Breaking News

Mijin Malama Book 2 Page 33


[10/12, 2:09 PM] Aisha Baby Novel: _*Nimcyluv sarauta 85*_
Duk yadda Khalil ya kai ga jarumta, dakiya da Æ™arfin zuciya da wata iriyar murÉ—aÉ—É—iyyar zuciya, amma a wannan karan neman su ya yi ya rasa, ganin yadda jikin mutum ya yi pieces a gabansa, kuma matarsa, kuma Æ´ar abokin dad É—insa Chancellor. Khalil ya dinga kallon gawar Debeka wacce É—an Æ™aramin bom É—in ya tashi da ita, ya juya ya kalli hannunta daya fita fit zuwa wani gefen nada ban, Ikon Allah kawai yake gani deep down na zuciyarsa yana kiran sunayen Allah Adadin iya abinda ya haddace, tunani fal zuciyarsa hakan na nufin Debeka aiki ta kewa Ddmaster bom? Meye haÉ—in shi da ita? Wacce hujja ce ta sanya yanzu take waya da shi? Something is fishy!. Gimbiya tana tsayen da take bata motsa ba, fuskarta looking ok as always, ba zaka taÉ“a ganin yanayi mai kama da tashin hankali a tattare da ita ba, a karo na farko ta É—an kalli gawar Debeka sai kuma ta É—auke Idanu, a sanyaye cikin rashin damuwa domin idan da sabo ta saba da ganin fiye da hakan cikin izza da jinkimar ta ta furta. “Who is she?” Ta É—an sauke numfashi tana juya idanunta a taushashe kuma a É—an kasalance ta Æ™ara furta “What are you accusing her of?? Ka tattare gawar” Ya yi mata shiru, ta fahimci baya son haÉ—a Idanu da ita, ta gane kuma firgicin daya shiga duba da yadda naman jikinsa ke rawa ga zufar dake tsastsafowa daga goshinsa, a hankali tana É—an haÉ—e yatsun hannunta can ciki ta ce “Ibrahim, ur wife is coming” Khalil ya É—aga kansa da sauri sai kuma ya kalli Ummi, jin motsi daga Æ™ofar part É—in Jee ya saka Khalil zare rigar jikinsa ya goge jinin hannunsa dana Æ™afarsa ya cilla rigar bayan kujera, a É—an gaggauce ya buÉ—e Æ™ofar ya shiga daidai nan itama ta Æ™araso Æ™ofar tana Æ™oÆ™arin murÉ—a handle É—in ta ji an buÉ—e, ta É—an tsaya tana kallonsa kamar wacce ke shirin fahimtar wani abu, ya san kaifaffan tunaninta sai yaga ta hararesa tana shirin bi ta gefensa ta nufi waje ya yi saurin saka hannu ya kamo Æ™ugunta tare da dawo da ita baya, ta ware manyan sexy eyes É—inta a kansa tana É—aga masa gira, a taushashe ya ce “I need u wife” Ya faÉ—a a hankali yana mai saita muryarsa a hankali kuma ya murza hancinsa a nata bayan ya yi covering fuskarsu waje guda, mamakin yadda zuciyarsa ke tsananin bugawa da Æ™arfi wacce bata taÉ“a ji ba tayi ta miÆ™a hannu tare da É—ora shi a saitin zuciyarsa kasancewar Æ™irjinsa a buÉ—e yake kuma a faÉ—aÉ—e ya bayyana, ta manne hannun sai kuma ta É—aga lafiyayyun lumsassun idanunta ta kallesa a hankali ta ce “Your heart is beating way too fast, are you okay?” Ya zubawa fuskarta Idanu, tunaninsa ta yadda zai yi keeping É—inta busy yake a cikin bedroom É—in, ko ya sanyata bacci. “Man” Jee ta furta tana riÆ™e nasa Æ™ugun ganin kamar tunaninsa ya KaÉ—aita ya É—aga mata gira, ta ce “Ba kaci komai ba, ur food is ready” Ya yi shiru sai kuma ya girgiza kai yana kama kunnenta tare da É—ora bakinsa ya ce “Tunda na sameki na rage ci, abincina kala biyu” Tayi saurin kallonsa ya kashe mata ido ya ce “This is your husband, Ibrahimul-khalil, now I’ll feed on u later I’ll eat the food” Yana faÉ—in hakan ya sunkuceta yana zare hijab É—in jikinta, ta riÆ™e shi kamar za tai kuka ta ce “Khalil, Ummi” Yana kwantar da ita saman gado ya saka hannu ya Æ™ure a.c yana zare ribbon na kanta ya ce “Who is Ummi abeg? tasan gidan sabbin ma’arauta ta zo, da zaki kyauta kiyi screaming yadda zata ji ta gudu” Majeederh ta ware Idanu ta ce “Ni ina gudun abin kunya” Ya murza bakinta ya ce “Ni gaba na bashi” Za ta yi magana ta tashi ya yi saurin kissing nata yabi ya mayar da ita kwanciyar a hankali ya ce “Kila ciki na biyu zan baki, garin hadari sai ki haifi twins” Jee tayi dariya tana tura hannunta a sumar shi ta ce “Gaskiya Khalil sanda ake topic É—in Biology bacci kake” Bai sake mata magana ba domin baya hali na fahimta….

