Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Mijin Malama Book 2 Page 30


Khalil na driving a hankali idanunsa akan titi deep down na zuciyarsa tunanin yadda zai tunkari DDMASTER BOM yake, da yadda zai samu nasara akan shi. Ya sanya hannu yana ɗan hargitsa sumar kansa a nutse, shi fa duk duniya Allah daya halicce shi kawai yake jin tsoro, bashi da tsoro ko shakkar tun karar kowa, ya saba ɗaukan kasada tun kafin yanzu, balle wannan da yake ganin ko rayuwarsa ce ta salwalta, to ya yi sacrifice ne akan taimakon al’umma, daman bazai taɓa barin abinda yau zai ji ko mutuwa ya yi bashi tunani ko fargabar zuwa lahira. Ya sauke ɓoyayyiyar ajiyar zuciya a hankali kuma ya danna bluetooth ɗin kunnen shi,yana yin roundabout a taushashe ya yi lallausan murmushi tare da lumshe idanunsa, still driving on the direction he was heading to.. zuciyarsa a bubbuɗe yake sauraran abinda take cewa da ɗan sauri kuma ya saki kan motar ta fara ƙara “ƙiiiiiiit” Ta cikin wayar Jee ta ce “Are you okay?” Ta ji shiru, har yanzu kuma motar tafiya take yaƙi riƙe kan nata, jin shiru ya sanya ta ruɗe sosai ta ce “Are you there ? Man, Man!” Duk ta ruɗe She wondered if there was an accident on his way, in a state of love and passion ya furta “I love you” He said that from the bottom of his heart full of weakness. Jee bata taɓa jin Khalil ya furta kalmar ba a gareta, sai ta ji sabon hargitsatsen yanayi, a hankali kuma nutsuwa ta fara saukar mata, ta yarda ta amince da dukkan abubuwan da zuciyarta ke gasgata mata, a hankali ta ce “You scared me” Ya dawo a hankali yana riƙe kan motar, kamar tana gaban shi ya sake furta “I love you, i love u Madam” A hankali ta ce “I know” Ya yi shiru sai numfashinsa dake sauka ya rage gudun motar a nutse a taushashe ya ce “How do u know?” Clamly ta ce “Your action, and emotions” Ya girgiza kai kawai yana shiga cikin Bristol Palace Hotel can ƙasa ya ce “Lallai yarinya” Jee ta ware idanunta tana jin kamar yana kusa da ita ne a hankali ta ce “I am older than u, am 35 u’re just 20” Khalil ya dinga murmushi a kasalance ta ɗauka ma ba zai magana ba sai kuma ya ce “Kuma ƙwaninin yaron nan ya baki ciki in one time” Idanunsa ya sauka akan wani mai Guava ya ce “Madam” A hankali ta ce “Man” Ya furta “Guess what?” Tayi shiru sai ta ce “Ka shigo gida” Ya girgiza kai ya ce “Guava” Majeederh ta ce “Haba? Plz kazo mini da ita” Ya ce “Tab, ba zan tsaya ba” Ta ɗan yi tsakin shagwaɓa ta ce “Plz Man” Ya shafa gemunsa ya ce “With?” Ta ce “Apple, ice cream, pizza, with…” Ya dakatar da ita da “Hold on Madam, idan kika ci wannan How can you eat me?” Jee tayi saurin kashe wayar jin magana mai girma. Khalil na zaune saman kujera yana kallon mai martaba dake cewa “Sai yanzu?” Khalil ya ɗan kalli Mai martaba Ajlaal Sultaan yana harɗe ƙafarsa a kamalance da nutsuwar dake wanzuwa a jikinsa a kullum a ko yaushe tana ƙara fidda wata kwantacciyar Ilhama dake bayyana mazantakar shi da fitar dashi daga tubali na ƙuruciya zuwa na zalllar nagartacce, numfashi ya sauke a ɓoye yana shanye mamakin ganin Rohaan da Zaytoon a wajan ya jima yana kallon su, su ɗin ma shi suke kallo. Ya ɗauke ido
“Sorry, i took so long” Khalil Answered starring around them, a kuma taƙaice ya yi maganar
