Abbu ko Little ko Aaliyyah wani ya mutu, ta kasa cewa komai sai jikinta dake mahaukacin É“ari da Æ™yarma kamar an jona mata shocking.
Bar Aliyu Sufyan Alhassan da tunda ya yi parting da motarshi ya shigo gidan ya tsaya cak a ƙofar da zata sada shi da main parlour na gidan nasa, tun daga farkon conversation ɗin su har kawo yanzu ya ji komai, zufa ce kawai take yanko masa all over himself, jira yake ya ji me Majeederh zata ce akan requesting ɗin Latifa?.
“Majeederh say something, ki daina kukan hakan” Majeederh ta kalli Latifa Omar da rinannun idanunta wanda ba lafiya ya cika ba, ta ce
“Dole na yi kuka Latifa, ban taÉ“a tunanin watarana da zata zo ace zan auri mijinki ba, me ya sa kike tunanin zan iya auren mijinki, why should I do that? Me mutanen unguwa za su ce? Me Æ´an-uwan ki za su ce? Su ce na zama munafuka, maci amana mayaudariya, wacce ta aure mijin aminiyyarta? That’s what you want? Sbd ina kawo miki matsalata ashe ke tunaninki mijinki zan aura? Sbd Æ™addara ta faÉ—a mini shi ne zaki manna mini hauka ki zautar dani da gurÉ“ataccen tunaninki mara amfani a gareni, zaki forcing mijinki ya aureni? Bayan kin san mazan guduna suke, basa Æ™aunata, balle muradin aurena, banda Imran daya taÉ“a furta kalmar so a duniyata babu wani É—a namiji da ya ce yana so na, ko da sunan iskanci ne….,” Kukan da ya ci Æ™arfinta ne ya sanya ya kasa ci-gaba da maganar ta haÉ—e kanta da qiwwa kamar Æ™aramar yarinya. Latifa kukan take sosai ta ce “Ba zan taÉ“a forcing Aliyu ba, nasan ba zai gujewa maganata ba, ku zauna da juna na 1week am sure zaku Æ™aunaci juna, mutanen gari kuma ki barni da su” Majeederh ta miÆ™e tare da goge hawayenta tas ta saki liÆ™ab É—inta. “Kin Amince?” Aliyu dake tsaye cikin zuciyarsa ya ce “Say Yes, Hawwa’u”
Har bakin Æ™ofa Lafita ta biyota amma Majeederh bata kulata ba, lokaci É—aya suka saka hannu akan handle jin an murÉ—a ya sanya Majeederh saki tare da komawa baya, a hankali ya buÉ—e Ƙofar ganinsu a har gitse ya sanya Aliyu dake cikin nevy suit hannunsa É—aya riÆ™e da rigarsa ta lauyoyi sai zabga Æ™amshi yake, a hankali ya ce “What did i miss?” Latifa ta ce
“Ka tsayar da ita” Muryarta bata fita sosai ta ce “Bani hanya” Gefe ya koma ta raÉ“a ta shige abinta, muryar Latifa na rawa ta ce “Me ya sa zaka bata hanya, ba zata taÉ“a dawowa ba fa, kuma na ce ka tsayar da ita” Bai ce mata komai ba ya mayar da Æ™ofar ya rufe, hannu tasa zata buÉ—e Ƙofar Aliyu ya yi sauri riÆ™o hannunta ya ce “Let her go, Wife” Kuka ta fashe masa da shi ya jawota jikinsa “Sorry” kawai ya samu zarafin faÉ—a sbd zuciyarsa da tayi masa nauyi, ganin taÆ™i yin shiru ya sa ya jata har zuwa bedroom É—insa dake tashin wani cool Æ™amshi na air-freshener, cikin dabara ya shiga bata saÆ™o albarkacin Majeederh Aliyu ya samu abinda ya daÉ—e bai samu ba a wajan matarsa Latifa tsayin wata wajan goma. Yana zaune saman wata Æ™atuwar kujera ya harÉ—e Æ™afafuwanshi saman sofar idanunsa lumshe breathing É—insa na sauka a hankali alamar bashi da lafiya, ya Æ™ara yin wani farin idanunsa sun faÉ—a, cikar haiba da da zati da kamalar shi na nan zaune daram a jikinsa. Wata Embroidery Islamic jallabiya ce a jikinsa fara tas, sai jiramin daya É—ora akansa looking so good. Rohaan dake tsaye cikin damuwa ya ce “Allah ya Æ™arawa