Breaking News

Mijin Malama Book 2 Page 43


Aisha Baby Novel: Khalil bai dawo da Alhassan ba sai ƙarfe biyu na dare, kamar yadda ya fita dashi, yanzu ma yana goye a bayansa ya kama windown bedroom ɗin Jee ya hauro, gently ya kwantar da yaron a tsakiya shi kuma ya zauna gefe, wani irin kyakkyawan murmushi Khalil ya y, wani irin nutsuwa na saukar masa, a ransa yana jin ya samu abokin hira da cin kai, domin basu baro Orphanage ba sai da sukai kaca-kaca da parlon part ɗin John, suka sauya masa kama su ice-cream, chocolate, tea butter cookies komai suka watsar a parlorn a hankali kuma ya ɗauke Alhassan suka gudu jin John yana fitowa ya san kuma Faɗimatu ya bari da aiki for sure.
Khalil raya daren ya yi yana kallon Matarsa da kuma fitinannan É—an shi Alhassan, idan ya kalli wannan sai ya juya ya kalli wannan, deep down na zuciyarsa yana son ganin biyunin Alhassan wato Al’hussain yaga ya yake shi kuma? Idanunsa zube a fuskarta yaga tana É—an marairaicewa kamar bata jin daÉ—in kwanciyar, ya É—an matsa kaÉ—an tare da sanya hannunsa a saman goshinta yaji zafi sosai, cike da tausayawa ya É—an rausayar da kansa gefe guda yana kallonta da wani sabon yanayi ga wani so da Æ™aunarta da a kullum yake Æ™ara narkar masa da zuciya, a yanzu kuma idan ya ce zai taÉ“a ta to wlh ba zata iya kwatar kanta ba, kuma dole asirin shi ya tonu duk da ashirye yake da hakan, but not today dole ya riÆ™e kansa.
“My everything, Æ´ar Aljanna” Ya yi mata peck a goshi a hankali ya ce “Thank You,for everything” Gently ya miÆ™e har zai fita ya sake É—aukar farar powder ya shafa a fuskarsa, a nutse cike da kamala hannunsa zube cikin Aljihu ya nufi waje, luckily yaga Æ™ofar part É—in General a buÉ—e, ya É—an tsaya yana tuna maganganun General da Zaleehat yana ganin rashin adalci Æ™arara, domin tun a asibiti jikinsa ya bashi akwai wani abu a Æ™asa yadda Zaleehat keta kallon General kuma yana fita harabar asibiti yaga Bilal, a hankali ya nufi cikin part É—in yana shiga bedroom General na fitowa daga bathroom É—aure da towel a Æ™ugun shi, idanunsa ya sauka akan Khalil dake sanye da farar kaya ga farar powder a fuskarsa, jikin General ya fara rawa, domin yasan Khalil is dead already, babu mai kama da shi, idan ba Aljani ba to fatalwar Khalil ce. Yadda jikinsa ke É“ari da kyarma ya sanya yaji cikinsa na juyawa, cikin rashin sani towel É—in ya zame ya faÉ—i Æ™asa, neman abin kare jikinsa yake amma tuni towel din ya yi nasa wajan, Khalil duk miskilancin shi ji ya yi kamar ya tuntsire da dariya ganin General Alpha Bello khan! Tsaye a gabansa kuma naked.
“Innalillahi wa’inna ilahir raji’un!! Kai da kake kabarinka me ya fito da kai?” Khalil ya buÉ—e baki yana zare ido kansa a hargitse ya ce “Matata!” General ya ce “Mata kuma? Ina matacce ina mata?” Khalil yana matsawa wajan Alpha tare da miÆ™a hannu kamar zai kama shi ya ce
“A wajanka nake matacce, a gurinta mutum ne mai numfashi, ka aureta amma ruhina yana tare da ita dare, rana,safe, yamma, ba zan barta ba” Zufa ta dinga yankowa Alpha yana jin kamar ya saki fitsari ya saka hannu ya daddafe mararsa ya ce “Amma ba adalci bane, ka riga da ka zama matacce kake bibiyar matata?”
“Matarka ko tawa? Bari ka zama matacce sai mu yi daidai da kai” Ya miÆ™a hannu zai damÆ™o shi, Alpha ya saki ihu yana “Na yarda matarka me kake so nayi yanzu?” Khalil ya karkace baki ya ce “Ka cire wannan pictures É—in na Matata a bedroom naka, hakan zai sanya ruhina cikin salama, Æ™amshin su da naji ya jawo fatalwa ta nan” Ya kai maganar da Æ™yar Æ™irjinsa na bugawa saboda yadda maganar tayi masa tsayi sosai.