Roohan dake kula da Khalil ɗin ne ya ce “What’s bothering you?” Roohan asked bitting into his finger. Khalil bai ce komai ba, bashi da niyyar cewa komai ɗin Zaytoon ta ce “Ibrahim kana tunanin uwa zata wofintar da ɗan data haifa? Kana jin a ranka da gangan ta barka?” A ɗan fusace Khalil yana saka ƙafa tare da buga table ɗin gabansa nan take ya tarwatse ya ce

“I don’t have a mother in this world, if you called me just to tell me that I have a mother, I’m sorry am not interested” Ya miƙe tsaye yana hargitsa sumar kansa sai huci yake ya sake kallon Zaytoon ya ce “Granny, ki faɗa mata ni ta bar mini gida, me ya sa ta barni, ya akai sukai aure matsalarta ce da mijinta, yadda na tashi ba kulawar iyaye ban wulaƙanta ba, yanzu ma babu abinda zai sameni, su ne su kashe kansu ma sbd girman kai da jinkimar su, i don’t want her in my life anymore”
Yana faɗin hakan ya ɗauki wayarsa da rigarsa ta sama ya yi waje, suka bisa da kallo Roohan kallon ikon Allah kawai yake, idan ba kuskuren gani ya yi ba, bakinsa har wani tiririn masifa yake. Mai martaba Ajlaal Sultaan kawai yake girgizawa a hankali yake sakin lallausan murmushi daman ya ji a jikinsa hakance zata kasance. Zaytoon da abin duniya ya isheta ta ce “Ikon Allah, Ubangiji ka sassauta masa zafin zuciyar nan” Roohan ya ce “Amin, ku haɗa da ragowar ruwan sallar asr, matarsa na haƙuri”

“Kuma aka ce zai yi mata haka?” Mai martaba ya furta a hankali yana gyara zaman shi kamar baya so, cike da kamala kuma ya ce “Khalil loves his wife more than anything, he is afraid of losing nothing but his wife, ya sadaukar da komai saboda ita, ya sota fiye da kima yana kan sonta a yanzu, a gobe,jibi har gaban abada idan akwai, yanzu da ransa yake a ɓacan nan ba zai ƙarasa mata haka ba, sai ya samu nutsuwa” Roohan ya ce “Ɗan kwali ya ja hula kenan, kada dai labarin soyayyar ya zama na LAYLERH DA MAJNOON” Mai martaba ya ɗan kalli Roohan ya ce “Kasan labarin Layler da Majnoon? Roohan ka sani?” Roohan ya ɗaga shoulder ya ce “Na dai san an zuba soyayya, ina son labarin soyayya” Mai martaba ya girgiza kai kawai ba tare da ya ce komai ba, Ƙhulud dake tsaye ta ce “Ita Layler mutuwa take duk soyayyar da suka sha, shi kuma Majnoon haukacewa yake, ai asalin sunan shi Ƙais Majnoon ana nufin mahaukaci” Roohan ya yi kamar zai yi kuka sosai ya ce “But sun yi aure before Layler died?” Ta girgiza kai ta ce “Ko kaɗan, basu mallaki junan su ba” Ya sake cewa “To irin Soyayyar nan fa masifa ce, bata da wani amfani” Da sauri Zaytoon ta ce اصمت يا” روهان، لا أريد أن أحدث الكثير من الضجيج” Zaytoon ta ƙara cewa “Yin Allah, ƙaddara haɗuwa ko rabuwar masoya, baka da iko ko zarafin ja da hakan”…. Latifa na zaune gaban Dr ta ce “I’m still wondering Dr” Ya ware Idanu ya ce “Reason?” Ta ce “Taya kasan ni ba ƴar Babanmu bace? Nasan Blood group baya ɗaya daga cikin abinda ke sawa a gane ɗan wane ko ba ɗan shi ba” Dr ya jinjina kai ya ce “Exaclty, u got it well, kafin rasuwar Malam Umaru ya shaida mini yana zargin Alhji Bashir akan shi ne mahaifinki ya taɓa ganinsa da wata yarinya mai tsananin kama dake, domin zargin shi ya tabbata ya ce ayi DNA test, shi da kansa ya bani gashin kanki” Latifa Omar ta goge zufa ta ce “Dr ya DNA test yake?”

