Breaking News

Mijin Malama Book 1 Page 42


Wani irin jijjiga shi ta shiga yi bayan ta mirgina ta zame jikinta sai kanshi dake saman cinyarta. “Khalil? Ibrahim buÉ—e idanunka” Duk ta rikice ganin yadda ya sanÆ™ame baya ko numfashi. Debeka dake tsaye jikinta ya É—auki rawa, Allah yana gani bata yi don ta kashe shi ba, he so much loves him,She loves him very much, his jealousy makes her feel that she will never let him be with another woman other than her. Tsananin kishi ya rufe mata idanu ya sa ta kasa controlling kanta. Gang team É—in kallon Debeka suke sun san ko da wasa suka taÉ“a ta sun shiga uku. Majeederh gently ta zame kan Abraham dake cinyarta tana zuwa bata tsaya jiran komai ba ta É—auke Debaka da wani mahaukacin mari, sai da ta jera mata maruka guda biyar cif wanda suka nemi zautar mata da tunani. Tana pointing É—inta da hannu ta ce.
“Baki da tarbiyyar da zaki iya haÉ—a inuwa da Khalil, mara tsafta irinki sam bata dace da shi ba” Debeka da kumatunta ya kumbura ta ce “Who are you? Waye ubanki a duniya bakiÉ—aya, da har kika mareni kike tunanin kin mari banza?” Ta cikin liÆ™ab Majeederh ta watsa mata harara cike da tsana wacce bata taÉ“a yiwa kowa ba ta ce “Me? Forget about my father, ki tambayi wacece ni kaina, I Malama Majeederh Abdul’aziz Khan! Idan kin sani better, idan baki sani ba You can search on Google zasu gaya miki” Debeka ta girgiza kai sosai ta ce “Ok shi ne sbd abin kunya wata tsohuwa dake sbd kin rasa mijin aure kika liÆ™ewa masa ko? Kinga sabon jini, daman ke ce wacce kika shiga tsakani kike masa yawo da zuciya har ya kasa accepting nawa matsayin budurwa balle ya kwanta dani? Kin fa haifeshi haba Mama” Sosai Majeederh ta ji zafin maganar jin ta kirata da tsohuwo hala bata san matsayinta a wajan Abraham ba. Ta juya ta kalli Abraham dake kwance su Taj na shafa masa ruwa ya riÆ™e mararsa gam zufa na yanko masa, ta dawo da ganinta kan Debeka ta ce “Me kika ce? To ina nan ina addu’a da izinin Ubangiji babu wata Æ´ar iska data isa ta ja hankalin Khalil sai matarsa da sunna wacce addini ya bashi ita duk wuya duk tsanani, ba zai taÉ“a aikata zina ba, naga kamar baki da cikakken hankali idan baki sanni ba su abokan nasa sun sanni, na raineshi da hannu na yi masa wanka da hannuna, na goyasa a bayan nan nawa, ya yi bacci a jikina akan Æ™irjina tun yana 3yrs a duniya, Abraham is my son, ni nake da ikon zaÉ“a masa matar data dace da rayuwarsa wacce zata taimake shi ya É—ora shi akan tubalin zuwa aljanna, wacce zata ribaci ra’ayinsa ga taimakon al’umma, wacce zata dawo da shi akan hanya, mace mai tsafta da hankali nutsuwa kamala, mai addinin ba wacce ke bin gidan maza ba” She slowly heard him say “The woman you are praying for me to marry is none other than you” Debeka ta saki dariya ta ce “Kenan kanki kikewa fatauci ko? Sannu uwar guzuma kune hajiyoyin dake lalata Æ™ana nan yara kenan no wonder”
Abraham na jin su, maganganun Debeka kamar saukar mashi haka yake ji, amma ya yi shiru yana son Majeederh bakinta ya buÉ—e ta fara kwatarwa kanta Æ´anci ba sai an shigar mata faÉ—a ba. Hakan ya sanya ya yi shiru yana mayar da numfashi yana jin yadda lokaci guda jikinsa ya É—aukeki zafi sosai, mararsa sai harba masa take tana wani irin yi masa masifaffen ciwo. Ganin Majeederh taÆ™i cewa komai ya sanya Debeka cewa “Na miki al’Æ™awarin zan tafi, ban miki al’Æ™awarin zan bar miki shi na har abada ba, domin don ni akai Abraham, mahaifinsa ma ya san da zamana, ke uwar riÆ™o ci ki zauna a matsayinki na hakan, don’t interfere this is family issues, wlh wlh wlh ko wa kika aura masa, ko ke ya aura ku shirya zaman mace biyu a cikin gidan, ba lallai ki yarda ba, amma zaki tabbatar da hakan lokacin da na shigo cikin gidan Abraham Denial David matsayin mata, no one’s can stopping me even him” Tana faÉ—in hakan ta juya ta É—auki wayarta ko kayanta bata É—auka ba ta fice daga cikin gidan.