Da sauri Khalil ya kunna switch É—in bedroom É—in, saboda daman a Æ™a’ida baya buÆ™atar haske,sai yaso zai kunna, ya dinga kallonta ganin yadda take bacci a nutse, kamar yadda ya yi al’Æ™awari gashi ya sata baccin, ya É—an shafa kansa sai kuma ya yi kissing forehead É—inta a hankali ya furta “Rest of my life” Ya miÆ™e ya nufi waje, tsaye ya yi a wajan ganin babu gawar ba alamarta ya juya ya kalli Ummi dake zaune saman kujera ta harÉ—e Æ™afa tana danna waya, ba zaka taÉ“a cewa ta haifi Khalil ba, rashin ganin gawar da jinin yasa Khalil Æ™arasawa wajan Gimbiya da sauri yana zama kusa da ita cikin rashin sani da sabo ya É—ora hannunsa a shoulder É—in Gimbiya yana É—an leÆ™a fuskarta a hankali ya ce “Ummie ina gawar?” Ta juya ya kalle shi sai kuma ta kalli hannunsa a hankali ta ce “Ku shirya kayanku, now” Ta miÆ™e tsaye still tana danna iphone É—in hannunta yadda yatsunta ke sauka zaka gane wani muhimmun abu takeyi, ya tashi jiki a sanyaye har ya juya ya ji ta ce “Hi Young Man” Ya kalleta sai kuma ta nuna ya je kawai.. Motar su Majeederh ce ta fara fita a sirrince, Jee ta ce Ummie ta bata tayi driving É—in, ita dai Ummie bata kalli Majeederh ba, da wani irin masifaffan gudu taja motar, kana gani kasan ta Æ™ware a juya mota ta kuma saba da tsere da ita, bayan tafiyar su Jee Khalil ya fito daga shi sai three quarter daman komai nasa Gimbiya ta wuce da shi, sai ya nuna kamar unguwa za shi ko mota bai É—auka ba, ya fice a Æ™afa fuskarsa da face masks ya jima yana tafiya da É—an tsalle kamar training yake ya nemi napep ya tsaida ya sanar masa inda zai kaisa, kai tsaye airport ya Æ™arasa a nan yaga Mai martaba Ajlaal Sultaan, Zaytoon, Roohan, Ƙhulud, Zoya da Zohal, sai Majeederh dake tsaye gefe, yana zuwa haÉ—aÉ—É—an private jet É—in na sauka, daman suna waiting room, ne duk suka miÆ™e zuwa bakin vip daga nan suka shiga harabar jirgin, Mai martaba Ajlaal Sultaan da Ƙhulud suna champer ta É—aya, ta tsakiya kuma Roohan ne da Ƙhulud sai Gimbiya, ta Æ™arshe Khalil ne da Matarsa Jee a haka jirgin ya tashi zuwa sararin samaniya ya nufi Saudiyya da su.