Ya ɗan juya a hankali yana danna abu kafin ya juya mata system ɗinsa ya ce “A DNA test (genetic testing) is a medical test that can identify mutations in your genes, chromosomes or proteins, Dna ƙwayar halitta ne, mutum daga wanne dangi ya fito, ko yanki, idan akai sample na Dna yana tantance uba da ɗa, waye wanda ba ɗa da uba bane, har ƙabilar da kake ciki Dna test yana bayyanawa, musamman idan ana tantama akan ɗa, ana amfani da gashi wajan yin gwajin ko jini, idan har daga jikin mutane biyun ya fito, ko so kake ka gane kai ɗan wanne gari ne, gwajin Dna test yana nunawa” Latifa Omar ta share zufa” Dr ya ce “Genotype kuma ana yi kafin aure wajan tantance samuwar dacewar ƙwayar halitta, da gane wanne Iyali za a samar, misali idan AA da SS suka yi aure yaran da za’a haifa zasu kasance AS ne kariya, sannan ba normal Genotype bane, idan AS da AS suka yi aure idan sun samu yara huɗu biyu za su iya kasancewa sikila zallar jininsu ya zama SS, biyu kuma kariya AS” Latifa ta jinjina kai ta ce “Yanzu ina kake tunanin zan samu Alhji Bashir ɗin sunana ya yake?” Ya ce “Shi ɗin mai arziƙi ne sosai” Ta sauke ajjiyar zuciya ta ce “Alhamdulillah” Sai kuma ya ce “Amma ya samu karayar arziƙi, don gidan da yake ma na haya ne, kinsan shi haihuwa da arziƙi na Allah ne daman” Ta kasa cewa komai ta sake shiga IG taga still Northern ɗin ba su yi mata reply ba, ita sam ba zata iya tarar Majeederh da wannan maganar ba, kuma tana buƙatar yafiyarta sosai..

Ddmaster bom na zaune saman wata mahaukaciyar kujera, ya rufe fuskar shi da ƙyalle wasu jibga jibgan mutane ne zagaye da shi, ko wanne ɗauke da manyan makamai da bindigogi na masifa, ya gyara zama sai kuma ya saki wata mahaukaciyar dariya yana sake duba I.d card ɗin ɗan nasa Khalil wanda ya shiga hukumar NAPTIP domin kawo ƙarshen shi, a fili ya ce “Baka san waye ubanka ba, lokacin da zaka sani kuma a ranar zaka mutu, kamar yadda na kawo ƙarshen Taj abokin ka, na sanya mota ta markaɗe shi” Wani babban yaron Ddmaster bom ya ce “Oga wai me ya sa kake son Gimbiya tazo nan?” Ya ce “Ina son kawo ƙarshen jinkimar ta, zuwanta gare ni shi ne zai zama silar kawo hakan, tun kafin na aureta na yi al’ƙawarin bawa wani Babba ita su kwanta saboda mugwayen kuɗin da zan samu, amma jinkimar matar ya rusa komai a lokacin kuma ta san waye ni tana ƙoƙarin tona asirina na saka a kasheta kisa na wulaƙanci amma sunci amanata ashe bata mutu ba” Ddmaster bom ya miƙe tsaye sai kuma ya sheƙe da wata dariya yana ƙyaƙyatawa ya ce “Akan kuɗi babu abinda ba zanyi ba” Ya sake kallon I.d card ɗin Khalil ya ce “MIJIN MALAMA?” Yaron na shi ya ce “Brother, yanzu mene plan ɗinka?” DDMASTER BOM ya ce “Sister ɗin Abraham ta zama cikakkiyar karuwa, kuma ni ne sila har yanzu bata san ni ne babanta ba, ina masifar son yarinyar saboda tana da masifar wayo, zata iya yin komai irin zuciyata ce da ita, ta kawo mini arziƙi da yawa ita take taimaka mini wajan samun matan da zamu cire musu ƙoda a fitar waje a siyar ko idanu” Mutumin ya sake cewa “Kuma da aure ka