Takaici ya sanya Majeederh juyawa itama zata bar gidan. A shagwaÉ“e ya ce “Kin kureta kuma zaki tafi?” Ta juya suka haÉ—a idanu ya narkar da nashi idanun cikin nata, da sauri ta janye nata sbd abubuwan da take gani cikin Æ™wayar idanun nashi ya dafe mararsa ya ce “Mami come and see zafi sosai” Bata saurare shi ba, domin gabaÉ—aya a dame take jin kanta, ganin zata fita ya sa ya daddafa ya miÆ™e tsaye yana dafe da mararsa “Taj Close the door” Cikin sauri ya sakawa Æ™ofar password. A hankali ya juya ya kalle su, É—aya bayan É—aya suka miÆ™e tare da barin parlourn zuwa can garden suka fara hausan dambe a tsakaninsu.
Tun kafin ya Æ™arasu inda take ta haÉ—e fuska sosai, bai damu ba walking slowly yana marairaice fuska cikin salo na jan hankalin wanda ya sanya Majeederh É—auke Idanunta sbd tsigar jikinta dake tashi tana zubewa, Abraham ya Æ™arasa yana sauke numfashi can Æ™asa ya ce “Ta nakasa miki ni” Ta yi masa banza ya Æ™ara narke fuska ya matsa tayi saurin ja baya, yana binta tana yin baya har ta Æ™arasa jikin Æ™ofa, ya saka hannu É—aya ya dafe jikin Æ™ofar ya yi mata rumfa da Æ™irjinsa da sauri ta runtse Idanunta ta ce “Leave” Ta faÉ—a muryarta na rawa, sbd gani tayi gabaÉ—aya ya sauya mata kamar wani babban mutum ya haÉ—e fuska kamar bashi ne mai yawan ce mata “Sorry Mami ba” Wani irin kallo yake mata magana yake son yi amma bai ma san me zai ce ba, sbd abin baya kansa kuma bai saba ba. Hana ya miÆ™a zai riÆ™e nata tayi saurin make hannunsa ta ce “As frm today kada ka sake riÆ™e mini hannu,ko gigin shigewa jikina” Slowly ya ja idanunsa ya lumshe yana jin wani abu na bin jikinsa musamman da tayi maganar kamar faÉ—a ta Æ™areta a sanyaye. “Me kike tsoro? Idan na riÆ™e?” Ta yi masa banza tunda magana take son yi amma ta lura idanunsa yana saitin bakinta kaÉ—an yake jira. Ya Æ™ara matsawa tare da sakar mata Æ™irjinsa wanda yake buÉ—adÉ—e sbd É—aga Æ™arfe, ji tayi numfashinta yana fisga da Æ™yar ta ce “Ka danne mini Æ™irji, ni Maminka?” Ya ware idanu sosai wanda da Æ™yar yake buÉ—ewa ya ce “Tafiya zaki?” Kamar Æ™aramar yarinya ta É—aga masa kai sbd ta gama tsorata, a karon farko cikin harshen Hausa ta ji ya ce “To ni fa?” Hausar ko daÉ—i a baki ba tayi masa ba, abin dry kuma idan ya yi magana. Ta haÉ—e fuska ta ce “Look! Wai meke damunka ne Son?” Silently ya ce
“Call my name, bana so son” Da wani Expression na tashin hankali ta ce “Ok open the door” Speaking calmly ya ce “In one condition” Kamar tayi kuka ta ce “Wai son mene haka? What exlty wrng wiz you? Ni mahaifiyarka kakewa haka? Kana neman albarka?” Wani lalataccen murmushi ya saki iya laÉ“É“a da sauri ya matsar da bakinsa daidai kunnenta ya ce “You’re not my mother, u never be my mom, you’re my life partner” Yana faÉ—in hakan ya zame bakinsa tare da kai hannu ya É—age liÆ™ab É—in, yadda fuskarta tayi jajir ya san kuka take daga can cikin zuciya. Ya É—aga gira yana zuba hannu a aljihu kamar wanda akaiwa dole ya ce “Uncle I told me that, ke uwar riÆ™o ce, ba kene kika É—auki ciki kika haife ba, and i also agree with him, tunda muryarki idanunki attacking É—ina ina jin sha’awarki, Uncle I ya ce zan iya aurenki” Jikinta ne ya