Mai martaba Ajlaal Sultaan lafiya, wannan tunanin da kake isn’t good for ur health” Mai martaba Ajlaal bai magana ba sai idanunsa ya buÉ—e yana kallon É—an uwan nasa Rohaan, ganin kallon da Mai martaba Ajlaal Sultaan yake masa ya sa ya ce “Ba tare da sanin abinda ke faruwa ba, a karo na farko wani jininmu ya sako Æ™afa zuwa Nigeria, ka matsa yanzu kuma gashi ka ce mu tafi ba tare da yin abinda ya kawo mu ba” Nan ma Ajlaal bai ce komai ba, Rohaan ya numfasa ya ce “Idan akwai abinda ke damunka yana da kyau ka faÉ—a, tunda kasan idan har a duniya yake dole zaka same shi, ka tsallake Zaytoon, da Mimi wacce kai kaÉ—ai kake controlling ciwonta idan ya tashi, ka bar Fulani Ƙhulud da tagwayen yaranta, Palace ba kowa sai Hadiman, Meke faruwa dakai Mai martaba? Yana da kyau ace….,” “Rohaan” Ajlaal ya kira sunan Rohaan da É—an Æ™arfi a kuma taushashe, Rohaan ya ce “Tuba nake Mai martaba” A nutse Ajlal ya duba agogon Rolex dake hannunsa yana mai kikewa tsaye cikin izza har ya je bakin Æ™ofa sai ya tsaya ya juya kaÉ—an ya kalli Rohaan, da sauri Rohaan ya durÆ™osa ya ce “Prvt jet É—in na hanya, ban san ya akai aka samu labarin zuwanka Nigeria ba, gabaÉ—aya zuwan naka shi ne latest new in the world” Da wani irin Expression Mai martaba Ajlaal Sultaan yake kallon Rohaan jin abinda ya ce, zufar dake tsastsafo masa a tsakiyar goshinsa ita ke nuna tashin hankalin jin mummunan labarin, ya dunÆ™ule hannu tare da kallon Rohaan alamar Æ™arin bayani.
Rohaan ya ce “A karo na farko Sarki makka Mai martaba Ajlaal Sultaan magajin Ex Sarkin Makka Sultaan ya sauka a Nigeria, har yanzu ba a san dalilin zuwansa ba, ana kyautata zaton zuwan sirri ne ya zo ganawa da wani É—aya daga cikin sarakunan Nigeria, zuwan nasa ya ja hankalin dubban mutane ganin tun Æ™arnin baya na kafuwar masarautar Saudiyya jininsu bai taÉ“a zuwa Æ™asa Nigeria ba, ko mene dalilin zuwan nasa?” Daga nan Rohaan ya kashe T.v da remote É—in hannunsa ya ce “Ire-iren wannan sune news É—in da suke trending a duniya da Social media tare da photonka, alamarin ya fi tsamari a Al Jazeera, BBC World News,CNN International da kuma Arise News” Duk maganar da Rohaan yake a tsorace yake yinta, Ajlaal ya zame idanunsa yana riÆ™e kansa da kyau, duk da tashin hankalin da yake ciki, a taushashe cikin tarin ilhamarsa nutsuwa da kamalar dake zaune a jikinsa cikin kamilalliyar muryarsa yana lumshe idanu ya ce
“A san yadda aka yi, aka dakatar da news É—in” Ya shiru yana juyawa can ya Æ™ara fesar da iska ya ce
“Kowa na Palace, ya zama lafiya, a san yadda akai aka Æ™aryata zuwan namu Rohaan” Da girmamawa Rohaan ya ce “An gama Mai martaba, Allah ya Æ™ara lafiya da nisan kwana” Tuni ya kai cikin bedroom É—insa yana hana kansa jin abubuwan da suke masa yawo a jiki… Majeederh na zaune a Æ™asa an haÉ—a family meeting kowa da kowa yana nan cikin babban parlourn na gidan Abbu, Uncle Isma’il da Uncle Bello, Innati,Yaya Bilkisu, Maman Alpha, Anti Hajiya Maryama, Sona, Du’a, Widad, Raihana, Ruma, Aaliyyah, Mami, Jawaad,Sahar. Kaf Familyn Khan General Alpha ne kawai babu a ciki, Idanun Maman Alpha ya nuna tsananin kewar É—anta da take shekaru sun ja, babu ko labarinsa gashi abin mamaki fur Uncle Bello ya rufe ido akan bai yarda ayi cigiyarsa ba, ko headquarters na sojoji ba a