“Yanzu Insha Allahu zan cire” Yana faÉ—in haka ya fara cire all frames É—in hotunan Majeederh dake bedroom É—insa. Idanunsa jajur ya zube gaban Khalil ya ce
“Ka tausaya mini, wallahi wallahi ina son Malama Majeederh, ina son zama mijin malama na har abada, da soyayyarta na rayu shi ke É—awainiyya dani, ban taÉ“a son wata a duniya irinta ba, ba kuma zan taÉ“a so ba don girman Allah ka bar mini ita i so much love her!” Kau! Khalil ya É—auke General da wani irin mahaukacin mari wanda ya sake tabbatar masa wannan ba hannun mutum bane, without allowing him to recover ya sake sauke masa wasu tagwayen maruka, nan da nan idanunsa ya yi wani jaa gefen baki ya fashe, jini ya kwanta fuskar ta yahe tare da kumbura Khalil ya fara loosing control É—insa a lokacin jin yadda wani Æ™ato yake cewa yana son matarsa ta sunna uwar yaransa? Alpha ya ce “kiyi komai fatalwa, amma karki azabtar da zuciyata ta hanyar rabani da wacce nake muradi, na Æ™aryata matata Zuleehart gudun kada Majeederh ta ji ina da aure taÆ™i accepting nawa as her husband” Khalil ya wargaza kansa, yana juya rinannun idanunsa a hankali ya nufi wajen General ya kama hannunsa kamar zai miÆ™ar da shi tsaye, wani irin ihu da kururuwa ya yi lokacin da ya ji Æ™arar karyewar hannunsa biyu! Wani fitsarin azaba ya shiga zubo masa, ya taÉ“a jin harbin bindiga har babu adadi, saran maciji a daji, amma bai taÉ“a jin azaba irin wannan ba, jikinsa ya jiÆ™e sosai da zufa, Khalil ya ce “Uwar data haifeka nagartacciyya ce, baka san darajar mace ba, ka gaggauta Æ™aryata kanka ka wanke zunubanka da gasgata zancen Zulee” Yana faÉ—in hakan ya saka hannu ya kashe wutar É—akin, General ya fara ihu yana faÉ—in “Ƙarya nake, matata ce ita É—in uwar yarana,Bilal, Waheed da Dina ce, nine mijinta Æ™arya nake muku…,” Daidai nan aka kunna wutar bedroom É—in, tuni kuma Khalil ya haura ta window É—akin Alpha. Halin da Uncle Bello yaga É—ansa ya gigita shi fuskarsa ta wani irin kumbura bakinsa ya karkace, Maman Alpha tayi tsaye tana mamakin me ya same shi? “General lafiya?” General ya girgiza kai ya ce “Abba ba lafiya ba, matata ce ita É—in matata ce” Uncle Bello ya ce “Wace matar taka?” Ya ce “Zuleehart, wallahi Allah kenan she’s my wife, Bilal, Waheed, Dina Æ´aÆ´ana ne su” Wani irin bahagon mari Uncle Bello ya zubawa General ya nuna shi da yatsa ya ce “Ka bani mamaki, dama zuciya nata raya mini akwai wani abu, sai dai baka cuci Zuleehart ba kanka ka cuta, ka sheganta yaranka na cikinka da bakinka” Alpha ya ce “Ban sheganta su ba Abba” A hargitse ya ce “Ka ce baka son su, baka da haÉ—i da su, ba yaranka bane hakan daidai yake da sheganta su, shashasha kuma sai ka saki Majeederh” General ya runtse idanunsa abubuwa da yawa sun haÉ—e masa zuciyarsa kamar zata fito waje ya ce “Abba kayi mini komai banda raba zuciyata da Æ´ar uwata, banda rabani da matata” Uncle Bello ya saki tsaki tare da ficewa daga É—akin, Maman Alpha ta nemi waje ta zauna tana kallon shi a hankali kafin ta sauke ajiyar zuciya.