shiga rawa tana girgiza kanta ta ce “Yanzu kai auren nawa zakai?” Ya É—an É“ata fuska yana lumshe idanunsa har ga Allah muryarta kaÉ—an azabtar da shi take, Abraham bai wani damu da kyau ba a rayuwarsa, babban dalilin daya hana shi kula mata sbd duk yara ne shi kuma yana mutuwar son babbar mace, maturel enough. “Har ciki zan baki ma” Sulalewa tayi zata zube a Æ™asa don tashin hankali ya yi saurin taro ta, tare da kwantar da kanta a chest É—insa a hankali ya yake bubbuga bayanta, wani irin kuka ne ya kwancewa Majeederh tana jin kamar ranta zai fita, me ya sa Uncle Isma’il zai mata haka? Sbd kawai ba tayi aure ba zai lalata tsakaninta da Abraham ya sanya masa ra’ayin da bashi da shi a zuciya? Ya ja mata raini? Duk yadda take da dauriya da riÆ™e kanta tana mamakin yadda take da saurin kuka a gaban Abraham, he couldn’t feel yadda tears É—inta suke rige rigen sauka a Æ™irjinsa, bai hanata kukan ba sai ma access É—in daya bata ya kwantar da ita jikinsa ya riÆ™e gam ganin har wani jijjiga da take, kuka ne wanda yake fitowa tun daga Æ™asan zuciyarta wanda ta tara shi shekara da shekaru yake cinta a rai. Idan ta buÉ—e baki da nufin yin magana sai ta ji wani kukan ya sake taso mata, Abraham idanunsa sukai jajur daman yasan zai sha fama da Maminsa ya riga ya fahimci rauninta tuni, duk wanda ya fahimci rauninka kuma ya gama da kai. Ganin kukan ba mai Æ™arewa bane ya sa ya É—an kwantar da kansa a wuyanta a hankali maganarsa ke fitowa kamar raÉ—a ya ce “Crying Mama, Crying jee cry as so much as you can!” Kamar wacce ya Æ™arawa volume haka ta Æ™ara narkewa jikinsa tana wani irin kuka mai cin rai. A hankali ya fara rarrashinta duk da bai iya ba cikin kunnenta yake hura mata iska silently with sexy voice yake cewa “Shiii, sorry” Jin tsigar jikinta na tashi ya sanya tayi saurin haÉ—iye kukan sai hawaye, a hankali ta kalli Abraham kamar yadda yake kallonta ta ce “Enough is enough ka bar maganar iya nan” A hankali ya ce “Ohk, until we get Marriage” Idanunta na wani wajan ta ce “Tsaurin idanunka ya yi yawa, sbd Æ™addara ta faÉ—a mini har na kawo yanzu ba aure shi ne kake tunanin zan aureka? Kalleka U just 16 yrs, gwanini da kai kake cewa zaka aureni? Kai tsakani da Allah baka ji kunya?” Ta gyara tsaiwa ta ce “I understood, baka son ganina babu aure ne? To i promise you zan fito da mijin aure ka ji Yarona, kabar maganar u still be my son my baby” Abraham she dry ba ta bashi magana take amma bakinta rawa yake inda take kalla kuma da ban. A hankali ya taka har inda take tsaye ya É—an leÆ™a fuskarta tayi saurin rufe Idanu ya taÉ“e baki numfashinsu na haÉ—iye can Æ™asa daga shi sai ita ya ce “I want you Jee, i want to you to be in my side, Ina son ka Æ´ar madara” Ta watsa masa harara ta ce “Har abada, Æ™uruciya ke damunka” Hannu ya miÆ™a zai riÆ™eta ta yi saurin yin baya ta ce “Is prohibited in my religion” baya ya ja kaÉ—an yana É—aga mata hannu a taushashe ya ce “Ohk, Your religion is difficult” Ya É—an shafa kansa yana maida hannunsa baya a shagwaÉ“e ya ce “Marry me, I’ll give u all the happiness in our life” Majeederh ta yi shiru, wannan kamar wani opportunity ne na gyara Abraham zuwa yadda take so, zata gyara masa rayuwarsa da tarbiyya da komai. Murmushi ta yi ta ce “Khalil” Calmly ya ce “Maa” Kujera ta nuna masa, ya miÆ™a hannu zai riÆ™e ta ta Æ™ara janye wa ta haÉ—e fuska. Zama ta yi saman kujera, shi kuma ya nufi wajan fridge ya buÉ—e ya É—auki Favorite juice É—insa da apples guda biyu, gently ya juya ya ce “Maa i need food”
