Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Mijin Malama Book 2 Page 37


*Lokaci da dama ina son yin magana amma bani da lokaci ko zarafin fidda abinda ke maÆ™ale a zicciyana, sautari kuma ina ganin abinda zan faÉ—a ya sha bamban da zaton ku, lissafin ba zai zo nan ba, _ALLAH YANA GANI_ kuma shi ne shaida, ban yi haka da nufin ci zarafi wani É—an-adam ba, domin ni ba macace mai damuwa da al’amuran mutane ba, balle na fahimci y rayuwarka take har na rubuta wani abu na yaÉ—awa jama’a, abinda baku sani ba ban taÉ“a sha’awar rubuta true life story ba, ina da labarai na gaske irin su *MUNAFIKIN MIJI* *labari ne da ko wacce Æ´a mace zata so ji da sani, amma ban rubuta ba, sbd ban fiya son surutu ba, shi kuma baki tsatsa ne guba ne, dole ka ji tsoro a hakanma muna tare da falaÆ™i da nasi su ayatul kursi邏. Ya zama last time da mace zata zo mini da maganar ina na santa na É—auki labarin rayuwarta na rubuta, wlh da true life story zan rubuta zaku sha mamaki a nan media, bana cika baki bana cewa na iya ba zan taÉ“a cewa na iya ba, kafin kayi rubutu wasu sun yi, bayan kayi rubutu wasu sun yi, rayuwar ai kamar juyin waina a danta ne邏 gobe kai ne jibi wani, to gaskiya kai na baya iya É—aukan tension _ALLAH YANA GANI_ Ina masifar son mai suna da Æ™aunar rubutuna, wala writer’s wala reader’s, kawai ka kame kanka yadda Allah ya yika shikenan, gaisuwa ta musamman ga NIMCY REAL FANS irin su Mom Sani paid藍su Oum Safna da ake fama da laulayi su Balkisa mai awara, su RuÆ™ayya Sabo Gambo mai adawa da Khalil, Ummu imam kwaila樂 Nazeefa sabo Nashe, Fareeda Abdullahi writer, Ummu Fatima writer, Mom muhseen writer, Amjat writer, Aishamadawaki, Hajja Ayusher, Hajja FATIMA, Hajja Fatima M Maddibo, Hamzzatumaimunat huhuhu a bini bashi*

*Ga special people group hajiyoyi salamu alaykum藍 ga Arewa readers irin su Zaleehat, Salmerh, Mr su Maryam Abba zannah su Farida, Sophia sadeeq, Aisha Isma’il Dalhat, shertu sweet Bakery, Easha, Lubabatumuhammad, Rabi, Baby samdi… Sauran mu haÉ—u Monday…. Zaku samu MIJIN MALAM tun daga 89 zuwa 100 Arewabooks daga weekend zuwa Monday, love you*