Tsirgen da Alhassan ke yi a gadon shi ya tilasta mata miÆ™ewa zaune tana jin wani irin kasala a jikinta, bata da kuzari ko kaÉ—an ga masifaffen Æ™amshin perfume É—in Boadicea The Victorious da take mutuwar so da Æ™aunar shaÆ™a a hancinta, ta kifa kanta bakinta É—auke da addu’a, jin motsi da Æ™arar sun yi yawa ya sanya ta juya idanunta ya sauka akan Alhassan dake zaune É—are-É—are akan window yana Æ™oÆ™arin dira ya haura Æ™asa, ta miÆ™e da sauri tana zaro kyawawan idanunta waje wanda suka Æ™ara yin laushi sosai, tana zuwa ta ce “What are you doing my love?” Alhassan ya lumshe idanunsa masu laushi yana girgiza kai ya ce “Aby” Majeederh tayi shiru sai kuma ta ce “Aby kuma Love?” Ya sake nuna mata Æ™asa ya ce “Nan Aby” ta ce “Get down, zaka ji ciwo” Ya zuba mata ido kamar yadda Khalil yake idan ya san zai aikata abu bata ankare ba taji ya dirga Æ™asa ya faÉ—i, wata Æ´ar Æ™ara ta saki “Na shiga uku” Ina Alhassan ya gane haura katanga? Daga ita sai Lingerie night wear white colour cinyoyinta a waje ta É—auki hula mai gashi gashi ta saka, Æ™afarta cikin Scuff faux-shearling slippers ta nufi main parlour.

“Majeederh ina zuwa haka?” Ta juya ta kalli Yaya Bilkisu sai kuma ta ce “Alhassan ya kama window ya haura, zan É—akko shi ne” Maman Alpha ta riÆ™e haÉ“a ta ce “Wanne irin haura window ni Æ´ar nan? Mun shige su” Ta girgiza kai ta ce “Daman yana yi?” A hankali ta ce “A’a” Yaya Bilkisu ta ce “Khalil ya tafi Khalil ya dawo” a mamake Majeederh tayiwa Yaya Bilkisu wani hargitsatsen kallo sai kuma ta nufi waje, daidai nan Alpha ya fito daga mota fuskarsa jajur saboda azabar É—orin da akai mata, ga fuska a kumbure. Ya zubawa Majeederh Idanu cike da Æ™auna, ga wani irin masifar kyau da tayi ta ciko sosai ba zaka ce ta shayar da yara har biyu ba, fatar jikinta sai glowing take da wani shinning. Sam bata kula da shi ba ta nufi bayan window É—inta, amma ba Alhassan babu mai kama da shi a tsorace ta dinga dubawa amma ko inuwar shi babu, ta fara kuka tana kiran sunan shi Maman Alpha da Yaya Bilkisu suka fito, haka Uncle Bello da yake Æ™oÆ™arin fita wajen aiki, suna tsaye sai ga Al’hussain ya fito da sauri Yaya Bilkisu ta ce “ÆŠan banza gashi nan ai” Majeederh ta kalli Æ™wayar idanun Al’hussain sam ba irin ta Khalil bace Alhassan kuma komai nasa irin na Khalil ne ta ce “Al’hussain ne wannan, na shiga uku where is my son” Mamakin yadda bata É“oye son yaran a fili suke, suka shiga dubawa lungu da saÆ™o amma baya nan basu ankare ba su kaga Majeederh ta sulale tare da faÉ—uwa a sume, da hanzari Uncle Bello ya kira family Doctor. Jigum sukai kowa da tunanin da yake a ran shi, Yaya Bilkisu ta ce “Mun shiga uku ina wannan yaron ya yi?”

“Tunanin da nake ta yi kenan yaya, sai dai wani ya É—auke shi bayan yaran ko entrance bata barinsu fita balle compound?” Maman Alpha ta furta cike da damuwa haÉ—i da zullumi na rashin sanin abin yi, da rashin gane takamaimai inda Alhassan É—in ya shiga, saboda shi yaro ne mara yadda ba mutane, ba ruwan shi da kowa idan ba Majeederh ko Al’hussain ba. Yaya Bilkisu ta Æ™ara shiru ta ce “Ni kakannin yaron na masarauta ma nake ji, yadda suka Æ™wallafa son duniya akan yaran nan musamman miskilar matar nan ai sai ta saka a É—auremu” Uncle Bello ya sauke numfashi ya ce “Yanzu lafiyar Majeederh muke son fara gani tukun” Dr daya gama bincike da gwaje-gwaje ya ce yana zuwa wajan 20 minutes ya É—auka kana ya dawo lokacin tuni Uncle Isma’il ya zo Dr na murmushi ya kalli Majeederh data farka ya ce “ku bata tea yanzu” A hankali ya juya ya kalli General Alpha dake zaune ya ce