Ta yi masa shiru har ya gama kwasu komai, ya dawo ya zauna ya É“alle murfin lemon idanunsa lumshe yake É—an sha yana ya mutsa fuska he lost his appetite. “Who are you, Ibrahim?” Sosai ya jita ya basar ya ce “Yunwa ina ji” Ta ce “Ibrahim-Khalil” Ya zuba mata idanu sosai ta ce “Who are you? Where are you coming from? Me kke É“oyewa?” Shortly ya ce “hiding?” Ya girgiza kai ya ce “Jesus” Ta numfasa cikin dabara ta ce “Ka taÉ“a ganin ayi aure ba a san mutum ba? Iyaye family e.t.c?” A hankali ya ce “Me kike son sani a kaina?” Ta ce “Ur Father, country da sunan mahaifiya” Murmushi kawai taga ya yi, tare da yin baya ya kwantar da kansa yana rufe idanun, bottle É—in hannunsa ya matse nan take ta fashe juice É—in ya zube hannunsa ya fara zubar da jini. “Khalil” ya yi mata shiru tana danne tsoranta ta ce “Abraham” Idanunsa ya buÉ—e tare da zuba mata su, wani irin ja taga yayi wanda bata taÉ“a ganinsa ba, a nan kuma ta Æ™ara tabbar da zuciyarsa rauninsa kuma iyayensa. Murmushi taga ya sake yi wanda ya fito da kyansa duk da baya yanayi na jin daÉ—i cikin sauyin murya ta ji ya ce “Mother? Uhm” A hankali ya sunkuyar da kansa ya ce “I don’t know her, ban santa ba, she’s alive or not I don’t know” Kallonsa kawai take a hankali ya sake cewa “Idan an ce uwa ke nake kallo, kece mace ta farko data kula dani ta nuna mini soyayya ta uwa, wacce na rayuwa da wannan soyayyar har yanzu, Bayanke maza ne kawai suke tare dani Gang team É—in nan su ne ahhalina, ina da 10yrs na gama secondary school na fara University a wata Æ™asa” Ya yi shiru ta ce “Wacce Æ™asa?” Calmly ya ce “Germany” Ta ce “Ohk ina jinka” Ya Æ™ara lumshe idanunsa wanda duk suka rine ya ce “Daga nan na sauya University, har dai na kammala” Ta jinjina kai ta ce “Ur Father?? Mahaifinka fa?” Ya ce “I hate him” Da mamaki ta ce “Why? Me ya sa me ya yi maka?” Murmushi kawai ya yi yaÆ™i ce mata komai. Ta ce “Ok Shi ne ya biya maka kuÉ—in makaranta?” A nan ya yi wata kalar dry sosai yana girgiza ya ce “Funny, ina yaga kuÉ—in kai ni Germany? Kuma Karatun Likitanci, Welder fa yake” shi kansa ya san ya yaudari kansa sai ya ji kansa ya masa girma na Æ™aryar da ya yi. Majeederh ta ce “Kuma ina kai kke samun kuÉ—i? Me haÉ—inka da Gang team É—in nan?” Ƙuri ya yi mata da idanu ta ji ya saki dry ya ce “you’re asking too much, are you trying to change me? use your chance on me” Ya Æ™ara yin murmushi kawai idanunsa jajur jijiyoyin kansa duk sun fito kallo zakai masa kasan ba daÉ—in hirar yake ji ba, ya watsa hannunsa tare da cusa yatsunsa cikin suma ya birkitata ya zuba idanu ya ce “You can because I love you, kawai dai Gang team is my happiness in bani da lafiya sune, suke iya É—aukan haukana” Idanunta ta ji ya ciko da hawaye sbd tausayinsa ya yi kamar bai gani ba ya ce “Me kike so?” Ta ce “Bana son Debeka” Da wani irin