maganar shi har sun yi replacing nasa da wani, kamar wanda aka rufe musu baki aka saka makulin a ruwan maliya. Bayan Addu’a da Anti tayi kasancewarta malama ita ma Yaya Bilkisu ta gyara zama ta ce “Ina Hawwa’u?” A sanyaye Majeederh ta É—aga kanta ta kasa amsawa, a hankali kuma ta juya zuwa direction É—in Abbu taga sam ba ita yake kallo ba, ko fahimtar yanayinsa ma ba zakai ba, ya sha shadda Light blue É—inkin Jamper da babbar riga ba zaka ce haifi Æ´ar shekaru 31 ba, kullum Æ™ara fresh yake kuÉ—i sun zauna jiki ya murje. Yaya Bilkisu ta ce
“Wannan zaman naki ne, dominki akai, Majeederh É—ago kan ki sosai ki dubeni” Majeederh ta kalli Yaya Bilkisu “Dubi a gabanki aka haifi Widad yaranta nawa? Du’a, Sahar, Raihana, Ruma gabaÉ—aya akan idanunki suka zo duniya yanzu ko wacce tana É—akin mijinta ta rufawa kanta asiri, ke kuma kina nan zaune kina tsofa a gida, Hawwa’u mene damuwarki ne? Kina da kyau, ilimi, boko da arabic, kina da kuÉ—i kina da asali kowa yasan waye mahaifinki, yau a gabanmu a gaban iyayenki ki faÉ—a mana mene ya hanaki aure?” A wannan karan ma Majeederh ta kasa cewa komai sai kanta data É—aga zuwa direction É—in Abbu cikin sa a Idanunta ya shige nasa daya jima yana kallonta, ya zame idanuna ya miÆ™e tsaye zai bar wajan Uncle Isma’il ya ce “Daka zauna ai” Ya zubawa Uncle Isma’il ido a hankali ya ce “You can handle it” Ya faÉ—a tare da gyara zaman babbar rigarsa ya shige cikin part É—insa, gorar y É—auka ya É“alle wani chaset É—in magani ya watsa a baki a hankali ya kwanta kan bed yana rufe idanunsa feeling relieved. Majeederh zata tarwatsa masa zuciya da issues É—inta, Allah ya ware masa ita matsayin Æ™addararsa yaran dake neman É“ata masa suna a duniya, she really disappointed him, actually. Sosai Yaya Bilkisu ke faÉ—a kamar zata ari baki ta ce “Mun gaji da sanya miki idanu, tunda ke baki amfani da iliminki ba, wallahi wallahi idan baki fito da miji in few days ba zaki sha mamaki, wannan Æ™annen naki duk sun fiki martaba a idanun jama’a, kuma tunda haka kika zaÉ“a aiki da neman kuÉ—i da kurÉ—a kurÉ—a ya fiye miki aure ga Sahar zata haihu sai ki ma zaman daÉ“aru mutuniyar banza” Anti ta ce “Ki yi haÆ™uri Yaya Bilkisu komai fa lokaci ne” Yaya Bilkisu ta ce “Saurara Maryama wannan yarinyar dole mu nuna mata ikonmu na iyaye” Maman Alpha ta ce “Haka ne, amma dole a fara binciken daga ina matsalar take?” Mami ta ce “Wacce matsala? Kawai ba auren a ranta tafi gane yawon Ngo É—in nan da Foundation” Uncle Bello ne ya ce duk yaran su fice, su kaiwa Majeederh faÉ—a sosai kana ya ce “Ki shiga ki bawa Mahaifinki haÆ™uri bashi da lafiya” A sanyaye ta miÆ™e ta nufi ta nufi part É—insa tsaye ta gabashi hannunsa riÆ™e da waya kamar yana kallon wani abu ko dannawa. “Abbu” Cikin sauri ya kifa wayar ba tare da ya ce komai ba, Majeederh ta zube a Æ™asa ta ce “Abbu ni mai laifi ce a gare ka, don Allah ka yafe mini In sha Allah zan yi abinda kuke buÆ™ata” Ya juya da sauri ya kalleta a hankali ya ce “Zaki me?” Ta ce “Zan kawo mijin aure” Wani dugun numfashi ya sauke ya ce “Are u sure?” Ta jinjina kai ta ce “Kayi haÆ™uri Abbu, na sanya maka damuwa a zuciya ban zama yarinyar arziÆ™i ba, ina ladama da kasancewata mara amfani a gareka, ka yafe mini ka dinga amsa gaisuwata” zuciyarsa ta kare tausayin