“Congratulations General, your wife is pregnant na kimanin sati uku” General ya yi saurin kallon Majeederh ita kuma tayi saurin kallon cikin nata tana shafawa a hankali, lokaci guda wani irin sanyi da farin ciki ya fara mamaye zuciyarta ta san ba cikin kowa bane sai na ruhin mijinta Khalil, ta nemi dukkan wani Æ™uncin ta rasa a zuciyarta a hankali ta lumshe idanunta hawaye masu zafi suna zirarowa ta cikin idanunta. Yaya Bilkisu ta kalli Dr ta ce “Dr ciki fa? Na sati uku to yaushe Majeederh ta tare har ta samu nutsuwar É—aukan ciki?” Innati tayi Æ™asa da murya ta ce
“Bana faÉ—a miki maye bane? Gashi nan ya turmushe Æ´ar mutane ya É—urka mata ciki, ita kuma dake kamar matar ayu take har ta É—auki ciki? Yanzu zamaninmu ayi haka sai fa mace tayi shekara É—ari ko yatsa mijinta bai riÆ™e mata ba” Innati ta rushe da kuka ta ce “Ina zamu kai wannan zunubin Balkisa? Muna cikin gidan nan akai iskanci hadda É—aukan ciki fa? Ba dole iyaye suke sakawa yara idanu ba? Allah na tuba ban san komai ba nikam” tsananin shock ya sanya Alpha kasa magana idanunsa har duhu suke a sanyaye ya ce “Thank you Dr”
“Ba cikinsa bane, na ruhin mijina ne” Duka suka kalleta Uncle Isma’il ya ce “Thank you Dr, you can go?” Dr ya ce “Ok, Allah ya inganta” Dr na fita Uncle Isma’il ya ce “Kika ce me?” Ta ce “Ba cikinsa bane, na ruhin mijina ne shi ya yi min ciki” Tsit Innati tayi ta raÆ™ube bayan Yaya Bilkisu, Uncle Isma’il ya ce “Majeederh kina da hankali? Kin san me kike cewa? Mutum ya rasu tun tuni amma kice wai cikin ruhin mijinki ne? Shin daman yanzu akwai fatalwa ne? Anya Æ™waÆ™walwarki bata samu matsala ba wajan sarrafa tunaninki ba kuwa?” Ta dinga kallon Uncle ta girgiza kai sai kuma tayi murmushi ta ce “Lafiya lau nake, believe me Uncle wallahi cikin Khalil ne, kullum yana zuwar mini a mafarki, yana cewa daga kabarinsa ya fito yana faÉ—a mini ba zai iya barina ba, wallahi cikin Khalil ne” Kafin Uncle Isma’il ya yi magana wayarsa ta fara ringing baÆ™uwar number ya gani but a special digit number ya É—auka ya miÆ™e da sauri ya ce “Alhamdulillah! Yanzu kuna compound tare da Alhassan É—in?” Majeederh tayi saurin miÆ™ewa tayi waje, gabaÉ—aya suka rufa mata baya har Alpha, tama riga ta mance kayan bacci ne jikinta gashi yanzu ko hular babu, gashinta ya baje ya sauka a saman kafaÉ—arta da goshinta Æ™afarta ko takalmi babu ta nufi compound É—in, cak tayi ganin wanda ta gani tsaye kamar ta gane shi, John ya yi murmushi yana Æ™asa da kansa saboda yanayin kayan jikin nata, Uncle Isma’il ya ce “Kai ka kira? Ina Alhassan É—in?” John ya matsa jikin mota tare da buÉ—e back seat, Alhassan ya fito da sauri yana sanye da wata farar shadda mai azabar kyau, hadda babbar riga an É—ora masa babbar riga da hula, Majeederh ta dinga kallon Alhassan gabanta na dukan uku-uku ya washe mata fararen haÆ™oran shi ya langwaÉ“e kai ya ce “Aby” Ya faÉ—a yana nuna mata Æ™ofar mota daidai nan Khalil ya sako Æ™afarsa waje wacce take sanye da Derby shoe black colour, hannunsa dake É—aure da Rolex ya riÆ™e Æ™ofar motar da shi, gently ya fito yana É—an yatsuna fuska, sanye yake da dakakkiyar shadda gezner, ya É—ora jaddara a kansa, ya Æ™ara cikar haiba da kamala musamman Æ™asumbar fuskarsa, ya tsaya a kan Æ™afafuwansa yana zuba hannunsa a aljihu.