sauri ya É—ago ya kalleta bai ce komai ba, ta ce “Bana son Shaye-shaye, yawon banza, kula matan banza, bana son faÉ—a da kowa ka koyi controlling kanka, kana zuwa wajan mahaifinka bana son gajeren wando ka maida hankali akan sana’arka, idan ba wani doke ba bana son shiga cikin Gang team É—in nan” Tunda ta fara magana yake kallon bakinta da idanunta ta ce “Kana jina?” Calmly ya ce “Ohk” A wannan karan da Æ™yar muryarsa take fita ta miÆ™e tsaye zata ta fi ya bita da idanu ya saka remote ya cire password sai da ta je bakin Æ™ofa ta ji ya ce “Zan aureki dole, Abraham baya Æ™arya” Da sauri ta fice daga cikin gidan tana sauke numfashi. Akan idanun Bar Aliyu ta fito da sauri ta shiga motarta tare da yin key, dake ya sauya mota bata sani ba, kuma bata hayyacinta hakan yasa sam bata gansa ba. Kifa kansa ya yi a kan hannun motar yana jin zuciyarsa kamar ta fito gabaÉ—aya ya rasa yadda zai yi da rayuwarsa, he want Majeederh in his whole life, amma tsoranta yake sauya masa take a ko wanne lokaci, duk sanda ya yi attempting faÉ—a mata he loves her sai yaga kamar ba ita ba, nan da nan ransa ya É“aci. He couldn’t sleep, eat, everything komai nasa ya tsaya ya yi asarar contract da yawan gaske. Failing a Shari’a ba a magana. A hankali ya kunna motarshi kai tsaye gidansu ya nufa, lokacin Hajia da Almustapha na zauna a parlour. Tunda ya shigo Hajia ke Kallonsa har ya nemi waje ya zauna yana mai da numfashi ta kasa daurewa ta ce “Aliyu lafiya?” Ba tare daya buÉ—e ido ba ya ce “Good, ina yini Hajia?” Ta yi shiru ta kasa amsawa. Wayarta ta É—auka ta kira Dije ta ce “Ki haÉ—awa Babana abinci yanzu” Dije ta ce “Done Hajia” Ta É—auke kallonta ga Aliyu ta ce “Almustapha ya matar taka?” Ya ce “Da tare zamu zo ma, bata jin daÉ—i ne” Ta ce “Ohk, Allah ya sauwaÆ™e” Ya É—an juya ya ce “Papa fa?” A nutse ta ce “Ya je meeting, kasan an fara shirye-shiryen tsayar da É—an takara” El ya ce “Kai, Shi Papa mene haÉ—in sa da wani takara ne, ban son ya tsaya wata siyasa wlh” Ta yi Murmushi kawai El ya Æ™ara cewa “Ohk i understand, jam’iyyar su ai ke kan mulki a yanzu, baya so mulki ya fita daga hannunsu” Almustapha ya yi dry ya ce “Kuma wallahi na ji jam’iyyar hamayya da Æ™arfinta ta fito, suna da Æ´an takarkaru har biyu dole sai sun yi primary election zaÉ“en cikin gida kafin fitar da gwani, amma da ina zaÉ“e Abuturab zan zaÉ“a, he’s a kind of person that i have never seen before, a dai Æ´an siyar nan tamu, ya taÉ“a neman takarar ko house of representatives or assembly na manta, yanzu na kamar ya yi aure wai, amma baya Æ™asar jinya yake” Aliyu zancen ya ji yana hawa kansa haka kurum kuma Abuturab É—in bai masa ba. Hajia ta ce “To Aku, duk ina kake jin wannan labaran?” Almustapha ya ce “Hajia media, a twitter a nan nake ganin latest news na Æ´an takarkaru, musamman wanda suka ke viral suna trending in the world” Almustapha ya ce “Kuma Æ™yakÆ™yawa da shi so Masha Allah” Sai a lokacin Aliyu ya buÉ—e ido tare da kallon Almustapha ya ce “To kai mace ne? Da zaka na description kyan É—an uwanka namiji?” El ya ce “Kai ban taÉ“a cewa kana da kyau bane? Idan kaga abu mai kyau ka yaba shi ne kawai, day before yesterday na