Maman Alpha na zaune tana kallon Baby Khalil dake wasan shi, General Alpha ne ya shigo cikin wata Kamfala mai kyau hannunsa zube cikin Aljihu ya zauna a hankali yana cewa “Barka da hutawa Mama” Ta ce “Yauwa General, ka ji meke faruwa?” Ya buÉ—e ido ya ce “Mefa?” Ta ce “Al’amarin Æ™asar nan, wai wasu mata masu shan jini sun bayyana, suna sallama da a taimaka musu da abinci kana basu suke zuÆ™e maka jini, ga tsadar man fetur, abinci ya yi tsada mutane nata mutuwa” A hankali ya ce “Oops, Allah ya kyauta”
“Yanzu wacce kalar rayuwa muke ciki ne? Anya! Hakan zai tabbata, shin shuwagabanni basa gani ne? Jami’an tsaro suna ina? Hukumar kare hakÆ™in rayuka da lafiya ta Æ™asa da jiha suna ina? Rayuka na salwata, yawan mabarata suna Æ™ara tu’azzara, ga Shaye-shaye na Æ™ara yawaita, wai me ake nufi da al’ummar Annabi Adamu ne? Shin sun manta su wad’anda za’a tambaya ne ranar gobe Æ™iyama? Suna yini basu ci ba suma? Ko mancewa suke da ranar Yaumal Æ™iyamati, tunanin su ba zasu mutu ba?” Ta share hawayen daya cika a Idanunta ta ce “Yanzu fa Æ´an mata guda ashirin aka nema aka rasa, ga wata mata data mutu saboda yunwa, Wayyo, innalillahi wa’inna ilahir raji’un!” A sanyaye General Alpha ya ce “Allah yana gani, stop bothering yourself Maama” Ya kalli Baby Khalil har zai É—auke shi sai ya fasa saboda wata mahaukaciyar kama da suke da Khalil, nan da nan ransa ya É“aci ya runtse idanunsa, zuciyarsa na bugawa wani irin zafi da raÉ—aÉ—i yake ji a ransa har yanzu kuma bai fidda rai da samun Majeederh matsayin mata ba, yadda abubuwa suka same shi dalilinta ya saka yaÆ™ini lashakka zai sameta ko da ace yana samunta zai koma ga Ubangiji. Jin Æ™arar wayarsa ya sanya ya É—auka da sauri kuma ya miÆ™e yana Æ™amewa tare da É—aga hannunsa ya sara da Æ™arfi ya ce “YES Sir!” Sai ya yi shiru sai can ya ce “Ok Sir, i am ready” Yana gama faÉ—in hakan ya kira wata number ana É—agawa ya ce “Oba, oba, oba 012 are you with me?” Aka bashi amsa ya ce “Ready, Major Janar Mohammed Yusuf, shugaban sojoji ya sauka a Kano shi da Field Marshal, zamu je wajan shi tare da kai, abu ne na gaggawa da yiyuwa juyin mulkin sojoji za su yi a Nijeriya, kasan kuma idan hakan ta kasance duk wani Gwamna na jiha sauka zai yi soja ne zai hau” Ya yi shiru jin anyi Sallama Zaleehat ce ta shigo hakan yasa ya kashe wayar suka gaisa da Maman Alpha tana ce mata ya mai jiki saboda Baby Khalil da bashi da lafiya, Alpha ya nufi waje Maman Alpha ta ce “Allah ya tsare” Ya nufi waje sojojin birjik a compound na gidan Uncle Bello, yana Æ™oÆ™arin shiga mota aka ce “General” Ya tsaya sai kuma ya juya idanunsa ya sauka akanta, a hankali ya ce “How are you?” Zaleehat tayi Æ™asa da kanta ta kasa cewa komai idanunta ya cicciko da hawaye, Alpha ya É—an lumshe idanu sai ya buÉ—e ya É—an juya yaga ba kowa da sauri ya Æ™arasa wajan Zaleehat tare da jawota ya rungumeta ta fashe da kuka ta ce “I am tired, General” Ya rungumeta sosai a hankali ya ce “I am sorry dear am sorry” Kuka kawai take ta ce “But u know i missed you” Ya