Innati da yaya Bilkisu suka kurma ihu tare da cewa “Wallahi ita ce, fatalwa, fatalwa” Innati ta ce “A’a ba fatalwa ba Fatale” Suka haÉ—a kai tare da yin gware, General wani irin fitsari ne ya kusa kufce masa ganin Khalil ya Æ™ara tuna masa da abinda ya same shi jiya, wani irin rikitaccen tashin hankali ya ruftawa zuciyarsa zufa ta dinga yanko masa, Uncle Bello da Uncle Isma’il salatin da duk yazo bakinsu suke furtawa a fili a kuma bayyane, Maman Alpha dai tayi tsaye tana son ganin ikon Allah domin wanda ya mutu baya dawowa. Kallon kallo ake tsakanin Majeederh da Khalil ko wanne zuciyarsa na bugawa da Æ™arfi, ita na ganinsa tsaye akan duga-dugansa yana sakar mata wani murmushi mai laushi, shi kuma bugawar zuciyarsa ta ganin shigar dake jikinta ne. Jee muryarta na rawa sosai ta shiga nuna Khalil da hannu “Ma…maa.. man?” Da gudu kuma tana Æ™ara fisge drip É—in hannunta ta nufi wajansa, yana ganinta ya yi É—an baya gudun kada su faÉ—i da wani irin Æ™arfi ta faÉ—a saman Æ™irjinsa tana Æ™anÆ™ame shi sosai tare da sakin wani raunataccen kuka, sukai baya kamar zasu faÉ—i ya yi saurin riÆ™o Æ™ugunta ya manne da nashi ya rungumeta da kyau a Æ™irjinsa a hankali kuma ya tallafo fuskarta yana….[10/12, 2:09 PM] Aisha Baby Novel: A zafafe cikin faÉ—a da wata dakakkiyar tsawa wacce ba a taÉ“a ji Uncle Bello ya yi ba ya ce “Kin yi kaÉ—an Barrister, baki da wannan ikon da hurumin, idan har ni na haifi Alpha, kuma Majeederh Æ´ata ce to aure tsakaninsu ya haramta har gaban abada wallahi tallahi” Yana faÉ—in hakan yana saka hannu tare da miÆ™ar da Khalil tsaye ya kama hannun Majeederh ya sanya acikin na Khalil, da sauri Khalil ya damÆ™e hannunta yana sauk’e wata ajiyar zuciya. Majeederh ma ta riÆ™e hannun mijinta tana Jin kamar ta rungume shi ko zata samu sauÆ™i a zuciyarta, bata da tension É—in komai a kanta, ta yarda komai ya faru da bawa hukuncin Ubangiji ne, ba wanda ya isa ya É—ora maka abinda Ubangiji bai nufa ba, wani abun lesson ne a rayuwarka. Maman Alpha ta share idanunta tana kallon mijinta ta ce
“Damuwar wasu ka sani banda É—an daka haifa? Ashe zaka iya zuba idanu É—an daka samar da shi ransa ya salwanta akan abinda kake da ikon mallaka masa?” Uncle Bello ya É—aga mata hannu ya ce “Look! Barrister ban iya son zuciya ba, ba zan fara saboda Alpha ba, idan a matsayinki na Barrister mai kare hak’Æ™in É—an adam da talakawa wanda aka cutar bai sanya kin gane illar abinda kike shirin yi ba, to nima ba zan mara miki baya ba, General musulmi ne yaci ace ya yarda da Æ™addara ya yi kuma imani da ita” Ya juya ya kalli Khalil da kansa ke Æ™asa ya É—ora kansa a wuyan Majeederh idanunsa a lumshe Uncle Bello ya furta “Ibrahim É—auki matarka ka je, yanzu ne za ku yi rayuwar farin ciki da kwanciyar hankali” Khalil ya ware idanunsa a hankali yana mai jinjina kansa.
Uncle ya Æ™ara haÉ—e hannayensu waje guda ya ce “Ibrahim da ga yau ka zama tsaki kume gefe na rayuwar Hawwa’u, ka É—auka bata san kowa a duniya ba sai kai, ka zama garkuwarta, duk sanda Majeederh tayi kuka saboda kai i won’t forgive you, idan Majeederh tayi kuka saboda kai to daga ranar zaka san waye Bello,kuje maza kuje daga yau yanzu babu wata matsala da zata sanya hankalinku tashi, ko da akwai zan yi maganinta ba tare da saninku ba, Ubangiji ya yi muku albarka ya baku zuri’a ta gari ya wadataku da arziÆ™i mai amfani” Idanun Majeederh cike da hawaye ta rungume Uncle Bello ta ce “Na gode Uncle” Uncle ya shafa kanta yana jin sonta har zuciyarsa ya ce