Follow me on Facebook
@Na’ima Sulaiman Sarauta

John was looking at the doctor with excitement all over his face, yana jin wata nutsuwa na saukar masa jin bayan shuÉ—ewar shekaru biyu da watanni yau Khalil ya farka daga halin jinyar daya samu kansa a ciki, John ya kalli Dr É—in ya ce mata “Are you sure? Khalil has really recovered from his situation?” Ta jinjina kai ta ce “Yes, Sir” Ya shafa kai yana rufe idanunsa a hankali ya furta “Ma sha Allah, Alhamdulillah” Farar matashiyar wacce ita ta kasance Dr ta kalli John domin sam bai mata kama da Musulmi ba, wata line ta É—an danna ta shiga magana da turanci akan É“angaren da Khalil yake kana ta ambaci sunansa John, ta kalle shi ta ce “He felt so relieved, kana iya zuwa ka gansa” John jiki na rawa ya ce “Thank you Dr” Yana faÉ—in hakan ya juya zuwa direction É—in É“angaren Da Khalil yake na musamman. A hankali ya tura handle É—in Æ™ofar tare da turawa ya shiga bakinsa É—auke da sallama, haÉ—aÉ—É—an bedroom ne wanda ya kasance a cikin hospital É—in, ba zaka taÉ“a cewa É—akin jinya bane, Idanun John ya sauka akan Khalil dake zaune a tsakiyar bed kamar wani sarki ya tankwashe Æ™afafuwansa, hannayensa zube akan cinyoyinsa kansa a Æ™asa idanunsa a lumshe, wata green É—in riga ce a jikinsa kamar uniform, shi kansa John É—in green É—in riga aka bashi ya saka, wata hular leda itama green ga safar Æ™afa data hannu, farin ciki kwance a fuskarsa ya Æ™arasa sai kuma ya kalli Dr wanda ke ciki yana duba abubuwa ya ce “Dr how is he? Da matsala ko wani abu?”
“Not yet, but jikin ya yi sauÆ™i, daga yanzu zuwa ko yaushe zaku iya tafiya” Dr ya É—an duba abu sai Kuma ya ce “Babu matsala dangane da zuciyarsa hatta wajan da wuÆ™ar ta É—an shafa a gefen zuciyar yanzu lafiya take, matsala É—aya tasirin da poison É—in tayi a jikinsa, zafin zuciyarsa will increase more than before, baya buÆ™atar reasons wajan yanke hukunci, zai dinga acting madly, rashin maganar shi zai Æ™aru da zarar ka masa ihu aka, kansa zai fara juyawa daga nan zuciyar zata fara aikinta na zafi, sai abu É—aya…” Dr ya É—an yi shiru yana kallon Khalil wanda sarai yana jinsu kuma yana fahimta, kawai abubuwa ne sukai masa yawa a zuciya yana farkawa kuma da sunan “Jeena” Ya farka. John ya ce “Go on, Dr”
Dr ya sake kallon Khalil ganin yana É—an hargitsa sumarsa ya sake wani masifaffan kyau ya sauya gabaÉ—aya, duk baÆ™in fatarsa sai da tayi haske tai wani chocolate saboda tsananin kulawar da ake basa, ba zaka É—auka jinya yake ba, ya zama jibgege ya kuma buÉ—e sosai musamman daga Æ™irjinsa, ga wata suma da saje data sake yawa a fuskar zuwa madaidaicin Geminal ya yi wani kyakkyawan yanayi na É—aukan hankali, kai tsaye Dr zai iya fahimtar halin da Khalil ke ciki musamman da yaga yana lullumshe Idanu a hankali kuma yake cije lip’s É—insa sai hargitsa kai yakeyi. John ya taÉ“a Dr ya ce “Are you with me? Akwai damuwa ne bayan haka? Is there any problem? Badai matsala ya samu ba? Da tunaninsa ba kuma loosing memory ya yi ba?” Dr ya yi murmushi ya ce “Before that is he was married?” John ya kalli Khalil sosai sai kuma ya ce “Yes of course, yana da mata da ciki ma ya barta” Dr ya zare Idanu sai kuma ya ce “If I remember correctly, his wife has already given birth?” John ya jinjina kai ya ce “Sai dai basu san yana raye ba ai Dr” Da mamaki Dr ya kalli John da Khalil da yanzu ya É—ago idanunsa jin ance ba a san yana raye ba? Kamar kuma ji ya yi ance zuwa yanzu matarsa ta haihu? What’s going on?