kasa magana sai kuma ya yi Æ™asa da murya ya ce “Same dear” Aaliyyah ce tsaye tana kallon Aliyu daya É—an rausayar da kansa gefe kamar maraya a hankali ya ce “plz dear” Tayi Æ™asa da murya ta ce “Meyasa kake tunanin ga Anti Latifa ni zan iya aurenka? Me ya sa? Haba Yaa Aliyu koba komai akwai alkunya” Ya harÉ—e hannu a Æ™irji ya ce “Oh, now tell me do you love me? Alkunya kike ko so na ne bakya yi?” Kafin ta yi magana wayarta ya fara Æ™ara ta É—auka ganin Du’a ce ta ce “Sister Du’a ya kike?” Du’a bakinta na rawa ta ce “Ajiye gaisuwa gefe, na kira number Anti Jeederh baya tafiya” Aaliyyah ta É—an yi shiru sai kuma ta ce “Meke faruwa? Lafiya dai? Akwai damuwa ne?” Du’a ta ce “Ke daÆ™iÆ™iyar Æ™waÆ™walwa ce dake sometimes, check your WhatsApp, ki duba IG account É—in Northern kiga komai” Du’a ta kashe wayar daga nan tabi kowa na family ta faÉ—a masa. A tsorace Aaliyyah ke karanta posting É—in Northern wanda malama ta saki 20 minutes ago, but comment sama da 3k gabaÉ—aya tsinewa Latifa Omar suke, Aliyu ya matsa kusa da ita ya amshi wayar ganin yadda take kuka kamar ranta zai fita, tashin hankalin Aliyu yafi na Aaliyyah ya yi baya kamar zai faÉ—i ya jingina da mota, ganin abinda Latifa Omar ta ce a Æ™arshe “Malam bayan hakÆ™in Majeederh kuma Bestie,nasan hakÆ™in mijina Aliyu ma ba zai barni ba, na zubar da cikinsa sau babu adadi bisa umarnin boka, na yanke shawarar faÉ—a miki ko zan samu sassauci daga zuciyata na samu su yafe mini na cutar da Majeederh cuta mai yawa wacce babu wata aminiyar arziÆ™i da zata iya yin haka, na yarda ni muguwa ce azzaluma, saboda a baya ina baÆ™in ciki da duk abinda Majeederh take musamman kyan da take dashi da farin jinin data taso da shi, hakan yasa na daÆ™ile farin jinin na mayar da ita mujiya, hatta mijina Aliyu bani yake so ba, ita ce zaÉ“in shi amma ni ce tubalin rasa muradin zuciyar malama wallahi ni ba aminiyar Æ™warai ba ce….,” Aliyu Sufyan bai Æ™arasa karatun ba, yaji wani irin jiri ya kwashe shi ganin zai zube yasa Aaliyyah tare shi ya yi saurin jawota ya rungumeta idanunsa na zubar da hawaye a hankali ya ce “Marry me pls Leeyerh” kukan take itama wallahi sai ta auri Aliyu ko dan taci kutumar uban Latifa zata gane bata da hankali sai ta gigita mata lissafi kuma ba zata taÉ“a bari Aliyu ya saki Latifa ba, baÆ™in ciki ne zai sanya zuciyarta bugawa one time.. Gimbiya na tsaye tana danna system a É—an gaggauce hannunta É—aya a kunne, a hankali Khalil ya Æ™arasa ya kara kunnen shi muryar Dad É—insa ya ji yana cewa “Akan rayuwar Æ´arki ma jinkimar zakiyi? Ki gaggauta zuwa ko na tura miki da wuyanta, zaki sha mamakina na baki 24hrs” Ba tayi masa magana ba ya ce “Ki amsheta ki bani Abraham, kuma daga nan ki fita sabgar shi kamar yadda kika fita a baya daman ba ciwon shi kika sani ba, i am waiting for you” Yana faÉ—in hakan ya kashe kiran, Khalil na Æ™oÆ™arin É—auke kunnen shi ya ji ta kama kunnen ta murÉ—e da É—an Æ™arfi, ya saki Æ™ara “Auchhh” Ba tare daya sani ba da kuma soyayyar uwa mahaifiya dake fusgar shi