je gidanka ai” A tsorace Aliyu ya ce “But baka faÉ—a mini ba?” Almustapha ya dinga kallon Aliyu, shi kuma Aliyu tsoro da kunya ya kama shi “Na je, matarka ta iya girki sosai fa, na ganta tare da wata kamar munafuka mai liÆ™ab” Wata É“oyayyiyar ajjiyar zuciya Aliyu ya sauke, Majeederh ce ta yi girkin. Suna zaune Dija ta kawo Hajia ta saka Aliyu a gaba sai gashi ya tashi da abincin cikin babban plate Kallonsa kawai take tayi tambayar duniya ya ce “lafiya”…. Abuturab na zaune feeling better gabaÉ—aya kwanan shi biyu da dawowa Æ™asar daga Switzerland. Idanunsa ya buÉ—e da Æ™yar jin Maysoon na cewa “Ka fita duba lafiyarka, ka dawo and you’re still sick wai meke damunka ne YallaÉ“ai? Ina ta Æ™oÆ™arin ganin na kyautata zamana da kai but i couldn’t, ka hana ni duk wata dama da zan kafa soyayyata a zuciyarka” Hawaye na zubu mata hannunta dafe da cikinta wata tara ta ce “Nasan baka so na, amma ni ina son ka, bani da tabbacin zan haife cikin nan lafiya, inma mu mutu tare inma na mutu na barsa ko ya mutu ya barni, don Allah ka nuna mini soyayya a kwanakin nan kafin cikar EDD É—ina na roÆ™eÆ™a Haydar” Kuka Maysoon ta saki sosai tana dafe cikinta, Abuturab ya zuba mata Idanu a hankali ya miÆ™a mata hannu ya ce “Come” Ta Æ™arasa ya zaunar da ita saman cinyarsa idanunsa akanta ya riÆ™o fuskarta ya ce “Maysoon” Tana kuka ta ce “Sir” Ya ce “Ina da Æ™ulafuci ina da naci, zuciyata nada kafiya akan abinda take so,ki yi mini uzuri ki amsheni a yadda nake, first love É—ina tana wani wajen ke kuma Allah ya Æ™addara zan zauna dake matsayin mata, ina baki ci sha, suttura ina saka miki kuÉ—i a bank duk wata, Maysoon ina jin zafi a zuciyata ina jin raÉ—aÉ—i ki taimaka mini na samu abinda nake so ta hanyar addu’a, yadda nake son ta ko mulkin nan dake tunkaro ni bana so haka, mene matsalarki?” Kuka take sosai ta ce “Are you going to insulate me? Kana faÉ—a mini Æ™arara baka so na, dole akai maka, me ya sa ba zaka duba irin son da nake maka ba YallaÉ“ai? Ni bani da matsala kaso ko wacce kawai kulawarka nake nema lokacin ka nake buÆ™ata, hatta wannan cikin na jikina Ubangiji ne kawai ya Æ™addara samuwar shi, yaushe rabon daka raÉ“eni?” A hankali ya ce “Sorry Maysoon” Kuka take ta ce “Please ko sau É—aya ne” Ya ce “Am not in the mood, ki je” Za ta yi magana ya daka mata tsawa tare da hankaÉ—eta ta faÉ—i Æ™asa saman Æ™aton cikinta, wata Æ™ara ta saki tana runtse Idanunta Abuturab ko ta kanta bai bi ma ya nufi part É—insa, Æ™arar data kuma yi ya ya jawo hankalin Mama da mai aikinta suka shigo parlourn a guje jinin dake malala a Æ™asan Maysoon ya sanya Mama rikice Maysoon tuni ta fara kokawa da ranta, Mama ta fara kuka sbd tausayi cikin ikon Allah kuma suka fara jin kukan jariri da sauri Mama ta É—aga Maysoon ta matsar da babyn Salati Maysoon take tana kiran sunan Abuturab tare da yin wata jijjiga idanunta na rufewa, Abuturab Mama ta shiga Æ™walawa kira yana ji ya yi shiru ganin numfashin Maysoon na tafiya baya dawowa yasa Mama fara kalmar shahada,idan ta kira sunan Maysoon sai ta faÉ—i kalmar shahada cak numfashinta ya tsaya jikinta ya saki idanunta ya yi sama rai ya yi halinsa Maysoon died.

 

No comments