haife su?” Ddmaster bom ya ce “Of course YES” Ya jinjina mai bai taɓa tunani za a samu mutum mara imani da tausayi kamar Ddmaster bom ba, ƴar shi ta cikinsa? Ddmaster bom ya haɗe fuska ya ce “Plan ɗin, zan saka Khalil ya kashe ƴar uwarsa da hannunsa, ni kuma zan ɗora alhakin hakan akan Gimbiya yadda zata tafi gidan prison har abada ko na bata zab’in dawowa gareni, ta kwanta da mutumin nan a bani kuɗin, wanda idan tayi hakan naci galaba a kanta na kawo ƙarshen jinkimarta, KHALIL kuma akwai allurar data ke plan za a yi masa tsayin shekaru wacce zata juyar da tunaninsa, idan na samu Khalil a cikin harkokina nasan zanfi kowa dace domin tunaninsa a kaifafe yake zan kuma raba shi da matarsa…..,” Ya saki ihu da kururuwa ya ce “Bom! Sorry Gimbiya, Zaki rasa komai Khalil zai kashe ƴar uwar shi da hannunsa” Sai ya yi baya ya ce “I am waiting for you son, am waiting for you MIJIN MALAMA”
Khalil ne ya fito daga mota a hankali ya nufi cikin gidan a tsaye yaga Gimbiya wajen green ɗin flowers tayi tsaye ya ɗan kalleta yaga kanta a ƙasa, jikinta duka rawa yake zufa ta wanketa ga jijiyoyin kanta duka sun tashi, kamar zai shige sai ya tsaya ya ƙarasa yana zuba mata Idanu wata ƙatuwar kunama ya gani a tafin hannunta, wacce babu mamaki ta jima da harbinta, amma ko motsi Gimbiya ba ta yi gani take kamar ta zubar da jinin sarauta da jinkimar ta a banza, da wani irin sauri Khalil ya saka hannu ya ɗauke kunamar tare da saka ƙafa ya murjeta ya damƙe hannu Gimbiya a gigice, wanda shi kansa bai san yayi ba, ganin yadda tafin hannun ya yi jajur yasa Khalil rausayar da kai ya kwaɓe fuska a hankali yace “Ummie…” Fitowarsa kenan ya nufi wajan Jee ya sameta tana wanka ya sanya ƙafa ya tura ƙofar bathroom ɗin a hankali ya zubawa gadon bayanta Idanu da wani irin fitinannan yanayi, Majeederh a jikinta ta ji ana kallonta tana juyowa suka haɗa idanu da Khalil ta wani haɗe fuska ta ce “Me?” Ya nuna mata da idanu bata gane ba ya ce “Mala-mala nake gani” Ta runtse idanu tunda taga yaƙi shigowa tasan alwala ya yi ta ce “shigo mana” Ya girgiza kai ya ce “No, I’ll be fine here” Ta ce “Alwala ka yi?” Ya yi mata shiru, tasan ba zai ce a’a ba tunda ba zaiyi ƙarya ba, ta fito zata kamashi tasan tana taɓa shi komai ya lalace ya yi baya ce “Please Madam karki taɓa ni” Ganin da gaske janyo shi za tayi ciki ya ruga da gudu tare da bar mata ɗakin, yana fitowa ya samu Debeka tsaye tana waya a hankali was the first abinda ya ji kalmar Ddmaster bom, da wani irin sauri ya damƙi wuyanta ya ce “Who are you? Ina kika san DDMASTER BOM? Who are you?” Debeka ta zare Idanu ta kasa magana, daidai nan Gimbiya ta fito tare da yin tsaye, Khalil ya shaƙe wuyan Debeka idanunta sukai waje ta fara kakarin mutuwa da ƙarfi a hargitse ya ce “Waye shi? Who are you?” Da ƙyar ta buɗe bakinta ta ce “Dad….ssdd” Bom! Khalil yaga Debeka tayi pieces a gabansa Bom ya tashi da ita wanda babu mamaki ya jima a jikinta, ya sake buɗe idanu yaga hannunta can gefe ɗaya yana motsi……
[

Post a Comment for "Mijin Malama Book 2 Page 30"