“It’s my responsibility dear, ki kula da mijinki kin ji? Duk son da kukewa juna hakan bazai hana ku samun saÉ“ani ba, ki kyautata masa, kiyi supporting nasa always be by his side” Ta jinjina kai, Majeederh ta kalli Alpha dake kwance gefen idanunsa na zubar da hawaye ta miÆ™a hannu zata taÉ“a shi Maman Alpha tayi saurin cewa “leave him alone” Uncle Bello ya ce
“Majeederh bi mijinki, I’ll talk to her ” Khalil ya É—an matsa kusa da Uncle a karo na farko ya É—an rusuna with so much respect, saboda Uncle ya masa abinda ba kowa zai masa ba, ya dinga tattaro abubuwan da zai furta a wajen yi wa Uncle Bello godiya da bashi haÆ™urin dukan É—an shi da ya yi amma ya kasa, can Æ™asa muryarsa so Calm ya ce
“I am sorry” Uncle ya shafa kansa ya ce “I wish you all the best and happiness in your life Ibrahimul-khalil” Khalil ya miÆ™e ya kama hannun Majeederh suka fita, suna zuwa corridor ya ji ta sake shi ta tsaya ya juya yana zuba mata narkakkun idanunsa, wanda suke cike da gajiya a hankali ya É—aga mata gira alamar “Miye?” Ta Æ™arasa da sauri ta rungume shi tana kwantar da kanta a Æ™irjinsa muryarta na rawa ta ce “I love you, I love you Man, na ji tsoro!” Ya riÆ™o fuskarta yana kashe mata ido É—aya, yana jin zuciyarta na bugawa, sun jima a haka kafin ya kama hannunta suka nufi reception, Alhassan na ganinsu ya tafi da gudu ya nufi wajen Khalil yana faÉ—in “Aby” Khalil bai saki Majeederh ba ya É—auki Alhassan ya Æ™arasa inda su Innati suke da su Abbu, Innati ta riÆ™e haÉ“a hannunta riÆ™e da bottle water mai É—an iskan sanyi sai turiri yake ta ranÆ™washi Alhassan ta ce “Algungumi to kai dai ba abokin arziÆ™i bane a gaskiya, wani abu ne kuma Aby?” Majeederh ta yi murmushi Mami ta ce “Har kun fito?” Ta ce “Eh Mami” Innati tayi Æ™asa da murya ta ce “To ya naji ban ji wani ihu yana tashi ba?” Abbu ya kalleta da mamaki a hankali ya ce
“Ihun me kuma?” Innati ta ce “Na mutuwar Soja mana?” Abbu ya sake kallon Innati da mamaki sosai ya ce “Wani ne ya ce ya mutu?” Innati ta ce “To jira nake a fito da gawa fa? Ashe bai mutu ba? Zaman me yake ba gwara ya margaya uban kowa ya huta da rashin tawakkalinsa ba? Wai da gaske yana raye?” Ba wanda ya ce mata komai ta fashe da kuka sosai tana zare gefen zaninta ta ce “Bafa Æ´ar iska bace ni da zanna magana ana mini kallon wata arniyar legas, kawai a kira dreba ya kai ni gida duk sanda ya mutu na dawo” Khalil ya É—auke idanunsa wallahi kamar an masa dole dole wajan furta “Zamu tafi” Mami ta ce “Tafiya kuma? Yau É—in nan Khalil ko can gidanmu ba kuje ba” Jee ta ce “A’a zamu” Ta ce “To shikenan” Majeederh ta amshi Al’hussain ta rungume, Khalil ya kama hannun Baby Khalil su biyar abinsu sukai waje, Khalil ya kalli Majeederh sai ya É—an kwaÉ“e fuska ta haÉ—e rai itama ya miÆ™a mata key ya ce “Plx” karÉ“a kawai tayi ta nufi wajen driver, bayan ta ajjiye Al’hussain a baya, baby khalil ma na baya, Alhassan na cinyar Khalil tayi Bismillah tare da yiwa motar key tai reverse a hankali ta harba motar zuwa bakin gate ganin zata nufi hanyar gidan Uncle Bello a taÆ™aice ya ce “Hubb Lodge Road” Ta kalle shi waya yake dannawa ta É—auke kanta4d, a jikinta take jin duk motsinta akan idanunsa, tayi murmushi kawai tana mai ci-gaba da driving.