Æ´ar tashi ya kamasa ganin ko hawaye ta kasa sai Æ™irjinta dake harbawa, ya miÆ™a mata hannunsa ya ce “Stand up” Kama hannu ta yi ta miÆ™e, yaro a gaban iyayensa baya tsofa ya taka har gabanta ya saka hannu ya riÆ™o fuskarta a hannayensa cikin kasa da murya ya ce “Hanyar aljanna nake nema maki, ke É—in tamkar amana ce dake da Aaliyyah” Ta saki kuka ta ce “Am sorry Abbu” Kasa magana ya yi sai buÉ—e hannunsa da ya yi ya ce “Come” Cikin sauri ta shige jikinsa tana wani irin kukan farin ciki yau Abbunta ya rungumeta rabonta da jin É—umin jikinsa tun tana Æ™arama. Can ya saketa ya juya zuwa bedroom da sauri…. Bayan sallar Issha tana zaune a bedroom É—inta dake ba sallah take ba, ta jawo wayarta jin Æ™ara kafin ta É—auka ya katse miss calls wajan 10 na gani 7 na Son my world, 2 na Latifa 1 kuma babu suna wata mahaukaciyar special number ce da bata taÉ“a ganinta ba, number Abraham ta kira tana fara ya É—aga “Assalamu alaika Baby little me” Tana jin sanda ya sauke wata É“oyayyiyar ajjiyar zuciya jin bai amsa ba ta ce “Khalil” Nan ma shiru ta Æ™ara cewa “Baby are you okay?” Harta fara tunanin ko kiran ya katse ta ji can Æ™asan maÆ™oshi ya ce “Are you crying?” Ta haÉ—e fuska kamar yana gabanta ta ce “Uhm Baka damu da Maminka ba, no calls no text, anyway how are you?” Ya yi shiru ta ce “Zan ajjiye wayata” Can ta ji ya ce “You’re still crying as always, wahh happen?” Ta yi Ignoring nasa ta ce “Khalil ina mahaifinka wai? And ur mother ina ne garinku ina son sani Please kuma dai ba kana cikin wannan yaran bane ko? Baka faÉ—a da kowa….,” A tsawa ce Abraham ya ce “Stop asking too much, why are crying? What’s happening eh?” Ya faÉ—a tana jin yadda yake fidda huci kamar ma baya cikin hayyacinsa, haka kawai tsoransa ya kamata ta fashe da kuka sosai tana marairaicewa ta ce “Shi ne zaka mini tsawa Mamin taka?” Ya yi mata shiru cikin faÉ—a da kuma alamun damuwa ya ce “Don’t let me to repeat myself Mami” Ta Æ™ara fashe masa da kuka ta ce “To ba cewa akai na fito da mijin aure ba?” Wannan karan a hankali ta ji muryarsa tana sauka ya ce “In english” Duk a tsorace take da tsawarsa cikin turanci ta ce “Abbu da Uncle’s É—ina sun yi faÉ—a sosai wai na fito da mijin aure kwana nan, na rasa yadda zan yi kuma bani da kowa ba wanda ya taÉ“a cewa yana so na ko da wasa yanzu Little ya zan yi?” Ya yi shiru ta wayar yana jin tashin kukanta Æ™it kuma ta ji ya kashe wayar, da sauri ta sake kira ta ji a kashe, sai yanzu take mamakin yadda akai harta faÉ—awa Abraham a matsayinsa na É—anta bai dace ya ji wannan matsalar ba, raba dare ta yi tana tunani daga Æ™arshe ta yi addu’a ta shirya cikin kayan bacci ta kwanta, bata kashe wutar É—akin ba sbd bata son duhu ko kaÉ—an… Can cikin dare fitsari ya kamata ta buÉ—e idanu da Æ™yar ganin duhu gabaÉ—aya a bedroom ya sa gabanta ya faÉ—i, ko nepa aka É—auke? Ko ai basa amfani da nepa inji ne 24/7 ta miÆ™e a hankali ta shiga laluba hanya, can ta ji hannunta ya sauka akan chest É—in mutum ga suma nan fal kwance luff a tsorace take Æ™oÆ™arin cire hannun ta ji an saka hannu an fizgota ta faÉ—a Æ™irjinta baki ta buÉ—e za ta yi ihu ta ji ya rufe bakin da na….

 

MIJIN MALAMA pay before you read please….. If you want to Subscribe my book via WhatsApp number… 08119237616.

 

No comments