“Tunanin waye wannan?” John ya ce “I have no choice, no option, no opportunity, bayan É“oye Khalil, tun zuwan Khalil Pakistan muke Æ™asar nida Joshua, muna bin duka wani motsin Khalil musamman da a kwana ki biyun baya mai da hankalinsa akan companies É—insa, lokacin da ake haska faÉ—an shi da Ddmaster Joshua na wajan jami’an, gurin wani abokinsa, a nan yake ganin komai immediately yazo wajena, banyi zaton wani abu zai faru har haka ba, na É—auki mota sak irin wacce Joshua ya É—auka, sai shi ya tsaya wani lungu ni kuma na nufi wajan Khalil, bayan an biyoni sai na shige lungun da Joshua yake saboda i was very afraid da yadda naga muggan makamai, Joshua didn’t stop to hear the explanation I was going to give him, He didn’t give me a chance to speak at all, sai ya ja motarshi ya fita mutanen suka bisa” John ya yi shiru yana jin kamar a lokacin komai yake faruwa a hankali ya sauke numfashi ya ce. “As Khalil’s wife often says, everything that happens to a person is written as adestiny, No one can change his destiny, ajali ya ja Joshua zuwa Pakistan, He sacrificed his life to save Khalil’s, akan idanuna Joshua ya babbake, da shi da motar suka zama toka, mutane sun É—auka ni da Khalil ne muka mutu tunda motar iri É—aya ce ba wanda ya tsaya ya duba su waye a ciki, na ji tsoro, kuma tsoron Allah ya sake kamani ainun na Æ™ara yadda da imani babu abin kaÉ—aitawa sai shi, Annabi Muhammad S.A.W Manzon Allah ne” John ya sauke kansa Æ™asa a hankali ya ce “Na ji a raina kamar mutanen Ddmaster bom za su bibiyi rayuwar Khalil, na yanke shawarar nesanta shi da Æ™asar bakiÉ—aya domin ayi masa magani, babu abinda ke motsi a jikinsa haka muka taho U.s da visar mara lafiya urgently, nama yi zaton ya mutu Likitoci suka karÉ“e shi immediately, a haka muka dinga zama a U.s secretly har tsayin shekara biyu da wata shida”

Dr wanda yake da zurfin tunani sosai gashi so friendly, zuciyarsa mai kyau da tsafta duk da kasancewar shi Kirista, amma zaka É—auka Muslimi ne a fuska saboda nutsuwa, ya sauke numfashi ya ce “To tabbas matarsa idan har tana raye yanzu ta haihu, babbar damuwar zata iya yin wani auren ma” Sai a lokacin suka ji saukar muryar Khalil a É—an raunace irin ta zallar marasa lafiya da Æ™yar ya buÉ—e baki yana dafe kansa ya ce “Tunda na kasance a raye, My wife most definitely be alive” Suka kalle shi lokaci É—aya ba zaka É—auka shi ya yi maganar ba, can ya É—ago kai idanunsa sun yi masifar jaa saboda halin da yake ciki a É—an gaggauce ya ce “She will never marry, she made me a promise that she will never forget me, balle ta haÉ—a jiki da wani, idan na tabbatar wani ya aureta…” Ya cije bakinsa yana girgiza kai irin bai ma san me zai ba, domin ko bai cirewa mutum mazantakar shi ba, wallahi sai ya nakasa shi, har Æ™asan zuciyarsa yake jin ba zata taÉ“a yarda da ya mutu ba, ko uban kowa zai yarda, ya samu labarin tayi auren “Uhm” Da mijin, da wanda ya haÉ—a auren, da waliyyan wallahi sun shiga uku. John ya ce “Dr kana magana É—azu, me kake son cewa?” Dr ya ce “Poison d’in ta Æ™arawa kuzarin shi lafiya, ta Æ™ara masa zafi, da hauhawar sha’awa ta neman iyali, maybe an yi hakan ne domin a sanya shi neman mata kamar hauka, domin at least zai iya neman mace sau uku a rana, Æ™arfinsa ya Æ™aru kamar zaki na gudu lokacin da yaga nama ne, ko yanzu abinda ke damunsa kenan, bai dai fahimta bane, so the choice is yours” Yana faÉ—in haka ya fita abinsa, John ya kalli Khalil yana riÆ™e dariyarsa a hankali ya ce “Kai ai gata poison É—in nan tayi maka, yanzu ya? A kawo taimako ne ko zaka rakata haka?” Khalil did not look at John, and he did not speak, he was silent and acting like a king. Khalil ya kwanta tare da mirginawa ya yi rufda ciki yana lumshe gajiyayyun idanunsa, sai a lokacin komai ke dawowa kansa can Æ™asa daga shi sai zuciyarsa ya ce “Ummie? Clara?” Wani irin so da Æ™auna haÉ—i da kewar mahaifinsa ya wanzu a zuciyarsa.
Wajan 6 na yamma John ya sake dawowa ya samu Khalil ya yi wanka ya yi sallah, gefensa ga cup É—auke da green tea a ciki, kamar yadda ya ganshi É—azu yanzu ma haka yake, yana tsakiyar gado ya tankwashe Æ™afafuwansa, ya É—an zuba hannunsa a saman cinyoyinsa, John bashi da tabbacin Khalil ya amsa sallamar or not, domin kansa a Æ™asa yake idanunsa a lumshe, a hankali yake sauke ajiyar zuciya yana danne lip É—insa na Æ™asa wanda yayi jajur. John ya ce “Ranka ya daÉ—e” Khalil ya yi shiru John ya sake cewa “Jinin sarauta ya fara aikinsa kenan, have you eaten Ranka ya daÉ—e?” Khalil ya É—ago kansa yana zubawa John rinannun rikitattun idanunsa wanda sukai laushi da sanyi, yadda idanun Khalil sukai ya sanya John tuntsirewa da wata mahaukaciyar dariya yana durÆ™ushewa ya ce “Goodness, kamar zaka ci babu? Have you eaten?” Khalil ya yi shiru sama da 40 seconds kafin John ya ji Khalil ya furta.
“Zani gida, i want to see my wife and child” John ya ce “Ka ganta? Ko ka yi having….” Wani hargitsatsen kallo na mutuwa da Khalil ya yi wa John ya tilasta masa yin shiru kafin ya ce “Tuba nake ranka ya daÉ—e, sai nan da kwana goma zamu koma” Khalil ya rausar da kansa gefe yana É—an kwaÉ“e fuska “Have you eaten?” A fusace Khalil ya juya saboda ya fara jinsa sama sama ya kasa riÆ™e kansa da yanayin wani tsoko yake jin mararsa ke masa “Ka daure kaci ko fruits ne” A hankali a sanyaye cike da shagwaÉ“a ta É—an fari data motsa masa yana kwaÉ“e fuska a taushashe ya furta “Ban jin daÉ—in komai, i want my Jee” John ya girgiza kai ya ce “Akwai matsala, naga wata baturiya nata zagawa ko a kirata?” Khalil ya ce “Ubanka zan mata?” John ya miÆ™awa Khalil visa ya ce “Congratulations, Our flight will leave for Nigeria at nine o’clock tonight” Khalil ya dinga kallon John so yake ya ce “Thank you” Amma ya kasa bakinsa ya masa nauyi sosai “I understood, ur Wlcm”