Suna zuwa daidai Æ™ofar gidan Barrister Aliyu Sufyan Khalil ya ce “Stop the car” Ta juya da sauri ta kalle shi bai kalleta ba har zuwa lokacin gashinsa a zube yake a baya da gefen fuska ya fito, tana Æ™oÆ™arin fitowa ya sakawa motar key ya nufi gate É—in gidan Barrister Aliyu, ya É—an tsaya, daidai nan kuma manyan motoci na Æ´an sanda wanda Khalil yama IGP Latif Mahdi waya yana buÆ™ata, kasancewar IGP yasan khalil ya kuma san ba zai iya cutar da kowa ba dole akwai dalilinsa na yin haka, ya sanya ya buga waya kai tsaye aka turo, Majeederh na cikin mota tana kallon ikon Allah tana addu’ar Allah ya sa ba wani abu Barrister yama Khalil É—in ba, Khalil ya shiga gidan tare da knocking ba jimawa aka buÉ—e Aaliyyah ta yi wani fresh saboda cikin jikinta, ta zare idanunta ganin Khalil ta ce “Kspider, Yaya Khalil?” Ya É—an fuske dole shi Yaya ne ta ce “Come in,ka shigo” Ya É—an yi jim sai kuma ya shiga, banda wani irin Æ™amshi babu abinda parlon yake komai gwanin sha’awa, ya nemi saman sabuwar kujerar dake parlon ya zauna, ta miÆ™e ta ce “Bari na kawo maka drinks” Ya É—an murza yatsun yana Æ™arewa parlon kallo ya taÉ“e baki speaking calmly ya ce “Ina…,” Sai ya yi shiru ta ce “Yaa Aliyu?” Ya zuba mata idanu bai magana ba ta ce “Latifa?” Ya lumshe idanu ya buÉ—e ta ce “Tana bedroom É—inta ta kulle, ai police ne suka zo kamata Yaa Aliyu ya hana tun daga nan ta shige bedroom ta kulle” Khalil ya miÆ™e yana zura hannu a aljihu ya zaro wani master key ya buÉ—e bedroom É—in dake ta dawo down strairs da zama, yana buÉ—ewa ya ce “come in” ba a É—auki lokaci ba polices É—in suka shigo, wasu manya guda uku amma mata. Latifa na Æ™uryar gado taga an faÉ—o ciki hantar cikinta ya kaÉ—a ganin police ta fashe da kuka ta ce “Don darajar Allah da Annabi kuyi haÆ™uri ku yafe mini kuji tausayina don Allah..,” É—aya daga ciki ta daki bakinta da Æ™asan bindiga nan da nan jini ya fara zuba, suka damÆ™eta zuwa waje, Barrister Aliyu dake sakkowa Æ™asa ya bi Khalil da kallo domin da farko bai gane shi ba, sai ya yi masa kama da actor’s É—in Nollywood, domin ko fuskarsa ba a gani sosai sai jajayen laÉ“É“ansa. Latifa ta kalli Barrister Aliyu ta ce “Sweetheart don Allah don Annabi karka bari su tafi dani na shiga uku na lalace dame zan ji? Daman nasan hak’Æ™in Majeederh ba zai barni ba, Khalil Oga sir kayi haÆ™uri saboda Allah Majeederh ta yafe mini itama” Khalil ya saka hannu ya tura sumar shi baya yana kallon Latifa ya ce “To bata yafe ba, idan ma haka ne ni mijin malama ban yafe ba” Ta dinga kuka tana turjewa tana kallon Zaki yaÆ™i kallonta ta juya ta kalli Aaliyyah ta ce “Aaliyyah ki taimaka mini idan na je gidan maza ni kaÉ—ai kashe ni za su yi”
“Sanda kike zuwa wajen boka kina k’ulla sharri saboda kawai ki cutar da É—an adam, É—an adam É—in ma wanda ya yarda dake kin nemi taimako ne?” Aaliyyah tayi dariyar rainin hankali ta ce “Kinci uban É—an iska a rainin hankali, ai uban kuturu ya yi kaÉ—an balle na makaho, ita rayuwa daman juyin wainar tanda ce, kuma rawar Æ´an mata na gaba ya koma baya, duk wanda ya ce tukunyar wani ba zata tafasa ba, billahi tashi ko É—umi ba zatayi ba, ayi dai mu gani idan tusa zata hura wuta, maza gidan É—an kande na jira ko zaman can zai wanke miki zunubanki”