ya faÉ—a jikinta ya rungumeta a hankali a É—an fakaice tayi Holding nasa back, da sauri ya saketa yana sakin numfashi, a karo na farko bayan wasu shekaru ta saki wani Æ™lkyakkyawan murmushi tana juyawa, Majeederh tayi masa dariya ta ce “Wai meye kake gudunta?” Ya É—an kwaÉ“e fuska a hankali ya ce “ban san me zan ce mata ba, ban santa bafa, kunyar ta nake ji” Kafin tayi magana ankira shi daga hukumar NAPTIP Musbah ya ce “Private Investigators É—in mu sun shaida mana DDMASTER BOM yana Pakistan, zuwa jibi zai É“ace zamu tura maka komai na tafiya nan da 24hrs ka shirya ka tafi don’t let anyone know” Khalil ya jinjina kai saboda Jee dake kusa da shi, Musbah ya ce “And where are you now? Ina buÆ™atar sanin location, Æ™asa, ko Area” Khalil ya yi jim sai ya ce “No, a shirya komai a tura ta waya” Yana faÉ—in hakan ya kashe wayar, ya É—aga kansa kenan ya hango Gimbiya a hankali tana fita ta Æ™ofar baya hannunta riÆ™e da trolley ga wani ticket da yake gani, tunani yake where is she going to? Sai ya É—aga shoulder kawai, ya nufi dinning zai ci abinci Jee kuma ta nufi wani part, kasancewar abincin larabawa ne aka zuba wani masifaffan pepper a ciki, ga ba wani É—anÉ—ano duk so da Æ™aunar da Khalil kema abinci baya Æ™aunar yaji ko da wasa, gigita masa lissafi yake ko yana Æ™arami idan yaci yaji ya dinga hawaye yana zaro tongue yana “Mami pepper, Mami my tongue zai cire” Har wasu Æ™ananun guraje ke fito masa, ya zubawa abincin idanu ganin rice É—in ta É—an yi wani colour gwanin sha’awa ya sanya ya É—auki spoon, tare da yin bismillah ya sanya a baki, da wani kalar sauri ya cillar da spoon É—in, wani zufa na yanko masa jikinsa ya É—auki rawa da É“ari, idanunsa sukai jajur suka fito waje saboda azaba, babu wanda ya fahimta, gashi ya kasa magana sai fito da harshe yake yana dunÆ™ule hannu wata kalar gigitacciyar azaba yake ji tun daga kan yatsar Æ™afarsa har zuwa tsakiyar kansa, yana jin har wani tiririn azaba yake ji na fita daga kansa, idanunsa suna Æ™anÆ™ancewa tunda yake bai taÉ“a jin abu makamancin haka ba, shi yasa ba abincin kowa yake ci ba, a hankali ya kifa kansa a dinning É—in jikinsa duka ya jiÆ™e sharkaf da wata kyakkyawar zufa wacce tsananin azaba da gigicewa ya fiddo da ita, numfashinsa ya fara sarÆ™ewa tsakiyar Æ™irjinsa na masa zafi zafi da zugi, Mai martaba Ajlaal Sultaan da Zaytoon magana suke a hankali hakan ya sanya gabaÉ—aya basu farga ba, Roohan waya yake dannawa Ƙhulud kuma abincinta kawai take ci, zaton su kuma Gimbiya na sashin ta, Daidai nan majeederh ta fito Æ™amshinta a kullum dake alamtawa zuciyarsa zuwanta shi É—in ne a yanzu ya sanar da shi, ya miÆ™e da Æ™yar jiki na Æ™yarma Jee ta ce “Granny ga fresh milk É—in…,” Bata Æ™arasa ba ta ji an damÆ™ota hanka ya jawo hankalin jama’ar wajan. “Khalil lafiya?” Cewar Zaytoon amma ina babu bakin magana Jee dake Æ™oÆ™arin yi masa magana taga ya yi sauri a gaggauce cike da neman É—aukin jin harshen shi zai tsinke da wani fitinannan wahalallan yanayi ya haÉ—e bakinsu waje guda…
[

No comments