Majeederh na zaune a parlour kanta a Æ™asa kullum hijab ne a jikinta kamar mai takaba, tun safe kuma ta gudu daga gidan Alpha dake kusa dana Uncle Bello, yanzu ma kamar wanda ake family meeting akanta, kowa faÉ—a yake mata da wa’azi akan tayi aure tayi accepting Alpha as her husband, wanda ya mutu baya taÉ“a dawowa har gaban abada, ita musulma ce ta yarda da Allah tayi imani da Manzon Allah, da Sahabban shi, ta yarda da Alk’ur’ani mai tsarki, ta yarda da tauhidi ya zama dole ta yarda Khalil ya mutu ba zai taÉ“a dawowa ba. A hankali ta furta “To” Yaya Bilkisu ta ce “A’a ba wani to, cewa zakiyi ba komai Allah ya yi ma tsohon mijinki rahama ya sada shi da Mala’ikun rahama, na amince da É—an uwana kuma jinina matsayin mijina zan masa biyayya In sha Allah” Ta É—aga jemammun idanunta da suke farare tas ta kalli Yaya Bilkisu, ba tare da tayi musu ba ta ce “In sha Allah” deep down na zuciyarta ta san Khalil yana raye ko baya raye ba zata taÉ“a cin amanar ruhin sa ba, har abada tana so da Æ™aunar ruhinsa ya kwanta cikin salama ba tare da tunani ko zargin taci amanar so da Æ™aunar da yake mata ba, balle yadda take jin zuciyarta ta san he’s still alive. Yaya Bilkisu ta ce “Allah ya yi miki Albarka, ya raya miki Alhassan da Al’hussain, daman ba ruwana da Alhassan Mai masifar zuciya, É—azu fa tas ya fashewa Barrister Glass cup É—inta saboda ba’a haÉ—a masa tea da wuri ba” Uncle Bello murmushi kawai yake, Innati ta fashe da kuka ta ce “Amma ba wasa wallahi ba a kyautawa kululu ba, daga mutuwar mijinta sai a laÆ™aba mata mutumin daya gudu ya barta? Daman ni fa ba wani sanin zuciyar sojan nan na yi ba, yarinyar kamar wacce ake farin ciki da mutuwar mijin nata?” Kuka sosai Innati keyi kamar ranta tana fyace majina da gefen zani ta ce “Ni dai Allah yana gani ba ruwana, kada ma ruhin mijinta ya Æ™ullacan balle ya dinga mini fatalwa, ina ake haka a cikin Æ™abilar Hausawa? Mace sai tayi shekara goma cif tana takaba ba uhm ba uhm’uhm ruwa ma sai dole zata sha balle abinci, don Allah kiyi haÆ™uri ni dai Æ™arfina suka fi amma a kaf duniya iya legas ne zasu iya aikin gaÉ“a gaÉ“an da su Isma’ila sukai” Tayi Æ™asa da murya ta ce “Ai dake legas ba wasu cikakkun Hausawa bane a can, gawa ma ba a wani damu da ita ba, acan mukai Æ™uruciya da Aminiyyata Naila babar Mai martaba Abduljabar, lokacin da É—ansa Zain ya mutu matarsa Haukacewa tayi fa? Ita Kululu a barta tayi kuka na cikakken shekara É—aya ma Æ™unci sai masifar aure shi ma Sojan dake tsohon maye ne bayan duk nasan me ya kewa?” Ba wanda ya kulata, Latifa Omar ta shigo duk ta jeme ta fita hayyacinta, Majeederh na ganinta ta miÆ™e tana É—aukan Alhassan da baya taÉ“a yadda ya yi bacci idan ba a jikinta ba. “Don Allah don Annabi Majeederh ki tsaya ki saurare ni don Allah” Majeederh ta ce “Look Latifa ni abinda ya daman ya isheni, bana buÆ™atar jin hujja ko dalilin ki na abinda kikayi” Tana faÉ—in hakan tayi ciki, Baby Khalil daya girma ya yi wayo ya zubawa Latifa Omar idanu itama shi take kallo sai kawai ta miÆ™e ta fice ba wanda kuma ya kulata a cikin su.