Latifa idanun na zubar da hawaye ta dubi Aaliyyah dasu ta ce “Aaliyyah ni kike faÉ—awa haka?” Aaliyyah ta saki dariya ta ce “Warr, ke awa karan kaÉ—a miya? Ina ruwana da girmanki? Ai Karen Bana Shi ke Maganin Zomon Bana, kin rufe idanunki kin cutar da rayuwar wacce take matsayin uwa mahaifiya , duniyata, kin raina wayonta saboda kina baÆ™in ciki da baiwar da Ubangiji ya yi mata, idanunki sun rufe kin manta Sara da sassaÆ™a ba sa hana gamji toho”. Lafita ta ce “Haba Aaliyyah sharrin shaiÉ—an ne na gane kuskurena ki bani dama na wanke laifukana, ni ban É—auke ki kishiya ba, ki bawa Oga sir Yaya Khalil haÆ™uri muyi zaman amana ki yarda dani don Allah” Aaliyyah ta zare Idanu ta ce “Ina ganin Kura da Rana yaya zan yarda ta cije ni? Na shiga ban É—auka ba, bata fidda É“arawo, uhm wannan falsafar taki bata samu tunani mai kyau ba” Barrister Aliyu dai na tsaye, Khalil ya juya baya domin zai iya kaiwa Latifa duka shi kuma duk jikin da yake É—auke da najasa da datti ba zai taÉ“a saka hannu akai ba, police É—in suka ja Latifa har zuwa waje, Khalil ya juya zai fita Aaliyyah ta ce “Yaya Khalil Anti Jeederh fa? Ka zauna kaci abinci mana” Ya É—an shafa kai clamly ya ce “No Thanks” Yana faÉ—in hakan ya juya saboda bashi da business da Aliyu, yana zuwa motar Æ´an sandan na barin wajen kai tsaye kuma state C.i.d Khalil ya ce a shige da ita daga nan a shige da ita prison saboda yana da d’aurin gindi. Hankalin Majeederh ya tashi taso ko albarkacin baby khalil Latifa taci, ta dinga buga Æ™ofar Glass amma a rufe kafin a fitar da Latifa Khalil ya yi waya da gidan Æ´an jarida na t.v dana redion Latifa tayi bayanin abubuwan data aikatawa Jee har yadda aka samu cikin da wanda ya yi shi, voice É—in ya dinga zaga ko’ina dake live ne, abin ya yi trending cikin Æ™ank’anin lokaci, laifin Majeederh ya wanke a idanun jama’a da wanda suka aibatata da masu tsine mata, suka shiga neman yadda zasu ganta idanu rufe aka shiga tsinewa Latifa da mahaifinta Alhaji Bashir. Khalil na kallon yadda jee ke binsa da idanu bai kalleta ba taja motar bisa direction É—in daya saita mata, babu inda kuma map É—in ya tsayar dasu sai gaban wani haÉ—aÉ—É—an gidan mai masifar kyau da tsari ganin sunan Orphanage ta juya da sauri ta kalle shi, kafin tayi magana yara da yawa farare da baÆ™aÆ™e sun taho da gudu sun rungume Khalil, daga mai É—ane bayan shi sai mai riÆ™e hannunsa suna “We miss you Daddy” Majeederh taji idanunta ya cicciko da hawaye ashe ta wannan hanyar Ubangiji ke buÉ—awa Khalil ta rasa yadda a kullum arziÆ™in Khalil Æ™ara yawa yake ashe ga dalili, ta É—an yi baya tana tuna sanda take kaisa orphanage É—in shima when he was little, a hankali ta ce
“I love you gwarzona” Ya juya ya kalleta domin ya ji me ta ce hawayen daya gani a fuskarta ya sanya ya saki yaran, Alhassan tuni ya shige cikin yaran ya fara dambe dasu har an yaga masa riga, ya Æ™arasa inda take a hankali ya buÉ—e bayan mota bata lura ba ta ji ta faÉ—a ya bi bayanta yana rufe Æ™ofar ya É—an yi tafi driver yama motar key, Khalil ya yi Æ™asa da glass suka haÉ—a idanu da FaÉ—imatu Majeederh ta dinga kallon yarinyar tana tuna sanda ta ganta a Vidcall É—in Khalil, John ya Æ™araso yana yin Æ™asa ya ce “Ranka ya daÉ—e” Khalil ya zubawa John Idanu ya ce “Nace maka me?” John ya jinjina kai ya ce “Kace yau tarihi zai maimaita kansa, zaka nunawa Malama Majeederh yadda kake sonta?” Khalil ya lumshe idanunsa speaking calmly ya ce “I love my wife John, kamar bata yadda ba amma zan tabbatar mata yau É—innan” Ya sake sauke numfashi yana buÉ—e zuciyarsa ya Æ™ara kallon John ya ce “Mun É“ata time, Sexy mama When will fasting begin?” Sexy Mama Majeederh ta maimaita a ranta tasan da ita yake, bata kalle shi ba ta ce “Today” Khalil ya ware idanunsa yana É—an dukan kafaÉ—arta “Sexy mama!” Ta harare shi ya É—age mata mata gira ya ce “But you didn’t tell me” Tayi masa shiru ya saka hannu ya mintsineta a bombom da sauri ta ce “Ohh sorry!” Khalil ya juya ya kalli John ya ce “Kayi lists na komi ka turamin, ka bar su Alhassan wajen ka” Ya sauke glass yana riÆ™e numfashi da shafa Æ™irji ya kalli Jee ya ce “Saboda na É—an shafa ki?” Ta tura baki ta ce “Mintsinina kayi fa?” Ya damÆ™ota yana Æ™asa da murya ya ce “Bari mu Æ™arasa yau za kiga asalin mijinki da yadda ake Mintsini”
[

No comments