Misalin 1:20 na dare Majeederh na bacci a bedroom É—inta dake gidan Uncle Bello domin bata koma gidan Alpha ba, a hankali ta ji Æ™amshin da har gaban abada ba zata manta da shi ba, ta kasa buÉ—e idanu saboda nauyin da sukayi mata, Sosai Æ™amshin ke ratsa hancinta zuciyarta na mata sanyi nauyin da tayi mata yana raguwa, ajjiyar zuciya mai sanyi ta saki jin ana zagaye lip’s É—inta da yatsa mai taushi, kuma an yi mata rumfa, gently kuma taji ana sauke siririn hannun rigarta zuwa Æ™asa, cikin wani irin hargitsatsen yanayi jikinta na tashi yana zubewa, tana jin kamar she in dreaming ta ji an kifa kai tsakanin Æ™irjinta hannunta ya sauka a lallausan sumar kansa cikin wata kalar raunatacciyar murya ta ce “Who…. who are you?” Daidai kunnenta ta ji an furta “Mu’azzam, ur husband” Ta É—auka da gaske irin mafarkan da take da shi ne na kullum gasu tare sai bata damu ba, ko ta buÉ—e Idanu tasan ba zata ga komai ba sai darkness or shadow, yadda ake sauke numfashi a gaggauce a wuyanta da yadda ake bin ko’ina na jikinta da wani irin mahaukacin deep and hot irin italian kisses É—in nan ya sanya ta buÉ—e baki da Æ™yar za tayi magana ta ji saukar tattausan lip’s cikin bakinta a haukace….
[

Post a Comment for "Mijin Malama Book 2 Page 37"